Sashe 1
Wasu Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*WASU MAZAN*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMSY"
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
PAGE 1
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Cikin tashin hankali take tafiyar tana duba lokaci a wayarta. Duk wanda ya kalleta ya san cewa tana cikin tsananin damuwa! Damuwar da ta sanya canza yanayin fuskarta.
Musaddik ta ƙara gyara goyon da ta yi masa daidai lokacin da wayarta ta fara ringing alamun ana kira.
"Na shiga uku! Har ya dawo ban iso gidan ba." Ta furta tare da dage ƙirjinta hawaye na bin ƙuncinta.
"Hello Abban Raihan, wallahi gani nan na shigo cikin unguwarmu, ka bani mintina ƙalilan zan shigo gidan."
Daga can ɓangaren aka tsaki wani wawan tsaki." Ni dai ba ki ɗauke ni a matsayin mijin ba ko Nasreen? Tun da karatun ki yafi girkin sai na ga uban abin da za ki ci a gidan, domin kin ji na rantse miki yau ke da abinci sai ƙarfe sha ɗaya inna daw..."
"Don Allah ka yi hakuri ko don yaranmu. Ka san horan yunwa ba shi da amfani. Kuma kana ganin ragowar taliyar da muka ci jiya da daddare, shi na sawa Raihan ta tafi makaranta da shi." Ta katse shi cikin rawar murya tana faɗin haka.
"Kin damu da ita ne? In har kin damu da ita tun lokacin da na kira ki, ya kamata ace kin bar duk abin da kike yi kin dawo, tun da na ga karatun bokon ba lahira za ki tafi da shi ba."
"Ka yi hakuri lecturer ɗin ne san ba shi da hakuri ko na ɗauki excuse ba zai lamunta ba."
"Tun da ubanki ne ba." Ya ce tare da jan tsuka ya kashe wayar.
Hawaye ne suka ci gaba da bin ƙuncinta. A yanayin da take ba za ta iya biya wa ta ɗauko Raihan ba, musamman da ya ke jiranta.
Da sauri ta ƙarasa shiga cikin gidan bayan ta buɗe ƙofar get ɗin gidan.
A harabar gidan ta same shi yana ƙoƙarin shiga motarsa. Da sauri ta ƙara da gurinsa dai-dai lokacin da ya shiga cikin motar ya rufe ƙofar.
Ganin ya ta da motar ya sa ya ta ruga ta buɗe masa get.
Sai da ya zo bakin get ɗin ya kalleta ya ce,"Tun da kin fi jin maganar Malaminku sai ki je ya ba ki abinci."
Hawaye shar! Suka zo mata. Yayin da cikinta ya yi wani irin ƙugi na yunwa.
Ganin ya fice daga gidan ya sa taka ƙafa zuwa inda Musaddik yake ta ɗauke shi.
Falon ta shiga ta zauna jabar tana jin yadda zuciyarta ke tuƙuƙin baƙinciki. Cikin rashin dubara ta miƙa zuwa kicin da sauri. A tunaninta ko ya kawo mata cefane, amma babu komai. Ƙofar ɗakinsa ta ja a kulle
Komawa ta yi ta zauna tana jin yadda zuciyarta ke bugawa tamkar za ta fito waje.
Saboda takaici ta kasa fita sai kiran Maman Muwadda maƙociyarta ta yi, ta roƙeta ta turo mata Raihan.
Tana zaune a gurin tana karanta wasiƙar jaki suka shigo.
Da gudu ta rugo ta faɗa kanta." Umma, kin dawo?"
"Eh Raihan, ya makaranta?"
"Lafiya lau kuma an mana karatu sosai. Sai dai abincin da kika bani lalacewa ya yi tunkafin na ci, haka na yi ta wuni da yunwa har sai da na dawo Maman Muwadda ta zuba mini."
"Allah Sarki! Ki yi hakuri ina can ina tunanin zai iya lalacewa saboda akwai wake."
"To,"Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta zauna a gefenta.
Tun tana saka ran zai ji tausayinsa ya dawo, har ta cire tun da ba shi ne farau ba. Bayan ta isar da sallar Isha ta yi shafa'i. Wuri kuma ta barshi da ninyar in ta tashi da daddare za ta yi."
Ɗaukar Musaddik ta yi ta shinfiɗar da shi kan gadon bayan ta yi masa shinfida. Sannan ta kama hannun Raihan suka shiga ciki.
"Ummu, har yanzu Abba bai dawo ba, kuma bacci na ke ji ga shi ina jin yunwa."
"Bari na ɗauki miki ruwa kisha ki kwanta in ya dawo na girka zan tashe ki, kin ga Musaddik shi ma ya yi bacci."
"To," Ta ce bayan ta hau gadon.
"Addu'ar bacci fa?" Ta ce mata wanda ya sanya ta ƙaranto sannan ta rufe idanunta.
Ita ma cire kayan jikinta ta yi sannan ta kwanta tana karanta addu'ar bacci ta shafa musu.
Tana kwance sai juyi take yi kamar wata maciya. Hawaye ke kwaranya a ƙuncinta yana jiƙa matashin da take kwance.
Cikin dare ta kasa bacci janyo Musadik da yake kukan ta ba shi mama. Duk da cewar babu komai a ruwan nono, amma ihu kukan da yake mata wanda zai iya tada maƙota ya sanya ta saka mishi fatar a baki, wanda ya shiga ja yana ajiyar zuciya.
Tausayin yaron ya cika mata zuciya dai da suka yi nasarar zubar ƙwallar dake idanunta.
"Ka yi hakuri ka daina jan fatar nan babu abin da za ka samu." Ta ce masa da tare da ƙoƙarin janye fatar nonon a bakinsa, wanda ya sanya shi canyara ƙara.
Cikin sauri ta mayar masa ina jijjiga shi. Ganin ya ja babu komai a fatar ya sanya shi saki yana faɗin,"Umma, ci ci." Cikin gwaranci yake daɗi yana dukanta da hannunsa.
Miƙewa ta yi na nufi kicin da sauri tana jijjiga shi duk da ta san cewa babu komai. Ka yi hakuri ka kwanta?" Ta yi masa maganar tamkar ba ƙaramin yaro ba, tana nuna masa kular da babu komai.
Ganin ta miƙa masa kular abincin ya sanya shi turewa yana kuka.
Turus! Ta tsaya ina kallon yaron da bai wuce shakara ɗaya da rabi ba cikin tausayawa
Kukan da yaron yake yi ya sanya ta kasa komawa baccin wahalar da ya ibe ta. Wannan dalilin ya sanya ta kasa yaye shi don na samu rangwame da ga tsotson da yake mata.
Cikinta ne ya yi wani irin ƙara tare da bada sauti. Da sauri ta dafe cikin tana jin yadda kayan cikinsa suke juyawa, tamkar za ta yi aman da ta san kummalo kawai zai fito.
Kanta ta ɗaga tana duba agogon bangon dake cikin ɗakin. Ta san cewa ba ya dawowa da daddare, amma na yau ya fi dadewa. Wani irin juya yake rufe mata idanuna har ba na iya ganin komai na cikin ɗakin.
Ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba tuna halin da ta ke ciki. Zaman aurenta; da ba shi da maraba da zaman gidan yarin! Mijinta Farouk bai san darajarta ba. Ko na ce bai ɗauke ta a wata aba wacce Allah ya yi wa daraja ba. Irin rayuwar da suke gudanarwa ta gwammace gara mutuwata. Sai dai, ba ta da gatan da ya fi nan.
Tunaninta ya katse daidai lokacin da na ji alamun buɗe get tare da shigowar motarsa. Da sauri ta mike jikinta na rawa ta fito ta isa ƙofa ta buɗe masa, tare da fita don ta ɗauko kayan da ya zo da shi.
"Saboda iskanci kin ji na dawo tuntuni ba ki fito ba? Uban wa kike kira ya zo ya kwashi kayan?"
"Ka yi hakuri sankatan ne ya ƙi budewa da wur.."
"Ke tsaya!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka, wanda ya sa ta ja ta tsaya ba tare da ta ɗauki kayan da ta buɗe gaban motarsa don ta ɗauka ba.
"Wallahi kin ji na yi miki rantsuwar ɗan musulmi matukar kika ɓata mini ƙofa sai dai ubanki ya gyara mini "
Da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa, yayin da hawayen da take ƙoƙarin maida su, suka shiga turereniya a kyakkyawar fuskarta.
"Eh, kin ji ai ubanki na ce har wani daraja ya ke da shi da ba za a dage shi ba? Mutumin da ya kasa ci daku ballantana ya ba ku ingantacciyar rayuwa?"
"Ka ji tsoron Allah Faruk, ka daina zagin iyayena. Ban san me na yi maka ba, ka auro ki ka kawo ni cikin gida ka, kana gasa mini aya a hannu, sannan ka matar da ni kamar baiwar ka. Rayuwar aure ba kangin bauta ba..."
"A hakan ma ai gata na yi miki, da yanxu kina can kina fama da ƙanzon tuwo da garin kwaki in an samu." Ya ce yana watsa mata mugun kallo.
Ranta ne ya ƙara ɓaci jin tozarci da yake mata ta rintse idanunta tana faɗin,"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Alllahumma ajirni fi musibati!"
"Zagina za ki yi ko ƙarya na yi?" Ya furta yana ƙoƙarin matso ta da shirin zare bell din dake wandonsa.
Matsawa ta shiga yi domin in har ba ta yi watsa ba, sai ya ɗumama mata jiki kafin ya kwanta.
"Ka yi hakuri." Ta furta tare da saurin iban kayan da ya siyo
"No, da ki tsaya ki yi mini rashin kunya tun da ba ki da tarbiyya. Yanzu ki kwana a gidanku da ko gurin kwana ba ku da shi mai kyau. Stupid girl. Har wani baki kike da shi na magana. In mata ne ga su nan birjik a duniya sun yi kwantai ba irin ki ba, kin yi da ƙugu kamar an daurawa taɓarya zani. Wata jemammiya dake." Ya ƙarashe maganar daidai lokacin da ta shige cikin falon.
Kuka ne sosai ya kubce mata har sai da ta duƙa.
"Jiran ki na ke yi ki zo ki kwashe kayan fa." Ya daka mata tsawa yana faɗin haka wanda ya sanya ta fito da sauri ta ɗauki sauran kayan.
Tsaki mai ƙarfi ya ja tare da rufe mirgina motar har ya kusa haɗawa da hannunta. Sannan ya bita cikin gidan yana takun isa. Wayarsa a hannunsa kamar yadda ya saba duk lokacin da ya dawo ita ce take zama abokiyar hirarsa.
Da ya shiga cikin falon sai ya zauna a kan kujerar ya hakimce yana latsa waya, yayin da take gefensa cikin damuwa tana kallonsa.