Sashe 9
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
33
..tayi mata ranar suna bata kara sawa ba. A gurguje nayi wanka na murxa man kuli-kuli a sawayena da yatsuna kada a gansu furu-furu, fuskar kuwa sai tayi fayau, na murxa kwalli don boye rama. Na kawo sabon gyalena mai-barewa na yafa, ban daura dankwalin atamfar ba don haka na nannade mayafin a fuskata, sai na fito ya bakuwar balarabiya. Karo na farko a rayuwata da nayi tunanin shafa turare a jikina. Na dubi turaren wuridin Amarya wai shi (Dan-Daula) na bulbula. Muhammad na gaba ina bin shi a baya har kofar gida Waxiri. Ya tambayi samarin wurin da ke kofar gida, ko Yallabai yana ciki? Suka ce yanxu yayi baki 'yan dubiya daga gidan Maimartaba sun wuce gidan sa na bayan gari..... Muhammad ya dubeni, ''kina ganin muje, Baba ba xai yi fada ba?'' ''Ba xai yi ba, dubiya ne fa, na mutumin da yake matukar kauna, fiye da mu, Baba ya amincewa Yallabai fa Muhammad''. Muna tafe muna hira, har muka kawo gidan yana gaya min asalin gidan Yayan Bello, dan wurin Maimartaba, shi ya gina shi domin sauka idan ya xo da iyalin shi, daga baya kuma ya mallakawa Bello halak-malak shi kuma ya dora wani sabon gini a jikin katangar wannan din. Ya nuna min shi da hannun sa. Gidan karami ne hawa daya tsarin ginin turawa, shuke- shuke sun kawata harabar gidan sosai, motoci har biyu tabbacin da baki, na lura Muhammad ya rude, tafiya yake tamkar bai so. A babbar kofar gilashi ya tsaya, ya danna wata 'yar danja kamar abin kunna fitillar lantarki, muryar mace ta amsa ''Yes, Muhammad, shigo''. Yace ko xaki tsaya in kirashi waje? Kannen shi mata ne suke falon'' ''muje kawai ba komi'', cike da xargi na fada. Bello kishingide jikin abin tada kan saraki (tuntu) daga shi sai jallabiya ruwan toka-toka ya xubawa allon talbijin ido, daga gefen shi dai-dai kan shi wata kyakkyawar farar budurwa ce mi dan jiki take sanya mai wani irin abu da akayi da fulawa da ban sani ba a baki, ta kuma sanya mai gongonin lemu ya kurba. Ya dubi Muhammad sannan ni, yace ''Kai ina ka shiga ne tun daxu ina neman ka?''
34.
Muhammad bai amsa sai da ya nunan wurin xama, na xauna a darare sannan yace ''naje wurin Atine ne, Atine ku gaisa mana'' Na dan xamo daga cikin kujera na russuna nace ''ya jiki?'' ''jiki alhamdulillah, ina kika baro min Atika?'' Tana gida, tace a gaida ka da kyau'' Ya maida dubansa ga 'yanmatan, ''ku, baku gaida baki? Kanwar yarinyar da xan aura ce, Atika'' suka kyabe baki gabadaya, mai bashi abincin tace ''na dauka itace Atikar, da nace ai tayi kankanta da aure, me xaka aura anan, abu uwa KYANDIR!'' Suka kwashe da dariya shima dariyar yayi yace ''me xa'a kawo miki; lemu ko ruwa ko ko coffee?'' Wallahi Bello, kaman bai taba gani na ba, sai ranar. Babu wannan kallon so da kaunar da yake mani. Na mike jiri na kwasa na, na samu na dafa bango na isa kofa ''ki ce Fatima na gaida Atika, tunda tayi min fashin miji, to tayi mashi kyakkyawan riko kamin in iso, xan amso abina koda a ta biyu ne'' suka kyalkyale da dariya. Muhammad ya biyo ni ''me na gaya maki Atine? Bello baya cikin hayyacin sa wallahi tun a Jos, ya koma min haka..'' sai hawaye, yasa hankici ya share fuskarsa ya fyace hancin sa yace ''Atine, kiyi hakuri ki saurare ni, koda rabuwar ce bai dace mu rabu da haka ba. Xa'ayi wa Muhammad addu'a xai warke, wallahi xai komo dai-dai''. Hawaye ne masu xafi suke fita min tarara, amman ban fasa tafiya ba shi kuma bai fasa bina ba ''da yake shine autan maxa, ai dole ayi masa addu'a mana, mutum lafiyar sa lau na gani da ido na kace wani a yi masa addu'a, to dama BAN TABA FURTA INA SON BELLO BA, koko na taba? Ka je ka tambaye shi''. Atine, ki fahimceni mana, nasan kina fa da hankali, Muhammad ba yin kansa bane...
35.
''yin kafafunsa ne, tunda ba yin kansa bane. Kaga wallahi ka rabu dani tun ban xage ka ba. Ina ganin mutuncin ka Muhammad, kada kayi sanadiyyar da sauran matuncin xai xube, tunda nace ka rabu da ni, ka daina bina, to ka rabu da ni. Baxan mance kaunar da ka nuna min ba, amma maganar aure ni da Bello BABU ITA HAR ABADA; WA XAI AURI MAI KAFA KAMAR MABURGI? KYANDIR? Ai wallahi ko ni na miji ce baxan aura ba''. Muhammad yace ''duk naji, amma Atine, komai akayi shi cikin fushi, sai anyi dana sanin aikata shi''. Dai-dai lokacin da muka kawo kofar gidan mu, na dube shi duba na karshe ''ni ba cikin fushi nake ba. 'Yar uwata fa jinina Bello ya koma yana so? Kuma sai inyi fushi, don ni mahaukaciya ce tamkar shi? Kaga tafiyata, kada ka sake kayo aike kace inxo ko Babana, xaka ga kaskanci, na gaya maka, na kara gaya maka wannan!''.
[9/24, 9:12 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/24, 9:13 AM] A A Dboy: Tuna Baya 36 to 40
36.
Na juya na bar shi anan tsaye, na isa ga dakin mahaifiyata, na kamata na rungume na shiga rusa kuka mai matukar tsanani. Digar hawayen Amarya cikin kunnuwa na ya tabbatar mani, taji yadda mu kai da Muhammad. Ni nasan Allah ne ya hutar da Goggo ganin abin bakin ciki. Maganar ta ta fado min a ranar da xata tafi ga sarki Allah ''Yau nake ne, gobe na wanin ki ne''. Kenan ba abin damuwa bane don Bello ya nuna min so jiya, gobe ya koma wani na; Atika? Yayata da muke Uba daya? To amma ya xanyi da son BELLO WAXIRI? Da ya riga ya kanannade ni ba tare da sani na ba. To wai ance in so cutane, to hakuri ma maganine, xan hadiyi hakurin in gani? Ko xai mini maganin? Na dago na dubi Amarya nayi murmushin karfin hali ''To meye abin damuwa Amarya? Bello ba shi ne autan maxa ba. Ni wallahi gare ni ba komai. Amarya bata ce komi ba, na share fuskana nace mata na tafi gidan Liman in ga Sadiya.
Kakata Luba na daka, nayi sallama na shiga, Sadiya ta sheko da gudu ta rungume ni, Luba ta aje tabaryar ta dube ni sosai ''wani mummunan labari xan ji, Atine meya faru, can gidan ku ko ko gidan Waxri?'' Na tube silifana na ja kujera 'yar tsugunne na xauna ''eh to, Bellon ki ya canxa Luba, kamar bai sanni ba kamar bai taba gani na ba....'' hawaye suka xubo min sharrrr! Luba da alama xancen bai ko dadata da kasa ba.
37.
''Idan kika sake kuka akan Bello, ke ba jikar Liman bace. Labari ya xo min, Lami ta sa duk kadarorin ta a kasuwa, bata a birni bata a kauye ta raba ki da Bello ya dawowa Atika, tun lokacin mun dukufa addu'a a kanki, asiri bai ci ki ba, domin jikin ki shiryayye ne. To idan Lami a sammako take, ni a can na kwana. Kakan ki a tsaye yake kwana, da asirin ta mai ci ne, da Saude bata kai yanxu a gidan Maikalwa ba''. ''Don Allah Luba, kada ku wahalar da kanku, ni Bello ya fice min a rai, auren ma baxan yi ba, ko na rasa mijin aure na barwa Atika, Bello, dama ban taba furta masa ina son shi ba''. Na mike xan tafi, Luba tace ''yaro dai yaro ne, an ce kashe makiyin ka kafin ya kashe ka. Idan ke baki san ciwon kanki ba, baki san muhimmancin auren irinsu Bello ba, ni na sani. Jeki ku karata da saunar uwarki da rashin baki ke cutarta''. ''Ni dai nace na yafe dole ne?'' Tuni har na kai xaure, ta dandalin gidan Waxiri na wuce, gaba kadan da gidan Waxiri jingine suke jikin motar Muhammad. Bello na bulbular hayakin taba kamar mai hada gajimare, Muhammad kuma na magana suka dubeni gabadaya. Akuyar data debe su ma bata ishe ni duba ba. Baban mu ya dawo yana xaune yana harhada cinikin sa na yau wanda sulallan biyu da sisi, kwandalaye, sisi da 'yan ficikoki sun fi naira biyar yawa. Na xauna na taya shi, duk iya kokarinsa a satin, naira dari biyar ya hadawa Auwal, da kyar da sudin ludayi.
38.
Washegari ina wanka, hargowar mata cikin gude- guden gidan sarautar Karaye, na ji cikin gidan mu. Sai kuma sauke akwatuna da kuma maraba- maraban da Kandala aminiyar Inna ke yi musu, cikin dan lokaci na ji gidan ya cika taf da matan makota, 'yan gulma, ganin kwaf da 'yan bani na iya. Ban fito ba sai da na ji ficewar su kaf, akwatuna ne masu taya tun daga ta daya har xuwa ta uku, ga wata 'yar mitsitsiyar (kit), fanteku da kwallaye shake da kayan kunshi, tsibe a kofar dakin Inna su Kandala na kwasa suna shigewa daki da su, (a wannan lokacin ba kowa ake kawowa lefe cikin akwati ba sai wane da wane). Na wuce dakin mu. Amarya tayi xugum can uwar dakin ta. Na dubeta nayi murmushi duk da raina suya yake, wai in dan faranta mata, nasan iyaye sun fi dan su jin ciwon abinda ya same shi, tace ''Atika, Bello yace a kawowa lehe, daman ya santa ne? Na san dai ganin su da ita sau daya ne, ranar da muka fara haduwa kuma ko magana bai mata ba''. Amarya tace ''wannan abin mamaki da yawa yake, wannan duniyar cike take da rudani, tattare take da ababen mamaki. Mutanen cikinta, sun shagalta da kyale- kyalen ta basa ko tunanin karshen su. Atine, ki xama mai tawakkali cikin kowane hali, ba duk abinda kake so xaka samu ba.