← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 54

Sashe 51

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

115....
Ashe kuma labe kika koma yiwa antin taki? To kiy hakuri Allah ba don shawarar ta bane dama nima nay tunanin hakan tun kamin ta fada,kuma ina laifinta don ta nuna kulawa da lafiyarki? Tun yanzu har an soma kishin daman na gaya miki duk abunda kike fadi cika baki ne zamuje asibitinne ko kuwa a kyale shawarar ta tunda bakya so? Na dago hankali kirjina na harbawa dana lura shi fahimtar da yai mun ma daban ne da abunda ni nake nufi,nace cikin nutsuwa 'baban jawad kai namijine bazaka gane ba,ba kishi nake ba ba kuma labe nake maku ba illa irin wannan bai dace ake gaya mata ba don ko bata nuna maka ba zata ji dadi ba. In ma cikin ne ai sai a bari in ya fito kowa ya gani ko? Yace'na fahimce ki zubaidah so kiyi hakuri insha Allah ba za'a sake maimaitawa ba kuskurene. Nay murmushi nace'fahimtarkagareni a komi ita ke kara min kaunar ka. Nasara jar fata ya barbaza injina a kaina cikin kwarewa da sanin makamar aiki yana zakule zakulensa har Allah Ya bashi nasarar gano makalallen ciki har wata hudu. Mu na gaban teburin Dr. Dadrian Russo na asibitin Hilditch mun maida hankulanmu a kanshi. Ya dibi yallabai cikin jamami yace'ina tayaka murna domin matarka na dauke da ciki har wata hudu (wato tun farkon aurenmu) muka dubi juna a gigice muka yiwa juna murmushi sai dacta yace amma akwai matsala. Tuni murna ta burma ciki, yace 'kincekina al'ada don haka nayi analysing matsalar matarka sosai ciki dai akwai shi tabbas to amma ba'a cikin mahaifa ba. Daga ni har yallabai muka hada baki ba tare da sanin mu ba muka ce'to a ina? Yace'ku kwantar da hankulanku komi zaiyi daidai yana gefen mahaifarki ne yana girma a wurin don haka yanzu zaki hau gado in maida shi cikin mahaifa cikin gaggawa in ba haka ba ko saidai a cire shi in anyi sakaci a haka zai ta cgb da girma a gefenki sai ku gode Allah da Ya nufe ka da zuwa asibiti da wurwuri. Idona yay kwalkwal cikin tashin hankali na soma sharar hawaye,to amma yallabai ya fini rudewa ya lailayo ashar irin wanda ban taba zaton ya iya ba ya dannawa likitan yace'a gidan ubanka ne aka taba yin cikin a wajen mahaifa? Ya figi hannuna muka fice yana ta fadace fadace kamar mahaukaci,yace zakule zakulen bature na tsiya ya fara zama karya, muka nufi wani asibitin (Rudolph Guiliana Clinic) cikin (Central London) wata kwararriyar likitar mata ta dubani ba tare da bata lokaci ba ta sallami yallabai tace in hau gado ko bayanin ma bata tsaya yi mishi ba don ganin yadda yake shirin dukanta ta kulle kofa ta umarci nurses su hada kayan aiki nan da nan aka manna mun allura sai dogon barci kanin mu2wa daganan ban sake sanin me ke faruwa ba. Sai bude ido nay akan gadon asibiti wai yau yallabai nane da hawaye jage jage yana rokon su su cire cikin baya so. Mrs.Wilcox babbar likita na kwantar mai da hankali tace komi yay daidai yanzun sauran karfin jiki. Tay umarni na irin abincin da nurses zasu dinga bani a kuma kula da allurai da shan magunguna na akan kari. Allah sarki na tausayawa aljihun yallabai shi ko ta lafiya ta kawai yake bata komi ba. Asibitin ba'a zaman jinya duk aikin asibitinne,su suke kula da patient din su,abincinsa,walwalarsa da duk wani motion dinsa. Cikin sati 2 na warware garau jikina ya kara kyau komi nawa ya kara bunkasa, shining da haske kuwa sai abunda ya karu. Ni kaina a ranar da na dubi madubi saida na cillar. Yallabai yana makale dani muka dawo gida, rayuwa ta koma sabuwa.
[11/3, 8:37 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[11/3, 8:38 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔
~BOOK 2~
```SECOND TO THE LAST```
Tuna Baya2 115-120

116...
Cikina ya shiga wata biyar a lokacin komi lapia amma marata ko dan tasawa bata yi ba,in ba don ina jin motsi ba cewa zanyi karya ne bbu wani ciki,to balle kuma sauran mutane. Na tabbata idan naje kry a wannan lokacin kam ba mai ganeni,cikin ma kansa ba mai cewa ina da shi, idan na ishi yallabai da wannan korafin sai yace ai don ni doguwa ce,ba a faya ganin cikin mu ba. Maganar rashin ganewa kar wanda ya gane din, ya damu a gane nine? Shi dai yasan zai gane ni cikin kowanne hali koda ya gamu da laluran makanta ne da ya shafa lallausar fatana zai fiddani cikin dubban mata 'zubaidah cikin matan duniya duka ni a wurina daga na Africar har na turai bbu mai irin jikin matata idan mijin wata yaji haushi shima ya kiwata tashi yadda nake kiwon tawa,ya ji da ita yadda nake ji da tawa,ya riritata yadda nake ririta tawa shine ya burgeni. A irin wadannan lokutan na kan ce a zuciyata anya za'a samu? Bana tsammani. Shin akwai wacce zatayi sa'ar samun mujin dake sonta kamar yadda nawa mijin ke sona? Akwai wadda ta kai ni sa'ar aure? Bana jin akwai. Ashe gaskiyar taufiq ne da yace'am among d luckiest. Na kan tausaywa anti mubina sbd yadda yay watsi da al'amarinta bashi da aiki sai na kula da ni ko numfashi ji yake kamar yay mun. Cewa yake wai akwai macen da ta taba shan wahala irina? Ciki a wajen mahaifa? Shi kam bai taba ji ba. Sai ince har ma da wadanda suka fini akwai dan wasu ma in ya gani ba zai jure ba. Na damu kwarai mu dawo gida ko don anti mubina amma yace ina! Shi sai na huta. Sai cikina yay kwari. Itama mubinar taci lokacinta akan me zata ci nawa? A rana in bata bugo waya sau goma ba ta bugo ashirin,kullum dai uzuri daya yake bata na ta kara hakuri abubuwane sun sha mai kai damn too busy amma yana nan tafe. A wannan lokacin zan iya cewa babu irin kulawa,so da kaunar da ban gani daga yallabai ba,har saida cikina yay kwari sosai ya shiga wata na bakwai. Wannan zamani da muke ciki na kwamfuta don haka duk wani aikin ofis din shi ta computer yake tafiyar dashi. Watannin mu bakwai cif akan wata ukun da mukayi niyya sannan yallabai ya yarda muyi shirin tahowa gida. Inda ya hadani da credit card na kudi masu yawa wai inyi siyayyar haihuwa,maganartsarabe tsarabe duka ba ruwana shi zai kula da wannan, ni sai abun ma ya koma bani tsoro muka je kamfanin motoci yay cinikin 'roll-royses'guda 2 yace na alkawarin da kika yiwa taufiq da ibraheem,kana ya zabi wata dunkulalliyar 'ferraris' sabuwar shigowa ko 9ja bata zo ba a wannan lokacin,ruwan kasa mai sheki,ya danka mun mukullin yace'gift'din shi kenan na cikina,saura na haihuwa. To har sai na rasa bakin godia. To da me zan gode? Banda kauna ta har abada ga mijina abun kaunata?

117.....
bana bukatar komi domin ni kan a rayuwa a yanzu zance ba abunda Allah bai hore mun ba,sai nay tunanin yanzu ne ya dace duk wanda ke kaunata,ya rabi inuwar da nima nake ciki. Na kira Halisa kawata ta jiki a London diyar Ambasadan 9ja na ingila. Halisa sa'a ta ce sai dai ba tayi aure ba,tana kara2 a jami'ar Shiffield tun zuwan da mukayi gidansu bayan fitowa ta daga asibiti muka likewa juna da ingantattar abota ta hanyar ta ne nasan wurare da dama ta hanyarta ne nasan wai ashe duk yawancin matan manyan mu na nan 9ja dake zuwa sayayyar tufafi, kayan kawa na matan da suka amsa sunansu,da sarin kowanne irin (machandies)suna yinta ne a wata kasuwa dake ci ranar lahadi kadai a Liverpool Street wai ita(sunday morning market),nan ne matan manyanmu dake kasuwanci da London ke sayen lesussuka,atampopi,jewels,takalma da duk kayan amfanin mu na jiki dana gida wadanda sunfi arha kadai a sunday mrng mrkt. Ni da halisa muka shiga sunday mrng ranar lahadi karfe goma cikin motarta,na sayi lesussuka da atamfofin ingila masu karshen tsada(material yards) da shaddodi zuwa boyel boyel 'yan ubansu duk domin dangi,da 'yan uwana dana yallabai. A kantin jewelleries na sayi fashion necklaces da ear rings asamfurin Blue royale misaki venato da shimmering pearls domin assha sadia da anti fati,duk da nasan faty bata can amma bazan iya bawa sadia ban bata ba. Shiko abdulraheem agogon nan Raymond weil mai tsadar gaske da bandirorin shadda da boyel na siya mishi,na hadawa assha kayan shafa na'gres cabotine' da fari gudunmuwar aure naso hada mata. Yallabai yace kar in siya mata crystal daga kamfaninsu na yin crytal dake Washington zai tura mata ta can,haka takalma da jakunkuna daga Italy Kelvin zai turamin airport ta can,in rabawa al'ummarmu. Halisa ta hadan set din turaruka na'envy me,voyage da miyaki tace wannan ya zamanto na amfaninki kadai zubaidah,don ki fita daban da sauran mata a wajen mijinki. Inda duk ya jiyo unique kamshinki zai san kece koda kin bar wurin kuwa,haka in dosowa kikayi kafin ki karaso zai san kin taho,wannan wani sirri ne na matan manya. Sannan ta zaba min saitin wani gado fari sol (italian bed) da madubinshi da komai saiti biyu,tace inyi amfani da daya in baiwa anty mubina daya a matsayin tsaraba, kudin kowanne daya anan kudin mu na 9ja naira miliyan daya ne. Nace'wai wai kinason tace ya sakarmin bakin aljihu kenan fiye da ita? Tace'ai ko baki nuna ba zubaidah kallo daya za ai miki asan mijinki na sonki kuma yana ji dake,ya kuma mallaka miki duk abunda ya mallaka a dunia. Kudin sayayyar haihuwa kuwa rabasu biyu nayi, na kashe rabinsu a sittiru da kayan amfanin gudan raina MUHAMMAD JAWAD,da ragowar kudin ba abunda ban sayawa babyn ba amma unisex wato wanda mace ko namiji zasu iya sawa don daga ni har yallabai bamu amince da scanning ba sai motsin lafiyar jaririnmu.. Hatta cokalin da zai sha ruwa da gadon da zai kwanta zuwa motar da zai koyi zama ba abunda ban saya ba.
Chapter 51 · 0% Book details