Sashe 8
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
29.
Tun bayan rasuwar ta babu wanda ya kara xuwa siya, Baba ya yarda da shawarata can kuma yayi tunani yace kaya na magada ne, rabawa xa'ayi a basu, Allah ne gatan mu, ya kuma dogara gareshi yasan baxai bar shi ya tabe ba. A satin su Inna suka dawo a tare, kai da ganin su kasan cike suke da farin cikin wani abu, Atika ta daina kulamu kwata-kwata abinda xamu ci wannan kansa nema yake ya gagaremu domin kasuwar kalwa ta kara wulakanta a dai-dai wannan lokacin da kan jama'ar karkara ke kara wayewa da sana'o'i masu gwabi. Amma duk da haka Baba bai taba cewa a taba kayan Bello ba, ko mai yasa? Wallahi oho! Ina tsaye ina surfen 'yar ragowar dawar data rage mana xamu yi tuwon dare. Sallamar Haj. Talatu muka ji, ni na amsa ta, na santa baiwar gidan Maimartaba ce mai ji da kanta amma tasu taxo daya da Amarya, takan dan xago lokaci-lokaci su gaisa, tace ''Saude na ciki ko Lami?'' Nace ''duk suna nan''. Ban san me ya kawota ba, bayan tafiyar ta Amarya ta je ta gayawa Baba, kira mu duka ya dubi Inna da Atika yace, ''tunda Atika ta kasa fidda wani cikin manemanta, kafin Allah ya fiddo wani, xataje yin wanke-wanke gidan dan Maimartaba da yake aiki a Habuja, xa'a biya mu kudi naira na gugan naira har naira dubu goma a kowane wata. Ko na wata daya muka karba ai mun warke, ga auren Atine da ke tafe, wanke-wanken nan shine rufin asirin mu. Ni dama nasan nayi rashin mata kuma matallafiya, Indo Aisha. Don haka ku tallafa mani, Lami ki bar Atika ta je wanke-wanken nan ko na wata daya ne. Inna ta shiga keta wata irin dariya mai ban haushi tace ''WANKE-WANKE! WANKE-WANKE!! WANKE-WANKE!!! Allah ya sauwake Atika ta je muku bara, kuna xaune, tayi aiki da karfin ta da lafiyar ta don amfanin kan ki. Baka tura Sani kwadago koko makarantar Auwalu dole ce? Kai da baka yi karatun ba me ya same ka a rayuwa, ga ka nan da ranka da lafiyar ka daram ina ce?
30.
Atine 'yar gata, mai aure gida Waxirawa, me kuwa xai hana a yi wanke-wanke domin hidimar aurenta, tana xaune; kura da shan bugu, gardi da amshe kudi. To Atika, tashi maxa mu tafi taron nan ba namu bane''. Suka tsallake mu suka wauce. Baba ya sunkuyar da kai sabida kunyar abinda Inna tayi mishi a gaban mu shiko Auwal tsananin bacin rai sai yace ''Baba ni xani je kodagon, ko kodagon laifi ne ko talauci abin kunya ne?'' Baba yace ''a'ah Auwalu, ka kyale ni in yi tunani, mutuncin auren kanwarku xaka diba, bai kamata ace yayyun ta manya da xa'a karbi auren ta a hannun su kodago suke a tasha ba, karshen tsiya kenan. Abinda ya daure min kai maganganun Lami, ina Atikar tayi miji har ta xartar da hukunci kan gaban kanta, bada yawuna ba?'' Sallamar yaro a xaure yace wai Yallabai Bello ya xowa Baba gaisuwa. Baba ya mike tsaye yace Sani ya je ya gaya mishi idan ya xo ya daina aike, ya shigo kansa tsaye, nan gidan su ne. Ni da Amarya muka nufi daki, ko tatafasa Amarya bata tofa a xancen nan ba. Ina jiyo kamshin raina yayi fari, duk wani bacin rai da ke damuna naji ya yaye. Daga dakin Amarya, na hango Inna da Atika sun fito a hanxarce rike da koko, tabi kofar dakin Baba ta yayyafa tabi har soro ta yayyafa, ita kuma Atika garwashi ta debo a murhu ta xuba wani turare mara dadin kamshi tamkar na bori, ga bala'in hawa kai, ita kanta Amarya na lura hankalin ta na kansu, ina gani tana marmasa addu'a a bakin ta, ta mike ta dawo jikina, ta kama yatsun hannuna na dama da hagu tace ''rufe idon ki'' ban san me take tofa min ba, naji duk jikina yayi kwari gadagar tamkar na sha 'Daga'. Tayi shigewar ta daki. Na hango fitowar Bello, ya kara girma ya kara kyau da ilhama. Sanya kafar shi ke da wuya a tsakar gidan ya shiga atishawa ba kakkautawa. Baba na mishi 'Yarhamakallah'amma bai iya ya amsa ba sabida yadda atishawar tafi karfin shi. Da kyar ta tsaya ya kama kanshi da ke juyawa ya fice daga gidan da sauri tare da Sani.
[9/24, 9:12 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/24, 9:12 AM] A A Dboy: Tuna Baya 31 to 35
31.
Can xauren fita Sani yace ''bari in kira ma Atinen, na dauka xaka shiga ku gaisa da su Inna?'' Yace ''No, kyale ta kawai bana jin dadi, kaina kaman ana tsaga shi guda biyu. Xan je clinic in sha magani, gobe in naji sauki na bullo''. Sani jikin shi ya mace murus, ya soma xargin nan gidan Bello ya dau ciwo, shi kanshi ya ji kamshin mai hawa kai da bai san daga inda yake ba, bai kuma san ko na mene ne ba, ya dauka makotane, wala'Allah Bello bai son kamshin? Allah masani kwana daya, biyu, uku, hudu, biyar, ba Bello babu labarin su. A na shiddan ne labari ya iske mu yana kwance a can wani asibiti a Jos. Na rude, na rikice na rasa inda xan tsoma raina inji sanyi. Nayi kuka har na ba uku lada. Ina naga hanyar xuwa Jos, wa xai kaimu? Idan muka je gidan Waxiri, muka ce a kaimu Jos, ai munyi karambani da xakewa da yawa. Sati biyu bayana nan Muhammad ya aiko sallama da ni, ba karamin jin dadin xuwan sa nayi ba, don nasan hanyar gano abin kauna ne yaxo, na dan gyaggyara na fita. Kallo daya yayi min yayi dariya yace ''shin tsakanin ki da Dan Karaye, waye ke kwance ne? Kin ga yadda kikai koxai-koxai dake Atine?'' Ba wannan ne a gabana ba, a ganina Muhammad bai damu da ciwon Bello ba sam, barkwancin shi kurum ya sanya a gaba, hawaye xurrrrr... Suka bilbilo min nace ''Muhammad ya Dan Karaye?'' ''Sai kin fadi sunan yau, in har da gaske kina son sanin halin da angon naki ke ciki''. Tamkar in mangare shi, wannan mugun aboki ne, bai damu da Bello ba sam, yadda yake kiranshi amini. Ya ga dai bani da niyyar magana ya xama kintsatstse yace ''ki kwantar da hankalin ki Atine, Muhammad ya samu sauki, yanxu haka yana gida tun jiya muka dawo...'' ''amma shine ko ku neme ni a jiyan? Dan Jos, baka kyauta mani ba'' ''Kin san Allah daya ne Atine, ba laifi na bane, ba yadda banyi dashi ba muxo, ya ki, yanxuma bai san na taho ba da ya hanani.
32.
Yace wai baki damu dashi ba shine kadai yake haukansa, satin shi guda a kwance baki nemi da kije ba bayan in har kina nuna xaki, akwai masu xuwa kullum ba xa su ki tafiya da ke ba...'' ''Kaga ni don Allah ya ishe ni, idan naje gidan Waxiri duba shi, nayi laifi?'' Muhammad yayi shiru, ''tukunna kamin wannan, so nake na tambaye ki wani abu, amma don Allah kada hankalin ki ya tashi, ko kiyi tunanin wani abu daban'' nace ''to..'' (jikina ya soma sanyi). ''A ranar da muka kare jarrabawa, kayan da Muhammad ya aikewa Yayan shi dan wurin Maimartaba ya hado mishi daga Washington D.C suka iso, muka taho Karaye, cike yake da begen ganin ki, kada ki so kiga irin tsarabe-tsaraben da ya yo miki. Duk wani dan abin ado ya gani a jikin matan barikin Jos, sai ya ce su sayo mishi ya bawa matar da xai aura, har su ci riba da shi. Muna sauka, ko ruwa bai tsaya sha ba, karewama abinci nace ya tsaya in ci, ya ki, yace na same shi a gaba, ko Yallabai bai ganshi ba ya kamo hanya ya taho. Ya kima dawo mana ba a hayyacin sa ba ke kamar wanda yai gamo. Sannan ya ishe ni da xancen wai wata ATIKA shin wacece ATIKA ko kin santa?'' kafafuwa na sun sage, yawun baki na ya kafe, gangar jikina ya saki, kuxarin jikina ya kare nace ''Na san Atika mana, Atika yayata ce Uban mu daya, ba Mamaki Muhammad ko kadan ban yi mamaki ba, mu bar wannan xancen don Allah don ba shine a gabana ba. Kayi mani jagora kawai in dibo jikin Bello, shine ya dame ni. Don nasan ko ma menene ciwon shi, gidan mu ya kwasa, bai kuma kyautu in ki xuwa ba'' yace ''in kina ganin ba komi, muje?'' na koma na gaya wa Amarya xani dibo jikin Bello, tace ''haka xaki tafi ba kintsi, ba gyara Atine yaushe xaki girma ne? Kuma me xaki kai mishi?'' ''Me muke dashi, shima ai ya sani Amarya bamu da abinda xamu bashi, KALWA KO DADDAWA?'' Idanun Amarya ya ciko da kwallah, ta dauko min sabon xanin atamfar ta da bata da kamarta, kwadebuwa ce, ruwan anta, Liman ya aiko mata da ita tun haihuwar Sadiya, tun sawar da,