Sashe 3
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
9.
Don kar ya kara kwala shi da kasa gaba daya suka sa dariya, amma shi murmushi yayi, ya dube ni a lalace yace ''na baki assignment, mai kafa kamar MABURGI, ki je ki binciko, shin waye, BELLO WAZIRI KARAYE?'' Magana yake cikin gwalli da kwalisa, da wani irin tattausan hausa da ban taba ji ba. Ya sakar min goyon ya juya, 'yan koren shi suka mara mai baya. Sai a lokacin na samu damar kallon sittiran dake jikin shi. Yadi ne da ake kira shadda, ruwan kasa tirarre, ya sha aiki surfani na Saraki gaba da baya, da xare ruwan kasa-kasa. Wani abun birgewa ma, takalmin shi rabin sau ciki, da duk Karaye babu mai sashi sai Saraki, shima ruwan kasar ne. Wannan ba shine a gaba na ba, (wata xuciyar tace dani), abinda xamu cewa Baban mu, game da aiken da yayi mana. Ban iya karya ba, xan fadi wa Baba, dan gidan Waziri ne ya xage mu ya kifar. Dakin Amarya muka xarce, Atika mayafi a hannu, tana ta kwalawa Goggo ta Amarya kira, na sauke Jafaru wurin Inna dake bare gyadar miya a karkashin dalbejiya, ko kamin in karisa ciki, ina jiyo Atika har ta kai tsakiyar labari, na karasa ciki na samu gefen Guggona na xauna, nayi shiru, Guggo tace ''ke Atine, ina ke ina fada da Bello, babban dan Waziri da kowa ke ganin mutuncin sa a garin nan, yaro mai halin dattaku da girmama na gaba, shekaran jiya daya dawo daga birni, can inda yake karatu, ya kawowa Baban ku zakka har gida ya kuma dauko shi daga kasuwa a busukurin shi, me ya kaiki xagin shi? Da yace ku tsaya ku ji, koma mene ne don martabar gidan su ai kun sauraresu, wannan jin kan naki bansan inda kika samo shi ba, meye da mu? Mu su waye? Ki iya talaucin mahaifin ku kada ki jawo mana wulakanci a garin nan, in kinga Bello ko a ina ne, ki tsugunna ki bashi hakuri kin ji na gaya maki. Idan Baban ku ya ji wannan rashin hankalin naki, Allah kadai xe raba ku''. Cike da mamaki da takaicin Atika nace ''Goggo, Atika bata gaya muku gaskiya ba, wallahi xagin Baban mu yayi tayi, ya kifar mana da Kalwa, ya balle min goyo, yace wai kafana kamar maburgi,
10.
Wallahi kinji na rantse, yace wai waye uban mu, Maikalwa? Wallahi ba wanda ya isa ya xagi Babana in kyale shi, ai talauci ba hauka bane''. Amarya tace ''babu yadda xa'ayi yaron nan ya xagi Baban ku, ko bai sanku ba, balle kuma ya san ku, an ce Maikalwan,ba Maikalwar bane, an ce miki mai kafar maburgin, ko ba tsigigiyar bace? An kuma ce waye uban ku? Wanda duk yace xai ja da Saraki, ai kuwa sun tambaye shi waye Ubansa?'' Na mike ina kumburi nace '' Allah banda ni, babu wanda xai xagi Babana akan ido na inyi shiru in kyaleshi,ko Wazirinne, balle wata tsiya,Bello, don kuwa Babana, na tabbata bai taba xuwa roko wajen su ba''. Goggo tace gaskiyar ki Atine, nima ina bayan ki, ku kare mutuncin talaucin ku a ko ina, mulki da abin duniya duka Allah ke badawa,babu kuma wanda yayi mai rawa ya bashi. Jeki dauraye jikin ki duk kin cika mu da doyi, akwai wata Kalwar xan daurawa Rabi'u ya kaiwa Malam Ladan din''. Kwana biyu ina juya maganar Bello a raina, na kasa mantawa, nayi-nayi in mance na kasa. Ba wai ciwon abinda yayi mana ke damuna ba, don kuwa nima na rama, na kuma tabbata yaji ciwon sharewa yayi. A xahiri ni karamar yarinya ce, shekaruna basu fi 13 ba, ko kirgen dangi irin na Atika ban soma ba. Don haka baxan ce son Bello nake ba, amma ya dame ni, kyawun surar shi da cikan kamalar shi abin so ne ga kowa. Ba ga surar shi kadai ba ma, yanayin shi ma abin so ne, tsari da xubin halittar shi abin burgewa ne,balle ga mu kauyawa. Ban taba ganin shi ba sai ranar, sai de nasha jin labarin shi da irin karamcin shi. Dana ganshi se naga ashe yafi yadda ake tsammanin shi. Wato dai ganinsa yafi jin sa. Na kuma fahimci ashe macijin sari ka noke ne; bashi da mutunci ga wanda bai sanshi ba,ga wanda yasan shi, shi mai masifar mutunci ne. Kenan idan har ina son sanin hakikanin wanene shi, kamar yadda xuciyata ta nace da son sani, dole ne in binciko tambayar shi ta shin waye BELLO WAZIRI KARAYE? To a ina xan bincikan? Oho! Motsin dawowar Auwal naji a xaure,na bashi lokaci na tabbata ya gama duk abina ya saba,naje rumbu na fiddo masa abincin ranar sa, gudun kurna ne muka yi da miyar taushe.
[9/24, 9:09 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/24, 9:10 AM] A A Dboy: Tuna Baya
11.
Nayi sallama ya amsa, yana xaune bisa kwayar tabarmar karaunin da ke dakin, a hannun shi littafin boko ne yana ta rubuce- rubuce, na aje akushin na xauna gefen sa nace ''sannu da aiki yaya, rubutu kake tayi, kullum baka gajiya da rubutun nan dai'' ya aje biron yayi murmushi yace assignment aka ba mu nake ta kokari, wallahi naso ace Baba ya yarda an sa ku makarantar boko, babu abinda yafi ilimin xamani dadi Atine, xaki rubuta, xa'a rubuta miki bayani ki fahimta kamar da baki ne ake gaya miki...'' Auwal xuba yake, a yayin da ya fahimci ido nake binsa dashi kurum, amma xuciya ta bata tare da shi, tana ga wani dan matsakaicin hoto cikin firem da ke aje can gefe, Bello ne, rungume da yayan mu Sani, suna sanye da kayan kwallo na Manchester United kungiyar kwallon kafa da Sani ke masifar so, kullum ya dawo kasuwa, kallon kwallo yake tafiya can bayan gari, sai da yasan yadda yayi ya takurawa Goggo ta bashi kudi, ya kukkulla da taimakon abokai ya sayi irin kayan su. Hankali na ya dawo ga kalmar dana ji Auwal ya ambata yanxun nan wato assignment, tabbas naso naji ta a bakin Bello, ranar da ya xage ni, ban san ma'anar ta ba, illa xuciyata ta fassara ta yadda taga dama. Nace ''Yaya menene assignment?'' Assignment aikin gida kenan, kamar wani aiki da xa'a baki ace kije gida kiyi a nutse, a karbi sakamakon washegari, kin gane koh?'' Na maida ido daga kan hoton nace na gane, yace wannan na hoton naga baki san shi ba? Bello kenan dan gidan Wazirin Karaye Ai yaron, yana da mutunci sosai, ga son mutane, ga faran-faran, ga ilimi, Bello zakka ne a Karaye baki daya''. Nayi xugum, a raina nace ''ikon Allah! Mutumin dake xage talaka, ya ci mutuncin iyayen su, shine kowa ke so? Inda ranka kaga da yawa, wannan kadai ya isar mani tambayar wanene Bello Waziri? Amsar da kowa xai bani kenan. Sati biyu suka shude ban ji labarin dan gidan Waxiri ba. Xuciyata, cike take da begen sake ganin wannan kasaitacciyar fuskar rashin mutunci.
12.
Yau Goggo ta tashi da rashin lfy jikin babu dadi tun da safe, Inna kuwa sabgar ta take ba abinda ya dame ta da ciwon Guggo, tana girki tana 'yan wanke-wankenta irin na wanda gida yayiwa dadi. Da daddare wurin karfe takwas, garin Karaye, hadari yai holoko, sama tayi fari fat da kwantaccen hadari, sai iska da tsawa gami da cida ke kadawa kunnuwan 'yan adam ganga. Wannan bai hanani sulalewa in fice gidan kakana Liman ba, wai in amso addu'o'in da ya ce inxo in amsa bayan sallar isha'i in yiwa Guggo na, daren Juma'a ne ana yin dace da samun karbuwar addu'a. Tafe nake faram-faram, iska na kada ni inda duk ta ga dama, dama gani jiki kamar sillen kara, siririya ce ni sirit kamar haihuwar bakwaini, koda yake Guggo ta ce a BAKWAINI aka haife ni. Fuskata ma siririya ce, doguwa, mai dauke da siririn dogon karan hanci kamar shape din karas, wadatattun manyan idanu, kullum yanayin su kamar na mai jin barci, xubin su kamar kwan kaxar hausa, a takaice, komai nawa siriri ne maras kauri irin na Inna na, Amarya. Jin taku nayi a baya na, ga layin ba kowa, hasken farin wata da hadarin yasa ina gano inuwar, dogon mutumin da ke bina, kamar mai gadi na. Na kara sauri akan nawa na da. Iska ta yaye dan yalolon gyalen da nike yafe dashi, ban tsaya ba, sai na kara da sauri- sauri gudu-gudu, shima dankwalin yayewa yayi, ina ganin in na tsaya bin shi nima iskar dauke ni xatayi. Bakin tufkakken gashi na ya shiga fidda sheki da kyalli cikin hasken farin watan. Sai na daura dukkan hannuwa na na a ka, wai in suturta kan. Kakkaurar murya, wadda na tabbata duk Karaye, mutum daya ne mamallakinta, dai- dai sanda na kai kofar gidan Liman ita ke kiran ''A-ti-ne''. Nayi hanxarin juyowa, Bello ne, ban ce komai ba, illa na ja na tsaya, sai na tuna bani da ko mayafi balle kallabi. Na shige gidan da sauri na daga Asabarin Luba, duk a tsorace nake, Luba tayi salati tace ''Ke lafiya, ba dai Indo ta rasu ba?''