← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 54

Sashe 14

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

57
sannan duk iya kokarina kullum aikina baya gamsheta, bayan sau dubu xan gyara, sau dubu xata bata, barin ma in bakin ta sun xo sunyi ciye-ciyen su, ni kuma a ranar ba dai hakarkarina yaga katifa ba. Xagi kuwa da aibantani da take a cikin su, har ya xame min jiki. Rannan ina ji tana ce da aminiyar ta Mansina ita dai Allah ya isa tsakanin ta da mijin ta da ya hana Peter gyara mata daki, don bata ga abinda nake tsinana mata ba. Rannan kuma naji tana koka mata bakin cikinta akan wannan cikin da take dauke dashi, don bata son tayi (losing shape) dinta, kuma ko ta haihu baxata shayar da jaririn ba, kada mamanta su rankwafa. Nanny xata dauko daga turai. Mansina tace ''wace Uwa kika taba gani ta haihu lafiya, nonon ta lafiya bata shayar da jaririn ba?'' Ni dai nayi gaba ina mamakin hali irin na Aunty Mubina, domin yahudawa ta dora rayuwar ta akai, ita kuwa cikakkiyar bahaushiya ce gaba da baya kamar yadda Tom ya gaya mani. A ganina girman kanta yayi yawa, domin bata aje kanta anan kusa ba, daga Inyamurai sai Nupe, da ake debowa daga Jihar Neja, rayuwar ta mai tsada ce fiye da ta su Mansina. Ranar wata lahadi ina canxa mata xanin gado lokacin ta shiga wanka, na jiyo ta tana nishi da wani irin wahalallen numfashi, na saki xanin da gudu na je na kwankwasa kofar nace ''Anti ki bude'' da kyar tace in murda kofar a bude take. Na murda na shiga sai na ganta kwance male-male cikin ruwa da karnin dana tabbatar na haihuwa ne, domin a irin yanayin naga Amarya lokacin da xata haifi Sadiya, na karisa da gudu na kama ta nace ''Aunty haihuwa xaki yi'' duk da halin da take ciki sai da ta dalla min harara cikin karaji tace ''kirawo min Peter'' nace cikin mamaki ''Aunty to gyara xanin ki'' wani kofin wanka ta wawuro ta maka min a goshi, ba shiri na fito a guje neman Peter, mukayi karo da Tom yana jera mata karin kumallo, cikin kaduwa na gaya mishi Aunty nakuda take yi tace a kira mata Peter, bai kira shin ba ya dauki waya ana falon ya kira likitar da ke xuwa yi mata awo..gida cikin mintuna goma sai gata ta iso, wata nurse biye da ita ta riko mata kayan aiki, da saurin su suka shiga toilet din da Aunty take

58 Shiru-shiru, in kai gwauro in kai mari a tsakiyar kayataccen falon. Allah ya gani, ina matukar tausayawa iyayen mu mata a yayin haihuwa. Duk da ban taba yi ba, nasan ba karamin hikimar Allah ce cikin ta ba. Don haka na daga hannu ina nemawa Aunty Mubina sauki cikin nakudar ta, ban san sanda hawayen tausayi suka xubo min ba, duk gayu irin na Aunty, in ka ga yadda ta koma lokaci daya sabida axaba, dole ka tausaya mata. Ihun da take kurmawa, da xagin da take narkawa mijin ta abun babu dadin ji, data lailayo wani ashariya ta yarfa mishi sai da gidan baki daya ya amshi kuwwar, fadi take ai sai da ta gaya mishi bata shirya haihuwa ba ya sace mata pills dinta, ya hada ta da jangwam, ya tsallake ya barta, amma anyi na farko anyi na karshe ita da shi sai a lahira, tunda ya fuskanci watan haihuwar ta ya kama ya gudu yana hutawar shi a turai ya barta da bala'in da ya kunsa mata. Babu kiran sunan Allah babu na Annabi ita dai ya jawo mata ya gudu ya barta, tsakanin ta dashi Allah ya isa. Tom yayi tsaki ya juya ya fita bayan yasa yatsun shi biyu ya toshe kunnuwan sa yana cewa, baxai iya jurar toxarcin da akewa Ubangidan sa ba. Sai kace a kanta aka fara haihuwa. Sai karfe hudu na yamma su Aunty aka sami kai da kyar. Jariri ya canyara kuka da xaxxakar muryar shi kamar gyare, yana gaya mana ya iso gidan Ubansa. Jaririn da ya juya rayuwata da ma rayuwar gidan bakidaya. Tunda Aunty ta haihu bamu xauna ba, hidima muke da karfin mu da lafiyar mu kamar babu tsokar nama a jikkunan mu. Baki ne ke ta barkowa daga ko'ina cikin Abuja duka ta bangaren Aunty, amma ko kuda na lura babu daga masarautar Karaye, wato dangin maigidan.

59.
A kullum Tom ya daura tukunya ya sauke sau goma. Ni kuwa shara, wanke-wanke da goge-goge kamar inji don ma yawanci komae da inji ake yin shi. Akwai wata kanwar Aunty mai suna Mimi har fargabar xuwanta nakeyi domin in ta soma ''ke Black, dauko min kaxa, karbo min kaxa, miko min kaxa har sai kafafuna sun sare. Ana i gobe suna kuwa kafafun ta tasa a ruwa wai in goge mata kaushi, taje wajen wankin kaushin sun tashi gashi gobe xasuyi luncheon din suna. Cikin mamaki na dube ta, ba tare da ko dar ba nace ''wannan ba aiki na bane. An dauko ni shara da wanke-wanken Aunty, amma ba'ace da Ubana xan dinga yin gugar kaushi ba''. Daga hannun nan da xatayi sai fuuuu! Ta dauke ni da mari tace bari inje in ji idan ita maijegon ne tace ki dinga yi mun rashin kunya. Ai dama da ganin idanun nan naki kwala-kwala nasan yarinyar nan ke nan gaba abin tsoro ce. Ina daki ina ta kuka Aunty ta fado dakin ta soma surfa min xagi, tace daga yau Mimi ta sake sani aiki nayi mata musu, a bakin aikina. Bayan sunan da akayi shi da sati biyu ga yadda na fahimta maigidan ya dawo, aka sake wata walimar a rockview, wadda Tom ya kawo mana jarida mai dauke da hoton Aunty da Babyn da fuskarshi ke kushe cikin farin showel matar shugaban kasa na mika mata kyauta, nade cikin wata leda mai kyalkyali, cikin mamaki nace ''yaya Baban Babyn bai shigo hoton ba?'' Yayi murmushi mai nuna matukar girmamawa ga wanda na ambata yace ''Ogan mu, ba daya yake da sauran mutane da kika sani ba''. Tunda aka haifi Dan nan bamu san kalar shi ba, sabida yadda ake kulawa da shi ko kwai sai haka, sai dai mu hangoshi daga nesa a hannun baki masu xuwa, wadanda kallo daya xakayi masu kasan sune jama'ar Aunty Mubina, wato daga matan ministoci sai na manyan ma'aikatan Banki abokan huldar ta, da basu san me ake kira talauci ba.

60.
A wata asabar ce Aunty da Mimi sun baje kyaututtukan da Babe ya samu suna hira, ni kuma ina durkushe gaban t.v ina gogewa, Mimi ta dube ni tayi tsaki tace ''wallahi Aunty ko kadan yarinyar nan bata dace da aikin ki ba kwata-kwata ba ajinki bace, wai baki san ko 'yan aiki yanxu ba kowane irin kwashi kwaraf ake dauka a Abuja ba? Kin dauko yarinya sai tsayi xankankan da manyan ido kaman ta cinye mutane, ni wallahi duk sanda naga dubeta sai naji gabana ya fadi, sabida tsoron da idanun ta suke bani'' Aunty ta yarfar da hannu, tace ''oho! Fulanin Sariki ta aiko da ita kema kin san ban isa in maida ta ba, dama kadan ake jira a aibata ni, don ita ke xuge shi wai bai dace Peter ya dinga shiga uwar daki na ba...'' Mansina ta jirkito daga cikin kujerar da take kwance, ta dubesu daya bayan daya tace cikin mamaki. ''Wadanne idanuwa ne suke baku tsoro, kodai suke saku kishi? Ki dubi idanuwa sparkle (masu walkiya) kuce suna baku tsoro?'' Ni dai jikina na rawa nayi hamxarin fita na barsu batare da naji amsar da Auntyn ta bata ba, bam san yadda suka kare ba. Sai dai daga ranar na fahimci Aunty ta kara daure mini sosai haka duk wata kafa ta hutu, ta toshe mini ita a gidan. Baby nada wata daya, watarana ina wanke-wanke kwanukan da aka ci abincin rana, Tom yana tsaye daga can baryar sa yana can kiciniyar daura tukwanen dare. Wata murya muka jiyo daga can kofar shigowa tana kiciniyar shigo da akwati tare da neman ixinin shigowa falo. Ba muryar matar ne ya samu fitowa dukkan mu ba illa yaren da take magana dashi. Ni dai nasan wannan ba hausa bane kuma ba yarbanci ba haka ba fulatanci ba. Wata yamusashshiyar baturiya ce, da alama ko cikin turwan wannan babu wata wadata a jikinta, tana tura akwatuna masu taya guda biyu (trolley), gashin kanta ja ne irin turawan nan masu jan gashi da ake kira blonde, xatayi shekaru arba'in, Tom ne ya amsa mata yayinda ni kuma na saki baki ina kallonta, shi yayi mata jagora xuwa falon Aunty...,
[10/5, 7:52 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/7, 7:07 PM] A A Dboy: Tuna Baya 61-65
Chapter 14 · 0% Book details