← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 54

Sashe 50

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

112....
A cikin watan gabadaya nida yallabai babu komi a gabanmu daya wuce barje gumin soyayyar mu da ibadodinmu sai ko yawon bude ido. Wani irin sheki da cika da na soma yi ba yallabai ba har ni kaina abin ya tsorata ni. A yau ba muje ko'ina ba muna falo,muna kallon shirin film din America na (around d world in 80 days) wanda jackie chan da steve coogan ke gabatarwa. Ya dubeni kuri yace 'na dade ina zargin jikin nan naki zubi, ko aiki na ya samu karbuwa ne? Ya dace muga likita koko sai mun je Wellington jibi? Nace' susan ma haka tace amma ni ina al'ada ko shekaranjiya nayi wankan sallah. Yace toh wannan farin fa kau da kike na menene? Ban yarda da kayan shafar nan da susan ta sa kika sake ba,kwaso in gani. Nayi dariya na mike na kwaso kit dina na dire mishi, yay dube dubensa daya saba bai ga wani sabon abu ba yace'ke ban yarda dake ba Allah dole a gobe mu ga likita. Nace'duk yadda ka ce maigida haka za'ayi. Washe gari munga wata kwararriyar likita wai ita Dr.anna Branthwaite ta dubani thoroughly tace ita bata ga ciki ba. Yallabai yay dumm! Kamar an aiko mai da sakon mu2wa yace'toh canjin jikin fa? Komi nata ya canza ta kara haske kuma ta kara girma sosai. Sai ya baiwa likitar dariya nima na murmusa tace'ya danganta da sauyin da ta samu na abinci da ruwan sha da hu2,koko ince albarkar kasar mu ta amsheta. Duk mukayi murmushi. Mun bar Rio de Janeiro zuwa Wellington ranar lahadi,hakika nida susan munyi kewar juna ba kadan ba,tayi alqawarin zuwa 9ja musamman domin ni har kuka tayi lokacin da zamu shiga jirgi. To a Wellington a hotel muka sauka hakannan rayuwar bata canza ba,soyayyar ce dai ziryan da yawuwwukan bude ido. Kar kiso kiga zubaida a wannan lokacin ba shakka ta zamo hatsabibiyar da ogan ta ke tsoro da kyar in bata mance yadda ake daura zani ba. Jikinta mulmul fatarta kamar ka taba jini yay tsartuwa sabida tsabar hu2. A dan tsukin kuma na koma lalaci,haka karfin da nake baiwa abincin yallabai duk sai ya raunana. Komi nasa a baki na babu taste ina tsammanin abincin su ne ba dadi sai na daure na shiga dafawa da kaina duk da haka bata canza zani ba. Na lura a dan tsukin yallabai na kebewa yay ta hira a waya yana kyalkyatar daria abinsa. Rannan cikin kunnena naji yace'hakuri zaki kara mubina ni kaina duk hankalina yayo kanki to amma kinsan dole nida ke mu hadu mu dinga tarairayar zubaidah don anan din ma ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba wai komi taci bata jin dadinshi balle mun komo wadannan asibitocin namu marassa kula? Nakejin wani abu ta gaya mishi naji yace'a'ah dukkanmu bama tsammani don an dubata a Brazil sun ce babu..... Can anjima kuma yace eh toh hakan za'ayi nagode da shawararki don Allah ki kara hakuri muna nan tahowa cikin watannan in Allah Ya yarda. Ji nayi kaina ya shiga juyawa wani abu ya zo ya tokareni a kahon zuci,NAMIJI...sai a bar shi da ban takaicinsa.

113....
Wato duk inda suke sunan su daya,'yan uwan juna ne halin su daya. Nayi daki bana ko ganin gabana na zauna bakin gado nay tagumi sai hawaye sharr! Yanzu ni bani da sirri kenan sai anti tasan yadda tai ta kalallameshi ta ji,wai har cikin ma in ina da shi sai an ji,to idan ma gulma ce kuma zamannawa ya tsole mata ido kowa ya murza kanbunnashi na ga mai dawo mata cikin watan wai shi yallabai baisan kaidin mata bane? Ya karaso yana cin biscuit'digestive' ya zauna dab dani ya sauken tagumi yace na tsani ganinki cikin tagumi,any matsala? Kaman in ja tsaki ko na samu sanyin zuciyata daga wannan tonon sililin da yake mani gun kirkiro murmushin kissa nace nothng,kawai raina ne ba dadi,tun safe na kasa cin komi,komai na ci ji nake kamar zai dawo' yace'nima nay tunanin yi mana booking,jirgin London sun fi kowa kwararrun lokitoci,muje a gobe a duba ki sosai,mu koma gida ko don mubina dake jiranmu,ban yarda wai ba ciki bane zubaidah 'i luv a bby desperately' Dubar ni don Allah kato dani a yanzun daya dace a ce ina da diya a gidan aure ki taimakeni don Allah zubyna. Harara na bishi da ita kasa-kasa sbd matukar haushin daya bani a raina nace'wai kayi tunani ko an baka shawara. Ya dace in soma kwatarwa kaina 'yanci tun yanzun don bazai yiwu in zauna anti ta soma tsara mana abunda take so ba. Na dago ido na taf cike da kwalla nace'ni ba asibitin da zani,bani da komi. Yay sakale! Kamar yana mamakin musun da nayi mishi a yau amma bai furta ba. Yace'shikenan in ma wani abu susan ta rakaki aka makala miki don kar ki haihu ai Allah ba azzalumin kowa bane kuma bazan taba yafewa ba. A razane na dago na dubi yallabai bai taba yi mun magana ta irin wannan sigar ba,cike da zargi, tuhuma, rashin yarda da jin haushi, nace 'lallai! Sharrin da za'ayi min kenan,ba komi. Sai hawayen da nake ta tattali suka kwararo a kundukukina. Na soma girza kuka mai tunzura rai wanda dama zuciyar a cike take taf,da kishi, kiris take jira ta fashe. Mai neman kuka ne aka manna mai dunkulen kashi a baka. Amma yallabai yau ko gizau sai ma ya fice ya bar mun dakin kwata kwata. Yau ce rana ta farko da mukayi kwanan dacin rai tunda mukayi aure irin wadda bamu taba yi ba. Daga ni har yallabai ba wanda ya runtsa sai juyi a gefen da yake,ba wanda yace da dan uwansa ko sannu har wayewar gari. Washegari naga yana harhade yan abubuwan da ya san mallakinmu ne cikin jakunkunan mu bai ce min komai ba,nima ban ce masa ba. Karfe tara na dare taxi tazo aka sa kayanmu sai a nanne yace dani tafiya zamuyi bance komi ba na dau jakata na rataya nasa takalmi muka kulle dakin muka baiwa receptionist din mukullinsu muka nufi airport. Karfe goma na dare muna zaune cikin jirgi mai zuwa London daga Wellington. Da asubah filin jirgin saman (heathrow) muka wayi gari. Ambasadan Nja a ingila wanda ya kasance aboki na jiki ga yallabai shi ya tura da mota a taryomu, muna tafe cikin motar ambasada direban ya gaya mishi ance anyi mishi masauki a hotel din (Royal Horseguard) nan zai kaimu.

114..
Yallabai yace kar su damu da wannan. Na sha mamaki matuka da naga yallabai yasa makulli ya bude wani flat house a (Northumberland Avenue). Ashe yallabai nada flat a London? Surprised! Direban ya koma yace zaije ya gayawa ambasada ya cika aikinsa amma zai dawo da daddare ko zai zaga damu. Yallabai yay mishi sannu yace a gaida ambasada. Gidan flat ne mai farin fenti babu abunda babu,babunce kurum babu. Yallabai wanka ya fada ni ko jaka na aje a gefe na kunna injinan saukakama dan adam wahala na gyare ko'ina ya shiga sheki na feshe ko'ina da air freshner mai dadin kamshi. Na wanke toilets din fes fes ko'ina ya shige diban kamshi kana na fada wanka. Ina shafa a gaban madubi yallbai ya shigo,ya hade cikin caftan na farar shadda yana daura agogonshi na fatan damisa ya karaso har inda nake yana murmushi. Yay shiru yana shakar kamshin man 'caris' da nike murzawa lallausar fatata. Ya saki wata irin ajiyar zuciya mai nauyi yace 'kiyi hakuri kiyi hakuri dani kiyi min uzuri,Atine Zubaidah,i cn't do without u...... To ni ma din hakan nasan bazan iya fushi da Oga na ba. Naji tausayinsa,na tabbatar ba karamin azabtar da juna mukai ba a daren jiya kacal saura da me? Muka shiga biyan bashin juna. Daga ni har yallabai mun nemi afuwar juna mun tabbata shaidan ne ke son kawo mana matsala a rayuwar auren mu. Washegari mun tashi cike da farin cikin da baya misaltuwa, muka nufi wani restaurant wai shi Auberge muka karya kumallo muka komo gidan mu muka shiga maida bashin barcin da bamu samu munyi ba. Da yamma na shirya cikin jibgegiyar rigar sanyin birnin London har ya zarta hankali. Yace 'look zubaidah a yi maganar gaskia wai ke bakya tausayi na ne? Na dauke ki mai son duk abunda nake so ce wai me yasa kike man yawo da hankali ne? Kin ki gaya mun ciki gareki ko naji sanyi bayan ga alamu duk sun nuna. Yana nuna min jikina gabadaya yace'yanzu don Allah ba zaki taimaka mun in samu 'ya'yannan da nake burin samu kamin Allah Ya dau raina ba? Maganar shi ta sokeni duk sai ya dugunzumar mun da zuciya na nace to ai ni iya gaskiya ta na fadi Allah ina al'ada,kuma bana jin wani sauyi a jikina a kan me zan ki haihuwa har ka zargeni da abunda kaima kasan ko giya na sha bazan iya aikatawa ba? 'In hakane ki amince muje kwararru su duba ki wai akan me to zaki ce baza'a dubaki ba? Nace 'da idear' dinka ce mai zai hana in amince? Sabida Allah waya ce a kawo ni asibiti a London a dubani? Na tsatstsare shi da ido. Yay dan jim kamin yay dan tunani can kuma yace'toh me ya kawo wannan banzar tambayar ashe ni ban isa yin yadda nakeso dake ba? Na lura ranshi ya baci,na kara jin haushi na mike tsaye nace:kay hakuri amma ban zaci cikin yardar da mukayiwa juna akwai boye boye ba,ni dai nasan ba kai bane bana kuma son irin wadannan abubuwan da suka shafeni a dinga neman shawarar wani akai ni bama na son a sani ko cikin ne dani balle babu,ni ina ruwana da harkar wani? Ya tuntsire da daria yace waye wanin nan ne da kike ta ambato?
Chapter 50 · 0% Book details