Sashe 16
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
65.
Baxan biya wadannan makudan kudaden ba, sabida ba daga kasa nake tono kudin ba. Idan kuma ganin hakan bai maki ba, to xan dauke shi in kai shi gaban Fulani, tunda ke kika haife shi, kin fi kowa sanin ciwon sa, baxa ki xauna ki kula dashi ba. Kina kiran shi (unwanted Baby) Mubina, a gareni yaron nan yafi min komai a duniyar nan da abinda ke cikin ta. Don idan xaki ajiye aikin ki ki bashi kulawar Uwa da ta dace, to, in kuma baxa ki iya ba, to cikin biyun da na baki dole ki xabi daya''. Ga yadda tayi shiru bata kuma magana ba,maganar nasa ba karamin kada ta su kai ba, jin an ture kujera baya na taho falo nace kafa! me naci ban baki ba, kada suce ina labe, bayan kuma ba haka bane, aiki na ne ya kawo ni. Allah bani da wannan halin. Kafin axahar ba sai muka ga Elizabeth ta turo akwati ba tana xumbura baki, Ejiro aka danka wa nemo visa yana tsaye rike da passport dinta a hannu, yace ta bar yafiyar sai jibi wajen visa xasu je. Ni da Tom har tsalle a muka yi, a daki don murnar tafiyar Elizabeth, Aunty kuwa ta cika fafam, kiris take jira ta fashe don haka muma muka shiga taitayin mu ba wanda ya nuna yasan abinda suke ciki. Na shiga aiki washegari, da misalin karfe bakwai na tadda Aunty tayi shirin tafiya aiki, tana xaune a luntsumemiyar kujerar falon ta, tana cika tana batsewa wannan sabida tsabar son aikin ko ince sabida son kudin, ma'aikacin banki takwas take masa a office amma ita Aunty tsabar xafin nama bakwai da rabi a bankin su take mata shi kuwa miji ko oho, don shi kan sa Oga tana riga shi fita. Tom ne ya gaya min cewa Aunty Manajar Banki ce guda don haka nayi mamaki, tace ''ajiye tsintsiyar kixo nan'' da sauri naje na russuna a gabanta ''kina da masaniyar gobe ne Elizabeth xata tafi?'' ''Ban sani ba Aunty'' ''to in baki sani ba gashi na fada maki, don haka xaki dinga kula da JAWAD kamin in dawo don bana son Baban shi ya maida shi Karaye, kina jina?'' Na gyada kai da sauri.
[10/7, 7:07 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/7, 7:08 PM] A A Dboy: Tuna Baya 66-70
66.
''Daga yau karfe bakwai da rabi nake fita aiki, don haka xaki xo ki dau Jawad kiyi mai wanka, ki shirya shi yadda nurse xata xo ta koya maki, duk kayan shi dakin ki xasu koma bana son rainon Baby. A rana sau uku xan ganshi, in bashi nono sau uku; da safe kafin in tafi, da yamma idan na dawo da kuma da daddare kafin ya kwanta barci. Idan kuma na yaye shi, a wurin ki xai dinga kwana. Ki cigaba da wanka sau uku a rana, kamar yadda na gaya maki farkon xuwanki domin karki shafawa dana datti. Ayyukan da kike a da, gabadaya an dauke miki Peter xai cigaba da yi, dama shi yake yi. Dakin barci na kuwa tunda ya hana shi shiga, na dinga gyarawa da kaina koda a karshen sati ne in na samu lokaci. Don haka ki maida hankali bisa aikin ki na yanxu kadai, KULA DA JAWAD. Ba'a goya min da, kada a karya masa kafa domin siriri ne. Akwai gadon shi, akwai abin shan iskar shi duk xa'a kawo su wurin ki. A rana xaki canxa mai pampers sau shidda. Ki kwaso kayan ki ki koma dakin ki nada idan Elizabeth ta tafi gobe''. Nayi godiya na mike na fito duk jikina babu kuxari. Daga wanke-wanke kuma na koma 'Nanny' babu yadda rayuwa bata yi da dan Adam. Ta wani fanni kuma ni dama RAINO NA FI SO A RAYUWATA. Dana gayawa Tom yadda mu kai da Aunty, bude baki yayi cikin mamaki, ya kuma fi mintina biyu bai rufe ba ''Tine, ka lissafa kanka cikin masu sa'a a duniya. Uwar goyon Babe Jawad? Xaka ji dadi wurin Oga in har ka ba Jawad kulawa mai kyau. Yana son Jawad, fiye da komi a rayuwar shi.'' Ina wanka da safe naji ana kwankwasa kofa, na sanya wasu sabbin riga da siket jajaye cikin irin kayan da Talatu ta hada min ne. Na bude kofar ba tare da na tambayi ko wanene ba, wata macece mai dan jiki gajeriya, tana sanye da fararan kayan asibiti, da alama mai kirki ce tayi min murmushi tace ''kece mai rainon Jawad yanxu ko?'' ''Eh'' ''ni sunana Sister Sadiya Danladi, (nurse) ce, an turo ni musamman domin in koyar da ke yadda ake yiwa yaro wanka, da yadda ake bashi abinci bisa...,
67.
..ka'ida da sauransu don haka xauna ki saurare ni''. Tayi min bayani tiryan-tiryan har na gamsu nayi mata godiya ta tafi. Washegari da asuba na tashi, karfe bakwai na kimtsa shiri tsaf, irin wanda take so. Na je falo na jira ta har ta fito cikin shirin fita. Na gaishe ta bata amsa ba ta miko min jaririn. Na sa hannu biyu na amshe shi cike da dukkan kulawa. ''Sai karfe biyar nake dawowa, ba'a soma bashi ruwa ba tukunna, sai yayi wata shidda, yau watannin shi hudu, xaki fara shayar dashi madara yadda sister Sadiya ta gaya miki, an kai miki kayan tun jiya sai na dawo''. Na xauna bakin gadona na sanya Babe Jawad cikin ni'imtaccen gadon sa, na kura mishi ido kurrr! Allah gwani tsatstsarka, da ya nufi mummunar mace kamar Aunty Mubina da haifar kyakkyawan yaro irin Jawad. Fari ne sol, sumar kanshi mai yawa baki wuluk, hancin sa dogo xirit, labban sa jaxur 'yan kaurara, kanana, yana da cleft da kyawawan yatsun kafa da hannu. Ban taba yi masa wani kyakkyawan kallo ba sai yau. Kaunar yaron ta tsirga mani tun daga tsakar kaina, xuciyata, bargona, kasusuwa har yatsar kafata. Na fiddo shi daga cikin gadon na rungume shi tsantsan a kirji na, tamkar na tsaga kirji na sanya shi, in haifo shi ya xan mallakina. A haka barci ya sure mu, motsin shi na ji cikin barcin yana shafa ni yana neman nono kenan. Na tashi na farke katon din da ke ajiye gefe, na fidda wata irin madarar yara, wannan ta musamman ce. Hoton kyakkyawan Babie ne a jiki, amma sai naga bai fi Jawad dina kyau ba. Na debi adadin da Sister Sadiya ta ce min, na duba iya lambar da ta nuna mini a jikin feeder na tsiyayi ruwan dumi da ke cikin flask na hada na jijjiga sosai, ya bar shi ya dan shan iska, na xaunar da shi a cinya ta, nasa mai kan fidar a baki, ya ko kama da karfin sa, kadan yaki shanyewa. A raina nace kawai a ce baxan ba dan Adam ruwa ba, sai yayi wata shidda? Don bani da imani ko don me?
68.
Yaran gidan mu ana basu ruwa tun a ranar da aka haifesu, kuma sun rayu lafiya, don haka sai na ba Jawad ruwa. In Tom xai kawon abinci, yakan hado da wani ruwa da naji yana cewa FORMOSA table water, naje kithcen na dauko mara sanyi, na xuba a murfin fidar kadan, na daura mai a baki, yaro ya kwalkwale ruwa da sauri, na kara cika murfi, ya shanye, na kara mai, ya rage rabi, yana dubana da kyawawan idanun sa ya shiga bangala mani dariya, nima sai naji dariyar ta kamani. Na sashi a bayana da tawul din sa na goye shi cike da matsananciyar kauna.
Ko Uban wa yace mata goyo na karya kafar siririn yaro? Ni har bakwaini na goya, na kuma sauke shi lafiya. Daga goya shi sai barci ya dauke shi, na kwanta rub da ciki da shi a bayana.
A haka Tom ya cimmana, hannun sa rike da bakar leda, bai san sanda ya saki bakar ledar a kasa ba ''lalala! Ga goya dan kwan gidannan? Babu goyo, babu goyo, Aunty xata xage ka Tine'' ''Tom mu Hausawa da goyo muka rayu, itama Uwarta ta goya ta, akan me xata ce baxa ta goya nata ba? Akan wani dalili mara tushe da asali? Kayi hakuri baxan bari ta gani ba'' ya kyabe baki, daga bisani yayi dariya, nasan mamakin karfin hali da karambani na yake ''is not my own business'' ''me kenan kace?'' ''Nace (babu abinda ya shafe ni), i brought you something special (na kawo miki wani abu na musamman) wanda nasan xaki yi murna dashi''. Ban ji me yace daga farkon ba, illa naga ya xaro wasu littafai iri-iri daga ledar da ya shigo da ita, duka na koyon karatun turanci da rubutu, irin na 'A for Apple' da sauran abubuwa da sunan su ya fara da A, haka ya tafi har Z, kowanne da hoton abin radau a cikin kala, muka shiga karatu, ko abinci bamu ci ba. Karfe hudu ya tashi ya kawo min farfesun gudar kaxar gidan gona, da biredi wai inyi maneji kamin ya gama girkin dare. Nayi sallar la'asar sannan na sauke Jawad, sai ya bude ido, na sake dama mai madara, wannan karon harda nutrient din da tace kar in bashi wai ya wuce sha...,