← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 54

Sashe 49

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

109...
Nace 'albishir fa shine Tom da Ejiro sunce zasu musulunta,Tom har ya samo mata 'yar kary' Oga ya fita ya kamo hannun Tom da Ejiro ya zaunar su cikin kujera duk kunya ta kamasu,ya russuna agabansu yace'bansan irin farin cikin da nike ciki ba a yau,Allah Ya taimake ku. Yanzu muna sauri don haka komi sai na dawo kenan,amman yanzu gobe ku je kry zan wa maimartaba waya in gaya mishi duk abunda kenan za'a kula da komi naku, saidai zan so ya kasance kun nakalci kalmar shahada daga baki na har in dawo daga tafiyar da zamuyi zan ke tunawa da wannan ina kara godia ga Allah kan nasibobi da ni'imomin da yake mun iri-iri, sabida haka kuje maza kuyo wankan shiga musulunci kuyi niyyar shiga musulunci da zucia daya in nakalta muku kalmar shahada... Ya gaya musu duk yadda za suyi cikin 'yan mintuna sun dawo har da sabbin kaya a jikin su,ya karanto masu niyya suka fada kana ya karanta musu kalmar shahada suka maimaita har sau uku. Ya fiddo cek ya rubuta musu kudi masu yawa kamar yadda ya saba a duk sanda zaiyi tafiya. Peter duk yabi ya muzanta daga ni har yallabai ba wanda ya maida hankali a kansa saidai shima yallabai ya bashi kudi daidai da nasun,sauran ma'aikata duk ya sallame su har masu gadi,bayan albashishshikansu na wata 3 ya kara da karamcinsa ninkin ba ninkin albashinsu. Ya dubi Tom yace 'tom a da,TAUFEEQ a yanzu,da ejiro IBRAHEEM a yanzu,daga yau aiki ya kare a karkashin taheer sai ku nemi sabon ogan ku can a kamfanin siminti na dangote akwai gidaje guda 2 a (maitama) nasa an gina,naku ne halak malak na mallaka maku, komi na hannun Abdulraheem in kun je antinku wannan nauyin yana wuyanta na aza mata shi. Ya dubeni mukayi murmushi nace'na dau wannan alqawarin' to daga Tom har Ejiro an rasa mai bakin godia sai murmushin kauna ga ogansu,shiko peter sai zazzara ido kawai yake abun tausayi gaba dayan ma'aikatan suka shiga kwararo addu'oin alkhairi ga ogan su. A filin jirgin saman abj babu bata lokaci muka samu jirgin MEA da zamu hau har lokacin tashinsa ya cika. Toh muna shiga ana rufe jirgin kamar dama mu ake jira. Muna cikin bangaren nan mai matsayi da ake kira First Class manne muke da juna tamkar ansa super-glue an manne mu muna ta hirarrakin mu cike da so da kauna,abinki da jar fata ba wanda ke kula da harkar wani.

110....
Ina labartawa yallabai yadda mukai da Tom yana mamaki. Nace'na ji tausayin peter Allah da kake ta ambaton komi ba tare da shi ba. Yace'yes ina sane ina son nuna mishi karamci irin na al'ummar musulmi ne,ta hakan sai in kara kwadaitar da zuciyarsa ga son ya rabe mu kin ga dai ban ce dashi ba,amma na nuna mishi sun fishi daraja da muhimmanci a garemu. Nace shima Allah Ya ganar da shi. Yace'ameen' Karfe biyar na asubahi agogon mu na nan gida 9ja muka sauka kasar Brazil cikin birnin Rio de Janeiro. Ban zaci Brazil a yadda naganta ba,ashe jin ta ake ban san tafi yadda ake tsammaninta ba. Nigerian Embassy ta kasar ce tayiwa yallabai masauki a wani estate na baki wai shi Betna Guest Estate,gini ne samansa har kasansa ruf. Akwai dakin barci guda 2, bandaki 2, balcony wato baranda a saman bene sai katoton kicin da mota da direba ko muna bukatar zuwa wani wuri. Muna ajje jaka sai shower daga nan kuma sai bacci da mukayi a zaune cikin kujera cikin wani irin luntsumemmen gadon da ban taba tsammanin akwai a dunia ba. Bamu muka farka ba sai karfe 2 na rana shi din ma kararrawar kukun gidan ta tada mu mai nuna ya kamala abincin rana. A gaggauce yallabai ya dauro alwala nima hakan muka bada faralin sallar azuhur. Kamin mu kammala da wanka kuku ya jere komi bisa tebir,a yatsine yallabai ya shiga budewa yana yamutsa fuska alamar ba wanda zai iya ci a ciki. Yace'bari in je hotel ko zan samo African Food ke sai kici wannan din kamin in dawo ba dadewa zan yi ba. Nace'toh' suka fita shi da direban da ke waje. Fitarsu keda wuya na janyo jakata da muka zo da ita na soma sauke kayan girkin da nasa Tom ya hada mun waje daya nayi kicin nan da nan na tada tuwon semovita da miyar agushi,kukun jar fata ne yayi ficewarsa ya bani wuri musamman daya fahimci bana bukatar taimako. Na bude firji na tadda duk abunda nake bukata wato ganye iri iri da nama nau'i nau'i har dana alade,na ware shi cikin shara ba don na san shi ba sai don kowanne nau'in nama da sunanshi makale jikin dan karfe a kasanshi,na bararraka farfesun dawisu na juye a filas kana danwaken fulawa da mai da maggi da yankakken nunannen tumatur jazur na hada salad da waken gongoni,salad cream da sauransu,kana lemun da na matse daga ruwan tuffa zalla,na kara suga kadan da flavour nasa 'yar kankara na jere a dardumar tsakiyar falon bayan na shimfida ledar cin abinci. Nay kwaliyya na mike cikin kujera ina jiran yallabai. Bashi ya shigo ba sai karfe biyar na yamma barci ya soma fizgana kadan kadan,ya russuna ya sumbaceni a kunci nayi harr da idanuna yace'Allah sarki momin jawad na tafi na dade ba tare da niyyah ba gashi ban ma samo abunda nake son ba amman na kawo miki abinci mai dadi wani old frnd of myn ne na gamu da shi a hanya ya rikeni,suna nan zuwa shida matar shi da daddare. Na mike zaune na bude ledodin daya bayan daya aje bisa tebur,na shiga fiddo foil paper da aka nannade wani irin abinci,haba malam! Yawuna ya shiga tsinkewa na lashi tausasan labbana da halshena,ya tuntsire da dariya yace'kinsan sunanshi? Na yarfar da hannuwa alaman oho!
[11/3, 8:35 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[11/3, 8:36 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔
~BOOK 2~
Tuna Baya 111-115
111....
Yace'shi wannan da kike gani kaman cakulet nama ne suka dandake ya koma haka ana kiranshi flamed grilled rebeye' shi kuma wannan shine 'guiltless grilled salmon (kifi ne) nace kifi salmon da nakejin labari? Yace ki ci bakin ki zai gaya maki. Ina soma taunawa naji tamkar kunnena ya fice ban kara bi ta kan yallabai ba. Ina tunanin gyambon ciki(ulcer) ya kamani sbd yadda nake cin abinci a dan tsukin kamar hauka da kwalama kamar sabuwar mayya. Nayi mai nuni da ledar dana shirya mai abinci da yatsana sabbab,ya matsa ya soma bude dishes daya bayan daya ya shiga girgiza kai cikin mamaki kamin ya juyo ya jinjina mini yace'wat a surprise! Shin wai ke mai yasa kike da ban mamaki ne? Na lumshe ido a cikin murmushi 'ban mamaki har an fika baban jawad? 'Toh ai ke din ce,ke din ce zubaidah wata irin mace mai yin duk abunda zai sa mu2m yasha mamaki. Ya nade hannun riga ya zauna bisa kilishi ya soma kwasar irin garar da yake so nima ina kwasar tawa,lallai ra'ayi iri iri ne shi kuma haka Allah Yayi sa? Na lumshe ido cike da sha'awar komi nashi ina mai rokon Allah cikin zuciyata,ya cigaba da bani iko da lafiyar da zan cgb da farantawa taheer har zuwa ranar da muka daina numfashi. Karfe 8 na dare ina kwance gefen gado inata kallon yallabai dake dressing sassauka cikin farar shirt (DKNY) da bakin wando(tokyo) yay wani irin fes da shi kai ka ce saurayi ne dan shekaru ashirin da biyar komi nashi mai ban sha'awa ne, sai na mike cikin nutsuwa na amshe shi. Ina fesa mishi turare yay murmushi yace thnk u na shirya nima cikin wasu Pakistan masu ruwan madara kirar india,nay lullubi da yalwataccen mayafin kayan kai kace indiyar gaske ce yace'u look fresh nd beautiful,ni na rasa shigar da tafi maki kyau zubyna,ko don ina sonki ne? Nace'umh' Adaidai lokacin da kararrawar kofa ta soma kara yace'mu2mina ya iso kenan' Mukka rankaya a tare na bude kofar. Baturen dogone matarshi 'yar gajera da 'ya'yansu biyu duk mata,suka rungumi juna shi da yallabai itama matar ta kama hannuna a haka muka zauna cikin kujerar reception wadda ta kasance leather seat,farare sol yace da baturen'meet my bride Zubaidah,zubaidah wannan shine Mr.kelvin abokin kasuwanci na,yana daya daga cikin mutane hudu mamallaka kamfanin takalman mu dake Rome (italy) da matarshi Susan dukkanninsu haifaffun Brazil ne, sun zo ne musamman don ke,so ga susan nan,susan ga zubaidah na baki amanarta cikin wata guda da zamuyi honey moon a kasar ku. (yana magana cikin nau'in turancin da kasar ke amfani). Susan tace 'Zu- bei-dah u're highly wlcm 2 our beloved country. Muna fatan honey moon mai dadi a gareku cikin birnin Rio de Janeiro. Muna masu farin cikin gayyatar ku dinner gobe a gidanmu, ko kelvin? Na kamo hannun 'ya'yanta ina tambayar su sunansu,toh daganan sai hira ta barke. Basu suka bar gidanmu ba sai karfe goma na dare, mukayi masu rakiya har gindin mota. Washegari da karfe tara na dare Kelvin ya zo ya daukemu zuwa villa dinsu,muka ci abincin dare tare dasu. Bayan sati biyu mun gama wasttsake gajiya nida susan muka soma shiga gari tana nuna min wajeje masu ban sha'awa. Shigata 'safe snorkeling' na daga cikin abubuwan da bazan manta a zamana na kasar ba,domin abu ne mai hatsarin gaske can kasan ruwa,saidai alhmdlh mun fito lafiya. Cikin sati uku kacal harshena ya sarke da turancin Brazil da nake samu a bakin susan haka fatar jikina gabadaya ni kaina nasan na kara gogewa fiye da da.
Chapter 49 · 0% Book details