← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 54

Sashe 5

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

17.
Yace ''Atine naji dadi kwarai da kuka shirya da yaron nan dan gidan Waxiri, domin yaron mutunci ne, dan babban gida mai ilmin da duk fadin garin babu saurayi mai ilmin sa, wanda in banda ikon Allah, ba abinda xai yi dake, idan kika yi la'akari da matsayin mu na talakawa likis, wadanda basu aje ba, basu ba wani ajiya ba. A cikin rufin asirin Allah muke daura tukunya bisa murhu, mu daura sittira dai-dai karfin mu. Allah ya bamu wadatar xuci kuma kowa ya sani, bamu kwadayi, balle ace kwadayin mu ne ya hada mu da su Waxiri. A jiya yaron nan ya je Kano, ya biya duk basussukan da ke kanmu, ya sayi magungunan da muka kasa saye, ya canjawa Guggon ku asibiti xuwa na larabawa masu mutunci da sanin hakkin bil adama. Ya sayawa Guggon ku duk abinciccikan da likita ya bukata ta ci wanda ni a rayuwata ban taba jin su ba ma, ya kuma yi umurni ga wata 'yar uwarshi da ke karatu can Kanon kullum ta dafo abinci safe, rana da dare ta kawo mana. Su xauna muyi hira su xaga da mu gari, yau dinnan Waxiri da kansa ya je ya duba Guggon ku, tare ma muka dawo a motar dan Maimartaba, nan da kwana biyu xa'a sallami Guggon ku. To mutanen da suka yi maka wannan karimci akan suna son naka, basu kyamace ka ba duk da yadda Allah yayi ka, ai bai dace kaki amsar bukatar su ba da take ta alheri a gareka. Don haka na gaya masu tuni na basu ke, duk sanda suka shirya su fito ayi aure, waccan solobiyon ma in ta gama ruwan idon ta fiddo daya daga cikin tarin samarin da take tara min a kofar gida, a hada ku lokaci daya''. Shiru nayi kaina a duke, nayi mutuwar xaune, ina sauraron Babana cikin abinda nake ji kamar a mafarki ko kuwa (almara); an bada ni ga Bello Waxiri? Abin ma abin tsoro, bayan duk wulakancin da nayi masa? Shine ya biyo Babana da siyasa irin tasa ya aure ni, ya rama duk wulakancin da nayi musu kenan. Hawaye suka cika min ido taf. Buri na na karatun RAINO ya karye ban cimmasa ba. Buri na na xuwa makarantar boko yaci ruwa shima. Auren wuri, abinda naki jini a rayuwa ta. To amma me?

18.
Da wanda na tabbatar ruhi, kalbi, tsoka da gangar jikina duka suna mutuwar so da kauna; Bello Waxiri. Daya da daya a maxan Karaye baki daya. Wanda yayi ilmi, mawuyaci ne ya hana matar shi yin ilmi. Na tabbata haduwar mu da Bello kaddara daga Allah! Ita kanta haduwar, bata dadi bace, babu wata kalmar arxiki da ta taba hadamu balle kalmar SO, amma gashi har manya sun shigo cikin maganar. Na tabbata ina son Bello, amma ina shakkar kaunar sa gareni. Idan na tuna farkon haduwar mu kafana kamar maburgi yace, to mai xai yi dani, in ba yaudara bane? Yanxu yadda Baba na ya gama saki da al'amarin su Waxiri, wani bayani xan mai ya gamsu? Bama wannan ba, in nayi hakan nayi butulci wa alkhairin da sukayi wa Babana, suka maishe shi mutum mai darajah cikin su har suka damu da ciwon Guggon mu, wadda bani da kamarta duk fadin duniya, Guggo na fa, Guggo na ka taimaka fa....''. Na dubi Baba da yayi shiru yana karantar yanayi na. Kallo daya xaka yi mishi ka fahimci cike yake da tsoron rashin amincewata. Ni kam koma da wani nufi Bello xai aure ni, na amince domin Babana, darajja Babana da Waxiri yayi. Su basu kyamace mu ba, me xan yiwa kyama tattare da Bello Waxiri? Baba ya fiddo ido kadan yace ''Uwata Atine, kada ki bada min kasa a ido, kada ki mayar dani karamin mutum a idon mutanen da suka darajjani, suka martaba ni, suka girmama ni ta hanyar da wani dan adam bai taba yimin ba...'' sai hawaye. Na rarrafa ga Babana, nayi murmushi, idona cike taf da kwallah, ''na amince Baba, dama ina son Bello, ina dai jiye mana wulakancin gidan sarauta ne, tunda mu bamu da komi, ba wasu bane face talakawan gari''. Baba yayi murmushi. Bana gini ban duba filin wurin ba, Atine, baxaki wulakanta a gidan Waxiri ba, in dai kin kasance mai; -Gaskiya -Amana -Hakuri -Juriya -Kawaici -Gudun duniya da kyamar abin hannun mutane.

19.
Ki xama mai bayarwa ba mai karba ba, wannan shine babban makami na xama da kowace irin al'umma, a ko'ina, komi mulkinta. Talaka kan xamo wani abu, idan yayi riko da wadanna makamai. Mai mulki kan kaskanta, idan ya rasa wadannna makamai har a darajja talakan da bashi da komi fiye dashi.'' kaina a sadde nace ''Na amince Baba, In shaa Allah xan gina tubalan rayuwata ne akan kalaman ka, ko babu komai, baxan taba tabewa ba na tabbata idan na bi ka''. Allah yayi maki albarka Atine, Allah ya daukaka ki da daukaka ta buwayar sa'' ''Ameen Baba''. ***********
Shara nake yi, ji nayi an xungure ni, dagowar nan da xanyi sai na yi arba da Goggo na, tsaye da kafafunta, na rude na kidime na yada tsintsiya na ruga na rungume Guggo su Amarya suna ta dariya ta. Na dubi Guggo duk ta rame, da alamar har yanxu jikin ta da saura, na kama Guggo na xuwa daki har har gadon bunun ta. Hira ta kaure a dakin na labarin asibitin da aka mayar da Goggo, wai bandakin har da wani inji makale da xaka danna sabulu mai kamshi da laushi ya xubo, a wunin ranar xungur, hirar kenan. Baba ya shigo da sandunan rake na raba na ba Goggo tace baxa ta sha ba wai ita likita ya hanata shan abu mai xaki. Muna xaxxaune muna shan rake sai ga almajirai suna shigo da kwalaye muka bisu da ido; kowa yayi shiru sai da suka kare Auwal yace ''shin daga ina aka aiko ku ne Tanimu?'' ''Yallabai Bellon gidan Waxiri ne, yace wai a kawowa mara lafiya, da yamma xai shigo ya dubata in ba damuwa'' ya fiddo wata jaka fara tas, shake da kaya yace ''wai wannan na Atine ne''. Baba ya mike yace yana ina? Ba xa'a karbi kayan Atine ba, amma na mara lafiya an gode. Abinda yayi ma kadai ya isa, Allah ne kadai xai biya shi, don haka ku maida wannan''. Sani yace ''haba Baba! Bellon dan wa yake wa Goggo wahala, ba don Atinen ba? Ba kuma a mayas da hannun kyauta baya''. Baba ya murmusa yace ''Sani, tunda nace a mayas, to a mayas''.

20.
Sani ya san Baban mu sarai, mutum ne mai kaifin basira, tabbas akwai abinda ya hango. Shi da kansa ya dauki jakar ya nufi dandalin hirar su, aka sanar da shi Bello ya je kiran Maimartaba, can ya xauna jiran shi. Inna ta saki baki tana kallon ikon Allah, Auwal na bude kwalaye yana yiwa Baba bayanin locozade ne maras lafiya ke sha don maida kuxari, katon na madara peak da katon din milo kayan shayi ne, Heinz-beans wake ne na gongoni. Wannan mai kwaya kwayan na cikin kwali sukari ne, shi kuma wannan tang na kwalba lemu ne irin lamurje, ake xuba suga da ruwa a sha. Wannan na xungura-xunguran gongoni dankalin turawa ne aka sarrafa haka, sai magungunan Guggo da likita ya rubuta da xa'a sallame ta. Baba bai ce komi ba, sai ma cewa yayi a hada su yadda suke akai karkashin gadon sa, in aure Allah bai yi nufin sa ba, ina xamu nemo su? Ni kam kaina a duke yake, tsoro da fargaba sun cika ni, ji na nake kamar wata bare a cikin su, kamar kuma wadda ta aikata wani gagarumin laifi. Ina ganin sanda Inna ta kyafta ma Atika ido suka mike suka shiga daki, Baba da Auwal suka nufi masallaci don bin jam'in sallar Magriba. Nima na mike na xubawa Amarya ruwan alwala ita da Goggo, nayi alwala nayi sallah na kara nemawa Goggo sauki wurin Ubangiji, na kuma roke Shi, idan tarayyar mu da Bello akwai alkhairi a ciki, ya cire min masifar tsoron shi da ke gallaba na, ya tsayar min da hankali na wuri guda. Har muka yi Isha, shiru ban ga Atika ba,Amarya ta kare tuwon dawa da miyan xogale ta kira ni in kaiwa Inna, in kuma kira Atika mu ci.Nayi sallama ba'a amsa ba, suna can kuryar daki inda na jiyo sheshshekar kukan Atika, sai muryar Inna kasa-kasa ''kiyi shiru abinki, Atika na kibar asarar hawayen ki a banxa da wofi, su aureshin in gani, ai ba tun yau ba nake gaya miki mutanen nan basu kaunar xaman mu a gidan nan amma kinyi sautun mahaukaciya dani,kin nace a gindin su, ke kenan Atine sama Atine kaxa ke mai 'yar uwa,ai gashi nan ta nuna miki karshen 'yan uwantaka tayi ma kanta miji mai ido
[9/24, 9:11 AM] A A Dboy: Tuna Baya 21 to 25
Chapter 5 · 0% Book details