Sashe 27
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
115.
A kofar gidan su Ashsha, tsaye suke jikin farar Camry din Alphat. Gabadaya suka iso ga motr, Alphat ya bude min kofar. ''Ya, kawar mu lafiya dai kike wani a birkice?'' ''Ba komai, kaina ke sarawa''. Ashsha bata ce komi ba, ganina ina sauke akwatuna kamar wata wadda tai gudun hijiri, illah ta lallaba Alphat ya tafi. A dakinta take sanar dani Mamanta taje taron matan Women-Affairs jihar Calabar. Na nade kafa na warwarewa Ashsha komi, na kuma roketa da ta rakani Karaye. Na kare xaman gidan Yallabai. Ashsha ta dade tana kallona ''Kin taba gaya mani wani sentimental da Marigayiyar Goggonki ta gaya maki, ''Zubaidah! Gaskiya da karfi, sune kyawawan sutturar talaka''. To baki da karfi ne, ko baki da gaskiya? Mara gaskiya shi ke gudu, shi ke ja da baya. Ba duka da saki ba, kome Yallabai yayi wa Aunty Mubina, dai-dai da shine. Aminiyarta Mansina yayata ce Ubanmu daya, tana yawan korafin aminiyarta bata jin kyawawan shawarwarin da take bata. A ganina Baban Jawad, bai cancanci wannan butulcin daga gareki ba. Ke da bakinki kinsha gaya mani abinda yake maki ko Ubanki sai haka, baxaki iya biyan shi ba, kina tausaya mishi rashin dace da macen kwarai. Yanxu ne lokacinda ya dace ki biya wannan alkhairin da ingantacciyar kauna, kulawa da soyayyah, wadda bai samu daga matar da bata mutunta shi ba. Zubaidah! Baki dace da kowanne namiji a duniya irin Baban Jawad ba! Ki fidda tsoro, nasan kina so ba bakya so ba. Mubina ita ta yar, kika dauka, ba laifi bane, babu cin amana a ciki, tunda dama ita bata rike ki da AMANA BA! Ki xamo wise mana! Xuby na, ki maida martanin soyayya mai gardi, ki more miji mai tsada? Na dade ina maki sha'awar, hadadden Ogan nan naku. Maxa irinsu wuya suke 'never leave something you can do today, until tomorrow (kada ki bar abinda xaki iya yau kice sai gobe). Opportunity comes only once in life! Maxa tashi muje, in maida ke gidan aurenki, naga kinyi yaji harda su akwati, shame on you!!!
[10/15, 9:15 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/15, 9:16 AM] A A Dboy: Tuna Baya 116-120
116
Muje oya, tun bai dawo baki nan ranshi ya sosu ba. Mu je my dear one; Jawad, jikina ya bani ya fara kuka. Haba 'yar Karaye?'' Da haka ta sani dariyar dole, ta shigo motar mu tana kiran Alphat a waya, wai yaxo ya maido ta daga gidansu 'yar Karaye.
***********
Tom ya shigo inaiwa Jawad shafa ''Tine, Yallabai fa yana palour, ana bidar lemun ki mai sanyi''. Na mike kawai na hado kemu na bashi ''a'aha! Yau kuma mulki ake ji. Baxa ki kai ba? Nima baxan kai ba, in baxaki ba kada ya sha kenan''. Ni dai nasan bani tsoron Yallabai. Amma kunyarsa nake ji yanxu, kunya ba kadan ba. Na dake na gyara fuskana, na canxa kaya xuwa babban dinkin shadda Senegal. Dana na gaba ina biye, har falon Yallabai. Yana hada takardu Jawad ya ruga gareshi, ya kama shi ya rungume, wai sai ya gaya mishi inda yaje kwana biyu, bayan ba Canada bane? Ya ce ''naje Sheraton, na kwana na wuni ina hutawa, naso in tafi da kai, sai nayi tunanin Momin ka baxa taji dadin kwana ba kai ba'' ''to ba sai mu tafi da ita ba?'' ''Tambaye ta mana! Me yasa baxa mu tare ba? Bayan bamu da Momi yanxu sai ita? Ba ta tausaya mana? Ko mai yasa? Oho!''. Ya dawo gareni, da na takure a can gefensu ''Momina, kwanaki na ce don me bakya shiga dakin Daddyna? Kika ce ke ba matarshi bace. Na ce don me baxa ki aureshi ba? Kinyi shiru, to yanxu don me baxaki aure shi ba? Tunda waccan matar ta tafi?'' Nayi kus, tamkar ruwa ya ci ni, ina kallon fuskar Yallabai dake kan takardu yana murmushi kasa- kasa. Ya san yaron ya hada mani xafi ya kuma sani a kwana ''wai kai Jawad, komi sai ka ji ne? Ka fiya surutu'' na mike ina shirin tafiya ''sai yaji mana? Tunda ya shafi Babansa. Jawad, ka ji bata so na ko? Wai nayi mata tsufa, tunda na haife ka''. Ya yi wani iri da fuska kamar karamin yaro, yadda yaron xai ji ya damu sosai. Saura kadan, dariya ta kwace mani, Jawad, yayi shiru yana hararata, da kyawawan idanunsa.
117.
Nace ''ni kake harara ko? To gaya min ni da Daddyn, wa ka fi so?'' ''Ni ba ruwana dake''. Ya koma jikin Babanshi ya kwanta. Naji ba dadi, na fita raina a jagule. Na kwanta, amma barci yaki xuwa. Tom ya shigo da akwatuna biyu, wai tsarabar Jawad ne inji Yallabai. Na tashi na duba kaya, kayane irinna yaran da iyayensu ke ji da su. Kayane na 'ya'yan daga wane sai wane, na kara sakankancewa da kaunarda Yallabai ke yiwa Jawad. Ina hada kayan naji sallamar Yallabai, Jawad a gaba kamar marayan da ya rasa Uwa. Tausayin su ne ya kamani duka. Lallai duk matsayin mutum a fagen soyayyah, yaro ne. Kujera daya suka hade shi da Dan shi, na sunkuyar da kai, na rasa me yake min dadi? ''Ba mu yi fushi ba, mun biyo Zubaidah da kokon barar mu, taji kanmu, gatan mu Allah, kuma Zubaidah. Mai nema shi ke kasa har kullum, don haka gamu a dakin Zubaidah. Muna rokonki shin are we accepted?'' Gyada kai kurum nayi ''dama tana xuwar wa mutum sau daya ne a rayuwa''. Na tuna maganar Ashsha Hardo, gashi nima so ke ci na. Yallabai ya lumshe ido, kenan farin cikin ya fi gaban kwatantawa. Ya kannewa Jawad ido, ya nunani da baki ''to yanxu da ruwana dake'' na harareshi nima. ''Jawad wai me Mominnan naka ke shafawa fatarta ne? Ta xama farar Morocco? Tayi kyau, tayi fata lafiyayyu?'' Kunya ta kama ni, nayi cikin daki na barsu ina ji Jawad yana fada masa wai Aunty Ashsha ce ta kawo mata kayan shafa. A kofar dakin ya tsaya, a yayinda na koma can gefe ina jan carbi, wanda in xa'a kasheni, bana ce ga ayar da nake ja ba ''wallahi sai naga abinda ake murxawa. Don baxan yarda da wanda xai cutar ba. Ko ya kace Jawad?'' Ya gyada kai yana dariya da jerarrun hakoransa farare kal ''Kwarai Dad, u're quite right! Ai ni nasan inda suke'' ya soma janyo drawers ya xaxxage tulin kayan shafe-shafe.
118.
Oga yayi mamaki, ya kwashe duka a babbar leda. Ya daga ledar 'cleansers' din wurinsu Alphat ''clean&clear'' ya fadi a mamakance, ya kara fadi, ''ai bakin naki ne kilin-kiliyar''ya turasu duka a ledarsu ''sai da safenku, karshen wadannan dustbin baxa a sake shafasu ba. Bakin AREWA, nake son MOMIN JAWAD DA SHI''. Ni dai bance kanxil ba, ban kuma dube su ba, yana fita na dubi Jawad ''munafiki dan wuta ne inji Allah'' ''yanxu Momi munfunci nayi?'' ''Munafinci ne mana! Ina ruwanka da abinda nake shafawa?'' Ya kanainaye a jikina na ture shi, ''na tuba Mummy na. In ya xuba a dustbin, xansa Uncle Tom ya kaini in debo miki''. ''Ni ba ni xaka tubarwa ba, Allah da ya hana munafinci''. Yayi dagwalo kamar yayi kuka ''Allah na tuba'' na jawo shi na rungumeshi sosai ''shikenan ya karbi tubanka, Jawad. Domin shi yace mu gaggauta tuba''. ''Lah! Momona kin ga na manta, yace ga tsarabarki ta Canada, wai sai xamu kwanta xan baki'' ya xaro mani dan karamin kati daga aljihun wandon sa, cikin ire-ien mitsi-mitsin greeting cards din kasar Canada. Katin cike yake da xanar xuciya guda biyu. Ganinshi kadai xaki kimanta darajarshi, daban take da sauran cards. Dan gajeren rubutun ya sanyaya mani, ya faranta mani, ya fiye mani akwatin kaya daya saba yo mani. 'The truth..... I must confess! Since you arrived, you've touched and influenced my life dramatically 4 good. To the extent thay a day without a thought of you, is a dead day. You have in no little measure helped me to realized my life's dream. You've made my life rich in a wonderful way. Taheer.
119.
Ji nayi idona ya wani lumshe a hankali, A! Wai na canxa mai tsarin rayuwa xuwa mai kyau, KO DAI YA CANXA MANI? Maganar Maikalwa, Babana ita ke min yawo a wannan lokacin. ''Kowa yace gonar wani ba xatayi albarka ba. To tashin ce baxa tayi ba!'' Ni kaina nasan gonata, tayi albarka, ta kowanne fanni. Ilmi masoyi na hakika wane BELLO WAZIRI KARAYE?
*********
Jakunkuna ne da akwatuna Tom ke jera min, tun daga uwar dakina har falo. Yana dariya yana tafi ''Tine, ashe yau sai kwanan Karaye. Sai kwana gaban BABA da AMARYA. Xan ga Ya Auwal ashe?'' Sai naji maganar wata irin banbanrakwai. Lokaci guda, xuciyata ta soma harbawar farin ciki ''Oga yace ki diba kayansu Baba. Inda abinda xa'a kara in karo. Karfe 11:00am xamu dauki hanyar KARAYE''. Hawaye suka xubo min masu xafin gaske. Mafarkina na shekaru, me xan yiwa Abban Jawad dinnan in biyashi in ba kauna ba? Tamkar an tsikareni. Na fada wanka, a gurguje na kammala, Jawad tun safe da na shirya shi, yana can wurin Babanshi. Na kira Ashsha, ina cike da doki da murna ''Ashsha Karaye-xani-Karaye-xani, na rasa ina xan sa kaina ne don murna?'' ''Ki bari don Allah. A! Gaskiya nima baxa a barni a baya ba, xani inga Sadiya inga Ya Auwal. Above all, our beloved Amarya da Baba''. Allah Ashsha da gaske kike?'' ''Na taba yi miki wasa ne?'' ''Xaki iya kwanan kauyen mu? Da gidan mu da ko fanfo babu?'' ''In naje Tilde yaya nakeyi? Nima in mun dawo, xaki rakani Tilden, bikin wata cousin dinmu Joda'' ''kiyi sauri to don Allah ina jira'' ''kin fara yiwa me tafiyar bayani? Kinsan tsarinsa? Kika sani ko xai daukeni? Don naga alama Yallabai bai damu da kawancen mu ba''. ''Bari to inje in tambayo shi, haba! Xai yarda mana''. Na ruga a guje, sai kuma na dawo agujen, na daura xani bisa rigar wanka, na yafa babban gyale. A guje nake wallahi, nayi sallama bai amsaba. Na sake yi da alama baya kusa, Jawad yaxo ya bude.