← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 54

Sashe 28

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

120.
Ya dareni ''wai Kauye xamu inji Daddy?'' ''Ina Daddyn?'' ''Wanka ya keyi''. Na xauna cikin kujera, ina kallom tashar CNN dake ta aiki. Yallabai ya fito, cikin jallabiya fara sol, da farin towel akansa yana tsane ruwa. In banda kamshin bathrobb dinshi na dunhill ba abinda ke tashi a falon. ''Ga ni meye ake nemana urgently, kamar naci bashi ban biya ba?'' Na kunyata, na muxanta da xaman jiran da nayi, meya hana in koma in dawo, da naji wanka yake? Wannan jallabiyyan, ya fidda xahirin kira da xatin Yallabai ne. Har wani lafewa take a lafiyayyar fatar jikinshi. Yadin 'xeena-gaxar' ne iyakacinta kauri, bakaken gassu ne masu yawa suka rufe kafarshi baki daya tamkar wani balarabe. Dogo kakkarfan namiji, mai tashen talatin da biyar. Wanda ya tara dukkannin halittar karfafan maxa. Barin ingarmar kirjinshi, shike burge Mubina a halittarshi bakidaya. ''Yallabai na... na...dawo..'' na samu harshe na da tangarda a yayin furta hakan ''a'ah ki fada mani, yanxu xamu tafi, nagode da breakfast, a yi min lamurje a cooler. Tuwon shinkafa, taushe da naman tolo-tolo shine guxiri na. Jirgi xai tashi sha daya da rabi, don haka ki hanxarta''. Na mike kaina a kasa, naki yarda in kara dubanshi. Har na kai bakin kofa, na tsinkayo sautin shi na cewa ''idan munje, da kudin aurena, xan fara tarar Baba. Mu dawo Abuja a karasa jarrabawa. A kammala birthday, in cafki amaryata, mai kunya. Amma ina jin, da ta isa Wellington ko Rio 'de Janeiro (Brazil) xata koma hatsabibiya...'' Ina! Na kai kofa na fice, Jawad ya biyoni, shekarunshi bai kai ya fahimci me ke cikin xancen Abban shi ba, illah dai yayi dariya. Ya san tsokana ce yake mani. Barin da yaji ance 'a cafke' sai ya kara tintsirewa da dariya. ''Aisha Hardo na, ke neman matsugunin xuwa Karaye. Sabida ingantacciyar kaunar da take mani''. Haka na rubutuwa Jawad, cikin tafin hannuwanshi. Nace ya je ya kaiwa Daddy. Ya dawo rike da wayarshi. ''Wai ki rike xai yi miki magana''.
[10/15, 9:16 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/15, 9:17 AM] A A Dboy: Tuna Baya 121-125

121.
''Aisha Hardon, ta ci gidan su, nacinta da shishshigin ta yayi yawa. Kinsan mai yasa na tsaneta? Sabida taso ta kakaba maki Yusuf D. wani dan tsohon barawon Gwamnati''. Haka yace mani cikin wayar. Haushi ya kamani. Ya xanyi da kunyar Aisha? Dabara taxo mani, na kira ta nace mata Yallabai yace tayi hakuri ya turo mata da driver, domin yayi 'booking' kujeru ba ita. Allah sarki Ashshah! Tace min ba komi itama xata bi jirgin yawo. Mu hadu a Kano, filin jirgin saman Mal. Aminu Kano. Karfe 11:00 na kammala komi na xuba mishi cikin 'cooler' da 'flask' kaman yadda ya bukata. Tafiyar shi daban da tamu, sabida 'yan rakiyar shi. Hakanan Yallabai inda duk ya sauke kafarshi nan (escort) din shi xai mayar. A reception na hango Hardo, jingine jikin karfen bene. Sanye take cikin english-wears kaman yadda yake a al'adarta ta daura siririm kallabi a kanta. Hannunta na dama sakale da jakarta helena-ricci yayin da na hagun 'yar karamar waya ce Siemens. Muka hade da rabi-rabin runguma. Tuni direba daga gidan Maimartaba ya sha gaban mu, Jawad na gaba mu muna baya. Mun dauki hanyar Karaye, nake bayyana mata rashin jituwar su da Yallabai. Tayi dariya sosai tace xata neme shi a Karaye ta bashi hakuri. Ita dama tun sanda na gaya mata Oga ya hanani samari, ta san da kyar in ba kamu yake wa kansa ba. Da kyar in wanna Ubangidanci bai koma something special ba. Mun iso Karaye, kimanin 4:00pm. Na umurci direban ya saukemu dai-dai gidan kakana Liman. Bana son su Amarya su ji wani kugin mota. Sai dai kawai su ganni, kamar daga sama. Nayi mamakin yawan akwatunan da Ashshah tasa direba ya sauke, bayan na wurin Yallabai. Nayi mata magana tace Mamarta ce tasa ta hado su wai taba Amarya, da Atika da nake yawan bata labari.

122.
Duk yawan sauye-sauyen da garin Karaye ya samu sakamakon sabon 'chairman' mai aiki tukuru, jan gwarxo Honourable Sunusi Atta A karaye. Wannan bai hanani gane hanyar gidanmu ba, gidan Maikalwa da Daddawa. Abinda ya dan sani faduwar gaba, rashin ganin almajiran Liman, wadanda ada kullum basu rabo da kofar gidan. Tuni wasu almajirai sun yanyame mu, sun kwashi akwatuna, nace musu su kai gidan Maikalwa. Suna tafe muna biye dasu, har kofar gidan mu. Wani abin mamaki rusashshiyar katangar an tadata da siminti, xauren da ba ruff, an rufeshi ruf da Axara. Kalwar dake tike dashi babu ko buhu daya. An malale tun daga dakalin gidan har ciki da malalen siminti. Auwal na soma hange tsaye, fes dashi, cikin makubar shaddah keda ganinshi kinga wankakken dan bokon Kauye. Yaga yara yuuu na bin wasu 'yan mata wadanda da alama ba daga Nigeria suke ba, kuma gidansu suke dosowa, ya daka masu tsawa suka watse, suna ihun yeee! Ga 'yan Agulla daga Wantsandan da baturen Dan su. Jawad ya rude ya rukunkume ni, nayi masa magana cikin sauri da turancin da yafi sabawa da shi, ina kallon Auwal, ina doka murmushi. Ya koma relaxed. Har yanxu Auwal ya kasa magana, sai da muka karaso, xamu shiga ''can i offer u any help?'' Ya tambaya da alamun bai son mu shigar musu gida ''Ya Auwal kenan. Ni ko mutuwa nayi na dawo, na ganka cikin kowanne hali, baxan kasa ganeka ba!'' Xuciyar shi ta soma xolayar shi, wai wannan kanwar shi ce, ATINE, da aka kai wanke-wanke a birni? Haba! Ina Atine ta iya turancin da ya ji tana xabgawa wannan karamin yaron? Ina Atine tayi kyawun haka? Ina ta samo wadannan turawan? Bayan ance matar gidan dan Maimartaba take yiwa wanke-wanke? To ko waccan ce dan matar dan Maimartaban? To amma ai, basu fice shekaru daya da Atinen ba kai ina! Ficiciyar kanwar shi Atine mai siraran kafafi, ta koma tamkar 'yar sarkin Masar?

123.
Tuni suka baxama nemo Baba shiko Auwal neman pure-water ya tafi ya sawowa Aishah, da Dan da yake xaton kanin ta ne. Cikin dan lokaci gida ya cika fam da 'yan uwa da abokan arxiki kowanne yana shafata yana sunsunani, sun rude da yiwa Amarya murnar dawowa ta. Kakata Luba ta shigo xanin ta na kwancewa tana rikoshi, ta tsufa ainun. Na mike na tarota na rungume ''ashe Atine xan saki idona kamin tadda kushewa?'' Abinda take fadi kawai kenan, cikin xubda hawaye. Ashsha ta xama 'yar kallo, tausayin mu ya cikata. Ta tabbatarwa kanta ba karamin xaman kadaici nayi ba, yadda nake da iyaye da 'yan uwa masu kaunata haka. Sai ta shiga share hawaye. Shiko Jawad yayi wuri-wuri sai jefa ido yake waje-waje. A haka Maikalwa ya fado su Sani biye dashi, ''wai Uwata ce ta dawo?'' Ya ratso mutane ya iso ga wadda ake yanyamewa. Sanye cikin tsalelen Lesi ruwan kasa mai firgitarwa. Doguwar mace siririya sambal tamkar tarwada, mai tattare da duk wani sirrin kyawun da 'ya mace ke tinkaho da shi., daga yatsar kafarta har gashin kanta kyau ne xiryan, mai nuni da jikin da ya huta. Tabbas duka wurin babu kamarta. ''Atine na ce?'' Ya fada a yayin da hawaye suka wanke masa fuska. Na mike daga jikin Luba, na rungumo dattijon Babana, na xaunar da shi nima kukan dadin nake ''Babana, naji dadi da na sameka lafiya. Na tafi a MOTA na dawo a JIRGI, na tafi a wadda tayi rashin masoyi, na dawo da MIJIN AURE. Na tafi a JAHILA, na dawo a DALIBA mai 'yanci. Na tafi a KYANDIR na dawo a MUTUM, na tafi a MUBURGI na dawo a MUCIYA, na tafi a ATINE MAMMAN MAIKALWA na dawo a ZUBAIDAH MUHAMMAD KARAYE, to meye na kuka? Kuyi farin ciki, wanke-wanke alkhairi ne a gareni''. Baba yayi murmushi, tunda kika tafi Uwata bamu kara yin TALAUCI ba. Bamu kara saida KALWA ba. Bamu kara rasa kudin makarantar yara ba. Bamu kara saida KALWA ba. Bamu kara rasa abinci mai kyau ba. Wannan bawan Allah da kikewa aiki naira dubu hamsin yake bani a kowanne wata. Duk wata sai ya xo ya gaishe ni, ya gaya mun lafiyar ki kalau.
Chapter 28 · 0% Book details