← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 54

Sashe 35

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

38
Fuskarsa a tsuke tsam ba alamun sanayya,ba sani ba sabo ba gaisuwan mutunci balle alamun an taba haduwa da juna,sauti ja-rule ke tashi cikin motar cikin baitin da ya kira WANNA YOU TOO NEED ME.I WANNA BE THE FACE YOU SEE.WHEN YOU CLOSE YOUR EYES.I WANNA BE YOUR FANTASY AND BE YOUR REALITY AND EVERY THING BETWEEEN.I WANNA YOU TO BE NOT BLAME,FOR YOUR LOVE IS OVERALL TO ME' hannuwasa bisa sitiyari,ya na kallo mu ta madubin gaban motar na side din da yake, fuskar nan kamar hadari .wanni abu ya danna duk kofofin motar suka bude atare muhd jos ne a kujerar mai zaman banza shima bai kalle mu ba, kazalika bai cemana ko cikan kan ku ba muka shiga baya ni ina tsakiyar ashshah da lola, ashshah na rufe kofar daya wani fizgi motar sai da dukkaninmu muka birkito daya kujerar idanun ashshah suka yi kwal -kwal ta kankameni ganin mutuwa muraran,ni ko ko ajikina ai nace bazani ba suka takuramini? Irin gudun da yayi sai da motocin dake gaba da bayanmu suka dunga aikamasa da fitilun zagi.mun yi nisa da karaye sosai muhd jos ya dubeshi akufule bello in kisan kai zaka yi ka sauke ni.ban shirya mutuwa yanzu ba ya juyo gareni zubaidah kice wani abu mana
[10/23, 5:09 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/23, 5:10 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔
~BOOK 2~
39.
cikin kudurar ubangiji 'ya'yan hanji na babu duka wanda bai zunkuda ba mohd ya zuro hannu ya bude kofar dama ku kufito mu tafi ai ni tuni sun yi waje babu nema ba'asi zubaidah fito kin ji, wannan mugune,sai ya kasheki abanza awofi tunda bashi keda asaraba na daga kafa,da niyyar in fita amma ko motsata na kasa tariga tayi tsami sai hawaye suuurrrr,kafin na ankara tuni nayi dirshen a mazaunin mohd, cikin wani irin zafin nama ya rufe kofar ya sake fizgar motar (over 400 spead) ya dubeni yayi murmushi dukkanninmu babu mai tsira da rai.ina amfanin rayuwar kowannenmu bada wanda yake soba?sai kunci, sai bakin ciki wanda da karshe ni ya zautani, ku baku san ina yiba bazai yiwuba!ba zan keta miki mutunciba zubaidah ,don ba abin da yasani sonki ba kenan.idan baki mantaba,na soki ne tun baki mallaki komiba,tun kina kucakar 'yar kauyen ki idan nayi haka ashe karya nake ba sonki.bazan iya hakura da atine naba kuma bazan barmishi ni bakin ciki ya kasheni.ai gara duk murasa ...................daga haka ya dauke kan motar daga titi,yayi daji damu, ya saki sitiyarin motar tari ka karo da bishiyoyi har ta dangana da wata ribdediyar bishiyar tsamiya,ta jirkice glassanta suka kwankwatso a gadon bayanmu wani abu naji tsakiyar kaina garam.ban kara sanin inda rayuwata take ba.

40.
jinayi ana gogemin jiki da towel sannu ahankali na bude idona ya bala'in yimin nauyi dusu dusu nake gani amma na fahimci matar baturiyace na bude idona sosai wani haske ya dallare min ido. ba shiri na maida na rufe,na yunkura zan tashi naji ni a daddane oh thank god,you've recovered!ta danna kararrawa wani likita bature gajere siriri ya shigo tare da nurses suka ciccire na'urorin dasuka yimin dabaibayi dasu fita,da kamar minti goma bayan fitarsu aka turo kofar aka sake shigowa,yallabai ne agaba fatima na biye dashi fuskarsa ba yabo ba kuma fallasa.ta jamai kujera ya zauna dai dai saitin kaina ta daura hannuta akaina tace zafin kan ya sauka takama yatsuna kaji jikinta sanyi kalau sannan duk takumbura.anya baza ayi karin jiniba shiru yayi mata yana kallon wani wurin daban can kuma ya dubeta,ashe kin baro sanni hallayar dan adam kin komama lafiyarshi?tayimurmushi tafita bari inga abbansu mukhlas" na rutse idona na rasa meke mun dadi?kunya da nauyin yallabai da fatima suka dabai-baye ni yanzu ko awane matsayi yake dubana? Maciyiya amana,makaryaciya, maha'inciya. wannan shaidar da yayi mini shekara da shekaru a yau bello ya gogeta (bana karya bana ha'inci).gashi ko sannu yaki yayi min. na daga hannuna wanda ba bandeji narufe kwayar idanuna .wasu siraran hawaye kebin gefen idona suna diga cikin kunnuwana, ya mika hannu ya dauki jaridun dake bisa wani tebir yana nazari daga cikin wani dark glasss din daya boye kwayar idon shi,ko uhm bai ce ba.
[10/23, 5:10 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/23, 5:11 PM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔
~BOOK 2~
Tuna Baya 41-50

41.
aka turo kofar aka shigo wannan likitane na dazu sunyi musayar kalamai cikin turaci wanda na fahimci jinine za'a karamini.yace su gwada nashi ko na kanwar shi in zaiyi dai-dai?idan duk bazai ba bai san jininsu gara yasayi abincin da zai kara jini cikin dan lokaci,toh anyi sa'a nashi ne yayi dai-dai tun da dukkaninmu muna (groupB+), aka duba lafiyar jinin kamin a diba asamin,ina daga kwance ina kallon disar jinin abban jawad,cikin gaurayen jikina wasu hawayene suka ninka na da allah yagani muhd jos shaidanane har azuhur yana zaune ya diba lokacin sallah a agogon zallar 'diamond'dake hannushi ya fita fatima ta sake shigowa zubaidah dacta yace kada abaki abinci sai gobe.yanzu meke damunki?ita kanta kunyar ta nakeji kamar na nutse akan katifar da nake kwance.bance komiba sai karin hawaye.ta matso har inda nake ta ja kujerar da yallabai ya mike ta zauna na yunkura ta mike ta tusa min fillow kuka mekike tayi haka? Ai an gode allah da baki raunana tamkar mohd ba,da kin kwaramin yaya amarya da hatsari ranar aureta?'what a horrible'! idan kinga abbasu mukhlas sai kin ga naki ba komai bane.shin mai ya janyo hatsarine? Wannan ya tabbatar basu san da ganga bello yayi ba,na gode allah a raina nace dan jos bai gaya muku ba?shi cewa yayi,kun sauke su suyi sallar azuhur agidan mai ke kuma kikace zafin dukanki,shine wai ya zaga titi ki dan sha iska kamin su idar. yaga shiru-shiru baku dawoba shine yakira police suka duba.gaba kadan suka gane cewa 'stirring'ne ya kwace wa mohd .yayi daji kuka yi accident kai wannan muhd amma gwanin karyane,ban musa ba koni naso hakan da da wanne ido zan dibi fatima da yallabai?

42....
ana gab da daurin aure muka tsinkayi labari yallabai yayi ta fadan da yasani da baice mohd yakai ki asibitiba yasan shi bala'in tukin gangaci. Shi fa har karaya yasamu ahannu shi dama da hagu ga gocewar kashin kafa ke kuma buguwane kawai a pelvis girdles (kashin kugu)ki kan ciwon da za'a kai asibiti kenan.sai raunukan glass a tsokar bayan ki da targade ahannu, amma sun bada tabbacin nan da sati daya zaki warke sarai ta mike tana zuge labule. Na tambayeta wane asibitine nan?tace in mun fita na gani amma ina zargin idan har yallabai bai zargi tsakanina da bello. don daga ranar kullum ya shigo daga tambayar ya jiki bai ce min komi ba ba wani alamar kulawa.ba wannan murmushi da kalaman shi masu dadi,babu alamar kauna.fatima da nurses ke kula dani.ranar litinin wato ranar da muka cika wata guda sun tabbatar duk kasusuwan sun hade sai karfin jiki da ciwon jiki. suka sallamemu da shawarar yawan motsa jiki. munfito harabar asibitin da kafata nake tafe na daga kaina na duba na tabbatar ba nigeria nake ba jar fata ke ta sabgarsu a ko'ina .ta hanyar wani karamin notice board na asibitin na fahimci muna cikin birnin pittsburgh,USA ban ga yallabai ba, fatima kejan mu cikin wata kankanuwar mota ta zaman mutum biyu (bently) irin mai mannewa a kwaltarnan ce saman ta a yaye yake kalar ta brown wannan ya tabbatar min zaben yallabai ce mun iso wata kebantacciyar unguwa mai tsarin gaske da basan sunanta ba gidan da ta tsaya shine no (9)karamin gidane flat ma tsarin irin gini turai dai samarine guda biyu (afro american)dake kula da shukokin gidan suka bude kofar da alama sun santa tana daga musu hannu motoci har biyar a harabar gidan tabbacin akwai baki ta yafito da daga cikin su ta tambayeshi ko yallabai shi da wane? Yace suna meeting ne da

43.
wani corridor muka bi zuwa cikin gidan,akwai sassa guda biyu kawonne dabam da dan uwansa taba ni mukullan daya sassakine amarya zubaidah, ni zan yi amfani dana maman jawad, bakisan wata sa'a ba harda wata jakarta da dollers a ciki na tsinta.in kinaso nakawo mu raba ko ina take Allah sarki!kai faty akwai surutu kamar aku, nayi murmushi,ni banaso,ba abin da zanyi da kudi, nida bani da lafiya?in zamu tafi gida zaki bukata mana?ni dai na yafe, yaushe zamu tafi? jibi in an sallami mohd koda yake kune zaku tafi jibin ni zan tsa inkula da lafiyar mijina nida muhd jos wata kila har akare biki baza ku ganmu ba sai kunzo 'haney moon'a biyo ta gidan mu ko? na dan kyabe baki kadan, don sai naji banbarakwai. Faty tayi dariya tace kije kiyi wanka, in kin kintsa'exercisearea' zamu zaga.kinji likita yace ki dinga yawan motsa jiki.baza kiga angonaki ba sai yamma kinji sunce yana meeting fuska na yamutsa kamar zanyi kuka nace ni nace miki inason ingan shi?kai aunty fatima tayi dariya ta wuce daya 'part' din

44.
nayi wanka amma na rasa kaya da zansa in sauke sallolin dake kaina, na jikina sunyi datti kwarai, na bude dirkekiyar warddrove ta jikin bango dake dakin,kayan yallabai ne ajere abin sha'awa wani nabin wani.naja wata jallabiya ruwan makuba kirar omman,wani lafiyyayen kamshi take na yallabai dana dade da sani wanda bako wana taba ji dashi ba sai shi daya,na sanya nayi lullubi da sabon zanin gado na sauke duk sallolin dake kaina,inda duk yallabai yake bakya rabashi da karamin Alqur'ani mai tsarki.don haka ina diba wallet din shi na samu,bugun misra na karance fatiha,baqara al- imran,da nisa'i.nasoma maidah kenan fatima ta shigo tana rike da kayan hannuta ta shirya cikin farin dogon wando da karamin riga ruwan powder pink masu ratsi fari ,kanta cikin 'showercap'sai digar ruwa take tabbacin daga 'swimmingpool'ta fito ta dubeni tayi murmushi tace ba sai kin rokaba
Chapter 35 · 0% Book details