Sashe 37
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
51....
Da kirji kaman an tatsile kuliy bisa kwalta, amma ai ba zubaidah momin jawad ba,idan kuna arewa kiyi mai arewanci,idan kuna amurka,ki yaye bargon kunya ki yimai amerikanci kizama tantiriyar ba amurkiya, that's all.... Na tuntsire da dariya har cikina ya kulle.sai karfe goma muka iso gida ,har na gama abinda zanyi na kwanta, ban sa yallabai a idanunaba.barcinake ,amma hawaye basu bar zubamin ta gefen kunciba.na tabbata yallabai fushi yake dani tun daga ranar da aka daura mana aure,da ada yake kira special day a garesa.da asubah dan alarm clock din dana saita na makale jikin gadon shi ya tayar dani..na dauro alwala kenan ina shirin tada ikama naji motsin shi yana murda kofa..ya murda kofar ya shigo cikin farar jallabiyya da sallama ciki-ciki kaman bai son yi yace baki jirana mutada jam'i?daga yau karki kara yin sallah ke daya har in ina nan,ya jamu sallar yayi 'yan addu'oi muka shafa ,ya kunna wata 'yar karama rediyo mai kama da kwallo yara (ball)karatun alqur'ani mai tsarki ake daga masallacin madina ,yana bi a fili tirya tiryan ni kuma inabi a zuci .karfe shida gari ya soma haske ya kashe rediyon ya mike da niyar shiga wanka, na karkace kai na riko wuyan hijabi nace ina kwana yallabai?
Saida yakai kafor shiga toile din yace lafiya shima ciki ciki nakoma gefe na zauna shiru kamar icce wayyo Allah!ko wani kwakkwaran motsi na kasa kaman an kafeni a jikin bangon. ranar mun dade muna exercise nida faty,ko kadan ban gaya mata canzamin da yallabai yayi ba toh ina hauka ne? itama ta gano nice atinen aina bani na lalace ,bayan munci abinci mun zaga birnin pittburgh har da isabella,daga karshe muka kare a wurin kallon (polo)can muka lalace har yamma lis .nayi mamakin mai yasa faty bata ambaton mijinta,dan rigima muhd bello?na kare mamakina da tambayarta baza taje taga no muhd ba?budar bakin ta sai cewa tayi ai in ya soma fizgar, to ki tabbata antino atine a irin wannan lokutan baya baya nake da shi,kin san zuciya bata da kashi in na likemishi abin bazai yimin dadi ba, mohd jos na tare da shi,yallabai ma nasan tun safe yana can kuma naji yace da yallabai ya maida shi asibitin barikinsu na washington ya karasa jinyar acan gobe in kun tafi nima zanbi shi,tausayin faty ya kara kamani, kamar in zubar mata da hawaye,in ban da so da Allah ke dorawa bawa mena fi faty?ban ganshi ba!farace sol!mai ginannen dirarren jiki,komi na hallitta ta ya dace da ita ay sai yayi tayi ni ina ruwana? gani ga mijina me zai dameni?ina son shi,na kuma son yana min so fiye da wanda nake mai,hakanan nayi aure da zuciya daya insha Allah ba abin dake rabani da yallabai sai mutuwa itama ina fatan ta dauke mu tare. in ya gaji ya dangana bisa tilas, ace mutum bazai yadda da hukunci Allah ba,bazai yadda da kaddaraba? alhalin yana ikirarin shi musulmine,yaya kuwa za 'ayi yaga da kyau?yaga sauki da farin ciki a rayuwar shi?
52....
Ni nasan naso bello,naso komi nashi nayi fatan kasancewa matar shi har abada!amma daga ranar da yace wai ni kawar matar da zai aurane atika su fatima suka cemin KYANDIR,yayi dariya ya kuma kasa tsawatarmusu.duk wani so dana ke mishi a wurin ya narke, haka duk wata kauna a wurin ta zagwanye na tausaya mishi aranar wunin da yazo gidan mu don ganin yadda ya koma kamar mahaukaci,har naji birbishin son na neman tashi,shine har takaini ga furta kalaman da har yau nake nadamar furtasu ga amarya nace wa wai auren tausayi zanyi da yallabai ba auren so ba. dama turawa sukace wai when love dies its ashes remain alive.daya nemi kashe mu akarn banza na tabbatar ba shida birbishin imani,daman ance wai duk sojoji imaninsu cikin cokaline ,irin su bello ne koda ka auresu kuskure daya zakayi musu susa gindin bindiga su bubbuge ka ko su harbeka gaba daya,sun kuma kashe banza,na kasance tare da yallabai shekaru dai dai har takwas,na kuma fahimci shine mijin da nayi burin samu arayuwata sau tari na kan tambayi kaina a yadda zamanin nan ya tabarbare yanzu, daga samari har magidanta sun dauki zina ba abakin komi ba anya za' samu irin yallabai na?
53...
ya raine ni tun ina mitsitsiyata yake gyarani har na kawo matakin da nake kai ayau,wato mataki na cikakkiyar kuma haddadiyar buduwar,mai dauke da duk wata hallita mai jan hankali da namiji,bayan bamu hada dangi ba tako ta ina, karewa ma,ni baiwace a gare shi amma bai taba nuna ko sau daya yana sha'awana ba!duk da kowa yasan irin rayuwar auren daya keyi da matarshi a lokacin,alhalinyana da kowacce dama ta neman hakan, sai nake tambayar kaina sunan daya dace dashi in kirashi Brave,or Trustworthy? Ya tara duk wata suffa dana ji ashshah na fadin wai sune mazan dake tsada,duk matsayinshi,ga iyalinshi shi mutum ne mai sanyi dabe daukar kanshi a bakin komi,bai da son kansa,bai son matsama dan adam duk abin daya lura baya ra'ayi, koda shi yana matukar ra'ayin abun tausayin shi, addinin shi , kyautayinshi da akidunshi ababen kwatancene.Qualities ne dana tabbatar shi bello da kyar in ya hadasu duka,shi daya so gurbatamin rayuwa badon Allah ubangiji na tare daniba?nagode allah godiya mara iyaka daya sa nafi karfin zuciyata ban bi son rainaba dana biye mishi dana tozarta yallabai,lallaidanayi asara irin wadda ba a mayarwa har abada!yaje can ya karaci rashin imaninshi da matar shi dake son shi hakurarriya baiwar Allah fatima nasan ita zata jure tunda tason kayanta haka,gashi harta iyawa halinshi haka?tasan sanda zata rabe shi da sanda zata nisance shi? abinda ke daure min kai shine ta ina yallabai ya fahimto ni da bello?koda yake insu marasa kwakwalwane da karamin tunani sun yarda da karya muhd jos shi namiji mai cikkaken hankali zai amincene?wani irin a zaga dani kamin su iddar da sallah?mubama sallar?idan ni banida lfy bazan iya sallah ba,shi meyasa meshi da bazai yi sallah ba?har muka iso gida tunanin danake kenan nayi sallah nayi nafiloli na kwanta har zuwa lokacin banga yallabai ba saida asubah da yazo muyi sallah
54
Dayake aranar zamu tafi,muna idarwa ban tsaya sauraron karatun da yake sauraroba na janyo jakata na shiga harhada kayana,yallabai ko magana tun da muka fito asibiti bai min ba ina yi ina share hawaye da bayan hannuna najawo ledar sayayyar da mukayi na cosmetics daga durowar mudubi sai kayan ciki suka zubo gabanshi gaba daya,na russuna ina tsincewa ya kama duka hannuwana,ya rike,abinda bai taba yiba wannan shine karo na farko da yallabai ya taba kama jikina by mistake a take tsigar jikina ya tashi yar! shock ne har cikin kwakwalwana irin wanda ban taba jiba yace no akwai abin da zan diba nakoma nayi zaune bakin gadon ya shiga dibasu daya bayan daya yana mayar min ledata,wadanda basu yi mishiba in ya karanta ya ware ya zubar a dustbin wannan karon ma cewa yayi bakin AREWA, nake son momin jawd dashi daga haka ya juya ya fita,naci kuka na har nagode Allah oh ni zubaidah menayiwa wannan bawan Allah?kar dai baya sona ya aureni? Na roki Allah kada ya kara samin wannan mummunan tunani,
55....
karfe hudu ne jirgin TWA ya saukemu a filin jirgin saman lagos ma'aikata foreign affairs dake kar karkashinsa suka zo tarya yallabai Allah yayi yawa dasu mun sauka a wani guest house dake titin hearbeart macaulay, bansa yallabai a idanu na ba sai washegari ya shigo a masifar gajiye, yace kwana sukai suna meeting da ministocin nigeria gaba daya a fadar governor tinubu.koh um ban ceba har alokacin muka baro lagos a mota audi,tafiyace mai dadi dasa nishadi don direban baya gudu sosai haka moto cin dake take mana baya ga sanyi AC na ratsamu ganni yallabai na karatun jarida batare da ce min ko sannuba,hankalina ya kara tashi,na kifa kaina a cinyoyina kamar inyi ihu,anan nefa na tuna nima macece,mai zai hana inja ajina?sai nayi biris dashi na bude karamin Al'qur ani ina karantawa ? har muka iso karaye cike nake da dokin rungumar gudan raina JAWAD an sauke yallabai a gidanshi na bayan gari kamin ya sauka yace any matsala?na daga kai kurum yace toh sai gobe zan aiko abdulraheem ko to din bance ba 'yan rakiyar shi dake bayanmu duka nan suka tsaya, nace wa direban ya fara tsayawa gidan mai martaba ya kira min abdulraheem (abdulraheem kanin yallabai ne dake bin fatima yana level two a bayero) ya dan leko ta taga bakin shi a washe a'ah momin jawad har kun sauka?tun jiya muka je tarenku a airport din mallam aminu kano mun dauka tacan zaku sauka akace ba jirgin US da zai sauka muka gaisa ciki mutunta juna da sakin fuska na gayamai ta lagos muka biyo, sabida yallabai nada meeting nazo daukar dana ne yace Allah sarki jawad yananan yana takabarki,