← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 54

Sashe 21

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

85.
Duk abinda Ubana yayi masa, bai gani ba, ya manta, da baxar Uban wa yake taka rawa, bada ta Ubana ba? Idan yau nace ya bar kujerar sa, wallahi ta xauna. Don dama shekarunsa basu kai ba, Babanane ya shiga ya fita yasa shugaban kasa ya bashi ita. Sai dai ina ji a jikina Mansina, baxan iya rabuwa dashi ba. Shikadai ne a duk maxan da nayi hurda dasu kamin nayi aure, da xai kusance ni in san da namiji ne da ya san menene kauna?'' Ta karashe fadin maganar cikin murya mai ban tausayi. Tsaki Mansina tayi sabida haushin da ta bata tace ''kina amfani da kayan Indonesian da naki kawo maki kuwa?'' ''Har na Uwar Indonesia ma, nace maki ko ohon sa. Ni fa nasan ala tilas yake bari na kwana cikin gidan sa, don baxan ce aure ba''. Mansina murmushi take tana karawa. Tana kada kai tana kallon ta kamar dabba, ''ke dai ko a mahaukata ma ina jin ke ta musamman ce, har ban san sunan da ya dace in kira ki cikin jinsin mahaukatan ba, Uban wa yace maki baxai nemi mata ba irin wannan rayuwar auren da kuke, mai kama da wasan yara? Dadin dadawa yana turai wata da watanni ba matar aure, shi waliyyi ne koko ba lafiyayye ba? Tukunnama wannan 'yar rainon da kike kira 'BLACK', a gidan Uban ki take Black din? Wallahi in bakiyi wasa sai ta AURE TAHEER. Akwai wani sirrin kyawun 'ya mace a tattare da ita, wanda xai tunkudo, nan da 'yan shekaru. Irin wadannan matan Alkyabba ne ga maxajen su. Ki dubi fatar jikin ta, gashin kanta, fatan ta da wankakkun kafafunta, wallahi tana samun gyara da kulawa wanda yafi karfin na 'YAR RAINO. Ki xauna ki binciki, shin meke faruwa cikin gidan auren ki? Sakacinki yayi yawa Mubina. Ta yaya tana kula da yaron da YAKE SO FIYE DA KOWA ki ce xai banxatar da ita? Ke akan me ya banxatar da ke? Don kin kasa xama ki rainon mishi Jawad! Kin kasa xama ki gyara mishi Jawad!! Kin kasa xama ki ba Jawad abinci!!! Na gaya maki, na kara gaya maki ''MAI DA WAWA NE, INDA AKE SON DAN SHI A NAN YAKE!''
[10/8, 5:23 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/8, 5:24 PM] A A Dboy: Tuna Baya 86-90

86.
''Haba-haba! Yadda nasan Taheer da kyama, ba abinda xai ci da 'yar kauye kuma jahila, shi da bai ko xaman awa guda da jahili'' Mansina ta fara kuluwa tace '' 'yar kauye kika ce ko? Shi daga ina ya fito? Ko shi ba dan kauyen bane tunda dan Sarki ne? Jahila, baxa a iya kaita makaranta ba? Na gaya maki, na kara gaya manki wannan''. Tayi shiru xuwa can tace ''kin ce kin gaji da auren Taheer, wallahi kikayi saken da ya sake ki, ko wanda ya kama yatsar shi baxaki samu ba. Ba nan Abuja kadai ba har Nijeriya gabadaya. A kamanni da dirin halittar ki dai. Kin san banda kaddara da rabo, Taheer baxai taba auren mummuna kamar ki ba. Kin haifi Da, amma kowa yace Allah yayi masa gyadar dogo da bai dauko uwar sa ba. Kince xaki iya sa Taheer ya bar kujerar shi, to sauran connections din shi da kasashen ketare fa? Baban ki nada hannun sama masa shi? Ban taba sanin Mubina ke gaula bace wallahi sai yau. Tukunnama wa yace da ke abinda ya dogara dashi kenan? Kina auren mutum baki ma san hakikanin wanene shi ba, baki ma san hakikanin sana'ar sa ba, sai dai a xo a gaya maki daga waje, wannan ballagaxanci har ina? To bari in gaya maki abinda baki sani ba, in gaya maki TAHEER din da har yau baki san komi akan shi ba. Yanxu haka ya xuba manyan hannun jari a manyan kamfanoni uku a turai. Daya a kamfanin sarrafa takalma na (Andre Valentino) dake Rome (Italy), daya a kamfanin sarrafa (Crystals) dake Washington D.C, daya a kamfanin sittiru da kayan shafa dake Losbon din Portugal. Kina tambayar me Taheer ke yo wa a Canada da kika ki xuwa 'yan kwanakin nan? Kamfanin shi na kashin kansa na sakar carpet din xamani yake budewa, xancen da nake yi maki yanxu, har sun shigo mana nan Nijeriya da wasu sabbin salon rouded, squared da triangular centre carpets da ake rububi a halin yanxu. Duk abubuwan da kika lissafo Taheer da su a matsayin mai laifi a gareki, banga laifin shi ko daya ba, sai naki Mubina.

87.
Maganar gaskiya, idan xaki hango kuskuren da wani yayi maka, ka fara tunanin kai me kayi masa da har ya janyo hakan? Ba ka maida naka tudu ka hango nashi ba. A gaskiyance baki da lokacin shi, baki da lokacin Dan ki daya nuna maki yafi komai muhimmanci a gare shi, maimakon kiyi amfani da damar hakan da kika samu, ki nemawa kanki matsuguni, kiyi ta haifar 'ya'yan har su sayo maki kaunar da kike tababar baya maki, a'ah sai kika tsaya rudin duniya da akidun nasara da kika ara kika yafa suka xama jarogaran ki, wadanda a xahiri ya nuna maki sune yake kyama ba ke ba. Baki bashi kulawar mata ga miji balle girma da darajar da Allah ya baiwa maxa akan matansu. Ke dai kullum ke ce a sama, kece kika san rayuwa, shi bai waye ba. Ba ajinki bane, kin fishi, tunda Ubanki shine Ubangidan sa. In banda karya da homa baki iya komi ba. Kowa yasan Taheer yana hakuri dake ne kawai sabida darajar mahaifin ki, amma ba don tsoron ki ba kamar yadda kike tsammani. Kuma wallahi komi ya faru da auren ki nan gaba idan har baki canxa takun rayuwar ki ba, kada kiyi kuka da kowa, kiyi da kanki. Ki iya bakin ki Mubina, a yanxu Taheer xai iya sayen Alhajin ku da aikin shi a presidency. Idan kin so ki kama auren ki, ki makalewa mijinki, ki sauke wannan jin kan naki, ki rage wannan xafin naman, banga abinda kike samu a Omega Bank, wanda mijin ki bai mallaka maki ba''. Aunty Mubina ciki ya duri ruwa, ''yanxu ke don Allah Mansina ina kika ji sirrin Taheer? Xan iya rantse maki, tunda muke dashi yau shekaru hudu, bai taba budar baki ya gaya min wani abu da ya shafeshi ba. Illa ni aiki xani kasa kaxa, wuri kaxa sai rana kaxa xan dawo'' ''a to! Kin nuna kina son sani? Ni dai na gaya maki ki rungumi auren ki, da mijinki, a friend in need is the one who will tell you when your face is looking dirty.'' Jin sun yi shiru nayi sallama, da kyar Mansinar ta amsa na sauke Jawad a gaban su. Ya kallesu tamkar yaga abin tsoro da kyama, ya rabe a kafaduna, ta taso xata daukeshi, ni kuma na mike na nufi...,

88.
,..kofa yako biyoni a guje ''Momi-momi'' ya makalkale ni yana haki kamar wanda ya ga mala'ikan daukan rai, na tsaya a sandare don tsoro, yau naga yaro mai manta uwarsa na ce ''Mominka ce, ni bani bace'' a fusace ta xo ta figeshi ya kuwa gartsa mata cixo a wuya ta cira hannu ta dauke shi da mari, kau! Yayi taga-taga ya fado jikin Mansina, ta nemi kwayar idon Jawad, babu, itama kanta ta tsorata. Dai-dai lokacin da mai Dan, yayi sallama, cikin Suit-Spanish. Ya isa gareta ya daga dan shi, ba motsi. ''What's the matter?'' Shine tambayarsa. Na sa kai na fice, na shige dakina, na tura kofar na fada rub da ciki tsakiyar gadona na soma kuka mai tsanani. Idan yaron nan ya mutu, bana tausayawa kaina tamkar Babanshi daya maida shi farin cikinshi abin ganinshi ya ji dadi. Bar ta ni, mai komawa KARAYE, ba wannan ne abin damuwar ba. Tunda ko da Jawad, ko babu, tilas wata rana xan koma gida. Abin damuwar shine kaunar Jawad, da tabi bargo da tsokar jikina.
Nayi ta kuka har idona suka kumbura. Ji nayi an turo kofar, dauke yake da Jawad a kafadun shi. Shi kuma yaron nata faman tura kit-kat a bakin shi. Tun daga bakin kofa ya sauke shi ya rugo a guje yana kiran ''Momi na'' na bude dukkan hannuwa na ya shige na mayar na rufe, hawayen dadi ne suka xiraro mani suna diga gadon bayan shi. ''Sahad (na Abuja) muka je, kin gani Daddy na ya sai min kit-kat, ke kuma ya sayo miki 'ribbon'. Ya xaro tafkeken hair-bound cikin aljihun wandon shi, kalarshi 'brown'. Shi yana son kala 'brown' yawanci komi da xai saiwa Jawad, brown ne, nima hakan. Na amsa cike da murmushi ''to kaje kace ma Daddy, na gode''. Ya ruga ya rike shi ''Momina tace thank you Daddy''. Ban san me ya rada mai ba, sai ya dawo ya dare ni, ya karbi ribbon din a hannuna, ya xare kallabina, ya hada jelunan siraren kitso (Jennifer Lopez) dake kaina, ya xurasu cikin ribbon din, ya maida min dankwali na. Ya rada mani cikin kunnuwana, ''Daddy ya ce xa'a baki 'thank u daddy'.
Chapter 21 · 0% Book details