← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 54

Sashe 29

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

124.
Don haka hankalin mu duka a kwance yake, ni kaina nasan rainon ki, RAINON ALKHAIRI ne a garemu. Gashi a yau a dalilin rainon, ki xama mace abin alfaharin kowanne Uba. Lallai kowa yace GONAR WANI BAXATA YI ALBARKA BA, TASHIN CE BAXATA YI BA!'' Inna dake xaune wai sai ta kama kuka. Tana rokon in yafe mata, in yafewa Atika ba laifin ta bane. Ni wallahi na ma mance da xancen kaf. Nace ''ni mai kikai min ne? Me Atikar tayi min?'' Sai a lokacin na tuno wai wani saurayi can dan gidan Waxiri shine take kuka? Na bita har dakin ta ina rarrashin ta, ina tambayar ta INAA ATIKA? Sai ta kara tsananta kukanta. Ganin haka na kyale ta na dawo ga bataliyar dangina. Ana ta labarin bayan rabo. Wacce 'yar gidan wane ta mutu, wane ya mutu, wane tayi aure. A nan na tsinkayi labarin mutuwar kakana Liman, bayan tafiyata da shekaru biyu. Bamu samu kebewa da iyaye na ba sai misalin karfe goma na dare. Amarya na can madafi tana kokarin hadawa Ashsha abinci. Jawad tun maghriba Kakarsa ta turo Talatu ta tafi dashi wai taga Maigidan ta. Ni kuma a barni in xanta da iyaye na. Baba ya ba Auwal yayo cefane na musamman, Amarya kuma ta aika Sadiya sayen lemun kwalba mai sanyi wajen wani mai shago can wajen gidan Maimartaba, duka sabida bakuwar su, Aishah. Xancen cigaban da Karaye ta samu, shi yafi daukar hankali na. Ga dai ruwan sha mai tsbata, ga kuma wutar lantarki ta haske ko'ina. Ashsha ta ji dadin hira da Baba da Amarya, ba don komi ba sai don su mutane ne masu saukin sha'ani. Amarya ta kare shinkafa fara da taliyar macaroni, ga farfesun kajin hausa yaji kayan kamshi. Auwal ledar pure-water ya dire mana, amma Ashsha bata nuna komi ba, ta dauka ta sha fuska a sake, duk da nasan ko spring water ba kowanne take sha ba, wannan yasa na kara jin kaunar ta, ba don komi ba sai don fahimtar da nayi ita mai kauna ta ce kurum sabida Allah ba don wani abu da na mallaka ba.

125.
Babana ya rasa ina-yaka-saka-ina-yaka-aje da ni? Ya dubi Ashsha cike da murmushi ''Uwargida na, Indo, me xamu baki ki ci?'' Ashsha sai dariya take. Ta jero akwatuna dai-dai har bakwai, uku nata ne, hudu daga yallabai, ta farko ta Maikalwa ce, shadda, yadi, voyel bandir-bandir ga kudin dinkin su a kai har (N30,000), mai bi mata ta Amarya ce, tamkar kayan lefen budurwa, lesika, shaddojo, atamfofi (super-exclusive) da Aura. Aura ne kawai a ciki. Ta fidda turamen Hollan da Ingila guda bakwai tace wannan Baba yaba Innar Jafaru, na Atika ma wanda da kudin ta ta hada mata ta bude masu sun gani, tace sai hanu da hannu xata bata. Auwal, Sani, Salisu da Rabi'u kowanne ya samu kayan samari, na fito da tsarabar autar Amarya Sadiya da Jafaru duk ba wanda aka bari tamkar Yallabai ya binciki adadin mutanen da ke cikin gidan, koda yake nasan kadan daga aikin shi. Maikalwa sai kuka wanda baya mishi wuya yace ''shin meke tsakanin Atine da Yallabai Magajin-gari ne? Ni fa wannan abu ya soma bani tsoro''. Ashsha ta kalmashe kafafu tana murmushi tace ''koma menene Baba shi da kansa xai gaya maka. Amma in kyankyasa ma karambani, Yallabai auren Zubaidah ne ya kawoshi''. Baba yayi shiri da alama kanshi yayi xafi. Ya sunkuyar da kai ''In nace xan gaya maku abinda mutumin nan ke yi mani a shekarun nan, wallahi sai in yi karya in kuma mance wasu. Duk sanda yaxo Karaye, daga gidan Ubansa sai kofar gida na. Duk shaddar da ke jikin shi haka xai shimfide ta a kasa yace ''Baba ina wuni?'' Idan har akwai abinda xan mishi in biya shi bai wuce bashi auren Uwata ba!'' To a dakin Amarya ma xancen da suke yi kenan, ni ina uwar dakin Inna na barci mai dadi na dibana kadan-kadan sabida gajiya. Ashsha da Inna kusan kwanan xaune sukayi. Gabadaya rayuwata gidan Yallabai, makaranta da ya kaini, barmin rikon dan shi da yayi, rabuwar shi da uwar yaron, duk Ashsha bata boyewa Inna komi ba. To Inna ta nuna rashin gamsuwa da halayyar Yallabai tace da sanyin muryar ta ''kuma sai ya saki Uwargidan shi don xai auru YAR RAINO?..
[10/15, 9:17 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/15, 9:18 AM] A A Dboy: Tuna Baya 126-129

126.
Haka akeyi? Waya ke son mutum mai saurin saki? Ashsha ciki ya duri ruwa, nayi nadamar surutun ta da har bai boye wani sirrin tayi hamxarin gyara xancen ta da cewa ''ita ce tace baxata xauna da mai wanke-wanke ba, shine ya sallame ta''. Ga dukkan alamu Inna bata gamsu ba. Washegari tun kamin in tashi barci, da sanyin asuba har Ashsha ta sa tsintsiya ta share tsakar gidan mu tas, ta sharewa Inna Amarya daki, tasa tsumma a ruwa ta goge ledar. Ta hada 'yan kayan Sadiya ta ninke ta kimtsa dakin tsaf. Ta sa guga a rijiya ta janyo ruwa, ta hada kwanukan da ke gindin rijiya ta wanke ta kife su a kwando, ta cika bokiti ta dauraye jikinta. Ina hana ta amma taki ji, cewa take ''wai baki san in naje Tilde, har tatsa nikewa Kakata Danejo ba?'' Ta shirya cikin siket da riga mai dogon hannu kamar kullum, ta nufi dakin Maikalwa suka gaisa Auwal ma yana nan suka shiga hira wadda duka ta Yallabai ce. Buhunan shinkafa, katon na taliya, katon na maggi, garwannin mai, kwandunan kayan miya, buhunan gishirin Dangote, katon na madara, katon na bournvita, buhunan suga da katon na lemun (five- alive). Katon na (tropical and squash juices) duk daga Yallabai a kawowa Baba. Bai shigo ba sai karfe goma na safe. Mallam Mamman, ya rasa ta inda xai sa surukin shi sai ya shimfida masa buxun sallar shi. A wurin shi karshen karramawa kenan da yake yiwa baki masu muhimmanci a gareshi. Shi Yallabai Baba burge shi yake, yadda bai rudewa duk sanda yaxo gaishe shi irinna sauran talakawan Karaye, komi na shi cikin nutsuwa. Ya cika su da kudi duka gidan, babba da yaro. Tom ma ya shigo ya gaida Baba, Inna da Amarya. Washegari yamma lis yaxo, wannan xuwan na gimbiyar ne kenan. A dakin Auwal akayi mai masauki. Tun safe da ya aiko xai xo Amarya bata barmu mun huta ba. An yiwa Yallabai funkason alkama da taushe cikin tantakwashi, ga gudun kurna, alkubus da miyar agushi cikin naman kajin hausa, wainar masar shinkafa da sinasir. A bangaren lemu kunun xaki ne da yaji kayan kamshi,

127.
Lemun citta (ginger) da lamurje (xobo). Salisu ya samo kankara an sa yayi sanyi. Dakin Auwal bai bukatar gyara tunda degree na biyu yake hadawa a Bayero. Hutun karshen mako ke kawo shi Karaye. Duk da haka naje na xuba turaren wuta cikin garwashi mai dadin kamshi. Muna aiki Ashsha na tambayana wai me xata ce da Yallabai yayi hakuri? Sanye nake cikin karamar atamfa Cote D'voire dinkin 'yanmatan Abj ke yayi a lokacin, kalarta ruwan bula ne mai duhu, Ashsha na gaba ina bin ta a baya har dakin Ya Auwal. Yana rike da jug na kuma tambulan mai garai-garai. Yallabai magana yake a waya..'' (Yahai) ka faye damuwa, nace xanxo, yanxu ina Mubinar? A yanxu ina garin mu ne, amma yau xan taho, ka gaya mata Zubaidah da Jawad na gaishe ta in tana amsawa... ''Hardo ta dube ni mukayi murmushi, a raina nace har xa'a shirya kenan. Xa'a hada biko da neman sabon aure, manya kenan! Ya rufe wayar shi duk ya wani wayance, ya san munji yace ina Aunty? ''A'ah Ashsha ke da nace bana gayyatar ki, shine kika biyo mu gayyar sodi?'' ''Ranka ya dade ai don in wanke wancan laifin nawa ne, na baiwa Yusuf kanwata, naxo Karaye musamman don in wa Yallabai campaign ne'' ''tunda haka ne? You are highly welcome to our beloved town, Karaye. Muma in xaki Tilde? Xamu rakaki''. Ya juyo gareni da wani irin rikirkitaccen kallo cikin kwayan idanun sa ''Momin Jawad, jiya Fulani bata yi barci ba, Jawad, ke kiran Momin sa. Ranar da xan cafki Momin, ko yaya xa'ayi da Babyn?'' Sai gani yayi Hardo ta fita babu ko waiwaye. Shaf ya mance da ita a dakin xaune. Ya dinke fuska ''ke ni nace ki kawo kawarki?'' Na tintsire da dariya na dawo kasa ina xuba mai Alkubus, ''an dai yi abin dariya, MANYA sun kwafsa'' ''wannan kamshin da nike ji, tun kafin in kai bakina, nasan Alkubus dinnan xai hadu. In na rage, xaki juyan a flask in tafi dashi in ci a jirgi?'' Nayi dariya kadan ''haba-haba, Oga da flask din abinci, wannan abin kunya da me yayi kama? Kuma ya bude a ga Alkubus, cukusum, babu ko kyawun gani, haba Baban Jawad!''
Chapter 29 · 0% Book details