Sashe 17
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
69.
...shan shi, abinda local yara ke sha ne, na kuma bashi ruwa, na kaishi cikin robar wankan shi na fidda mai pampers, wadda bai yi komai cikin ta ba sai gumi. Nayi mai wanka da wani irin tsadaddan sabulun Babies dana gani cikin kayansa, bayan na xuba duk wani abu da sister tace in xuba. Ina sanya mai kayan sanyi Tom ya shigo dauke da tray, nace ''da ka koma dashi, wannan ya ishe ni sai ko 'dinner' naji kana cewa ko?'' Yayi min tafi ''Yauwa, haka nake so Tine, ka dinga rike duk abinda na fadi cikin turanci, da haka xaka saba. Daga sati masu xuwa, ka daina magana 'in Hausa'. Sati na xagayowa, na soma yara turanci da Tom, ya dinga kunna min labarun BBC, labarun kasa da sauran su, suna yi da babban turanci yana bani bayani cikin sassaukan turanci, rubutu kuwa na iya rubuta su Ant, Ball, Cup. A satinne ta kara tura ni saloon, da wurin gyaran akaifa, don wai taga alaman yakushi a wuyan danta, bayan shi ya yakushi kan sa. Wannan karon da Tom ta tura ni. Wani yammaci bayan ta fita, na gama dirkawa Jawad abinci na goya shi, na tadda Tom da Ejiro a kitchen, suna ta kiciniyar kwabin coconut-sandwitch da beef burger, abin ya burgeni, ya kuma bani sha'awa, ganin komi da inji suke yi, ba wahalar komi sai ta tsayuwa. Nan na xauna kallon su har suka kare. Na tabbatar abin ya xauna a kaina, ko yanxu akace inyi yadda sukayi, xan iya. Daga ranar duk sanda suke girki, in dai Maman Jawad bata nan, sai in goya shi inje in xauna inyi ta kallon su, muna hira ana kara min bayanin komi. Watarana nace da Tom don Allah ya samo min waken suya (soya-bean), ya tambaye ni abinda xan yi dashi nace wani kamu ne muke sha a kauye. Kullum sai inyi kamun waken suya mai tsabta, in shige da shi dakina in kulle, inyi ta durawa Jawad, shiko komi na bashi ya shanye shi tas. Bama bari yayi awanni biyu ban bashi abinci ba da ruwa, ba ruwana da wani kididdige, shiyasa yake yawan fitsari da kashi, in fidda in wanke shi tas, in canxa masa.
70.
Cikin watanni biyu kacal da dawowar shi hannu na yaro ya shiga wata irin kiba da wayo mai ban mamaki. Wani marece Tom yake ce da ni ''Tine ka iya raino mai kyau, hannu ka mai albarka ne. Dubi yadda Babe ya koma daga xuwan shi hannun kam yaro dan siriri ya koma Bouncing Baby''. Washegari ranar naga sun fiddi na'urorin gidan, dukkan ma'aikatan sun kasa xaune, sun kasa tsaye aiki suke cikin kuxari da xafin nama tamkar anayi masu allurar kuxari. Ga wani nishadi na babu gaira babu dalili, tattare da kowannen su. Maman Jawad ta iske ni har daki na tana daga shi da kyar, don wai bata iya daukar shi yanxu kada ya sata ciwon kirji. ''Yau Abban Jawad xai dawo daga tafiyar da yayi Kasar Canada, idan ya nemi Dan sa, ki je ki kai masa, ki tabbatar kin gyara shi sosai, in ya nemeni ki ce ina gidan kwamishina Mansina ce ke fama da mura, amma xan neme shi a waya''. Na amsa da ''to''. Ina sallah, nayi sujjadar karshe ina sadar da bukatu na ga Lillahi, Tom ya shigo, ya xauna ya xauna har ya gaji ya tafi, can kuma ya dawo ''Tine pieous (wato mai Ibadah), ni xani (lecture) sai biyar xan dawo. Mun gama shiryawa Oga Spanish-Lunch, idan xai ga Jawad xai neme ki da kansa, ba ruwan shi da matsantawa irin na Aunty''. Na rungume Jawad a kafaduna da ya soma kokarin tashi daga barci nace ''yauwa! Dama tuntuni ina so na tambaye ka Tom, tun da nake, ban san dan aiki yana da 'yancin xuwa makaranta ba, har ya fita sanda yake so, ya dawo sanda ya ga dama? Imagine!'' Ya kyalkyale da dariya sosai yace ''Ogan mu, mutum ne da baya dannewa dan Adam hakkin sa ko kadan. Mutum ne mai masifaffen ilmin boko. Ba kowadanne iyayen gida bane irin Ogana ba. Bai xama da wanda bai ilmi, shi ba maxauni bane haka matar shi da muke xamanta bata faya xama ba. Mu biyar ne duk maxa, ita ta kawo mu ba shi ba, amma yace lallai tunda munyi sakandire, mu tafi makaranta. Xama a karkashinsa baya nufin bamu da 'yancin sauran abubuwa masu muhimmanci a rayuwar bil adam musamman ilmi.
[10/7, 7:08 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/8, 5:11 PM] A A Dboy: Tuna Baya 71-75
71
Ni da Ejiro, muke kuku, don haka muke karantar catering, Peter da Joseph da ke kula da gida, tattalin gida suke karanta, Samson da ke kula da shukoki yana karantar ilmin tsirrai (Botany) a Jami'ar Abuja. In daya nada darasi, daya baya dashi, xai yi aikin gida kamin daya ya dawo koda ba aikin sa bane, wanda yawanci, mu ke cinye abinda muka dafa domin ita bata cin abinda ya hau wuta, sai na gongoni. Shi kuma Oga, asalin shi kauye, bai son wanna tsarin, in yana nan xai bamu odan muyi masa tuwon semovita miyan danyen kubewa da busashshen kifi, yace kunun aya yace kunu xaki. Wallahi idan kinga abinda yake ci, sai ki raina mishi. Matsayin shi; Minister of Foreign Affairs, (Ministan huldar Nijeriya da kasashen waje). Sun yi artabu da Aunty akan xuwan ki, domin a da, Peter ne yake mata dukkan ayyukan da kike yi, Oga yace bai lamunta ba, katon na miji ya dinga mata hidima, ya gayawa mahaifiyar shi cewa a sama mata 'yar aiki mace, kuma karamar yarinyam haka sunyi artabu akan cewa da yayi ke ki dinga kula da Jawad, tunda ta dage baxata bar aikin ta kan rainon yaro ba, domin Aunty ta dauko raino daga Brussel can cikin kasar Belgium (Elizabeth) da xai rika biyan ta tsabar kudin Amurka dubu dari da hamsin a kowanne wata, shi kuma ya dage, wanda ba dan AREWA ba, ba kuma dan masarautar sa KARAYE
72.
KARAYE ba, baxai rainon mashi dan jinjirin shi a duniya ba. Ita tana ganin Bahaushe kaxami ne, sai kace ita ba bahaushiyar bane. ('Yar asalin garin Xaria ce). Ki saki jikin ki da Oga mutum ne mai saukin kai, xaki ji dadin xama dashi fiye da Aunty, domin suna tare ne amma halin su daban-daban. Sai dai kada kiyi mata abinda bata so ko kadan, xata ci miki mutunci daga ke har shi, don bata darajashi sam. Talaka da dabba a wurin Aunty basu da maraba balle kuma dan aikin ta. In kinga yadda shi kuma yake jan mu a jiki, yana jin damuwar mu, kamar kannen shi da suka fito ciki daya, wadanda ta haramta masu xuwa gidannan sam, kiyi taka tsan-tsan da Aunty, ''bata da mutunci''.
Ya fada ya kara maimaitawa har sau uku, domin kara tsoratar dani ga kowace ce Uwargijiyata (Aunty Mubina). Bayan tafiyar Tom, na dade ina sake-sake, gami da jinjina abinda na ji a raina, ba a jima ba naji dirin ribda-ribdan motoci, na dau Jawad cikin nustuwa nayi mai wanka na fiddo sabbin kayan shi da ban taba sa mishi ba na kakin sojoji, na saka mashi, na xura mai sabon takalmin shi, rufaffe sak dana sojoji mahadin kayan, na taje yalwatacciyar sumar shi na mulke ta da mai mai kamshi, sai kyalli take ta kwanta lub a dokin wuyan shi. Na dauko turarukan shi Dune da Caleutta na feshe shi sosai. Na dura mai kamu na goge mai baki, na bashi ruwa yasha ya koshi yayi gyatsa, ga yadda yake mun rigima nasan so yake in goya shi yadda na sabar mashi bayan cin abinci. To amma ta yaya xan goya shin? Uwarsa ta hana balle Uban sa? Na sashi a kafaduna nayi ta jijjiga shi amma yaki yin shiru, kuka harda digon hawaye. Ejiro ya shigo ''A'ah Jawad kuka kake, why? Papa ya dawo'' ya karbe shi ''Nanny Tine, Oga wanna see his son, gashi yana kuka'' nace ''goyon da nake mai yake so, gashi bana son su san ina goya shi, kai dai kai shi hakan, watakila in ya ga Uban yayi shiru''. (An dan jima Ejiro ya dawo) ''kixo ki goya shi yace''. Gabana ya fadi dam! Xuciyata ta tsinke, na fiddo 'yan idanuwana hantar cikina na murdawa, muryata abun tausayi nace ''Haba Ejiro? Meyasa kace ina goya shi? Idan ya gayawa Aunty fa?'' Ejiro ya kyalkkyale da dariya, yayi mai isarsa ya gaji ''Tine, Oga ke biyan ki ba Aunty ba, shi yace kiyiwa Jawad rainon AREWA, shima dan garin ku ne ya san goyo. Shi da kansa yace in kiraki, ki goya Jawad yayi barci. Ya kuma tambaye ki, me kike ba Jawad yayi girma mai ban mamaki cikin watanni biyu da yayi bai ganshi ba?'' Gabana tamkar ana luguden kirjina, doguwar rigar jeans ce a jikina mai kauri, cikin kayan da aka sai min babu kallabi balle mayafi, sai na dauki tawul dina da ke toilet na yafa, Ejiro na gabana ina binshi xungul-xungul kamar wanda...,