Sashe 19
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
77.
Tayi dakin ta bayan ta dangwarar da Dan da duwawun shi a dandaryar carpet, ya saki wani irin rudadden kuka. Gabadaya muka kai gareshi, ni da Yallabai, nayi sa'a na riga shi dauke shi. Yace ''ki je ki lallashe shi, xani 'meeting' Lagos. Idan na dawo xan kawo miki wani irin madaran da ake baiwa yaro in ya shiga wata shidda. Ki kular min da Jawad, ni kuma XAN KULA DA KE!'' Da yadda yake maganar, na fahimci ran shi a masifar bace yake. A daki na rungumi Jawad, a raina nace lallai ma wannan matar, ita bata san ita mummuna bace, Allah ya bata miji mai kyau take sakarci. Allah yasa kada wankin hula ya kaita dare. Ni kadai na ke gayawa kaina. Tom ya dawo muka koma karatu. A watanni na biyar da fara rainon Jawad, xama da su Tom, duk xancen su turanci ne, yau da gobe tafi karfin wasa, na soma iya rubutu da karatun turanci. Tom ya kara dagewa da kawo min littafan da xasu taimaka wurin koyar da ni sosai. Har ya xamanto in xai fita ya samu ina barci, ko sallah, sai ya bar min note a takarda. Xamana a kicin tare da su kullum, yasa na kware a irin girke-girken xamani da suke yi, da amfani da na'urorin saukaka ma dan adam wahala. Wata yammacin Litinin nace ''Tom, yau girkin gidan mu nake so in ci, ko xaka taimaka ka samo min kuka, daddawa, citta da garin tuwo?'' ''Muna dai da garin semovita, tun wani tafiya da Oga yayi British yasa na sayo, muna da citta, daddawa ne baxa a samu ba. Amma xan bada sako in xa'ayo cefanen wata, ko a cikin Neja xa'a samu''. Muna maganar ne da turancin broken dana soma koyo. Shiko Ejiro dariya yake mana. Ya kawo kayan girki na tayar da ruwan miya, da kayan hadi sosai. '' A dafa damu inji Tom. Sai na kara ruwan miya. A can gefe na dauki dakwalen xabi guda uku daga cikin freezer, na wanke su na xuba a wata tukunyar dabam na dora bisa cooker, na wadata su da albasa domin kashe karni, na daka kayan kamshin hausa cikin blender na xuba gishiri kadan, sai maggin knoor, babu kayan kamshin bature ko dis.
78.
Xabbi suka soma tafasa, duk gidan ya kauraye da wani bala'in kamshi. Na maido ruwan miyar cikin xabbin, na kada kuka akai, ta kadu, babu gudaji ko daya, na rufe ya dahu-ya-dahu yayi lugub, har tsokar ta salibe da kanta, nasa wani irin ludayi mai yatsu na xare kasusuwan tas. Tafasashshen ruwan banyi talge da garin semovitan ba, sabida kada yayi laushi da yawa, sai na xuba shi a haka, can anjima nasa muciya na tuke shi tsaf, daya kammalu na kwashe na rabe mana mu uku na xuba nawa a warmer da niyyar sai nayi wanka xan ci, Tom ya daura abincin dare kaman yadda ya saba. Dirin motocin da muka ji ba daya ba, ba biyu ba, mun san maigidan ne ya dawo unexpected. Bayan ya gama da mutanen kasa ya iso sassan mu. Su Tom suka je suka kwashi gaisuwa.Ya tsaya falon Aunty ''ku ina matar gidannan? Karfe shidda har da kwata yanxu, ba biyar take dawowa ba?'' Tom yayi shiru Ejiro ya sunkuyar da kai, ya kuta yace ''ina Jawad?'' ''Yana can dakin mai rainon sa''. Samson ya shigo da katon din madara ya umarce shi da ya kaiwa mai raino, ya kuma ce ta kawo Jawad. Ya dubi Tom ''na kwaso yunwa, tun safe muna ofis din Governon Lagos, sun bani cake ne da lemu kawai, ina fatan ka kare abinci?'' Tom ya kara nutsuwa ''Oga ban san da xuwan ka ba, xan iya hada emergency sai dai...'' yayi shiru. ''Sai dai me?'' ''Eh to,tuwo ne mai rainon Jawad tayi, muka ci. A yadda nasan bakin Oga na, Ba-Hausa ne, nasan xai iya ci. Domin yafi wanda nake wa Oga yana sa mun albarka.'' Yayi murmushi, ''naga alama kun xama wasu too- close da yarinyar nan, to a kawon xan ci, in ka tabbatar da tsaftar ta''. Oga, Tine in ban ce ta fini kula da tsaftar abinci ba a yayin girki, ba xan ce na fita ba!'' Sai ya sake murmusawa, dai-dai lokacin da wayar shi tayi kara, ya fiddo ta daga aljihun ba tare da duba sunan mai kiran ba, ya kara a kunnen sa, ''...wannan kuma ruwan ki ne. Ki cigaba da yi mun duk abinda kika ga dama, watarana da sadaka akace kimin wulakanci wallahi baxakiyi ba, an ce miki na damu ne?
79.
Ko ki dawo, ko ki kwana wurin watsewar ki, Taheer, na tuno ki yanxu ma don inga lafiyar yaro na naxo, in sallami ma'aikatana da albashin su da yake kaina. Jibi xan koma Canada, sai kin ganni sannan kiyi mun wulakanci, Mansinar kin banxa? Har ciwon Mansina yafi lalurar mijin ki, hakkin sa na wata da watanni, jaririn ki...idiot, stupid, nonsense...!'' Tuni Tom ya kama gaban sa. Yana huci bisa 'dining- table' ya aje abincin ya koma ya dauko lemun Yallabai (prime-lady) da tambulan ya aje ya fita. ''Tine, maxa gyara Babe din ki, Babansa na son ganin sa'' ''an ce ma sai Baban sa na nan, nake gyara shi? Dama a gyaren yake, awan sa daya da wanka, amma bari a sake sabo''. Ya fita yana dariya. Dinkakkiyar babbar rigar Voyel ce a jikina sa fatalar ta na daura, kalar su maroon, nasa Jawad a bayana na goya, nayi sallama na taras abinci yake ci. Ko kadan ban kawo tuwo na bane. Sai na juya da nufin in ya kammala na dawo mai da Dan sa. ''Yaki Maman Jawad, sauko shi'' na sauko shi na matsa na mika mai dan sa, ya rungume shi yana sunsunar shi. Ya lumshe ido a hankali, tsayin mintuna biyu bai bude su ba. Can ya dago idon shi jajur kaman wanda yayi kuka. ''Xan roke ki wata alfarma. Nasan aikin ki shine raino, amma xaki dinga dafa mun abinci a duk sanda nike nan Abuja. Ni cimata ta kauye ce. Su Tom basu yi mun mai gamsar da ni. A yau wanda kika yi mun irin na BABATA NE, xan ninka albashin da nike bawa iyayenki, daga goma xuwa talatin, kin amince?'' ''Ranka ya dade, ni wannan ba wani abun wahala bane, ba sai ka karawa Babana kudi ba. Ina tabbatar maka wanda kake bashi, ya ishe shi shida iyalinshi, na roke ka kada ka karawa Babana kudi''. Shiru yayi kawai yana kallona, ''ke, xan kai ki makaranta. Gobe in shaa Allah, kina da hankali na lura, kina so?'' ''Ina so mana'' ''shi kenan jeki, ga madaran da nace miki xa'a kawo miki, ki xuba ruwan dumi (2 litres) kullum a fidar sau uku a rana, kada ki rage kada ki kara, wannan ba'a mata karambani...,
...don naji Tom yace kina da kankanba, kuma ki cigaba da bashi dukk abinda kike bashi. Kada ki kara kawo shi wurin Uwar shi wai ta bashi nono, in tace don me? Ki ce nine na hana. In ta takura, ki kyaleta. Tashi ki tafi, kiyi shirin makaranta gobe. Anjima xa'a kawo miki duk kayan makaranta''.
80.
Na mike gwiwoyi na a sage, xuciyata a wanke fes, da murnar xani makaranta. To gudan raina MUHAMMAD JAWAD, an yi mai yayen kwara. Mai kula da shi din wato ni, ance makaranta xani. Na san kuma ba'a xuwa makaranta da kananan yara. A wani bangaren, yaya xanyi da bala'in Aunty Mubina? Dama tace mun wai, tarani take. Ta hana ni sa xani, na roki mijin ta ya dinka mun, ta ji kuma yace na ba dan ta ruwa, tun bai kai wata shidda ba. Kuma taji daga bakin munafikin ta (Peter) ina bashi wake. Sanna tace in bata danta ta bashi nono, ince a'ah, Da na ne? ''Atine, a kan umurnin wa kike? Mai gida, wanda ke biyan iyayen ki, tayi miki koma me xata yi miki, ai dai baxata kashe ki ba, bata isa ba kuma ta kore ki ba, tunda ba ita ta kawo kiba, ba kuma ita ke biyan ki ba, sannan ba xaman ta kike ba, to shin don me xaki damu da ita? Ai gara a kyautatawa wanda ke kyautatawa!'' Washegari na dage na xabga tuwon semovita, miyar danyen kubewa da ribdediyar kaxa a ciki. Na hada lemun xobo da kayan kamshi masu wartsake makoshi, na xuba flavor vanilla, nasa a firji don yayi dan sanyi. Tun safe Tom ya markada ayar kunun dana jika tun daren jiya, mai kyan 'yar Katsina. Nayi kyakkyawa kuma tsaftataccen kunun Aya, Tom ya diba ya kai matsayin karin kumalli. 'Yar boko, tun 7:30 ta fice aikin ta. Nayi wanka, na kasa shiryawa sai nasa kuka, ina makale da shi shima yayi lamo, a kafaduna. Sallamar Baban Jawad na ji ba xato. Ya shigo tare da Ejiro. Ya jingina da bangon dakin hannuwan shi duka biyun harde bisa kirjin shi. Kallo yake mana cike da sha'awa ''Maman Jawad, bakya son school, kuma dole kije. Bana xama da JAHILI duk wani wanda ya rabe ni ko JINI NA ne, koba Jini na ba dole ya nema ilmi''.
[10/8, 5:19 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/8, 5:23 PM] A A Dboy: Tuna Baya 81-85