Sashe 22
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
89.
Na kyalkyale da dariya ''menene kuma thank u Daddy?'' ''Ba ke kika fada ba daxun?'' Ya maida duba ga Uban a shagwabe ''Dad! Amma baxa a bawa wannan matar ta can dakin ba ko? Bana sonta! Daxu baka nan ta dalla min mari, wai don kawai naki ta daukeni, ko Momi na ai kina gani ko?'' Na sunkuyar da kai ban ce komi ba ''ki amsa masa ZUBAIDAH, anything it's, yaro baya son yayi tambaya ba'a amsa ba''. Sai na dago a hankali na dubi Jawad da dukkan idanu, cikin murya mai nuna kashedi da tsananin tsoratarwa ga yaro karami. ''A'ah, xa'a bata, itama Momin ka ce ita ta haife ka ni na raine ka ni 'second Mominka' ce. Jawad, kai ne ka cije ta kayi rashin kunya, ba'a cixon babba. Daddyn ka yace ''idan kayi wa babba rashin kunya, baxai kaika 'Military School' ba (baxai kai ka soja ba)''. Sai ya kwanto a kirji na, yana wasa da sarkar wuya na. Bai ce komi ba. Abban shi yayi mana sai da safe ya fita, ya ja mana kofar.
*************
Aisha Ibrahim Hardo, tun xuwana Nurul-Bayan ta ke kaunata, seat dinta na bayan nawa.
Kasancewa ta kwararriya a darasin turanci ni ce wakiliyar ajin mu. Aisha 'yar wani kusa ce a Abuja, suna xaune a Wuse Zone 6, Aisha bata son ace mata Aisha wai sai 'Ashsha', don tsabar son burgewa. Ni kuwa Allah ya daura mata kaunata kamar me. Tayi ta shishshige min niko taka-tsan-tsan nike dasu, don sanin ni ba 'yar kowan-kowa bace a Abuja. Har kullum maganar Goggo na tana nan tana min yawo a kwanya ''duk wata daukaka da kika samu a duniya kada ki boye Babanki Mai-Kalwa ne'' don haka da shishshigin Ashsha ya yi yawa, nace mata ''Goggo na, nifa ba tsararki bace, ni ba 'yar kowan-kowa bace, RAINO ne ya iso dani NURUL- BAYAN, mu 'yan Kauyene a can wata Karamar Hukuma a Kano, Karaye. Yallabai da kike xaton Yayana ne, UBANGIDA na ne''.
90.
''Zubaidah, kina bani dariya, to waye ba asalinshi Kauye ba? Mu ma asalinmu Kauyen Jama'are can cikin Jihar Bauchi, rugar Kakana Hardon Fulani a can yake, sai dai kawai don ban isa bane? Don nasan bani da kyawun da xan jere, a matsayin kawarki''. Baki na bude hangangan cikin mamaki, ''kiyi hakuri Ashsha ba haka nake nufi ba, kuma tunda kin ce haka shikenan''. Daga ranar muka xama wasu irin aminai, duk inda Ashsha Hardo take, kaga Zubaidah Karaye. Malaman mu da abokan karatun mu, duka sun san mu tare. Rannan Ashsha tace wai xata xo gidanmu su gaisa da Jawad Babe, nace mata Jawad bai son baki, amma bata yarda ba tace wai bana son ta je ne. Da yamma lis, wurin karfe shidda, Aunty Mubina tayi parking Volswagen-Bettle dinta, Ashsha ma tayi parking (Volswagen) amma ba (Bettle) ba. Bata ko gaida Aunty ba domin ita yarinya ce mai jin kanta; Ubanta (Commisionern kudi, uwarta Ministan Mata), kanta tsaye ta tura kai cikin gidan. Tom da Ejiro sukayi mata kyakkyawar tarba, Jawad da nake shayi, shima yayi mata murmushi yace (I've been hearing alot about u) Aunty Ashsha, naji dadin ganinki''. Ashsha taji dadi, ta fito sayayyar da tayi mashi kayan ciye-ciye da lashe-lashe masu bala'in tsada. A daki na muka sha hira, ta tambayi Yallabai na sanar da ita yana Canada. Tace Uwar Jawad fa? Nace lokacin tasowar ta yayi, da kyar ma in bata shigo ba. Ta xaro ido ''ba dai wannan mai nanannen hancin da mirimirin idanu da gajarta uwa an kife kwarya ba? Data gani a shigen motarta?'' Na ce ''ki rufa min asiri, ki ceci mutunci na, ta ganki?'' ''Ta gan ni mana! Ko kulata na yi? Ni na dauka bakuwarta ce''. Gabana ya fadi, ni kuma na san yau sai yadda Allah yayi da ni ''ba yawo, ba kawa, ba kaxanta sune ka'idodina''. Ita kanta Ashsha ta lura tayi min ba dai-dai ba. Ta yi shirin tafiya tace in yi hakuri, daga yau baxa ta sake xuwa ba.
[10/8, 5:24 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/8, 5:25 PM] A A Dboy: Tuna Baya 91-95
91.
Na lura ranta ya baci, na kamo hannun ta na xaunar da ita, nayi mata bayanin yadda muke da Aunty Mubina dalla-dalla, Bata san ina xuwa makaranta ba kuma ba'a son ta sani, don haka xata yi tunanin ina na samo Kawa? Ni da a tsammanin, ko makota bana xuwa? Ashsha ta fahimceni sosai, tace xata fiddani in nuna mata sassanta. Ban san me ta gaya mata ba, sai gani nayi wai har ta rakota kofar sassanta. Bayan tafiyarta Aunty ta kirawoni, wai wannan bakuwar 'yar garin su Tom ce, taxo ganinshi daga America take, tana son sayen share a Bankin su Omega ta hanyar ta, xata kawo wasu takardu in ajiye mata. Mun hadu da Ashsha, washegari a class, nayi dariya har cikina ya kulle itama hakan. Ta rubuta 'short note' tace in bata. ''Aunty, kiyi hakuri don Allah, munyi magana da Babana, yace Omega bai mishi ba, mun saya da Allied Bank, don haka baxan dawo ba. Ashsha Hardo. Da na ba Aunty, ta buga tsaki, ta runduma mata ashar, nima duran xagi tayi, ba girma ba arxiki na kama gabana. Wata rana muna hira da Ashsha a dai-dai (Biology Practical Room) ta ce ''wai Zubaidah mai yasa bakya kwalliya ne?'' ''Kwalliya fa kika ce Ashsha, me yayi ruwan 'YAR RAINO DA KWALLIYA? Kin gan ni, daga wanka, man shafawa mai tsada da Abban Jawad ya aje mani katon daga Lisbon sai farar 'powder' ko kwalli ban sawa''.
92.
''Zubaidah don kina 'yar raino, wannan baxai hana ki yin kwalliya ba. Ke kyakkyawace, kin cika mace a fannin komi, ki dibeni ba abinda xan nuna miki ta fannin kyawun halitta, amma sau nawa xam yi samari ke baki da ko daya? Ba kuma komi bane illa rashin gyara irin wanda maxan yanxu ke so a jikin mace. Ki daina wulakanta kanki. Ki dinga jin kanki 'YA MAI 'YANCI tamkar yadda Ubangidan ku ke so kuyi. Ki dubi Tom, motocin da yake shiga, baya nuna cewa shi kuku ne, sai ke? Wallhi ki yi kwalliya ki gyara jikinki, ki ga abin mamaki cikin Abuja''. ''An ce maki ina da ra'ayin soyayyah? Samari basu dame ni ba Ashsha, na taba yin soyayya can baya wadda ta wargaxa min farin cikin rayuwa. Ban kara marmarin soyayyah ba har yau! Ba kuma na fatan xan yi ta nan gaba. Ko xanyi aure sai don cika sunnar Ma'aiki, amma namiji daya ne, na taba so, na so da dukkan ruhina. Ba kuma xan iya kara son wani tamkar shi ba. Don kada ki ce na ki shawar ki, daga yau xan dinga kwalliya!'' a karshen hutunmu, wanda daga shi in mun dawo, xamu xana 'final papers'. Wata rana Ashsha ta fiddo wasu irin cleansers 'yan Humburgh, wai cikin tsarabar 'Fiance' dinta Alphat daya dawo New- Orleans in da yake karatu. Sai kuma wani da ta ce min a nan ta saya mai tsadar gaske, wai in dinga amfani dasu safe, rana da dare bayan wanka, xasu bada wata irin kala ga bakar mace. A raina nace ''oh, ashe abinda kike yi kenan kalarki kamar matan Morocco, na cigaba, yadda ta koya mani, hakanan duk dinkin da akayi mata a gida, irin shi xata kawo mani dinkin, kalar har komai. Daukana ta yi bayan mun tashi makaranta, ta kaini wani katafaren shago nasu na 'ya'yan gata ('N' park shopping complex). Kayan kwalliya na 'ya'yan hutu, ba wanda Ashsha bata sai min ba, turaruka, jambaki da mayukan gyaran gashi harda 'hand- dryer' ta ce ''ke kanki xaki ji dadi a jikin ki, ki ga kinyi kyau, kina kamshi mai dadi''.
93.
Ashsha na masifan son Alphat, dan wani kusa ne aminin Babanta, dake karatu Jami'ar Grosslow ta New Orleans. Duk cikin masoyanta ba wanda tafi yi min xancenshi kaman Alphat Rumah. 'Yan asalin garin Rumah ta Juhar Katsina. Ni ma ina son in ganshi, in ga wanda ya haye kan Jewel in the Savannah tamkar, Ashsha Hardo. To yau da albishir din xuwan sa yi mata week-end ta xo mani, kuma wai lallai in bita mu je can gidan su mu gaisa koda Uniform ne shi ba ruwansa, sai ta maido ni kamin karfe hudu, gidan su Ashsha ba abinda ya dauki hankali na kamar yadda nayi xato don bai kai gidan Yallabai komi ba, sai (swimming- pool) da babu gidan Yallabai. Sai karfe uku ya xo, ni ban ga abin son ba wallahi ban da dai ance shan koko daukan rai. Irin sakarkarun 'ya'yan masu hannu da shunin nan ne kawai, shi kansa bai kama kansa ba, balle ya kama aure, tare da wani abokin sa, da alama abokin yafi nutsuwa, muka gaisa, sabanin Rumah din da tashi gaisuwar ga masoyiyar sa ta nuna min babu tarbiyya cikin al'amarinsa, ko da yake a wurin su wannan ba komi bane, wayewar ce. A gurguje mukayi hirar don hankali na yayi kan Jawad da dawowar Aunty, har kofar gida suka kawo ni bayan sun cikani da tsarabar sittiru cikin wanda suka kawowa Ashsha, da faya-fayan music wanda ni sam ba harka ta bace. Na tarar Jawad yayi kuka ya gaji, su Tom sai aikin rarrashi suke yana dukansu da kafa da kutufo, nayi kiranshi cikin kakkausar murya ''Jawad! Uncle kake bugu, sai na gayawa Daddy, wato in yana nan ne kake dan kirki, in ya tafi mai rashin kunya ko? Ka tuna yace ''Idan kayiwa babba rashin kunya, baxai kai ka Military School ba, (ba xai kaika Soja ba)''.