Sashe 26
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
109
Addinin Musulunci ya sanar damu cewa idan ma'aurata suka doshi akalla watanni ukku, basu kusanci junansu ba, haka kawai, ba wani dalili, to sai an gyara auren, domin kamar ba aure ne tsakaninsu. A bar wannan xancen, don ni bai dameni ba, ba shine a gaba na ba. Maganar da kika yi, na wadda kika kira, Black! Wadda ainihin sunan da Ubanta ya rada mata , ZUBAIDAH! Kin yi gaskiya, akwai abin dubawa a ciki. Dama na dade ina tunanin abin, don haka ne gwanda da kika tunasar da ni. Zubaidah ta isa aure kwarai, shekaranjiya dana lissafa ya kama nan da wata uku xata cika shekaru ashirin da daya. Ta xo mana nan shekarunta goma sha uku, na kai ta Primary tayi shekaru biyu ta xarce babbar makaranta daga aji biyu (JSS 2), a yanxu tana shekarta na karshe. Bai fi wata uku ba xata xana (Secondary School Certificate) din ta. Allah ya bata mijin aure tuni, da ta kammala xan shirya masu birthday a can KARAYE, ita shekara 21 Jawad 'seven'. Idan xaki muna maraba da ke. Harma kawar ki, data fi mijinki muhimmanci a gareki, MANSEENAH IBRAHEEM HARDO. Xancen su Tom, kada su lalatata! Allah ya kare, wannan yarinya mai sanin darajar kanta, addininta, iyayenta, mutuncin ta na talaka, wanda bai aje ba bai ba kowa ajiya ba.
110.
Ta yarda ta saida mutuncinta ga KIRISTOCI, tayi shiru bata gaya min ba. Kuma in gaya maki gaskiya, yaran nan baxa su taba cin amanata ba... Suna kaunata, kaunar dake bakya mini, suna kula dani, kulawar da ke bakya mani, suna kyautata mani, kyautatawar da ban samu daga gareki ba. Suna kaunar Da na, da bani da kamarsa a duniya. Don haka nima bani da kamarsu, baxan taba xargin su da abinda xuciyarki ke tunani ba. Ba don kudina suke xaune dani ba, sai don na nuna masu suma suna da 'YANCIN KANSU, talaka nada 'yanci a gidan mai kudi, 'yancin da xaiyi abinda yaga dama, daga cin abinda yake so xuwa amfani da motocin sa, kwana a gidansa shiga dakinsa, ba tare da wani kyama ba. Na nuna masu everybody have right to education. Ba sai dan wane ba, ba sai wanda Uban sa yake wane a Abuja ba. Don haka baxa su taba xalintata ba. Baki san wani abu bane, wani kiristan yafi wani musulmin tsoron Allah. Yafi wani musulmin rikon amana. Tom, tamkar Uba yake ga Zubaidah.
[10/15, 9:14 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/15, 9:15 AM] A A Dboy: Tuna Baya 111-115
111.
Shi ya koyar da ita A,B,C,D, ya koya mata yadda xatayi rayuwa cikin masu kudi, yadda xatayi magana cikin turanci tamkarsu, yaya xa'ayi ya nemeta? Yaya xa'ayi ya bari wani cikinsu ya bata ta, bai gaya min ba kada ki karayin wannan tunanin game da bayin Allahn nan, domin kin masu KAXAFI. Dole Zubaidah ranar da ta kammala makaranta, ranar xan sadata ga iyayenta, tare da mijin aurenta amma yanxu tunda kince kin lura tana son gaini iyayenta, karshen satinnan xan kaita ta gansu, ta dawo ta kammala jarrabawar sai ta koma ga iyayenta suyi mata aure. To amma Mubina? YAYA XAMU YI DA JAWAD? XAMU BARWA MIJINTA NE, KOKO XAMU KYALESHI, KEWARTA TA KASHE SHI, KO RASHINTA YA SANYA MISHI CUTAR DA BAMU DA MAGANI? IN GAYA MAKI GASKIYA BAXAI IYA RAYUWA BA TARE DA ITA BA! Itace wacce;
- Ta rungume shi, a yayin da Uwar shi ta dangwarar da shi a dandaryar kasa, ta rungume shi a kirjin ta mai ni'ima.
- Ta bashi madara, a yayin da Uwar sa ta hana shi nono.
- Ta xauna dashi, a yayin da Uwar shi ke gantali. - Ta bashi ruwa, a yayin da Uwar shi tace wai kada a bashi ruwa.
- Ta goya shi ta rarrashe, a yayin da Uwar shi ke ganin GOYO XUBEWAR AJI NE.
- Ta wanke mishi kashi da fitsari da tumbudi, a yayin da Uwar shi ke ganin KAXANTA NE.
- Ta bashi dumin jikinta na Uwa, wanda yafi komi dadi da muhummanci ga yaro, a yayin da Uwar shi bata da lokacin wannan.
- Tayi mai murmushin Uwa, amsa tambayoyin yarinta, ba gaxawa ba hantara. Shin ya xa'ayi ba xai so kasancewa da ita har abada ba?
- She is some1 who knows all his needs, his hopes, his dreams and desires.
- With a genuine interest in all that he do, some1 who guides him and inspires.
- Her smile to him is loving and tendered. By her maternal understanding and gentleness too, makes his life more rich and complete.
- She is full of true wisdom and strength to loveliness, insight and grace.
- She is some1 whose love he will cherish forever!
112.
Amma ta yaya wai xaki ce yanxu xaki kula dashi? Kuma ya yarda da ke, bayan ya sha gaya mana BAYA SON KI! Waccan matar yake ce miki. Yarinyar nan, na kokarin ta wurin fahimtar dashi ke ce Uwarsa! Ita 'yar Raino ce. Bata taba boye masa ba dai-dai da rana daya. Don haka? Wanda yayi wa jininka wannan abu? Akan wasu 'yan kudi kalilan, da bai ma taba karba da hannunsa ba, bai tabbatar ba, ana bashi ko ba'a bashi? Me kike ganin Uban yaron nan xai mishi, ya biya shi, yayi mishi karimci fiye da wanda yayi mishi? Motar banxa! Mubina na barki da wannan, barci xanyi, kada ki sake ki rabe ni bana so!''.
Ya juya, yayi kwanciyarsa. Ta dade a xaune tana jera kuka mai tsuma xuciyar miji. Amma mijin ko gexau. Ta mike ta kunna fitilar dakin, dakin ya gauraye da haske. Ta dafa kirjinta da hannunta na dama, idanuwanta cike taf da hawaye, ta soma magana; Taheer dan Usman, dan Sarkin Karaye! Akan mai yalayen hakora, mai kafa kamar ta shanshani, dadiron ka mai rainon ka, ka wulakanta ni, ka manta alkhairin da Ubana yayi maka.
113.
Daga dan Kauye ya kai ka makaranta, ya maida ka dan birni. Daga Dan Sarkin Kauye ka koma shugaba a Ministry of Foreign Affairs, amma sakamakon ka; wulakanta da toxarta 'yar da baya da kamarta. Ba sai ka tsaya kwana-kwana ba, kwana-kwana ai na kananan maxaje ne, wadanda matansu suka fi karfin su, kai ko nasan namiji ne, dan Sarki jikan Sarki, mai ji da kansa da ilminsa, amma ka tsaya rabe-rabe? Ai kawai kace xaka auri 'YAR RAINO, tir! GIRMA YA FADI! (sunan littafin Takori mai xuwa), koda yake dama tuntuni ya fadin, don daga ganin yarinyar nan tana shining tana haske tana cika, nasan an saba holewa. To ni Mubina, 'yar Balarabe Dango! Idan har na haifu cikin Uwata da Ubana... Baxa ka auri yarinyar nan ba. Koda hakan na nufin xamu koma yawo cikin bante da dako ni da iyayena, baxa ka aureta ba! Sai na salwanta rayuwar ta, na kakkarya kafafun shegiya, na munana fuskar tsinanniya, na maida ta NAMIJI. Namiji sai ya auri namiji kenan''. Yallabai ya mike, tana gab da kaiwa bakin kofa, ya fincikota ta fado tsakiyar dakin ''ai gara a baki garanbawul din tafiya mayar da ita namijin, idan ke kika halicce ta''. Ya figo belt, tafkeke cike da karafa, ya soma shimfida mata tana ihu tana kara maimaitawa sai ta maida 'Black' NAMIJI. Ya yada 'belt', bayan ya tabbatar yayi mata ligi-ligi, bakin ya kumbura suntum, jiki yayi birda-birda da karfe. ''Bari in baki guarantee na tafiya Xangon-Kataf, kije na sakeki saki daya. Saboda mutuncin rainon Jawad, wata tara da nakudar haifeshi. Da kuma karamcin Balarabe Dango.
114.
Gobe inji an sallameni daga kujerata, karewa kenan dama baso nake ba, asiri akai min to Dango kije ku cigaba. 'Yar raino kuma da kike ambato KAMAR NA AURETA NA GAMA. Kin san kakan holewa? To har shege mun haife mun kai KARAYE. Ranar duk da kika xo kofar gidana, sai nasa an yanke maki wadannan kafafun masu kama da tabarya! Ranar duk da naji wani abu ya samu 'yar mutane, sai kin kwanta a kiri-kiri... '' Yana fadi yana ball da ita, har iyakan falonshi. Kwana uku suka shude, ba mu sa Yallabai a idonmu ba, hankulan mu sun tashi ainun. A na hudunne ya nemi Tom, a waya ya sanar dashi yana nan lafiya. Yana hotel din Sharaton, yana samun hutu, sabida baki masu xuwa suna damunshi. Ejiro ke kyankyasa mana, wai yana tsammanin Oga ya saki Aunty, bayan ya dankara mata dan banxan duka. Domin jiya General Balarabe Dango, yaxo neman shi a rude, shi Ejiron ya samu inda shi kuma ya bayyana mishi basu san inda Oga ya tafi ba, kwana biyu. Kuma ya ga kannenta su Mami da Yayan ta Yahai sun xo daukar wasu akwatunan ta. Hankali na ya tashi ainun, na shige daki nayi ta kuka. Bawai tausayin Jawad nake ba. Na san a kowanne hali Ubanshi xai kula dashi. Amma ni na xamo annoba kenan? Ni ma tabbas ya gano wadda ta fini son Jawad din, ya dankara min duka ya sakeni. Allah yaso dama ban amsaba. Na shiga hada kayana tsaf, xaman me xanyi? Gida ba mace? Ba mai gidan? Dama cikin hutu nake. Nayiwa Jawad wayo na turashi kitchen wajen Ejiro, na hada kan kudadena masu yawa, wadanda yawanci irin wadanda Yallabai ke bamu ne, in xaiyi tafiya. Bana sayen komi, tunda bamu rasa komin ba. Dama ance ajiya maganin watarana. Sun tasamma naira dubu tamanin (N80,000), akwatuna biyu kawai na diba. Na kai su waje da dai-dai da kyar. Nace direban da ke kaimu makaranta ya kaini gidan Kwamishina Ibraheem Hardo.