← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 54

Sashe 52

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

118...
Yallabai ne kwance falon mu na birnin London ana i'gobe zamu tafi,yana sauraron labarun BBC sashen hausa daga bakin Hindu Waziri. Mota ta shiga sassauke jibgi jibgi a harabarmu,nima ribdediyar jakata dankare take ba masaka tsinke muka fada cikin kujera shirim da ni da tirtsetsen cikina nace'wayyo baban jawad kafata'' yace 'wayyo sannu,idonshi akan jibgin kaya,ya gurgusa yace'wannan ai kece sunday mrng mrkt din shin boutique za a bude ne a Abuja ban sani ba? Ke da nace ki sayo kayan baby kawai shine kike karar da kudin a shirmen ku na mata? Nace 'ayya! Ai tsarabar mutane ce baka ga ba harda furniture marassa nauyi? Kudin fa suna da yawa in ba kantin kake son a sayewa babyn ba shi kadai? Yace'so wat? Kudin bana ubansa bane don wa ake nemosu ba don su ba? Nace hkn amma 'ya'yan jama'a ma suna da bukata sai shi kadai dan gatan daddy? Yace amman nace dake zanyi tsaraba kamar yadda na saba wa jama'ar kary,me yasa kike da kunnen kashi ne? Nace'i'am sorry angon karni ai tsaraba bata yawa duk sai a hada masu ba laifi bane. Ya tuntsire da dariar sabon sunanshi ya ciccibeni ko nauyi baya ji mukayi daki yana cewa 'muje ki gayamin wanene angon karnin? An gaya maki matata ko 'ya 'ya goma ta haife a lokaci daya zatayi karni ne? Karfe shida na yammacin washegarin litinin muna a 'gatwick airport' muna sallama da mutanen da mukayi zaman aminci da su musamman iyalin ambasada suna ta bani sakonni ne ga 'yan uwansu na gida dake jos. Muna cikin jirgi (boeing 745) mai zuwa portharcout din 9ja,kalmashe nake jikin yallabai sbd sanyin London mai shiga bargo shi kuma yana ta aikin lallatse waya yana gayawa kowa gamu nan mun taso daga London amma kar su je tun yanzu don Portharcourt zamu fara sauka. Jirgi ya daga ya nausa gida. Ba taheer din ba ba zubaidahr ba kowannensu ya gama murjewa ya kara girma akan nashi sbd tsabar hu2 da samun nutsuwa uwa uba dauwamammen Kwanciyar hankl. Da ganin su dai kaga well-fed-Londoners' wato wadanda suka ci suka hantse da diet din London.

119...
Su zubaidah aka shagwargwabe fuska'nifa jirgin kn zan shiga kai ne zaka hau na Abj don ni kry zani in haihu za'a fi kula dani tunda yake haihuwar fari ce. Kuma ya dace in baiwa antina enough tym din ta itama sai a gyara mun gidanmu na bayan gari mu zauna nida inna luba da mohd jawad. Yace'ai wlh baki isa ba,kinyi kadan kinyi tsararo ni kuma ya zakiyi dani? Kinsan dai zamana a kry ba zai yiwu ba sbd office ga aiyuka masu tsauri da zan je in taras. Na soma magiya nace'don Allah yallabai kay 2nani anti ma fa mu2m ce tana da hakki akanmu,ya dace a kula da hakkokinta itama ko don gudun daukar hakki. Yace'au to ni shine za'a dauki nawa hakkin? To ba'a isa ba. Hankalina ma bazai kwanta ba ku kuna can da tsohon ciki ni ina wani gari? Thnk twice lady. Saidai ko in daga ni har mubinan mu tarkato mu dawo kry a aje aikin Allah kinji na rantse. Na tabbatar ya gama magana kenan tunda shidai baya magana 2,sai nasa mishi kuka nace'to ni yanzu shine kiyi ta kuka kiyi ki koshi,har sai hawayen sun kare jirgi ya sauka mu tafi abj shine shawara. A daidai lokacin da aka samo sanarwa ta bututun maganar jirgi zai sauka a daura belt. Na fiddo powder a jakata(ailin) mai manne da madubi ina gyara hawayen fuskata na shafa lipshimmer sai yasa mun dariyar data kara kular dani. Ya karkatar da kai yace ke dai yi dan murmushin nan naki mai kama da flora bella rose in da gaske kina son zuwa qaraye.... Bansan sanda na murmusa bamhar 'yar wushiryata ta fito yace'to ko ke fa? Amma cewa nake cikinki yanzu ya shiga wata na bakwai gashi ba'a gani ba wanda ya sani balle ki ce za'ayi miki suru2n baki zo goyon ciki ba,in ya shiga wata na tara sai in kawo ki gaban fulani da amarya da kaina su ga irin kwazo na aure wata goma haihuwa wata tara... Na harareshi yay murmushi yace ko kuwa amaryar karni na? Nace haka za'ayi angon karnin,yadda kace bazan ki ba. Yace'yauwa 'yar matata shiyasa nakeso kauna da begenki sbd bakya yimin MUSU,bakya yi mun KARYA kuma bakya HA'INTA ta

120...
Nace 'banason in takura anti mubina ne,tay missing mijinta 4 so long zama na zai zama tamkar takura ne agareta.... Ya katseni yace'zan kula da adalci in Allah Ya yarda karewama ke ki zauna a sassan kasa nida ita mu manne a sama mu sha amarcin mu ke kuma ki karata da karnin ki ke daya ko ba haka kike so ba? Nay murmushin izgilanci nima,amma fa shaguben sa ya taba zucia ta na rama abunda yake mun in nayi mai gatse nace'ka jishi kaman gaske.... Muka tuntsire da daria. Da wadannan hirarrakin muka fito (Boiend 745) muka fada jirgin dan kabo mai zuwa abuja. Muna sauka daga matattakalar jirgi na sha mamakin dimbin al'ummar da suka zo taryenmu,'yan jaridu, manema labarai da kuma wakilan national television authority tare da tawagar Minister of Foreign Affairs sunzo taryen ogansu. A gaba gaba na gane anti mubina, muhd bello, fati, abdulraheem, assha, taufiq, ibrahim, peter. A gefe 'ya'yan bello ne mukhlas da taheer sun kara girma sosai. Naji haushin rashin ganin jawad a cikinsu, sai nake kimanta girman da 'ya'yan bello a yanzun na tabbata zai fisu. Ga yayyuna awal da sani jingine jikin motarsu da yayar assha mansina. Ragowar duk ban gane su ba. Anti mubina na sanye cikin rantsattsen leshi ruwan kasa wato kalar da oga ke so sai washe min hakora take wanda yafi kama da kuka. Ta juya tasa hankici ta share wasu ambaliyar hawaye da majina da suka kawo mata ziyara cikin wayau da dabara ba tare da kowa ya gane ba. Ita ko zubaidar jifanta take da tsadadden murmushinta sai hantar cikinta ta shiga rawa. Ko farcen BLACK dinta a yau abun kallo ne,ga mata 'yan uwanta ma balle maza. Bar ta kayan kawar da take daure da su hannu,kafa,wuya,gashi da kunne tamkar haifaffar Morocco. Kalarta ko abu ne da zai saka a shakku,don bazaka ce baka ce ko fara ce ko wankan tarwada ba,kawai ita daban ce wato unique ko a cikin dimbin matan dake wurin. Da ta doso su wani lallausan kamshi kurum ke dukan hancinan al'umma tamkar don ita kadai aka halitto wannan mayataccen turare. Ita kam duk a yawon ta kasashen dunia,da sayen turarukanta har a birnin Paris,bata taba jin kwatankwacin irin wannan kamshin ba. Ga wata irin cika ta halitta komi nata ya kai ya kawo, tamkar reshen bishiyar da iska ke kadawa sannu a hankali. Da tayi murmushi hasken wasu fararen hakora kaman kankara ne suka dallare ta. Ashe dai wannan itace real zubaidahhh da takejin labari?
[11/3, 8:38 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[11/3, 8:41 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔
~BOOK 2~
~THE END~
Tuna Baya2 120-127 End
Chapter 52 · 0% Book details