← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 54

Sashe 46

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

100....
Maimakon inga an nemi hanyar unguwarmu Minister's hill sai naga yahai ya dauke kan motar zuwa tsararrar anguwar asokoro. Yay doguwar tafiya a ciki kamin ya tsaya a wani sabon bungalow tsararre ginin kasar Canada tamkar an dauko ginin ne kacoka, dinsa an aza a wurin, kalar fentin gidan ruwan kasa ne mai haske daga waje da aka ratsa da ruwan madara daga ciki. Akwai balcony a harabar gidan irin gidajen nan ne na turawan yamma (western Europe) da ake kira super lux-finishing hawa 2 amma a idonka daga waje kamar hawa daya ne. Wannan ya tabbatar mun sabon gida yallabai ya gina saboda ni a cewarsa bai dace in yi rayuwar aure a gidan da nai rayuwar RAINO,wanke wanke da shara ba. Tom ne ya fara fitowa a guje sannan Ejiro kana Peter suna ta tsallen murna da rawarsu ta inyamurai tamkar wasu kananan yara. Ragowar motocin dasu ka yo rakiya duk yallabai ya koma yana sallama dasu da alqawarin zuwa masu ban gajiya, shima yahai komawa yay yana mun ala huta gajia kawai sai naji dan uwan anti mubina ya burgeni nima nace ya gaisheta. Muka doshi katafaren gidanmu wanda reception wato falon saukar baki zaka fara taraswa sannan kafar bene dama da hagu da zasu sada ka da wasu falullukan guda uku da dakunan barci suma uku,da toilet cikin kowanne dakin barci daya. Daya bayan gidanne aka yi baskwata domin masu aikin gida da wani katon kicin din a kasa wanda Tom ke girki a ciki domin baki. Ejiro ne ya farga bai ga jawad ba tuni ya ja birki yace ina master jawad? Idona ya cicciko na fada musu kome kenan, tuni murnar su ta burma ciki,peter yace wuh! Oga kenan,AREWA!! I luv dat i adores ol his doing,wato yana son hakan yana son yadda ogansa ke tafi da tsarin rayuwarshi. Ban shiga ba saida na karanta addu'oi masu yawa domin neman dukkan alkhairan dake cikin gidan aurena da neman tsari daga sharrikan dake cikinsa. A tsakar falon kasa tom yace'a yau bbu zancen TINE kin koma MADAME din mu. Na sha gaya maki ko a cikin yara ke ta daban ce. Madame ina mai farincikin shaida maki cewa u're among d luckiest tunda har kika yi sa'ar auren oganmu. Sabida haka ki godewa Allahnki,domin ba ko wadanne mazaje ne irin oga na ba/ na lumshe ido a hankali nay murmushi kana na bude ina mai gasgata kowacce kalma a cikin zancensa. 'Muna muku fatan alherin aure. Nace 'nagode. Kowannensu ya kama gabansa.
[10/23, 5:21 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[11/3, 8:33 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔
~BOOK 2~
Tuna Baya2 101-105

101...
Yallabai bai sami kansa ba sai karfe goma na dare. Nay kwalliya cikin leshi cotton mara nauyi ruwan bula mai karamin dinki nay amfani da fashion ear rings din honey drops na hade gashi na wuri guda na matse da ruwan bular ribbon mai laushi na fesa mishi turaren Dolce&Gabbana ina murza daurin kai,yallabai ya shigo cikin ruwan bulan pyjamas masu santsi abin namu kamar hadin baki amma is just a coincedence, kanshi na digar ruwa,ni'imantaccen kamshin bathrobb dinshi na dunhill ya kauraye ilahirin dakin wannan ya tabbatar mun fitowar shi kenan daga wanka. Ya amshi dankwalin ya murza mun aka yadda yaga dama ya juyar dani ga madubi na yace diba ki ga na fiki iya dauri. Ni kaina nasan daurin yay kyau dani sosai amma bance komi ba zuciyana a jagule take haka fuskana babu walwala. Nakejin abunda ya dakatar dashi kenan. Ya kunna fitila mai haske muka dubi juna ni ce na fara kawas da kai na koma can gefe na jingina da bango. Jikinsa yay sanyi ya zauna gefen gadon ya dafe kai yace'yau zubaidah ke juyawa mijinta baya? Na girgiza kai da sauri nace har abada bana fatan Allah Ya nuna min ranar da hakan zata kasance. Ya dago idanunshi jazur da bacin rai yace ashe ni ban isa inyi yadda naga dama da jawad ba? Bansan abu mai kyau a gareshi ba? Na lura shi fahimtar da yay min ma daban ce sai na zube akan gwiwoyina muryata a sanyaye nace Allah ba abunda ya bata mun rai kenan ba taheer. Ya dago ya dubeni da kyawawan idanunshi yace'ba kya mun karya ba kya ha'inta na tuntuni don haka tell me ko wani ne shine zaki huce a kaina? Na sunkuyar da kai to in ce ma? Raina yay bakikirin da jin cewa anti zata dawo cikin rayuwata kwanannan? Anya bazai ga wautana ba,ita da gidanta? To amma bazan taba yi mishi karya ba bazan taba ba in Allah Ya yarda har karshen rayuwata. Mukai facing juna 'umh tell me,ke nake sauraro zubaidah? Na kama in ina cikin rashin sanin takamaiman abun cewa nace'uh uh ni dai raina ne kawai ba dadi. Yace'akan me momyn jawad? Komi yana da dalili ki gayamin don bacin ranki azaba ne agareni. Ki tuna na sha gaya maki ke RUHI nace,ko so kike in miki kuka. Da sauri na girgiza kai a mamakance,a dimauce. Wannan oga na nefa da a yanzu darajarshi ta ninku ta zama ta miji agareni. Wanda aljannahta ke karkashin diga digansa mutumin dana ke ganin girma da kimarsa fiye da na kowa a duniya inka dauke iyaye na. Idan na bari yay kuka a domina(wanda na tabbata ya fadi ne baka da zuci,tunda shi baya fadan abunda ba haka yake a zuciyarsa ba,wai don ya burge ko ya farantawa wani,ai nayi asara! Na durkusa gabansa a gaggauce na saki fuska nace ni dai dama rokon alfarmarka nakeso inyi baban jawad. Don Allah idan anti ta dawo kada ka canza min daga yadda muke idan hakan ta faru bansan irin halin da zan shiga ba. Domin jin son ka nake har cikin kashi da bargo har bansan yadda zan fassara ba. Sai nake tunanin yanzu itama anti haka kakesonta shiyasa ta ke son ka. Duk soyyr nan da kake mun in ta dawo itama haka zaka ke sonta. Ka tafi wurinta ni kuma abar ni ni kadai watakila ma har ka manta dani. Kuma kaga anti ta fini girma ta kuma haifi jawad don haka zaka fi sonta ni kuma ka canza mun? Nay mai kirrr da ido yallabai ya saki kunnuwa yana saurarona yana gyada kai kamar kadangare tunda na fara bai katseni ba yana murmushi har na dasa aya. Yace' hakane abun? To shine ni za'a kwareni? nima ina rokonki ko antin ta dawo idan ranki ba dadin ko zaki huce a kaina to bata wannan hanyar ba zubaidah. Inason jikin ki da zuciyar ki na a tare. Ki dage kema ki haifo jawad na biyu sai kuyi girma daya da antin taki nema in so ki tunda kin ce bana sonki! To bude zuciyarka da idanunki yanzunnan in nuna maki SO da KAUNAR da ban taba nunawa kowacce 'ya mace ba......

102 Ya mika hannu yay musu dim lyt a zuciyarsa yana ta kakabin abun wai 'yar zubaidah tun yanzun ta san menene KISHI a shekarunta da wayonta da yake rainawa bai zaci haka nan kusa ba. Ba shakka yana tsoronta a nan gaba in haka ne yana da sauran aiki kenan amma gaskiya a yau yayi mamakin da bai taba yi a kanta ba. To sai muka bude sabon shafin amarci a abujar ma. A kwanakin da suka biyo baya yallabai bai sa komi a gabansa ba sai ZUBAIDAH da shirye shiryen tafiyar mu honey moon kasar BRAZIL. Karfe shida na yamma yana kwance cikin rest chair dake main falonshi yana sauraron labaran CNN daga tauraron dan adam a yayin da ni nake gefe ina mai matsar kafafu ya rufe ido ya bude ya janyoni gaba daya muka fuskanci juna. Yasa hannu ya ja karan hancina yace'wa ya koya miki tausa mai dadi haka? Zubaidah halayenki da dabi'un ki na burgeni. Ke kadai kin isheni rayuwar duniyar har ta lahirar baki daya. Ina son tausar nan taki ta kasance cikin abubuwanda ba zaki gaza da yi mun ba duk rintsi. Cikin jin kunya nace'i promised' yace 'shirye shiryen tafiyarmu fa ya kammala jibi zamu tashi zuwa Rio de Janeiro din ne ko Wellington 'yar matata mai kunya sai dai ina tsoron kar inje ki koma hatsabibiya don wannan sparkiling eyes din naki na bani tsoro fa? Bansan sanda nay dariya ba, domin zancen sa ya tuna min da muhawarar anti mubina da mukarrabanta,suma sun ce idanun suna basu tsoro. Sannan a bakin mansina na fara jin wannan kalma ta sparkle yau ga oga ya maimaita min ashe dai da gaske take,to sai me? Karar wayarshi ta katsemu tun kamin ince komi ya mika hannunshi na dama ya amsa na hagun ko na sakale cikin hannayena. Ya jima yana magana ban maida hankali na gare su ba na zame hannuna na nufi kicin na fara hadawa ogana kunun aya mai sanyin dadi,don dama tuni na markada ayar da kayan kamshi sai na juyo a jug da dambun naman kaza bisa filet din tangaran na zuba 'yan kananun kankara cikin jug din domin yay dan sanyi. Tom dake gefe yana jera cefane a firji na gaya mun irin cin mutuncin da anti tazo har gidan yallabai na Colarado close tayi masu. Wai sune manyan munafukan da aka hada baki dasu aka munafunceta suka ci amanarta,bayan ita ta dauko su tana nan tana shirin daukar fansa a kansu da zarar ta dawo. Nace(cikin rashin kulawa) ''don batawa kam an bata mata sai muyi juriyar daukar bacin ranta duka amma ni bazan gayawa baban jawad ba.
Chapter 46 · 0% Book details