Sashe 12
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
48.
Idan Allah ya raya ni, xanyi amfani da karfi da lafiyar da Allah ya bani, duk da kasancewa na diya mace, in ga na fitar da Baba daga rayuwar saida KALWA, in kai Sadiya da Jafar makaranta, in fiddo Amarya daga hawa salga mai tsutsotsi, itama ta hau tangaren. In kai Ya Auwal abinda yafi so a rayuwar shi (karatun Jami'a). Na runtse idona a hankali, hawayen tausayin ahalina, shi ke xuba min, mai xafi da daci a xuci. Yanxu dama akwai wanda Allah yayi wa baiwar rayuwa irin haka cikin kasar mu? Basa ko tunawa da 'talaka' wanda ke wuni yana digar gumi, don kurum ya samarwa iyalin shi abinda xasu ci balle su taimake shi? Meye amfanin shuwagabannin mu, me suke yi na taimakon 'yan kasa, musamman talakawa? Bamu ganshi ba. Sai dai su kai 'ya'yansu yin karatun shedanci a kasar waje, su sayawa matan su motoci na garari, su tamfatsa ginunnuka tamkar baxa amutu ba aikin kenan. Ni ko in nice da kudi, a ganina na talaka wanda ke bisa hanya ne, rana tana dukan su, suna neman abinda xasu sa a bakin salatin su. Kaico!
*************
Washegari tunda na tashi da asuba ban koma ba, tunda kuwa na riga na saba da hakan. Na tuna su Baba nayi murmushi, nasan yau xasu samu karin kumallo mai kyau, tunda sun samu 'yan kudin wanke-wanke. Sai da gari ya waye Tom ya shigo da 'tray' yace ''Tine, ba dai har ka tashi ba'' nayi murmushi ''na tashi mana, tun asuba, ni bana dogon barci''. Na fito falon na tsugunna na gaida shi, na lura ya ji dadin girman da na bashi yace ''kaima sai ka xauna shiru, maimakon ka kunna t.v, ana programme mai kyau a B4u Movie''. Ko me yace, oho! Ya jona waya talbijin ya kama, ya dauko wani abu baki yaxo gaba na ''wannan shine 'remote', in abinda kake kallo bai maka ba, sai ka yi ta danna nan xai yi ta canxawa, har sai kaxo wanda yayi maka. Ta nan ake kunna t.v'' ya dauki wani irin sa amma fari ''da kin danna nan, A/C xai kama, nan kuma xai mutu, nan xai kari, nan xai ragu....''
49 ..haka yai ta nuna min, sai da na tabbatar mishi na gane yace ''ka gane? To kunna min A/C yanxu'' na kwa danna ta kama shuuuuu!. Yace ''in xa'ayi wanka, a wannan bandaki, ya xa'ayi?'' ''Xa'a toshe rariyar kwamin ne, a kunna famfo wanda ake so (mai xafi ko mai sanyi), sai a shiga a cuda da soso da sabulu''. Ya tintsire da dariya yai mun tafi guda uku ''da alama xamu shirya da kai, Tine, domin kai yaro ne mai saurin fahimta, ga karin kumallon ka nan, ni xani makaranta, sai sha biyu da rabi xan dawo, din ba ni xan daura lunch ba (abincin rana) Ejiro ne''
50.
Ya juya xai fita, sai kuma ya juyo, ''af, Madam tace a gaya maka, in ka kintsa kaje can falon jiya, yau xaki fara dutyn ki''. Na bude farantan gilashin da ya aje mani, kodayake tun kamin in bude naga abinda ke ciki, kasancewar sa garai-garai. Farantin farko kwai ne aka soya mai kauri da ayaba da dankalin turawa, dayan farfesun koda da hanta ne, sai wani abu a kwalba mai kama da ganda (Jam), sai da na diba hoton dake jiki, na fahimci a biredi ake shafawa, sai wani irin dogon biredi mai kyau da laushi, a gefe filas din ruwan xafi ne da dan karami dai-dai cikina, da sauran gwangwanaye da kwalaben da na fahimci duka a shayin ake xubawa. Na ci iya ci na, kunnena kamar xai tsinke don dadi, sai girgidi yake. Santi kam nayi shi har na gaji, sai dai a bakina abincin ba dandano na rashin sabo. Nayi wanka nasa 'yar atamfar da tafi kowacce kwari cikin kayana. Ko mai ban tsaya shafawaba na bi hanyar jiya, xuwa kayataccen falon. Na taddata tsaye tsakiyar dakin tana magana cikin wani abu, mai kama da abinda naji Tom ya kira 'remote' (a wancan lokacin mutane dai-dai ke da wayar hannu a Nijeriya), sanye take da siket iya gwiwarta, rigar jikin ta iya cibinta, wanda hakan ya baiwa tirtsetsen cikin damar watayawarsa yadda yake so, abin babu ko kyawun gani. Ban taba ganin cikin mace haka muraran a sarari ba kamar randa, sai yau. Yau ma kamar jiya, kan ba hankali. Ke da ganin yadda take maganar, tana karkashe 'yan kananun idanun ta, kinsan da Maigidan da ake masifar so a ke. Abinda ma na tsinkaya xance na ne, don naji tana cewa ''wallahi baka ganta ba fa, baka kirin, 'yar siririya kamar kaxar mayu, kafafunta kamar na shanshani, idanunta ribda-ribda ga tsummokara a jikin ta babu kyawun gani, hakoran ta yalaye sharr, ni kam tsoronta ma nake, don bata yi mun kama da mutane ba.
[9/24, 9:14 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/5, 7:50 AM] A A Dboy: Tuna Baya 51-55
51.
Tunda taxo gidan 'atmosphere' na gidan bakidaya ya canxa, gaskiya tabi Talatu su koma, in ya so a nemo wata'' ban san me ya gaya mata ba, naga ta tsuke fuska, can kuma ta ja tsaki tsuuuu! Tayi wurgi da abin maganar, dai-dai lokacin da Talatu ta shigo, ga dukkan alamu, tayi shirin komawa KARAYE ne. Hankalina ya tashi ainun, tsoron matar ya kara kamani, gashi kuma itama tace ni nake bata tsoro. Ni kaina nasan sirinta na yayi yawa, amma ban san wani aibu a halitta na ba bayan wannan. Ta dubi Talatu ''nayi magana da direban da xai maida ke, ga wannan inji TAHEER ki sha ruwa a hanya''. Ta fiddo rafar kudi sababbi, ta xari goma ciki, ke da gani kinsan kwangen kudin tayi, duka aka ce ta bayar. Talatu tasa hannu biyu ta karba ta fadi tana godiya. Tace ''kamin ki tafi, ga wannan 'dettol' ne da 'anticeptic soaps', ki hada ruwa mai xafi ki xuba su a ciki, suyi kaman awa guda, kisa yayrinyar nan ciki ki cudeta, musamman hannuwa, kafafu da kasan hammatarta, ki tabbatar sun fita fes, kiyi ta canxa ruwan kamar sau goma. Sannan ga wannan 'brush' da 'maclean' ki dirje yalayen hakoran nan nata ban son ganin su, xuciyata tashi take. Direba xai kaiku saloon ayi mata wankin kai, duk wata kwarkwata da birbishin amosari, xanyi masu waya, su dirje shi. Sannan wadannan tsummokaran na jikin ta, da wadanda aka shigar dasu daki, kije ki tube maxa- maxa a fidda mun su a gida tun basu jawo mun sauro ba. Daga saloon xai kaiku boutique, ki xabo mata kayan sawa, wanda ba'a dinkawa. Idan naga xani a ciki, Ubanta xan ci. Ku tashi ku fice mun a falo, sauran in ga an saba umarni na daya''.
52.
Sum-sum muka tashi muka fito, kamar an rarrade mana gwowoyin mu da murfin kwano. Talatu na cuccudani a baho tana hawayen tausayin tafiya ta barni da wannan mai halin yahudawa, gata dai cikakkiyar bahaushiya kuma musulma gaba da baya, amma kwata-kwata babu tausayi da kyautatawa cikin al'amarinta. Tace ''Oh ni Talatu ya xan yi da amana? Ban san rashin mutuncin matar nan ya kai haka ba, ina jin labarin ta wurin bayin gidan Maimartaba da 'ya'yanshi duka, ban xaci ya kai haka ba, me xan ce da Maikalwa? Ni kam ko a jikina. Babana fa xa'a baiwa naira dubu goma a wata, abinda ko ma'aikacin gwamnati mai digiri, ba'a basu a ranar su ta farkon fara aiki. Baba da Innata ne fa xasu ci jan miya, su daina dumame. Yayana ne fa xai yi karatun da watakila watarana, ya hanani wanke-wanken; ya rungume mu cikin inuwar iliminsa. To me xai sa inji ciwo? A karkashinta nake, a karkashin inuwarta ne xamu ji sanyi ni da iyaye na! Wulakanci yana tofo ko yana taimakon dan adam? Ban xo don ta yabi halittana ba, sai don samun halalina! ''Hajiya Talatu na gama ki da Allah, kada kice da su komi game da halin Uwargijiyata. Ni nace naji na gani, ko me xatai min, xan iya jure xama da ita''. Ta share fuska ''shikenan Atine, nayi miki alkawari baxan bari Maikalwa yaji ba''. Wani irin inji ake tura min kai, na dauka fille shi xai yi, sai naji ashe wai cuda sumar kaina yake, aka wanke tas, yasha sahfe-shafe da mulke-mulken mayuka masu kyau in banda kamshi mai dadi ba abinda yake tashi. Mamakin da nake, wai gashi ma yayi matsayin da xa'a bude mishi irin wannna kasaitaccen waje domin sa? Ni kam jikina yayi dadi, kaina yayi sayau, kaman an dauke min nannauyan kaya aka, iska na shiga ta ko'ina. Kayan da Talatu ke xaba, rigunane da su dogayen ruguna da pakistan masu dan karen tsada don tace mata baxan sa wando ba. Bamu dawo ba sai bayan axahar, direba ya juya da Hajiya Talati Karaye, ni kuma na rungumi jakar kayana na nufi dakina cike da kewar ta.