Sashe 33
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
23...
Idonshi jazur sun razana muhd jos.niyyarshi da sun shigo ya rufeshi da zagi.Abu daya yayi wato lallabawa ya zare 'bullet' din dake cikin karamar 'pistol' din bello da durowas dinshi gabadaya.sai kuma tausayi ya kamashi daya dubi bellon shi, muhammad dinshi ma'abocin fara a da son barkwanci.amma lokaci daya ya zabge,ya koma kamar mara imani,kamar bai taba yin daria ba duk a dalilin SO.ya la'anci SO,ya kuma gode Allah da bai taba daura mishi ba.koda yake ya tabbata in shine bazai dauki abinda zafi haka ba. bello mutum ne mai tsananin zafi,dan sharp-sharp (komi ayi shi a lokacin daya dace),shiya sa komima yazo mai da zafi.da ace tun farko yabi shawararsa,da ba 'ayi wannan abin kunyar ba. yasan fulani dole ta gayawa 'ya'yanta.yayi tsaki ya bude firji ya fiddo lemun 'tropical' mai sanyi ya bincire hancin ya mikawa bello,ya karkatar da kai yana murmushi yace kasha don zubaidah? Ya harareshi,kana ya amsa ya kwace karan tabar dake hannunshi ya kashe ya cillar cikin 'ash tray' ya kuma tura hannu cikin aljihunshi ya dauke kwalin tabar gabadaya yasa a dustbin.zaman kurame sukai na tsawon awa guda,shiru ba wanda yace da dan uwanshi ci kanka.can bello kamar an tsikareshi ya mike.muhd yabishi,zai shiga seat din driver ya kwace ya zauna yace cikin murmushi Alasabbinani, sai ina mukai?
24......
Ya harari gidan yallabai tukunna da ma'aikatan dake ta faman gyare-gyare kamar yaune za a kawo amaryar,cikin hargagi yace ni bani da gidan iyaye?da zaka tambayeni ina zani? Dariya yayi wadda ta kara tunzura bellon,Allah yabada haquri,your majesty,gani ba ci bane,tauna ba hadiya bace,yaja motar sai harabar gidan waziry, ya zube a babban falon waziri yatasa shi gaba yana huci baice komi ba shi ma wazirin haka, shirin kudin sadaki yake da kanshi yan dubu dubu sabbi kar cikin katuwar jaka. kai kace bai san Allah yayi ruwan tsirarsa bama a falon.ya soma rera kuka tamkar wani karamin yaro.yanzu baba da saninka zakuyi min haka? baba kasanfa ina son atine batun yauba tun tana yar ficiciyarta. na auri fatima abisa son ranku to ni akanme bazaku bani son rainaba?yanzu baba har kafi son farin cikin taheer da nawa? Waziri ya kammala jera kudi a jaka,yaja zip ya zuge kai kace da kututturen ice yake magana.ya mike zai fita, sannanne yace lalle bello,ka isa soja.tunda har ka iya ka dosheni da zancen yar gidan mai kalwa a karo na biyu.a kuma kan cinikin yayanka.to kasani,Allah ya haramta ciniki akan ciniki.
25...
Wallahi koba taheer ne zai auri yarinyar nanba bazani kara nemo maka auren taba.nan kazo kasani jin kunyar jama'ar gari.kace kana neman kanwa,kadawo kace yar ce.nayi nayi dakai na fidda ma hawayena kan ka fiddani kunyar bawan Allahn nan,karufe idonka ka bada mishi toka.kai wai wata atika.baka san wata atine ba banda kanwarta.
Sannan yanzu don Allah yasaka mata,ta koma mutum,kadawo ka kawomin zancen banza? Da can kana sonta baka nemi inda takeba shekara da shekaru dai dai har takwas,sai yanzu?bayan ya gama wahala da yarinyar ya maidata mutum,ka kawomin zancen wofi?ance mani tsohon banza ne? Kana auren kanwarshi,kahada neman aure da shi? Sabida kai bakasan mutunciba,butulune mai manta alheri.dubi idanunka fiki fiki,wai zaka auri yarinyar da TAHEER zai aura ko kunya bakaji bello? Kaga sadakin zubaidah yar gidan mai kalwa. gobe zan dankawa ubanta.ince ko in Allah ya kaimu gobe kaga an shafa fatiha ka hakura,ka koma inda ka fito.ka hakura matarka,ka roqi Allah ya tura ma sonta? Waziri yayi shiru ya dubi danshi, babu alamun yana sauraronshi.jakar kudin hannun shi kurum yakebi da kallo,dayake jin tamkar ya fisgo ya bulbula mata fetur ya kyasta ashana.yana tunanin muddin ta bar gabanshi shikenan tayi mai gingimemen shamaki da ATINE sa.abinda bai taba kawowa cikin mafarkinsa ba.A kullum mafarkin sa na nuna masa zai dawo watarana ya auri ATINE.komai daren dadewa,yana da yaqinin atine bazata taba iya auren kowaba sai shi tunda shine first luv dinta,shiya bude mata ido da soyayya,bata san menene son ba sai akanshi.dai dai da rana daya bai taba kuskuren wannan mafarkin ba,to ta yaya atine tayi masa haka
26.
tsakanin da mahaifi sai allah.tausayin nashi ne ya kamashi bello ya zabge,yayi duhu, ciki kwana daya kacal.baisan san da ya dawo ba.ya tsuguna ya dafa kafadunshi.muhdbello! Ana barin halas, don kunya.dama allah yayi fatima ce matarkaba zubaidah ba! Baka yarda da kaddara?baka da hakuri? baka juriya? Idan zubaidah matarkace sai kaga wani sanadi yazo da zaka aureta agaba.bello komi yafaru kai ka jawo.tun farko meye nacewa baka auren atine? Alhalin kasan kana son ta? Bello ya sadda kai, kalamin mahaifin shi na sanyaya mishi kwarai.a sanyaye yace wallahi ranka yadade nima bansa ya akaiba.a lokacin ni kaina jinake tamkar bani ba amma kosu mallam mammam sai dai surufe ido su mance dani amma sun san inason yarsu tun tafiyarta ban rabu da kofar gidan suba. Nabashi hakuri yace ya yafe min, basan dalili sa nakin gayamin inda take ba, haka bansan dalili naken da yasa shi min haka yanzu ba, wasu hawayene suka shifido aguje. Waziry ya sadda kai. Ya dago bayan wasu yan dakikai kada muzamo masu son kan mu bello, kada muci amanar taheer bai cancanci haka daga garemu ba
27.
amatsayina na mahaifinka,idanhar na isa in gaya maka kaji,to kada kace da taheer komai,kada ka batawa matarka da dan uwanka.wallahi ko yaya makamanciyar wannan ta shiga kunne taheer bazai auri yarinyar nan ba, cewa zaiyi ya barmaka!! Haba bello!!!kai baza kaiya kwatanta irin karimcin da yake maka ba?ban taba kawowa ko a mafarki zaka iya hada neman aure da taheer ba, sannan ita yarinyar in kayi mata haka baka kyauta mata ba, tun da bakasan wane al amarine a tsakanin suba shekarun ta tara tare dashi.kasa saki jikinka, kabawar allah lamarin sai ya zabama abinda yafi alkhary,ka koma ka tafi da fatima gidan ka.idan kabarta anan abin da ke boye zai fito gida sarauta baya raina gulma tsegumi, kana jina? Zance yaushe kuma?tunda uwar su taji?ya fadi aransa. amma a fili sai yabi umarnin mahaifin shi, kamar dagaske sun dauko hanyar bayan gari ya ja burki, kuuuu! Ya razana muhd yayi saurin take burkin motar kada ya kifar dasu kamin ya ankara bello yayii round dakan motar ya shiga keta lunguna har ya tadda gidan MAI KALWA yaci taya ya tada wata irin dunkulalliyar kura a dan tsukurkurin lokon da mota ma bashiga take yiba haka ya kukkujje ta yashiga cikin zafin nama mohd jos , yayi saurin danna a wani abu ajikin motar glassai bakake suka mamaye gurbin farare yanda baza a hangosuba hakannan kofofin ba damar buduwa,yace a hankali bello kashe mu zakayi?tun ban tara iyali masu min addua ba?
28.
kabar su mukhlas orphans (marayu) akan farin cikinka kai kadai ?shin zubaidah nan itane kadai mace aduniya?tukun nama yanzu da kazo gidan su mai zaka yiwa yar mutane? Ya rika jeho tambayoyi daki-daki, anutse da alama shi ba abun da ya dameshi. Me kuwa zan yi mata? tambayar ta kawai zan yi dalilinta nayi mun haka ya bude murfin motar amma ko gezau
Ya harari mohd. Cikin matsanancin takaici wai meyasa kake mai dani mahaukacine? Yo ba dole im maidakai mahaukaciba?dubi kayan jikin ka, kakin soja afagen fama dasu zaka gidan mutane a kauye ka razana musu yaya bello anya are you in your full sense? (kana cikin ya yi cikakken hankalin ka) shiru yayi bai amsa ba.ya koma lallashi,cikin tattausan murya kayi hakuri muko ma gida ka fiddasu kasa na mutane sai ka dawo bello yayi shiru, again tamkar muhd da dutse yake magana duka daya yayi wa kofar motar da kafarshi ta bude,ba shiri ba zatonta ba tsammani. Dan jos ya bishi da ido baki a bude ya isa kofar gidan auwal nasawo kai zai fito sauran kadan su kara.mamaki ya kama auwal yayi ta maza in ji mata yamika bello hannu sukayi musabiha atine sun iso ko abinda yace dashi atakaice,awal ya gyada kai,cike da zargi,sai kuma yatuna tsakanin bello da yallabai,don ha ya juya cikin gida ashshah ya hango a kurkusa yayi kiranta yace ina amarya kice tana da baki a dakina kanin yallabai ne muhd ashshah tayi dariya uncle muhd mijin aunty fatima? Kace tana zuwa ta ratso mutane ta hada juice da ruwa taba auwal wai yabashi kamin ta tsamota.
29.
na idar da sallar la'asar kenan ina canza kaya zuwa farin cotten lace sassauka me yarfen kananun duwarwatsu kala daban -daban brown net nayi amfani da ruwa kasa r takalmi da jaka andre valentino ina cikin fesa turare hardo ta leko zubaidah kina da bako a dakin ya auwal tayi wucewarta cikin hidima, domin dai ita yar hidimace tunda muka iso kona minti daya bata zauna ba na tambayi fa'izah ko suwaye?tace ina zan sani ina kwance? Batare da wani dogon tunani ba na zura takalmana nayi zaure. A zauren mu,wani kamshi ne dana tabbatar dana dade da sani nayi iyaka tunani na waye ma mamallakin wannan ni'imtaccen turare? Iyaka tunani na bai bani ba don haka nasa kai tare da sallama ya juya baya gawani rubutun ajami, na wasu shekaru masu yawa abaya. Hannayen shi duka biyu harde a bayan shi.bai amsa sallamar ba kazalika bai juyo ba na sake sallama,na shigo tsakiyar dakin ya awal.gabana ya soma dukan tara-tara ba uku-uku ba wannan dogon mai jiki irin na yallabai cikin ko wani hali, bazan mance kamannin shi ba. Kowa ne irin hali,lumsassun idanun shi ya sarke cikin idanuna da kallon da yasan very irresistible, ne a gareni tuni na sandare atsaye.ya soma taku zuwa gareni,har yanzu idanunshi cikin nawa baya ko kyaftawa.na soma ja dabaya,shi kuma bai bar bina ba har sai da na dangana da katakon gadon ya awal na tsaya cak, kirjina na harbawa,zuciyata na neman faso allon kirjina sabida tsabar tsoro.