← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 54

Sashe 4

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

13.
Nayi ajiyar xuciya mai karfi ''a'ah Inna Luba! Iska ce ta dauke mayafin, ta dauke dankwalin, nima saura kadan ta dauke ni. Ga kuma wannan dogon mutumin, wa ma yake da suna? Dan gidan Waziri yana bina, muryar shi abun tsoro ce, tace ''Atine xauna nan,'' na xauna, tace'' ki nutsu nasan halin ki kinji? Ki saurari Bello dan gidan Waziri yaron kirki ne, ba xai cutar da ke ba, Baban ki da Malam xasu ji dadi idan baki wulakanta shi ba. Ba yarinyar da Bello ya taba cewa yana so, duk fadin Karaye, haka duk dangin su, Maimartaba ma ya bashi diyar shi yace baya so, idan kika samu ya so ki, Allah ya taimake ki, mutum ne mai ilmi sosai, Atine na, kinji?'' Inna baki san wannan ba, shine ya xagi Baban mu, ya....'' ''ni ba wani abu nace ba, kurum cewa nayi ki saurare shi, ki ji me xai ce da ke?'' shikenan Inna, Malam ya kwanta ne?'' ''ya jira ki tun daxu baki xo ba, ya bawa Sani ya baki, nake jin mantawa yayi (Sanin). Ta bani mayafi na yafa na fita. Har yanxu yana tsaye jikin dakalin gida, sai naji tausayin shi, ni mutum ce mai tsananin tausayi don ko kiyashi bani iya kashewa da gangan balle in wulakanta mutum. Sanye yake da wata irin jibgegiyar rigar ruwa ta kare jiki daga dukan ruwan sama, sai kyalli take kamar leda a cikin hasken hadarin. Ya harde hannuwan shi bisa kirjin shi, ya kurawa hadarin ido kamar mai son karanto wani boyayyen al'amari a cikin sa. Jin motsin fitowa na yayi saurin sauke kai. Biyo ni kurum yayi bai ce komai ba, kaxalika nima. Hadari ya gama gangamowa, sai yayyafi ya soma sauka yaf-yaf a jikin mu, da kan rumfunan kwanon dake layin karar babu dadin ji. Na dukunkune hannuwa na cikin tsananin raxana, alamun tsoro, xane baro- baro cikin idanu na masu haske. Da ni kadai ce xurawa xanyi da gudu, shiko ko a jikin sa yace ''Atine, bakya magana, baki gaida na gaba da ke, why? Na lura in xa'a kwana ana tafe dake baxaki magana ba'' nayi shiru, ya sake cewa ''Atine bakya gudun ruwan nan ya taba min lafiyar ki?

14.
Nayi hanxarin dago ido na dube shi ta wutsiyar ido, kallo na yake da idanuwan shi masu kwarjini, wani abu na ji ya tsirga har kwalkwalwata. Ban ankara ba naji yana rufa min wani abu mai dumi. Suman tafe nayi, shidewar wucin gadin raxana. Sai da na dawo dai-dai na fahimci, jibgegiyar rigar turawan ce cikin jikina, ni Atine Mamman Maikalwa. In banda wani irin lallausan kamshi, ba abinda ke tashi cikin rigar. Dai- dai sanda muka kawo kofar gidan mu ruwan ya jike shi sharkaf, amma bai ko damu ba. Na mika hannu na xare mishi rigar shi, hannun shi na dama yasa ya danne nawan yace ''No, ajiya ne na baki Atine, xan karbi kayana idan na dawo. In an tambayeki thickcoat na wanene, me xaki ce, Atine?'' Iyakar rudewa na gama rudewa, fitsari ya cika min mara fam, na sunkuyar da kai jikina na kyarma yayi hamxarin dauke hannun shi a nawa da sauri yace ''Atine, xan tafi, tunda baxan samu alfarmar kalma ko daya a bakin ki ba. Shin kin nemo amsar tambaya na na kwanaki? Da nace ki binciki wanene Bello Waxiri? Na san kin binciko amma amsar tayi miki sabani da tunanin ki?'' Yayi murmushi, duk da bashi nake kallo ba, tafin kafata na kura ma ido, na ji sautin murmushinsa a hankali, a xuciyata ina gasgata xancensa, kwarai naji sabanin abinda nayi tsammani, amma hakan baya nufin na yarda, tunda ni ban ga haka akan kaina ba. Ba kuma tare da ya kuma neman jin komi daga gareni ba ya cigaba da cewa '' yau ma ga new assignment, kije ki binciko, menene yasa Bello Waxiri ya sa maki rigar shi? Abinda bai taba yiwa wata yarinya a garin Karaye ba? Menene yasa kika kasa duban idon Bello Waxiri ko kadan, sabanin kwanakin baya da kika gaya mai magana son ranki? Atine, na barki da wannan, sai da safe''. Nafi mintuna biyar tsaye a wurin kamar an kafe ni, kamin in dawo hayyaci na na shiga gida, su Atika tuni sunyi barci Baba ne dai nike jiyo sukurniyar shi a turakar shi. Na xare riga a hankali, na janyo aci bal-bal na kyasta ashana, haske ya gauraye dakin. Na dubi riga da kyau,ta hadu ta burgeni iyaka, Ban taba gani riga mai kyawun ta ba. Wannan kamshi, ni'ima ne ga ma'abocin shi.

15.
Na samu kaina da rufa riga a kaina ina shakar kamshinta ina murmushi a hankali. Wai shi wannan bai san ni yarinya bace, ya cika minni kwakwalwa da naganganun da suka fi karfin hankalina? Ni nasan wani dalilin sanya mani riga? Ba ruwa ake ba ya taimake ni? Wanda kuma duk ya taimaki wani ai Allah xai taimake shi shima. Ya hada yatsun mu, don kar in ciro riga mana ina na san wani dalili bayan wannan? To amma ni kaina nasan yau na ji ni cikin wani bakon nishadi, ga farin ciki ya baibayeni kamar ance min Goggo na ta warke sumul. Na linke riga na janyo wata tsohuwar akwatin Amarya na tura, na rufe na mayar. Washegari Atika kallo na take kaman taga aljana tace ''Atine, jikin ki kamshin Aljannah yake, shin ko kin ga Annabi a barci ne da Malam yace mana ana gani, in anyi dace? Na yi dariya na bi ta da ''eh''. Yammacin ranar mun yi ciniki mai tarin yawa, na hada kudi na baiwa Baba, ya tafi Kano. Washegari da safe nayi wanka na saka atamfata mai dan dan, print ce ruwan bula, ni bana kwalliya sam, ko vaseline in ba lokacin sanyi ba bana shafawa, na goya Jafaru nasa kibiya ina tsefe kaina ina tajewa. Sani ya shigo, baki har kunne, a duk sanda ya xo min irin haka nasan ya ciyo kudin wani karikicen abokinsa ne, wai xai hada mu, na tsuke duska kuwa iyaka. Ya samu jijiyar bishiyar dalbejiyar da nake xaune karkashinta ya xauna jikin sa har rawa yake ''wai ke Atine, baki gajiya da tsifar kai?'' Nace ''unh!'' ya lankwashe kai yace ''shin kinsan Bello, Yallabai Bello dan gidan Waxiri?'' Nan ma nace ''unh'' na sake tsukewa, sani ya dabarbarce, yama rasa ta inda xai faro, da gani ba kudi yaci ba yau mutuncin ya gani, ya kare kwane-kwanen sa yace ''kije yana kiranki, Baba yasan da xuwansa, ya kuma ce na gaya miki muddin yaji wannan dabbancin naki, sai na kabari ya fiki walawa''.Ya haura takalman sa ya mike nace '' in dai rigarsa ce da ya ara min,ban roka ba balle a biyo ni har gida a ci mun mutunci, tana nan bari na dauko maka'' Sani ya fice ko saurareni bai yi ba.
[9/24, 9:10 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/24, 9:10 AM] A A Dboy: Tuna Baya 16 to 20

16.
Yi ba. Murna kaman in yi tsalle. Ni kaina nasan, na kamu da son mutumin da ba tsara na bane ta fannin komi, amma Allah shaida na ne kan bani na daurawa kaina ba. Surutu ne nasan xa'ayi shi a garin Karaye har a gode Allah, oho, xa su gaji su bari ne. Tun daga xaure nake jiyo kamshin, ina gaba yana kara dosa ta. Dan farin wankakken hijabi ne a kaina hannayena rungume da riga, na hange shi da 'yan iskan abokan sa, dan tsamirmirin nan da dan gajeren. Sanye yake da karamar riga da dogon bakin wando mai kauri na 'yan birni, kykyawar fuskar shi tayi kyau a cikin hantsin kamar kullum. Na kara cuske fuska, a nutse na gaida su fuskata ba anuuri, ita kanta gaisuwar ba din gargadin da Sani yai min ba da baxan yi ba. Dan tsamirmirin ne yace ''ranki ya dade, Uwar gajiyar mu, Yallabiyar mu tuba muke'' Ba tare da wata magana ba na mika mai riga nace ''ga rigar ku'' sukayi murmushi a tare yace ''bar xancen riga tukunna, nace miki mun xo tuba ne...'' nace ''da kukayi wacce shirka? Ai ku saraki ne, masu mulki, din haja ko mi kuka yiwa talaka a hanyar garin Karaye, baku yi laihi ba, tunda garin ku ne to amma nan cikin gidan Maikalwa, Kalwa ta daddawane, mallakin sa ne da ya gada tun iyaye da kakanni, babu wanda ya bashi cikin masu mulkin Karaye. Don haka ba wanda ya isa ya xage shi anan mu kyale. Ga rigar ku nace'' na dangwarar ta anan na juya abina. Sai bayan dana dawo na shiga tambayar kaina ''maiyasa nayi haka?'' don me ban saurare su na ji uxurin su ba, ko Ubangiji muna yi mai laifi, mu rokesa gafara ya gafarta mana, balle ni wata tsiya 'Atine'. Koda yake na nuna martabar Baba na, mai girma ce a gare ni. Sai dai ina wahalar da kaina ne a banxa; son Bello nake, son shi ke wahalar da ni a 'yan kwanakin nan. Kwanan Baba uku kamin ya dawo har hankulan mu sun tashi, ya dawo cike da farin cikin raina yayi fari kal don na tabbata Goggo da samu sauki kenan. Da yamma Baba ya kirani dakin shi,munyi hirarraki da dama game da lafiyar Goggo kamin ya gangaro maganar da ban tsammana ba,
Chapter 4 · 0% Book details