← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 54

Sashe 45

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

97...
Sai na kai habar mayafina da sauri na share hawayena. Duk sonda nike wa Jawad yayi wanda mahaifinshi day haifeshi ke mashi? Abdulraheem ya matso da ledaa da flask ya matsa ya aje gaban Fulani, yace "Fulani Zubaidah ta kawo maki na neman Albarka" sai ta maido da dubanta gareni, tayi murmushi cikin jin dadi, ta bude leda sannan filas, wani bala'in kamshi ya kauraye dakin bakidaya, tasa hannu ta tsamo tsokar tumbi ta lankwanma ta taune ta hadiye, ta dafa kafaduna tace "waya gayamaki abinda nake so diyata? Nagode Allah Yayi maku albarka", sai a wannan lokacin yallabai ya maida waya aljihu, ya juyo ya dubeni, ya dubi kayan dake zube gaban Fulani wanda shi din da muka kwana muka tashi tare bai san dasu ba, kana Fulani dake rike da kafaduna tana ta zuba min albarka, ya maida kai wani gefen daban. Son Zubaidah da darajarta ya karu a yau ninkin-ba-ninkin wanda yake mata, domin wani abu ne da bai taba ji ranar da Fulani ta budi baki ta sawa Mubina ba, to yaushe ma tazo garin? Zai iya lissafawa kwata-kwata cikin shekarun su na aure sau biyu kacal ta taba zuwa karaye. Sanda ya kawo ta su ganta kamin suyi aure da lokacin da suka dawo daga 'honny-moon' a Toronto wato bayan auren. Bayan wannan baisan wani ba, don ita aikinta da abin da ke gabantashine kawai mai muhimmanci. Ta kuma fada ta kara ita shi ta aura ba yan uwansa ba balle a takurata. Fulani bata kai mishi kararta, haka bata kusheta. Abinda takan ce da yayanta kawai shine Taheer yana aure, amma basu ga alama ba, don Mubina ba mata bace. Matar da bazata rungumi miji da iyayensa ba matar aure bace, ba kuma goyon mutunci bace. Shima wannan a bakin Bello yajishi amma shi bata taba taranshi ta gaya mishi hakan ba. Yanzu kam yasan yayi aure wanda ya wanke bakin cikin zuciyarta na shekara da shekaru akan matar sa. Saidai zuciyarsa nace dashi wai Zubaidah ma kamar Mubina zasu dunga samun banbancin ra'ayi, akan abinda yayi bisa gaskiyar shi da kyawawan akidun shi, shine har zata bata ranta a gaban kowa don yace abar Jawad a karaye tana zubda hawaye har ta fishi son Jawad? Yana tsoron kar wannan ya kawo masu matsala cikin rayuwar aurensu mai nagarta da suka soma shinfidawa, yayi zoton Zubaidah zata zam mai ra'ayi irin nasa, mai son duk abinda yake so to amma why zata soma karkacewa tun yanzu? Wani sabon bacin rai ya baiyana a kyakkyawar fuskar shi. Na langabar da kai abin tausayi, zuciyata tayi bakikkirin, ga zatona abinda nayi wa mahaifiyarsa shine ya bata mashi rai haka. Shin abun kirki ya taba zama abin tsiya? Wasu hawayen suka shinfido min a guje, nasa bayan hannuna na share. Fulani tace ciki sausasawa "Zubaidah daina kuka, don Allah, na maki alqawarin zan kula da Jawad kamar yadda kike kula dashi, kiso duk abinda mijinki ke so, ki zama mai biyayya ga umurnin shi.

98....
Ki zama baiwar shi sai shima ya zama bawan ki, ki kula da mijinki sai kiga farin ciki kema". Ta dade tana mun nasiha mai ratsa zuciya duk akan zaman aure, da yake su yallabai sun fita tuntuni. Nayi mata alkawarin zan kula da dauk abinda tace, na kuma gaya mata kukan da nake bana hukuncin da uban ya yanke akan Dan sa bane, kukan SABO ne. Na saba da Jawad fiye da kowa a rayuwata. Hakika zanyi kewar sa amma tunda haka Baban ke so shikenan. Tace "yauwa, haka nake son ki Zubaidah". Duk dakunan sauran matan maimartaba Abdulraheem ya raka ni, kowacce da irin abin kirkin ta da kullin alherin ta cikin leda. Kai ni dai yau na tabbata na shigo cikin zuri'an da ake sona, aka kuma san mutuncin dan adam. Fulani ce da kanta ta rakani turakar maimartaba na gaisheshi yasa min albarka yayi min addu'a mai yawa. Nasa hannun cikin jakata na fiddo guzuri na da ko yallabai bai san don wa na saya ba a Pittsburgh, wato collection na turarukan GIVENCHY, VERSACE, DIOR da BOSS INTENSE. Maimartaba sai yayi ta samin albarka yace "Zubaidah, ina nan ina jiranki shekara mai zuwa war haka ki kawon aboki ko sabuwar amarya don kin ga Fulani na ta tsufa". Abdulraheem yayi ta dariya niko sai na sake sunne kai cikin gyalena cike da kunya. A gidan mu, yallabai na dakin Baba niko ina tare da Inna na Amarya, muna hirar mu ta yaushe gamo, tana kara jaddada mun Muhimmancin addu'a cikin kawanne hali musamman cikin hali na farin ciki ba sai al'amara sun cakude cikin rayuwarka ba. Tace idan uwar Jawad ta dawo dakinta in bata girmanta, tunda ko ba komi TA HAIFI DAN DAYA ZAMO SILAR DUK WANI MATSAYI DANA TAKA A RAYUWA. Sani na kano, Auwal na lagos haka Salisu da Rabi'u duk suna can gidan Awal na kano tunda su suke kula da shago. Gidan sai jafaru na dake aji biyun karshe a sekandire sai yar autar Amarya Sadiya. Duk kudin da ke jakata na zubewa Amarya a gadonta, na mika hannu na ciro dankunnen dake kunnena na farin zinare hade da sarkar sa suma na zube mata. Na sabule duka zabban diamond dake yatsuna guda uku na zura mata cikin yatsunta tana ta mita tanata korafi wai me zatayi da su? Bata sani ba, yadda nake kaunar ta da zan iya cire raina in bata domin farin cikin ta ba abinda zai hana ni yin hakan. Ina son Inna na fiye da komi a rayuwata. Nace "kudi ki kashe, ki ci kaji kisha madara kiyi bulbul. Kayan ado ki daura kiyi sheki kiyiwa Baba yanga abun ki" Tayi murmushi tace Atine kina neman ki maidani kawar ki karfi da yaji, watakila kina mantawa ni ba GOGGON ki bace. Nace Allah sarki! Inama tana nan!! Da saita fiki yin sheki Amarya in har ina raye. Allah ya jikanta da rahma. Ya sanyaya makwancin ta. Na shiga bayin inna don rage mara na tadda bayan gidan sillubebe da shi fari kal ya sha tile. Ga masan tangaran yallabai ya ciki mani buri na ya gina ma inna na. Hawayen dadi ya zubo min ina shiwa masoyin kwarai Albarka.

99....
Haka Inna Lami na bata naira dubu biyar, na bada dubu uku hannun sadiya nace ta kaiwa Atika da wasu zannuwana da yawa ko daurawa ban yi ba, duk cikin lefena ne amma an diddinka. Shima Yallabai haka ya cikasu da kudi suna ta mitar tasu ta wahalar yayi yawa ya fice shi da Abdulraheem. Tare da shi aka raka mu filin jirgin Mal. Aminu, inda muka hawo jirgi mai zuwa Abuja. To kema dai kin san rabuwar tawa da Jawad dole ta zamo very emotional don da karfin tuwo aka bambare Jawad daga jikina yana kuka yana tirjiya. Maimartaba ya rungumeshi yana lallashi. Ban iya na ko juyo ba domin na kasa controlling hawayen idona. To haka har muka sauka a Abuja nida Yallabai ba kalmar data hada mu, kowanne tunaninshi dabam ne dana dan uwansa. Jami'ar da suka zo taryenmu abin ba'a magana. Ga dai Maman Ashshah na hanga a ciki, sai ko ministoci abokan Oga cikin su har da kwamishina Ibrahim Hardo (Baban Ashshah) da ma'aikatan Ministry of Foreign Affairs. Ban san wane irin matsayi Asshah ta bani ba a zuciyarta sabida yadda take daukar abubuwana da muhimmanci, gaba daya iyayenta sukutum ta turo su taryeni a madadinta domin a lokacin ita tana saudiyyah aikin umrah, don haka nima har gobe bani da aminiya tamkar ta. A gefe surukin yallabai ne General Balarabe Dango da babban danshi Yahai, na lura Yallabai ya ji dadin hakan. Motar Yahai muka shigo (Jaguar) da bata fi goma ba kwata-kwata a cikin Abuja gabadaya, yana gabatar mun da ko Yahai wanene kawai sai naji raina ba dadi. Yace yana mana murnar aure, amma baijidadi ba da ban gayyaceshi bikin auren mu ba sai a talbijin ya ji, ko bansan shi da Taheer Hassan ne da Hussainin shi ba? Nace yayi hakuri abin ne yazo cikin gaggawa kuma bani ya dace ya tuhuma ba Hassan din shi ne dan ni dai ban san shi ba. Yace to kai Hassan me nayi maka kake kin gayyana? Ya kyabe baki yace bana son sanya kaina cikin bala'in ku, ko yanzu ban san yadda akayi kayi tunanin zuwa taryena ba. Yadda ka ki fahimtana akan al'amarin nan Yahai banyi tsammani ba. A zatona ba Mubina ta hada mu ba amma ya zamto ita ta rabamu? Ka zauna mata suna zuga ka suna gaya maka karya da gaskiya ka hau kai ka zamar da kanka involved cikin al'amuran yara da haukan Mubina.ka bani mamaki!" yahai ya shafi keyarsa yana murmushi yace "nima daga baya ne nayi tunani na gane ban kyauta ba, tunda ko Baba ita ya baiwa laifi ammam yanzu komi ya wuce. Zubaidah Mubina na maki barka da zuwa cikin Abuja a karo na biyu, matsayin MATAR minister TAHEER USMAN KARAYE. So let the bygone be bygone, ba da jimawa ba in Allah ya yarda Mubina zata dawo dakinta". Ji nayi zuciyata ta narke, wani kululu ya zo ya tokaremin a kahon zucci, (kaji mulkin mallaka irin na Atine). Shiko yallabai na lura wayarsa kawai yake ba tare da kulawa da hirar mu ba, to amman sai wata zuciyar tace dani "ai fushin fari ba naki bane Zubaidah, tunda kin san ko ba dade ko bajima daman hakan zata faru. Tun a ranar da Taheer yasa kafa a gidan ku da sunan neman auren ki, kin ji da kunnen ki yace matarshi zata dawo. Ta dawo din mana? Ance da ita da da yanzu daya ne? Kowa tasa ta fishshe shi.
Chapter 45 · 0% Book details