← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 54

Sashe 39

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

62...
ta dawone inaji daga gona dan naganta abin ba magana .yau cikin saa ban tadda matan gidan masu neman cinyeni ba,ta shimfida mun karauni na zauna duk jikinta na rawa yake ,tana kuka tana fyatar hanci.nace atika, ki kwantar da hankalin ki,ni banzo don in saki kuka ba.idan kina mun irin haka sai kisa na dena zuwa wajen ki, kina mantawa gaba kike dani amma ki dinga kuka agabana ai sai kisa na raina ki ko girman ki ya zube a idona,wannan rayuwar da kukece ban gane mata ba. Tsakani da Allah kina son zaman gidan nan?atika kuka take haikan ,ko bana so atine ya zanyi?komi ya faru nina jawowa kaina koko ince inna ta jawo min dama Allah baya barin hakkin wani kan wani dana auri jibo dake sona tsakani da Allah ai da haka bata sameni ba ni bakida alhakina tuni na yafe miki.wai bakisan aurena ake ba amma baza ki leka gidaba?ki saki jikin ki dani,ni yar uwarkice da bakida wadda ta fini kin tsaya kina TUNA BAYA...... bayan bazai amfaneki da komi ba,ga kaya na kawomiki kije ki wanka kizo kisa ki fito a mutum.kizo muje cikin iyayen mu kiyi komi a matsayinki na yayar amarya ,ki daina jin kan ki bare a gareni ,saboda ni abinda dake damunku ke da inna ni ban dauke shi da wani muhimmanci ba. atika tana share hawaye dake mata zarya atine basan me zance miki ba.amma nagode,sai dai ki hakuri tunda na auri dawaye ban taba zuwa gida ba haka duk saura matanshi bai yarda da fitar muba inba gona ba. in kuma kin fita a bakin auren kine.nayi shiru, wannan har aurene? tunanina kenan. amma a zahiri sai na mike.na sakala jakata ba zan so in kashe miki aure ba kam.amma duk san da kika gaji,kika gane wannan ba aure bane wahala ne,ki nemeni.a shirye nake da in taimakeki yar uwa ta kowanne hali.na tuna maganar marigayiya goggona ne da take cewa (cikin ko wanne hali atine kada ki butulcewa atika)
Na gayawa yallabai zamu sokoto da mamansu ashshah a dawo lafiya kawai yace kwanan mu biyu a sokoto gidan dacta hafsi matar gwamnan sokoto na lokacin.

63.
Suna faman tsimani da duk wani nau'in kayan gyaran sokoto.itace aminiyar maman ashshah. dacta hafsi cewa tayi haka kawai taji na shiga ranta.daga yau duk matsalata da maigidana na nemeta,ta zama uwata a sokoto su ashshah suka yi dariya tace wannan gyaran danai miki zubaidah gyarane da babu kayan da'a a cikinsa face gyara na manya mata na uslin sokkotawa da muka gada iyaye da kakanni.ta tsabtatacciyar hanyar da matan farko suka koyar damu.insha Allahu ranar da duk mijinki ya dandani zumarki kingamadashi zubaidah diyata,tsakaninshi da sauran mata sai de hange daga nesa.babu so ba sha'awa domin kin masu fintinkau .kammo ki sai an danna a guje gaba daya falon ya kaure da dariya .ta karbi lambata na amshi nata ,mun basu kattin gayyata tabbatar mini ita da yayanta maza da mata,masu aure da marassa aure zasu bayyana a abuja ranar luncheoun bakuma zasu dawoba sai sun rakoni dakina.mun iso mun tarradda tawagar kawayenmu sun iso inda akayi kayataccen kamu ranar alhamis da yamma,ranar jumaa wunin tsofaffi mutanen gidan su yallabai da jamaar gidan waziry sunzo gidan yinin amarya da yamma su ashshah sunyi ashoben atamfar mitex fara sol nima ita nasa,saidai kala ya banbanta nawa brown ne takalma da net duka brown sun je gidan maza har dare suna tare da dagin yallabai mata. hajiya barmani mai coge ce ta buga kida a gidan maimartaba suka shiga fili , kanne da yan uwa yallabai sun masu barin naira ba kadan ba amma ni banje ba.ina gida tare da tsoffina,ga rigimar dan lelena jawad inda duk na aje kafa nan zai mayar,yana korafin wai mutane sun cika masu gida na koresu shi zai sha shawarma wasu mata kan tambaye ni wai ince ko dan farine?gashi da girmanshi amma halinshi na yara sai ince duk sokancinsa soja ne idan ya naushe ku sai kunkai kas na juya nace dashi waddanan mutane ka kyalesu sun zo tayamu murna aurene in kuma baka son da daddy sai in koresu? Sai ya rukunkume ni yana bazan sake ba momina

64....
da daddare su ashshah sun dawo tare da abdulraheem. suna ta labarin karamci mutanen su yallabai dana fulani.nikam banyi mamakiba,ai karamci sai dan karamci.abdulraheem yayi kirana dakin awal.ya bani waya sabuwa dal da recharge card mai cin naira dubu goma dakudi yan sardauna sabbi kar acikin jaka wai daga yallabai nayi hidimar yinin gobe na karba kawai dan ance baa maida kyautar maigida nace ni ba abinda zanyi dasu sai dai in aje mishi kurum yallabai bai san ciwon naira ba yayi dariya fulani na gaidaki, tace ai maki ban gajiya kuma tana gaida maigidata da bai son ta jawad ,naji dadi jin wai surukata na gaidani ,na tambaye shi mai fulani tafiso ai mata kyauta da shi a rayuwarta? ya karkatar da kai yace idan kika bata farfesun kayan cikin rago,zuma farar saka,man zaitun da turare miski kin gama mata komai nace nagode abdul. washegari munyi wuni yan matan mu mai tsari,su nana sunji dadi bikin karaye.da yamma aka rinka sauke kwalla da sanduka nakiya alkaki dubulan da bakilawa da sauran abinci gidan sarauta a gidanmu wannan aladarsuce,mai vedio nayi mai daukar hotuna nayi inda duk na gifta su daukeni. Lola rike da "yar kamararta ta dage sai daukar hotuna take don ita komi a hurinta bakone abin zuwa a nuna agidane kasancewarta ba bahaushiyaba igbo hakanan ta lalace a wurin hawan angonci su yallabai tana son ganin mutum akan doki musamman inya tigija akayan gashi manyan many lufdan taja saliha suka kutsa fadar gidan maimartaba tana ta daukar kowa ta gani bisa doki abinci da abin sha mutane karaye yau gidasu acike yake da kwanuka da gidanmu gidan maimartaba gidan waziry garar abinci kawai ake fitarwa.washegari da safe motocin daukar 'yanmata zuwa abuja sun iso tun tara duk sun shiga sun tafi gidan da unguwar sun yi kwal dagani sai ashshah don ita sunyi da alphat din ta zasu zo su tafi da ita ta karaye subi jirgi yawo zuwa abuja haka nima yallabai ya kirani yace kar in bisu ni dashi da gudan ranmu zamu tafi da yamma (jawad)

66...
a lokacin fatima tayo min waya ,nace ina samu lambar tace abdulraheen ya bata,tace bello yaji sauki yanzu haka yana bisa aiki cikin sojojin da aka tura kwantar da tarzomar kasar sudan don haka mu tafi da yaran ta zata iskemu abuja don haka da abdulraheem ya kawo su mukhlas nayi musu wanka dukansu har jawad na shirya su cikin sabbin kakin sojoji iri daya.kowannesu kan shi ya kumbura,jiya ke tafi dan uwanshi burgewa amma jawad yana fushi,yana kumbiri kamar ya fashe,na tambayi dalili ya cure baki yace wai momina,ya zaki sawa mukhlas kayan military? Bayan su baza akai su military school ba,babana ni kadai yace zai kai to akan me zaki sa mana kaya iri daya?kuma wanda yayi ma junior yawa dai dai nine, ki hada min duka kisa mi shi wasu . In wannan yai datti kamin uncle ejiro ya wanke sai insa wannan na kama baki ina mamaki hadama kenan mukhlas ya harareshi yace Allah baza a cirewa kanina ba wa yace dakai baza akaimu military school ba?mu da babanmu yake lieutenant yana da pistol yana zuba bullet yana zuwa operation lokacin da muna jos kai ko babanka baya sa uniform sai body guard dinshi kuma baya da pistol basan sanda nayi dariya ba shiko jawad tuni ya dunkule hannu ya kai mishi naushi na kwaceshi da kyar jawad kai ne fah babba yaya zaka ci zali?yasa kuka yace baki jiba yana zagin babana yace daddy na ba soldier bane? toh ai shima babanshi ne da uncle da daddy duka babankune kada ku kara fada akan su kunji ko?

67.....
suka duka suka gyada kai .mun baro karaye karfe shida da 'yan mitoci cikin mota jeep (BMW)wato sai tsayi ba tudu zuwa airport,inna ce ga ainihin kwalliyar da nayi sai in bata lokacin ku kawai.karfe takwas na dare muna filin jirge abuja dimbin al'ummar yallabai da nawa da suka zo taryanmu Allah yai yawa dasu nida yara nan muka nufa kai tsaye nan muka hade dukan mu shirye shiryen tafiya dinne a rockview hajiya hafsi da mutanen ta sun iso tuni.
Anyi dinner lfy ta kuma kayatar faty bata isoba sai ka shegari ranar luncheoun ni naje na tare ta da yaranta sai abdulraheem dake jan mu mun wa juna kyakkyawan runguma cike da farin cikin ganin juna biki yaci gaba yadda aka tsara bikine na yan boko masu ilmi kuma kusoshin nigeria gabadaya bikin da yaba dinbin tarihi a nigeria ke inkin ganmu nida yallabai alokacin baza kice akwai wata jikkakiyyaba a zuciyoyunmu ba tamkar zara da wata don tsabar dacewa da juna haka fuskokinmu inki duba zallar so da kauna zaki gani ga junan mu sai nayi fatan innama haka ne a zahiri ga yallabai? Wasu dumammun hawaye suka zubo min na faki idon kowa nasa hankici na daukesu amma duk da haka yallabai ya gani domin kuwa juyowa yayi kawai ba zato, bayan tun da muka taso yake ignoring hada ido dani abin daya rada mani a cikin kunnuwana ya gigitani,ya kuma kara dugunzuma zuciyata ranar bakin cikin a gareki ko?
Chapter 39 · 0% Book details