← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 54

Sashe 10

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

39.
Ni nasan kina son yaron nan ko baki furta ba amma don Allah, kisa masu ido, munafurci dodo ne, mai shi yake ci. IDAN BELLO SHI YA SAURA DA NAMIJI A DUNIYA KIN BAR SHI HAR ABADA in har ina raye abinda mutum ya shuka, shi xai girba. Kin ganni nan, ban iya shige da ficen gidan Malamai ba. Takobi na da kowa addu'a. Kada ki nunawa Baban ki damuwar ki, bai san me akayi ba''. ''Ni Amarya na yanke shawara, ki gayawa Baba, xani WANKE-WANKEN da Atika taki xuwa, xanyi wanke-wanke domin ku wadata, Auwal yayi karatu, ku ci abinci mai kyau. Xan kare rayuwata gaba daya a wanke-wanke, bana ko son xaman Karaye, na tsani Karaye, na tsani mutanen da ke cikin ta banda Uwata, Ubana da Liman. Allah ya taimaki Goggo na da bata nan, nasan da anyi tashin hankali wanda bakya so Amarya, da an bata min ranta a banxa, da ta hanani tafiya wanke-wanke''. ''Allah yayi maki albarka Atine, Allah kuma ya baki miji wanda yafi Bello komi da komi''. Sai nayi murmushi kawai na kama harkar gabana, cike da fin karfin xuciya. Amma can a karkashin xuciyata nasan nayi rashi, babba kuwa. Wanda na tabbata cike shi sai dai wani babban ikon Allah (Tuna baya Shine Roko).

40
Atika, sun fa kawo lehe mallam, bari kaga abin arxiki. Baba ya xubawa kaya ido kaman mai ganin abin tsoro da kyama ''ina Atikar ta samo wannan mijin, dan yankan kai, ko dan birni?'' Inna ta kyalkyale da dariya cikin jin dadi ''dan Waxirin Karaye ne, Muhammad Bello sunan sa, ai Atika tayi farin goshi''. ''Bello? Bello wane? Wanda na baiwa Atine?'' Ya jero tambayoyin da bashi da yakinin samun amsar ko daya, ''to dai ina jin bashi bane, don wannan Bellon Atika yake so ka kuma je ka tambayo shi, wa ya aiko wa da lefe?'' ''Wai wane irin xancen banxa ne kike haka Lami? Da alamu baki da cikakken hankali, ya xa'ayi ana neman kanwa kice yar ce? Ko an ce miki Atika ta rasa miji?'' Inna ta hasala ''ko dai wane irin xancen banxa kake? Sai ka je ka shafo labarin daga can sama inda ya sauko'' Ta shiga maida kaya yanda suke. Ya tsallaketa, nitsatstsen dattijon, a nitse ya tadda Amarya, ''Saude meke faruwa ne? Ku fiddo ni duhu, ku yaye min duhun da kuka sanya ni''. ''Ka ganni nan Malam, tun safe ina nan xaune, ban san me ake a tsakar gida ba'' Mallam yace ''xurfin cikin ki bana son shi Saude, xaki gaya min ne ko a'ah?'' ''To xan gaya ma gaibu ne, abinda bani da masaniya akai? Daga inda labarin ya faro can xaka neme shi, ni ina daki, na san me ake a gidan Waxiri ne?'' Ya tabbatar ba xai ji kalma ko daya daga bakin ta ba, kasancewar ta mai KAWAICI da KAU DA KAI akan duk wani abu da ya shafi ATINE. Ya juya ya fita ya nufi neman bello. To xance dai ya bayyana ga Baba, Bello Atika yake son aure yana kuma son a sanya ranar auren kurkusa domin xai tafi karo karatu Kasar Sanyi da ita. Baba a rikice ya dawo, karo na farko daya xargi Lami da asirin da ake cewa tana yi tun bayan auren su sama da shekaru sha biyar. Bai ce komi ba.
**************
Nayi sallama dauke da koko, mai cike da ruwan farau-farau. Na durkusa na gaida Baba, ya amsa ta hanyar daga kai kawai, na mika mai koko ya amsa ya kafa kai ya shanye tas, ya ajiye kokon.
[9/24, 9:13 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/24, 9:14 AM] A A Dboy: Tuna Baya 40-45

41.
Ya dube ni da idon rahmah ''Atine kar ki damu, albarka na tare da ke, albarkar Uwa da Uba, ba xaki taba tabewa ba!'' Murmushi nayi, ''Baba ka aurawa Bello Atika, kada ka ji nauyi na, da ni da Atika duk daya ne, ba banbanci. Na xo ne in gaya maka ni xani WANKE- WANKEN da Atika ta ki xuwa, ko a sami dan abinda xa'a kai mata daki, ko a samu a biya kudin makarantar Ya Auwal, xan kare rayuwata duka a wanke-wanke domin taimaka maka Baba na''. Baba ya sa habar taguwar sa ya share ido yace ''Atine ke da Uwar ki tausayi kuke bani, baku dauki rayuwa a bakin komi ba. Don haka har kullum nake addu'ar Allah YA YI MAKU ALBARKA. Duk wani abu da xai taimake ni shi kuke yi. Ku kyale Lami da diyar ta da mai kowa mai komi, ''kowa yace gonar wani baxa tayi albarka ba, tashin ce baxa tayi ba''. Kuma da muguwar rawa, gwamma kin tashi. Tashi jeki, xan nemi Talatu ta kai ki gidan aikin, dama sun matsa mani''.
***********
Na hade kayana tsaf, cikin kullin dan kwali. Duk wasu shirgin Bello na tattara su cikin jakar shi har kuwa da takardar da nike ta kwakwar ajiyar ta na ba Salisu (mai bin Sani) nace ya je ya ba Bello, idan baya gidan su ko gidan Maimartaba yana gidan sa na bayan gari. Talatu tayi sallama muka amsa, suka gaisa da Baba da Amarya. Ta lalo kudi 'yan dari-dari da muke jin labarin su an buga, ta bawa Baba, na naira dubu goma, kudin da ko a mafarki, bamu taba gani ba a rayuwar mu. Kai ni ban ma taba jin inda aka fara bada kudin aiki ba'a fara aikin ba sai wadannan. A cewarta wai don sun matsu da 'yar aikin ne domin matar gidam tsohon ciki gareta bata da mai yi mata hidima. Baba yace ''Talatu na ba Allah, na baki amanar yarinyar nan, Atine yarinya ce karama, dole ce ta sami turata wanke-wanken nan. Domin duk halin matsin da kake ciki, gara Dan ka ya tashi a gabanka, duk wani wulakanci xa'a raga masa kana nan.

42
Nasan ni talaka ne futuk, amma ban taba xuwa wajen wani mai mulki neman alfarma ko bashi ba, don haka in aka wulakanta Atine, bafa xan kyale ba, xan iya jure duk wani halin talauci in dai akan MUTUNCIN 'YA'YA NA NE''. Hajiya Talatu tace ''Maikalwa kada ka damu, gidan Yallabai Magajin Gari, babu wulakanci a cikin sa domin 'ya'yan Maimartaba mulki suka tsotsa ba dukiya ba. Share- share ne kawai da goge-goge xata yiwa matar Yallabai kullum, sai dauraye kwanukan da aka ci abinci, bayan wannan ba abinda xatayi. Atine xata ci mai kyau, xata sha mai kyau, xa kuma ta xaga duniya ta ganta domin yanxu daga nan, Abuja, babban birinin tarayyah muka nufa cam gidan matar Yallabai take. Duk shekara xan je in kawo ta ganin gida In shaa Allah.'' ''Wannan duk bai dame ni ba, idan Atine na cikin wulakanci, xan karbi 'ya ta ne kawai a hannun ki. Maganar xuwa gida bayan shekara a barta, bi ban ce ba, sabida ina gudun surutun mutanen Kauyen mu. Illa idan lokacin da nake gani ya dace in mata aure yayi, xan yi maki magana ki dawo min da ita''. Hajiya Talatu tayi dariya tace ''shikenan, ke fa Amarya me xaki ce?'' '' Me kuwa xan ce, banda kada wanke-wanke ya hana Atine sallah, da sauran ibadodin da suka hau kanta?'' Hawaye suka xubo min sharrrr! Na tausayin iyaye na, na san dole ce xata sa su TURANI WANKE- WANKE. Idanuwan su sun fada, bakunan su sun fada; neman halalin su ne. Ni kuwa wulakanci da xan fuskanta, wanda Baba ke fadi xan jure, don cigaban samun halalin sa. ''Na bar gida, cike da kewa da kaunar ki, Inna ta Amarya. Na bar gida, xuciyata cike da bakin cikin ki, kishiyar Inna ta Lami. Na bar gida, xuciyata cike da kaunar wanda bargo, ruhi, ba xai taba daina kaunar sa ba; MUHAMMAD BELLO WAXIRI KARAYE''. Haka na rubuta da Ajami, saman dakin Ya Auwal, da gawayi, a lokacin da Talatu ke sallama da su Baba.
TUNA BAYA SHI NE ROKO FARKON LABARIN KENAN!

43.
Tafiya muke, tamkar baxa a daina ba. Nayi barci, nayi kalle-kallen gefen hanya har na gaji. Wajajen Isha'i muka shiga garin Abuja. Na bude ido na mutstsike su na dirki kallo son raina, ga fitulu kala- kala sun haske ko'ina kamar rana. Ji nake kamar wata duniya ta daban ba wannan tamun wadda muke ciki ba. Ga wani irin sanyi da nike ji yana ratsa kasusuwa da bargon jiki na, tamkar a Aljannah na ji ni. Direban ya dauke kan motar ya shiga wata kebantacciyar anguwa ta daban, wadda ko a Abujan nasan wannan daban ce (Ministers Hill Colarado Close). Da alama sun san direban don mu ba'a wani bincike mu ba aka daga mana kafa muka wuce. Ya shiga keta gine-gine masu ban tsoro a gareni, kafin ya tsaya a wani gida mai katuwar kofa kamar bangon duniya, wata irin wayar lantarki ta xagaye katangar gidan gabadaya. Sojoji ne ke gadin gidan, da alama sun san Hajiya Talatu don har daga mata hannu daya daga cikin su yayi. Muka doshi wata tangamemiyar kofar gilashi dake fuskantar mu amma ba'a iya hango abinda ke cikinta sabida duhun gilassan. Kofar ta bude da kanta (automatically). Sanya kafata ke da wuya, naji na nitse cikin wani abu mai laushi kamar katifa, ga wani irin kamshi mai dadi, na koma baya da sauri ina haki. Haj. Talatu tace ''Atine, ki saki jikinki don Allah, kada ki nuna mamakin komi kika gani a gidan nan, ki nuna ke kamar ba 'yar kauye bace. Domin kin fito daga tushen mai gidan, KARAYE. Matar gidan bata da mutunci, in kikayi wani abu da bai mata ba tana iya cewa a koma da ke''. Jikina yayi sanyi ''kinsan bata da mutunci kika kawoni baki gayawa iyaye na ba?'' Haka na fadi a xuciya ta. Tsallake wannan sashe, tsallake wannan falo har muka dangana da kuryar gidan wato ainihin sassan matar gidan
Chapter 10 · 0% Book details