← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 54

Sashe 15

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

61.
Can anjima Aunty ta rika kwala min kira na je na tsugunna a gabanta, tace ''kwashe shirgin ki daga dakin ki, ki maida su dakin da ke kusa da shi, wannan falle dayan, Tom xai kwashe injinan sharar da ke ciki, na bayar a sayo maki katifa'' nace ''to'' murya ta abin tausayi. Ina kwashe kayan ina hawaye don ba karamin sabawa da dakina nayi ba, duk da cewa shima wancan dakin cikin bangaren Auntyn yake, amma babu toilet, don haka nakoma na tambayeta ko da wane toilet xan dinga amfani? Ta kunduma min ashar tace ai talaka wai iya samun wuri ba, a gidan Ubanki ba a filin Allah kike kashin ba? Kamar ince da ita ai in ma a filin Allahn ne, akwai kasar da xamu haka mu bixne, nan kuwa fa? Da tangareren shine abin takawar ku? Sai da taga dama tace in dinga shiga dakin muna amfani dashi mu biyu.
Daga baya Tom yake gaya mani mai raino ce baturiya Aunty ta dauko bada sanin Oga ba, sabida a gobe ne xata koma aiki, tuni ta so ta dauko ta tun Babyn yana sati biyu sabida hutun da aka deba mata ya cika. Yace Oga yayi-yayi ta aje aikin nan ta kula da yaron taki, nonon ma da take bashi, wanda ba kullum ba, ba karamar badakala a ka kwasa da ita ba kafin ta yarda ta dinga ba shi sau uku a rana, sai da yayi karar ta gun Baban ta tukunna. Don tana tsoron Baban ne yasa take bashi amma ita tana ganin rainon yara bai dace da ita ba wannan lokacin da take kan gabar kuruciyar ta, haihuwar ma Allah ne ya kaddari yaron mai numfashi ne a doron kasa, amma bata shirya mata ba, ba kuma kokarin da bata yi ba don xubar da cikin abin ya ci tura, karshe dole ta hakura, don har kasar waje ta je a fitar mata sun tabbatar mata ko dai ita a rasata ko mahaifar gabadaya, sabida cikin ya girma sosai a lokacin shiyasa ta hakura. Nace ''amma da aka haife shi ai gashi nan tana son shi, ko kuda bata bari ya taba mata shi''. Yace ''wannan ne kuma bani da tabbas a kai (tana son shi ko bata son shi?)'', Tun xuwan Elizabeth bama jin dadin xama da ita, kwata-kwata ta maida mu 'yan aikin ta sai kace itama ba 'yar aikin bace. Ita aikin Baby kawai take wanda nake ganin kullum ta sa shi cikin wani keke ta tura mai fankon fida a baki (kan fida kawai babu fidar da turawa ke sarrafawa don hana yaro kuka) ko ta dau keken goyon jarirai ta hada da bayanta ta kulle, bayan ta sanya shi a ciki, tana harkokin ta ko kallo bamu isheta ba. Wani xubin kuma sai ta sashi cikin wani irin lilo mai kamar gado tana cillawa a hankali, hatta madarar da take bashi a kididdige take, sai ta auna, ko kusa ko da wasa bata bari wani cikin mu ya je ko kusa da shi.

62.
Duk abinda Tom ya dafa sai tace bai yi mata ba, ya sake dafo mata wani. Wata rana kuma taje kasuwar Wuse (Wuse-Market) ta sayo kaguwa da dodon kodi taxo ta soya, yawancin abincin ta kwari ne, in ta so kuma ta aiki Peter manyan gidajen cin abinci dake cikin Abuja ya sayo mata abincin kasarsu, wanda duk rabin su tsutsotsi ne da ganyayyaki. Ranar da na fara ganin ta tana loma da tsutsotsin nan, wuni nayi ina kwarara amai sabida kyankyami, daga ranar kuwa ko plate ta taba bana kara cin abinci da shi, ita kanta ma tsantsamin ta nakeyi. Gata da kaxanta a toilet, sai ta cire auduga (pad) batacciya ta ajiye a kan bahon wanka, sai dai ni da abin ke daga min hankali in dauke mata. Ko ta jika kaya taki wanke su sai sunyi tsami haka tun xuwanta bandakin mu yake wani irin xarni. Ni dai na ji an ce turawa suna da tsafta, amma wannan ko a cikin kaxaman turawan ma ta daban ce. Ko brush tayi bata san tasa ruwa ta wanke kumfar daga cikin sink ba haka xata barta ta bushe, ko kuma ni in wanke mata. Gata da fadan tsiya, Tom boyi-boyin ta, Peter dan aiken ta, ni kuwa 'yar aikin ta, Ejiro da baya sakar mata fuskar har da xata raina shi, shi ta mayar makiyin ta, kullum cikin bata shi take a wajen Aunty, don dai Auntyn tana son aikin sa ne kawai da tuni tasa an sallame shi. Tsaye muke ni da Tom a kicin kowa na aikin sa, yayi kwafa yace ''nifa xaman matar nan ya ishe ni Tine'' nayi dariya nace ''da yake kai ka ajiye ta ba?'' yace Allah ba xancen wasa ba, kiga kullum sai na gama abinci taxo tace bai mata ba, in sake, an gaya mata aikin ta nake, Allah ko Oga na ban taba yi mai girki yace bai mishi ba, sai wannan matar, who the hell she thinks she is, tana 'yar raino ina kuku, matsayin me ta fini?'' Nayi murmushi da ya kara kular da shi don ni kadai nasan hakurin da nake da Elizabeth, shi nashi shafar mai ne ''kome yake yi daurin gindi ta samu daga Uwargijiyar ta, amma da baxa ta yi ba''. Tom ya kuta yace ''ban ga dama ba ne, na rantse da tuni da bar gidannan...,

63
...don Oga bai san da xaman ta ba, a tunanin shi Aunty na tafiya da Babyn wajen aiki ne'' nace ''akan me xaka fada mishi? Ina ruwan ka da sha'anin su, kai dai kayi aikin ka na kuku, a biyaka ba shikenan ba? Ni ka ganni abinda Allah bai daura mun ba kenan, shiga abinda babu ruwa na. Idan ba so kake Aunty tayi sanadiyyar lalata hanyar abincin ka ba''. Bai yi magana ba, amma yanayin fuskar shi ta nuna maganata tayi tasiri a tare da shi. Rannan Aunty ta tafi aiki, Elizabeth na wanka ta bar Babyn yana kyankyara kuka, ba tun yau ba ina kallon ta idan har ba Auntyn na gida ba bata wani mai da hankali kan yaron, sai ta bar shi yayi ta kuka har Allah ya gajishshe shi. Naji baxan iya jure kukan da yaron ke yi ba, domin kuka yake har cikin kwakwalwata. Na lallaba na leke dakinta naga bata fito ba, na shiga da sauri na sungumi Babe nasa a bayana, na dau towel din da aka nade shi da shi ina jijjiga shi. Wannan shine babban buri na a rayuwa; in ganni goye da jariri, ina jijjigashi, ina yi masa rawa ina cilla shi ina cafewa. Rabona da goyon jariri tun ina rainon Jafaru. Don haka yau na jini cikin wani sabon nishadi. Shi kuma jaririn da na tabbata ba'a taba goya shi ba, tunda uwar sa ta haife sa, sai yayi tsit daga kukan da yake, yana ajiyar xuciya. Sai naji tausayin yaron ya kama ni. Tausayin sa nake, ba don bashi da gata ba, yana da gatan komi, amma ya rasa gatan da yafi komi amfani da muhimmanci a gareshi, watau dumin jikin Uwa, a dai-dai lokacin da yake tsananin bukatar shi. Na tabbata ba kukan komi yake ba tunda babu yunwa a tare dashi, illa kukan jin sa shi kadai ba tare da kowa ba, balle Uwar da xai laluba ya rungume har ya samu damar tsotson abinda yafi komi dadi a gare shi, wato nonon Uwa. Ban san sanda Elizabeth ta fito ba sai jin ihunta nayi a kaina tana tafi tana kakabin a kawo mata agaji ''Help! Help!! Help!!! The baby will die'' wato Dan xai mutu. Nayi saurin sauke mata shi saboda yadda ihunta ya kidimani ya gigitani.

64.
Wai ashe duk wannan ihun da take na goya shin da nayi ne, da gudu ta xo tana tattaba kafafun shi ta gani ko na karya shi? A sukwane Ejiro ya shigo ta shiga gwada mishi tale-talen da nayi wa Baby har tana daukar filo tasa a bayan ta da xani, yayi tsaki ya fice nima na fice yana yi min korafin ni me ya kaini shiga shirhinta. Ashe bata bar xancen ba domin Aunty na dawowa da gudu ta kai mata dan ta tana kuka wai baxa ta iya ba tana gani in kashe shi a daura mata laifi, ta gwada mata yadda nayi mishi. Auntyn ta kira ni tasa ni a gaba, yau ma firji ta sani, wai karambani na yayi yawa, gobe in kara goya mata Da. Don haka washegari na tashi da matsanancin xaxxabi ko gani bana yi sosai, musamman da yake a watan Fabrairu muke, sanyi yayi tsanani ainun. Aka kuma sani a firinji, na kwana hancina na yoyo, kuma a cushe ta yadda hatta numfashi ta baki nake iya futar dashi. S haka na rarrafa na shiga dakin Aunty don ka'ida ne kafin ta fito naa gama da falo, da xarar ta fito sai in shiga cikin dakunan barcin in gyara mata. In banda rawar dari ba abinda nakeyi duk da riga (sweater) mai kauri da ke jikina, ina yi ina hutawa in na jiyo motsi in yi saurin mikewa, in cigaba. Sama-sama na jiyo muryar Aunty da ke 'dinning' wato kwararon da aka xagaye da farin labule da makeken tebur, domin cin abincinsu wanda ke gefe guda na cikin falon, tana lissafo kudin aikin ma'aikata na wannan watan, da alama da Maigidan ta take magana. Yana magana ne a hankali don haka bana jin me yake cewa, sabanin ita da take da karfi, don daga baya ma fada-fada ta koma magana wai babu inda Elizabeth xata, waye xai dinga kula mata da Babyn sai dai in shi xai dinga goya yaron yana tafiya nashi office din, amma ita baxa ta bar aikin ta ba, sabida wani yaro can (unwanted Babe) da yaxo mata ba'a sanda ta shirya haihuwarsa ba. A fusace kuma cikin fada yace ''ina yarinyar da ke maki aiki da Fulani ta aiko daga KARAYE? A bata Babyn ta dinga kula da shi, amma wannan matar yau xata tafi...,
Chapter 15 · 0% Book details