Sashe 11
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
44.
Hajiya Talatu ta danna wani abu a jikin kofar, sannan ne kofar shiga sassan ta bude muka shiga. Wata murya ce ke fitowa daga cikin wata farar akwatu mai hoto, da tafi min kama da akwatin talbijin, tana fadin wani abu cikin harshen turanci (computer). Hajiya Talatu tace ''tana wanka wai mu jira ta''. Nace ''to ke turancin kike ki? Koko talbijin din ce ta fada maki?'' Harara daya tayi mun na ja bakina na bame da mukulli. Xaune muke tsayin awa daya, biyu har uku, ta fito bata fito ba, a raina nace wannnan wanka ko daye fata? Amsa ga tambaya ta, sai muka ji motsin bude kofar ta, tana tafe da wani xungureren ciki irin na haihuwa yau ko gobe. Na dauka xan ga wata kasaitacciyar Hajiya wadda taba arba'in baya, sai ganin mace nayi tamkar budurwa. Baka, 'yar gajeriya, hancin ta da fuskan ta duka gajerun ne, idanta mitsimitsi kamar 'yar chinese sai dai 'yar lafiyayyar fatar ta mai tsananin taushi da sheki kadai, ta isheta yiwa ko wani irin hadadden namiji yanga; musamman a wannan xamanin da muke ciki da kyawun fata shine kyau, ba kyawun halitta ba. Tana sanye da dogon siket din Jeans wanda ya kama jikinta sosai da 'yar riga mai xanen tutar Amurka (ja,fari da shudi). Gashin kanta cure cikin wani xagayayyen abu da alama doki ne ya sammata, (ba nata bane). Ke da ganin ta kin ga cikakkar bahaushiya, amma 'yar duniya, idanunta a tsaitsaye kuma a soye kamar na soyayyar gyadar Kano (marau-marau). Tayi 'yar hamma tayi mikar data turo xungureren cikin ta gaba tace ''wash, Talatu sai yau?'' A dai-dai lokacin da ta kai dan duwawunta uwa tafin hannu cikin luntsuma-luntsuman kujera. Muka xube a kasa muna kwasar gaisuwa, tana amsawa a yatsine kamar dole aka yi mata, muryar ta kamar an shaketa, ta dube ni sosai tace ''mike tsaye'' tare da kai hannu ta toshe hancin ta. Ta kare min kallo tas, daga sama har kasa, tayi tsaki tace ''ina wannan 'yar siririyar yarinyar xata ita mun irin gyaran da nike so a dakunana?
45.
Da wanne kaxamin hannu xatayi mun wanke- wanke mai tsabta da maigidan nan xai iya cin abinci da shi?'' Talatu ta sauke kai irin yadda bayi ke yiwa iyayen gidan su cikin ladabi ''ranki ya dade, Fulani ce tace a daukota, domin 'yan gidan su nada tarbiyya, hakannan girman kauye ne sun saba da aikin wahala. Ki bar ganin ta haka lange-lange, babu irin aikin da baxa ta iya yi miki ba, wanda su maxa, karti, masu aikin ki suke yi miki. Amma idan kika ga kwana biyu baxata ta iya ba, sai a maidata a dauko miki katuwa'' tayi tsaki sabida haushin da Talatu ta bata, tana toshe hancin ta dai tace ''shikenan, xan gwada ta kwana biyun in gani, kuje falon waje xan turo Tom ya nuna mata dakin kwana, ke kuma ki kwana a dakin baki, gobe da safe xan ganku''. Bayan Talatu ta shiga dakin da xata kwana, wani saurayi ga dukkan alamu kabila ne, ya shigo ya dube ni ''Oya yaro muje in nuna maka daki in ji Madam'' na bishi a baya rungume da 'yan kullin kayana, ya bude wani daki da baya da nisa da sassanta, ya bani mukullin a hannu na ''ga dakin ka nan, ka kwanta ka mige, ka futa gajiya ko?'' Da alama shi mai kirki ne, nayi dan murmushi ''to''. Ya sake kallo na ''yaro kayi hakuri da Madam, she is bad (bata da kyau), muma duka muna hakuri da halin ta ne, ka kula duk abinda tace da kai, in kayi kuskure daya, ranka xaya baci.'' Na gyada mishi kai cikin sanyin jiki '' ya sunan ka?'' Ya tambaye ni ''Atine sunana, kai kuma fa?'' Ni sunana Tom. Atine, xan ke ce maka TINE, xaka amsa?'' ''Ba komi Tom, ka kira ni duk yadda ka so'' to sai gobe, ka kwana lafiya, Allah futa gajiya''. Na dubi daki matsakaici, an shimfide shi da jar darduma, amma bata kai taushin wadanda na gani a baya ba, haka labulayen dakin jajaye ne, masu kyau, ga wani bakin tebur (t.v stand) an daura wata 'yar akwatu akai (talbijin), a samanta ma wani dan akwatin ne (receiver). Akwai kofofi guda biyu a cikin dakin, daya a dama daya a hagu, na bude ta hagun; bandaki ne fari sol da shi, kamar tuwon ka ya fadi,
[9/24, 9:14 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/24, 9:14 AM] A A Dboy: Tuna Baya 46-50
46
Ka tsugunna ka dauka ka ci, komi dake cikin bandakin fari ne sol. Na bude ta daman. Ni Atine mai xan gani? Gado ne na gogaggen katako, lullube da lallausar bargo, da xanin gado mai taushi, ga filallika har guda biyu, mudubin dogon yaro da abin xaman sa (stool), ga sundukai masu taya irin na lefen Atika, babu komi cikin su, wanda ke nufin, in xuba 'yan tsummokarana a ciki. Na kuwa bude na jefa su ciki, uwar dakin ba darduma, sai wani irin falle-falle a jere irin na bandakin, wanda na lura duk gidan ma shine har jikin bango (tiles), wadanda in bakayi da gaske ba, sai su kayar da kai don santsi, don haka nake taka su a hankali ina kuma hadawa da kama bango. Ban kwanta ba, na shiga bayan gidan don in dauro alwala, in sauke sallolin da ke kaina, na Maghriba da Isha'i da suka riskemu a hanya. Banga wani famfo ba sai na jikin kwamin, mai kama d kwale- kwale, na tsaya daga gefe, ban yarda na shiga daga ciki ba kada inje in xame, na kunna famfon na tara hannuwana biyu, ba sai naji ruwan xafi tafasashshe ba? Na kwalla kara iyakar karfi na, ina yarfe hannu, na ji shigowar mutane a guje, Hajiya Talatu ta daga murya tace ''kina ina?'' Nace ''gani nan a bandaki'' tace ''to fito mana''. Na fito ina haki, ita da Tom suka hada baki suka ce ''lafiya?'' ''Ina fa lafiya Talatu, na kunna ruwa in yi Alwala na ji tafasashshe, don ma Allah yaso bai salube mun hannu ba'' na fashe da kuka. Talatu da Tom suka dubi juna, ya tambaye ta ko me nake cewa, domin hausar tashi bata yi kwari ba, tayi dariya sosai ta gaya mishi da turanci, shima yayi dariya, muka dunguma gaba daya cikin bandakin. Ya kashe fanfon dana kunna yana ta xuba yace ''baka gani famfo har guda uku me? Wadannan guda biyu, dake kwami, na wanka ne, na jikin 'sink' dinnan, shine na amfanin da ba wanka ba. In xa'ayi wanka, in ana bukatar ruwan dumi, shine ake kunna wannan, a kuma kunna wancan na kusa da shi ya sirka shi, bayan an toshe rariyan da wannan abun. A shiga ciki ayi wanka sai a bude ruwan ya fita.
47.
Wannan da yake rufe, xama akeyi ayi bayan gida, a murda wannan, tayi floshing dinsa, wannna na kusa da shi kuma sai a hau, a murda wannan sai yayi ma tsarki, ba sai ka sa hannun ka ba, O.K?'' Na gyada kai, ''gobe xan xo in koya ma kunna t.v da a/c, right?'' na sake gyada kai, suka fita na rufe kofar. Na idar da sallolin da ke kaina, na rufe da nafilfili na musamman. Na daga hannu nace ''Ya Ubangiji, ni baiwarka ce, mai yawan sabon ka, dare da rana, safe da yamma, fili da boye. Ya Allah kai ka halicce ni, ka raineni, ka bani ikon shigowa wannan gida, domin neman halak dina. Ya Allah kaine mai kowa mai komi, ya wanda Al'arshin sa yake sama, wanda Rahmarsa ke Aljannah, axabarshi da ukubar shi ke wuta. Ya masanin siirn da ke rufe, ya Ubangijin lamarina. Don sirrin dake cikin Suratul Rahman, Yasin da Waqi'ah, wanda in ance LA'ILAHA ILLALLAHU,, yake cewa MUHAMMADUR-RASU LULLAH. Wanda ikon ka, mulkin ka da buwayar ka ya xarta duk tunanin mai tunani. Ubangijin sammai da kassai, buwaya gagara misali. Lallai dukkanni na, xunubi ne. Kuma kaine mai rangwame, mai gafara. Na roke ka, ka sadar da ni alkhairin da ke cikin xama na a wannan gida, ka nesanta ni da dukkan sharri da abin kin da ke cikin sa. Ka bani hakuri, juriya da karfin xuciyar xama da iyayen gida na da duk wanda nake tare da shi cikin gidan nan lafiya''. Na kwanta a gadon da ko a mafarki, ban taba gani ba. Na ja bargon da ko a tunani ban taba tunanin irinsa ba. Na tuno karaunin mu, na tuno ginin gidan mu; katangar ta tsage, rabin ginin ya rufta. Dukkannin mu in damuna ta xo bama jin dadin kwanciya sabida yoyo. Na tuno sauron da ke kumbura mana fata, ba yadda xa muyi da shi, sai dai mu bishi da duka da hannun mu, in bamuyi sa'ar samun sa ba, ya dawo kunnuwan mu yana mana eho, ya sha jinin mu, muxo dukan shi mu doki kan mu