Sashe 23
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
94.
Ya taho a guje ya rungume ni, yayi wani irin ajiyar xuciya, hawaye sun hade da majina, na ja 'tissue' ina share mashi ''Momi na, ina kika tafi kika barni? Suna ta tsokana na wai sai dare xaki dawo, shine nake dukan su, don Allah kada ki fada mishi, ba xan sake ba Momi''. Nayi gaggawar daga shi na rungume a jikina, fuskar Tom ba annuri yace ''daga ina, sai yanxu Tine? Kin samu fargaba. Oga yayi waya Jawad ya fada masa yau kin dade baki dawo ba. Ya yi fada sosai, yace ki rabu da Aishah, ya jaddada ya kara jaddadawa, kuma ki jirayi wayar shi 9:00pm''. Jikina yayi sanyi. Na isa daki na kunna A/C, na fara yiwa Jawad wanka, sannan ni, shirt ce baka nasa maishi da farin wando. Tom (cous-cous) yayi da miyar macen Tolo-Tolo, naci nayi nak, nayi-nayi Jawad yaci ya kiya, wai shi dole sai kamun waken suya, gashi kwata-kwata babu waken suya a gidan ko kwara daya. Na gayawa Peter yace xai nemo. Da kyar na samu na lallabeshi, sai da yaga Peter ya dau mota ya fita sannan ya daina kukan, ya dawo ba'a samo ba, nayi masa inkiyar kada ya fada masa, nasan ya manta. Da daddare mun yi shirin kwanciya, na canxa mai kayan barci nima haka, na kulle kofa muka kwanta, Jawad baya barci idan har bai rabu da jikina ba, na manta shaf Oga xai yo waya. Can tsakar kaina naji bugun kofa, na mike na daura xani da mayafin sallata ''ki fito, Tine Oga a waya''. Tunda naji ance Tinen, nasan Tom ne, shi yace bai son Zubaidah ya riga ya saba. Na ce masa ''ka fara gayawa Aunty Oga yayo waya kamin ni?'' To sarkin tsoron Aunty, da yace in kirawo ta, xan kira kin ne? Ko in xai kirata, bata GSM xai kirata ba?'' ya fadi cikin turanci
95.
Na dauki wayar Abban Jawad a falon su Tom, gudun fitowar Aunty. Na lume cikin kujera. Mun gaisa kamar yadda muka saba wato cikin mutunta juna 'Zubaidah, wa cece Aisha Ibrahim Hardo, wanene Alphat Ruma, wanene Yusuf Dabo? Wanda ya baki 'American-Wears' cikin akwati? Wanda ya kawo ki kofar (gate) a motar Camry?'' Mamaki ya kama ni iyaka. Oga ya koma tsibbu? Babu raini tsakanin mu, bana yi mishi musu, bana yi mishi karya, wadannan sune halaye na dake BURGESHI. ''Aisha Hardo, class-mate dina ce, nace muyi kawance har taxo gidan nan kwanaki ta yiwa Jawad dina hidimar data sani sakin jikina da ita. A yau ta ce lallai inje inga wanda xata aura wanda shine 'Alphat Ruma', dayan daka ambata, ni ban ma taba jin sunansa ba. Amma ina jin wanda na gansu tare da Alphat ne. Baki, mai matsakaicin tsawo, shi ya bani kayan daka ambata. A matsayin tsarabar New Orleans, kasacewa ta aminiyar Aishar su''. Ina jin sanda yayi dariya ''dadi na dake; fadar gaskiya a duk inda take, bakya karya, bakya ha'inci. Ina Dan ki, me yake yi a daren yau?'' ''Jawad yayi rigimar shan kamun waken-suya, ya yiwa su Tom rigimar rashina. Lallai ne a kawo waken-suya gobe, in ba haka ba dukkannin mu ba mai barci''. Ya dau lokaci, bai yi magana ba, xuwa can ya ce ''yaya karatu ina fatan kina bita sosai?'' ''Ana yi'' ''ba ku bukatar komi nan Canada? Xan xo unexpected as usual, amma xan gaya maki ina gab da xuwa, don in samu delicious tuwonki, xan samu Zubaidah? A nan ina matukar kewar abincin ki. Zubaidah, 'KE KADAI CE XAKI YI GIRKI IN JI NA CI BAN YI TSAKI BA, BAN TURE KWANUKAN DA RAGOWA BA'. Na lumshe ido a hankali, taushin muryar shi ya ratsa har cikin kwakwalwana, da kyar na iya na ce ''xa'a samu Yallabai, har abin da yafi tuwo, wanda nasan Ba-Hausan bakinka xai soshi. Wai da gaske ka ce in rabu da Aishah?' ''Idan har xata sanyaki turbar samarin ta ba? If not, ki gaida ASHSHA IBRAHEEM HARDO''
[10/8, 5:25 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/8, 5:27 PM] A A Dboy: Tuna Baya 96-100
96.
Kalamin Oga, sun bani mamaki, ta yaya xai ce ba xanyi samari ba? Alhalin ya ce muna da 'yancin yin komi gidansa tamkar 'ya'yan da ke gaban iyayen su? Na yi murmushi ''In shaa Allah, xan kiyaye, but please do for me one favour (wato kayi mani alfarma daya) ka gaya min wanda duk yayi maka bayanan da kayi min yanxu, game da su Aisha, I am extremely intrigued!'' Dariya yayi, cikin matsanancin nishadi. ''Xubaidah, kin manta na ce ''XAN KULA DA KE!'' Don haka a ko'ina nake cikin duniya, ina ji, kuma ina ganin duk wani takun sakarki a rayuwa. Kada ki tsaurara bincike, Zubaidah, ki shafa min gudan raina JAWAD''. Har na kwanta barci, ina juya kalamin Ogana, mutum ne da wuya ka fahimci inda xancensa ya dosa. Idan ya murda wata maganar, bana iya warwareta. Ko ma dai me ke akwai, xan kula, baxan taba yin abinda baya so ba! ''Aishah, Abban Jawad na gaisheki'' ''Ke ma Alphat da Yusuf suna gaishe ki, sai dai wani muhimmin sako daga YUSUF DABO, wanda nike fatan ki amsa da hannu bibbiyu'' ta xaro wani dan karamin (complementary carde da akayi dan rubutu a baya, da farko kamar in ki amsa, sai kuma na amsa din. (Zubaidah! Luv, so easy 2 say, so easy 2 spell, but we've ever given luv a chance 2 spell itself 2 u) Yusuf . Na dubeta, cikin tsananin rashin fahimta ''me kenan?'' ''Ma'ana yana SON KI. Wallahi Zubaidah Yusuf dan manya ne, mai sanin ya kamata.'' Duk sai ta bani dariya. ''Goggo na kada ko kara yiwa kanki karambani irin wannan a kaina. Ki na so Oga ya kore no ko?'' Why, don me?'' ''Ra'ayin shi ne, ban kuma tambaye shi ba''. ''Shikenan xan wa Yusuf bayani''.
***********
98.
Mansina, ta dawo Indonesia ranar lahadi wurin karfe 9:00pm, bata xame ko ina ba sai gidan aminiyarta. Mubina xaune bisa 'carpet' din falonta, ta barbaxa takardu da 'yar karamar 'computer laptop' a gabanta, kai da gani kasan lissafin Bankinne da baya karewa. Mubina ta tare ta da murna, amma da ganin fuskarta, ta san labarin ba mai dadin ji bane. ''Me kike yi?'' Abinda Mansina tace da ita kenan tun kamin ta samawa kanta maxauni a falon. ''Wallahi sabon Manajan mu ne ya hada ni da aikin lissafa abinda muke bin wani 'foreign trader' amma nake jin na kammala''. ''Game da taryar mijinki fa?'' ''Wai mara mutuncin nan (Baban Jawad), cewa yayi xai dawo? Yaushe?'' Tayi xugum tana dubanta kamar ta makure ta don haushi, ''wato Mubina duk abinda na gaya maki, kinyi watsi dashi. Don ke naje Indonesia da kaina. Don in gyara ki, mijin ki ya soki, amma kina nan kina bobbotsaren taki. Jiya a labaran BBC naji sun taso daga Canada, me kika tanada?'' ''Yo in ma nayi kwalliyar yabawa yake? Inna yi shegen shaye-shayen ya san an yi? Kin ganni nan, gobe idan na bar gida sai goma na dare. Akwai aikin lissafin da xan yi... ''Na ji-na ji, Banki uwar ajiyar kudi, kina da labarin 'yar rainon ki, na shekararta ta karshe a makarantar su kanwata Aisha? Aisha na koya mata karuwancin kwacen miji? Mubina ki kama kanki, ki fidda 'yar rainon nan daga gidannan. Ga magungunan gyara na hado maki kiyi amfani da kowannen su a yau, (kuji sai kace wata uwar ta, Takori), ba Taheer ba, ko Sarkin Karaye kika danawa wannan tarkon, sai dai uwar shi ta haifi wani, amma ba shi ba kara kallon wata diya mace da sha'awar aure. Sauran dubarun na bar maki, kiyi amfani da hikimar ki ta diya mace, ki lallameshi cikin hila da kissa ya sallameta, ki karbeshi da murnar ki, ko kin samu ya taya, in ma bai taya ba, kada ki kyaleshi, ai hakkinki ne''. Da haka sukai sallama, xuciyar Mubinah tamkar tafasashshen ruwa. ''Black, a Nurul-Bayan?''
98.
To me xata yi mata ta huce? A doke dai, yanxu sai dai su kirbi juna. A xage, sai dai tayi ta kare, ba xata daga ido ta dibeta ba balle ta tanka mata ba. Abu mafi a'ala ta Mansinar ce da tace ta lallame shi, ya sallameta hakannan. Washegari, bakwai na safe a Omega tayi mata. Wai tayi ta kammala abinda xatayi xuwa shidda na yamma ta dawo. Tun karfe goma na safe, ina ji a radio saukar shigaban kasa da ministocin sa da sukayi mai rakiya xuwa kasar Canada, domin kulla cinikayyar man fetur tsakanin kasashen biyu. Shi kuwa Yallabai dama ya je da biyu ne, rakiyar shugaban kasa da karbar ragamar kamfanin su na carpet wanda a da yake mallakin su su hudu, wanda a yanxu ya xama nashi shi daya bayan wasu kudade masu yawa da ya biya sauran share-holders mamallaka kamfanin. Sun sauka ne a filin jirgin saman Abuja, karfe biyu na rana. Na rubuta komi, na baiwa Tom, ya nemo mu yiwa Oga abinda xamu burge. Sai gashi harda garin masara da tsaki daga wurin Kulu da Gasara mai kyau. Jawad na gefe a kicin din yana ta fama da bindigar roba, na tankade gari tas, na ware tsakin nayi kyakkyawan tuwon masara miyar xogale, da aka wadata da toxon Saniya. Sannan dambun tsakin masara da dambun shinkafa, wanda yaji kayan hadin su green beans, cabbage, carrot da sauransu. Maimakon nama, da yankakkun kananun hanta nayi amfani. Tuwon shinkafa mai sulbi da miyan taushe, wadda ta ingantu da kayan hadi cikin tsokar kaxar gona. Na hada kunun xaki da gasarar yaji kayan yaji da kayan kamshi. Lemu da na hada kayan marmari kala-kala har kala biyar wato abarba, lemun xaki,Inab, tuffa da strawberry, shi ne na karshe. Na adana kowanne a flask dinshi daban. Na kama Jawad yana ihun in barshi yayi wasan sa, nayi mai wanka, na shirya shi cikin wani irin 'suit' kalar 'brown' da fari ta ko ina kamshi yake. Yayi dariya a yayin da nike fesa mashi Dune ''Momi na, kullum Daddy yaji ina kamshi, sai yace Allah ya sakawa Momin ka alkhairi'' na ce ''na ji''.