← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 54

Sashe 30

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

128.
''To an ce maki ni xan rike? Kin ga in kin hana ne ki fada, ba sai inje in sa matar Waxiri tayi min ba?'' Na durkusa gaban sa a hanxarce ''Na tuba Yallabai. Na tuba na bi Allah, na bi umarnin ka! Allah ya huci xuciyar Yallabai na, xa'a bada Alkubus da taushe, harda funkaso''. Dariya na bashi sosai, ya kwantar da kanshi a masangalin kujera yana nuna ni da dan makullayen hannunshi, a tausashe yace ''Zubaidahhhhh, Atine-Zubaidah ki na BURGE NI!'' Duk abinda ke wurin nan Yallabai yaci kuma ya yaba yace ya gode. Kuma in ba Hardo hakuri daga yau aminiya ce. Mun rabu akan sati mai xuwa xamu koma makaranta mu xana JAMB da SSCE. In mun kare sai bikin birthday da xai shirya mana. Gobe xa'a kawo kudin gaisuwa dana aure duka, don Baba tuni ya bashi aure. Muna dawowa xa'ayi daurin aure da biki da biki gabadaya. Lefen ma duk kafin mu dawo xa'a kawo. Ya kuma bani waya nokia don in muna da matsala ya ji? Sai kudi don bukatan mu a Karaye. Kwana biyu ana ta amsar baki 'yan taya murna a gidan mu, na kudin aure da aka kawo. Kudin aure na da aka kawowa Baba dana gaisuwa, kamar kullum yace sun yi yawa. Sai kace sai da 'yar xai yi? Duk rikon wahalar da yayi mata? Da kyar Waxiri ya lallabeshi yace Taheer don kar ya firgita shi ne ya bada (100,000) gaisuwa da kudin aure duka. Amma ko auren shi na fari, a sanda ma baiyi karfin haka ba, ninkin haka sau biyar suka kai akace sunyi kadan, 'yar ma da basu san asalin ta ba balle tushen Karaye? Gabadaya dangin Yallabai suna murna da wannan auren, domin cikin dangin Yallabai kaf, babu mai shiri da Aunty Mubina, ba don komi ba sai don hali irin nata da kowa ke kokamawa. Masu xuwa ganina, duka Ashsha karbar mutumnci take masu, gata da son mutane, cikin dan lokaci kowa ya saba da ita. Jawad na wajen mu tun tafiyar Yallabai, sai dai tambayoyi kam, nasha su a wurin sa game da nan ina ne? Su waye tsofaffin nan, na nan gidan, da na can gidan? Wancen yaron da majina a hancin sa, meyasa? Wannan yarinyar Momi an fara mata kitso,

129.
Ba'a karasa ba. Kafar wannan tsohuwar, a tsatstsage Momi. Ni baxan sha ruwan rami ba (rijiya), ni baxa ai min wanka da ruwan rami ba. Ana I gobe xamu koma, na bar Ashsha da Jawad, xasu gidan wata kanwar Oga, na nufi gidan Kakana, Marigayi Liman. Inda nake tsammanin xan samu labarin 'yar uwata, ATIKA. Na tambayi Inna tace tayi aure kawai, shima Baban haka yace, 'ya'yan ta uku, sun ki suce a rakani gidan ta, haka shima Ya Auwal. Wai ina ruwana, sai naji kwakwaf? Ita Inna tun xuwan mu ta kasa sakewa a gidan, ta hana kanta sukuni, daga daki sai daki, to shin me ya faru ne?

Don jin wannan Amsa sai mu hadu a littafi na 2

Alhamdulillah, nan muka kawo karshen littafi na daya, sai mu saurari littafi na biyu
[10/15, 9:18 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*[10/19, 9:38 AM] A A Dboy: 🤔🤔 *TUNA BAYA*🤔🤔
~Book 2~
Tuna Baya2 1-10

1.....
Aslin Taheer da Bello
Usman karaye ya gaji sarautane tun iyaye da kakanni. alokacin duniya na kwance.mulkisa agarin mulkine na adalci da rangwame.matanshi na aure hudu da kwarkwarori biyar.kenan mata tara ne agidanshi in ka dauke bayi da barori wadanda baxa su kirgu ba , al'ummar garin na kaunarshi kwarai da gaske sabida tawaliun shi da kyautayin shi garesu.maimunatu ne uwargidan maimartaba wanda ake kira fulani ita ma yar sarautace gaba da baya daga masarautar kano ta gaya, mahaifinta shine sarkin gaya na uku kowa yasan son da mai martaba kema fulaninshi daban yake dana sauran matanshi the differences is clear(bambancina farraqe yake) awurin bikin aurantane waxirinshi yaga rabi'a qanwarta shima ya aura rabi'a ita kebin maimuna a haihuwa,ba abinda yaraba su,yadda maimuna take baqa doguwa mai jiki haka rabi'a take daga gidan mai martaba zuwa gidan waxiry bawata tafiace mai nisaba.maimuna tafara haifan TAHEER wanda yazamo dan lele a masarautar garin gabadaya.tun taheer na qanqaninshi mutumne mai kwarjini karamci da rashin hayaniya wannan yasayo mashi qauna ta mussan a wurin mahaifinsu. shekaru biyar bayan haihuwar taheer rabi'a ta haifi danta BELLO, bello bai dibo kamannin kowaba saina maimuna wannanne yasa suke yanayi da taheer hatta muryar taheer shigen na bello ne.taheer na matuqar son bello tun suna yara ko ina suna tare saidai muhammad bello yafi taheer son shiga jama'a hakanan yafishi karanbani. shi bello dan harkane akwai son jama'a da son yin abokai, bashida girman kai ko kadan kullum cikin hidima da jama'a yake,yayan talakawan garin sune abokan bello(very sociable person.

2....
yayin da taheer baya shiga harkar kowa bayason karambani kuma baya son hayaniya,tun yana da shekara biyar babu abinda yakai takarda da biro muhimmanci agareshi.shaquwar bello da taheer abun acikin jininsune.sukansu iyayan na mamakin yadda taheer kesakin jiki da bello, bayan ko qannanshi dasuke ciki daya baya harka dasu kamar bello. kwarai wannan nada nasab dakasncewar bello mutumne maishiga rai
Yana matuqar girmama yayanshi taheer, tayadda babu abinda taheer zaice yayi yace a'a.wadannan samari guda biyu sunzamo burin iyayansu tako wane bangare,bima'ana su akema hangen gadar masarautar tayadda har sunan taheer yabace saidai ace magajin gari shikuma bello da waziry mukhtar akece dashi (bello waxiry) wannan bayana nufin anhada sunanshi dana uban bane a'a kaitsaye ankirashi waziry ne.taheer yafi bello kyau,bello yafi taheer fara'a faran faran da harka da jama'a shiyasa ankafi sanin bello dayake dan waxiry akan taheer dayake dan sarki gabadaya.

3.....
Dukkansu a qaraye sukayi karatun firamare saidai secondry dakowannensu yaci daban yake dana dan'uwansa saidai duk acikin garin kano ne ra'ayinsu yasha bamban akan abinda sukeso a rayuwa,shi bello bayada buri kamar yazama soja shikuwa taheer aikin da zai zauna a ofis kasancewar shi mutum dabaya son kwaramniya. dukkan su Allah yacika musu burinsu,bello yasamu tafia makarantar koyan aikin sojata n.d.a dake jos, taheer yasamu gurbi a jamiar Abuja indayake karatu akan kimiyar siyasa(political science). A makarantarne yayi wani aboki waishi yahai, shi yahai bakatafene amma musulmi yan asalin garin zaria'shakuwarsu da yahai takai harsu kan ziyarci gidajen juna ,sau tari yahai a karaye yake'weekend' shima taheer yakanyi kwanaki a gidansu yahai har suka saba da balarabe dango mahaifinsu yahai.general dango ya yaba da hankali da nutsuwar taheer kwarai da yadda yake kula da addini,harkar mata da yahai keyi shi bayayi kullum cikin kula da karatun shi da addininshi yake,wannan ya kwadaitar dashi dayaja taheer a jiki,don yasamu ya auri watsatstsiyar diyarshi MUBINA dake karatu a portugal. Yayi yayi mubina tayi aure taqi,kullum cewa take tana 'finding Mr.Right' ne, domin mubina akwai son namiji mai kyau,duk da kasancewarta mummuna,to amma munin mace inhar akwai gyara ai adone ga maza.Rayuwarta mai tsada ce sosai.

4....
Ya tabbata inhartaga taheer zata soshi donshi a rayuwarshi baitaba ganin mutum mai tsari da zubin taheer ba,dan haka yace da taheer ya kwaso kayanshi daga hostel yadawo gidanshi yabashi daki kusada na yahai. bai yi gaggawar amincewa ba saida yayi shawara da mahifinshi tukunna yace in har musulmine yazauna dasu mana daman wake son kwanan makaranta in banda dole wannan shine mafarin zaman taheer a gidansu mubina. Daya kammala digirinshi na farkone mubina tazo hutu daga portugal. ganinta na farko da taheer ta rikicewa babanta itafa taga miji mr dango ya tausheta da cewa ta dakata harsai sunmaida taheer wani tukunna, yadda bazai iya qin amsa bukatar suba donshi yasan taheer Kamar yunwar cikinsa. Mace bata gabanshi a yanzu macen ma irin mubina kwata_kwatä (life_style) nasu badaya bane. Ba mamaki inyayi mishi maganar ta alokacin ya tattara yakoma hostel. hakan akayi mr dango yadauki nauyin karatun yahai da taheer a sussec, university of washington seatle.bayan kammala digirinshi na biyu mr dango ya tura mubina washinton jami'ar da suke karatun M.sc dinta akan qididdiga(Accounting) yakuma danqawa taheer amanarta.

5.....
yaya kuwa xai yi wasa da amanar ubangidanshi? Ya shiga kula da mubina bil haqqi tsakanin shi da Allah,tare dakokarin ganin ya rabata harka da kowanne namiji. Yana nuna mata illar hakan ga mutuncin ta na ya mace musulma mai daraja.tace ai kome nakeyi inayi ne sabidashi,don ni?akan me to? Tace akan ina son ka da auren da ka ke cewa nayi, alokacin dana lura kai baka masan ina yi ba".tun daga lokacin tashiga nuna mai soyayyah afili daya ga abin na gaskene sai yayi ta lallabata data bari sukare karatun xai aureta. dawowarsu nigeria yayi daidai da mutuwar autinsu data rike su mubina, dama mahaifiyarsu tuni ta gudu tabar babansu tun suna kanana sabida dukan da yake mata inyashawo giyarshi ko allurar sojin ta motsa. Wannane yasa mr. dango tausayawa su mubina da basu tarbiyya ta kowanne yayi abin da zabawa rayuwarshi. Mimi mai bin mubina a tanzania take karatun tarihi shi kuma yahai yakoma beijing din china inda yasamu aiki da kamfanin(bill gate)na sana'anta na'ura mai kwakwalwa.ashekarar mr.dango ya samar mai aiki a'foreign affairs' wanda sadaukar da kai da mai hankalinshi ya bashi matsayi daban-daban acikin ta har kawo yau,wato bashi baban (minister) na foreign affairs gabadaya da shugaban kasa yayi,badon shekarunsa sun kaiba illa don juriya da jajircewa bisa aiki da gaskiya irin nasa.
Chapter 30 · 0% Book details