Sashe 54
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
124...
Maimunatu Taheer (mahasi) 'yar kimanin shekaru ishirin da daya,daliba a jami'ar harvard amurka inda take kara2n likitar hakori mataki na biyu. Ta dago manyan idanun ta farare kal tana murmushi ta dubi mahaifiyarta tace'to momi baki koma kara2 ba? tace'bbu lokaci,gaba dayan lokacin rayuwata na TAHEER ne. Iyakar sa kenan sakandire. Sai bautar aure da ingatacciyar soyayya wadda har yau ake damata. Duk da ga furfura nan tsilli tsilli akan babanki ba abunda ya canza jiya i yau. We are meant 4 each oda. Raino wani bangare ne na jin dadin rayuwata. Don haka ne bayan ku shida dana haifa a cikina,kika ganni zagaye da 'ya'yan uwa duk kwato su daga hannun iyayensu ina RAINO. Na samu matsala a mahaifa bayan haihuwar mamman(MK) wadda an tabbatar mun bazan kuma haihuwa ba. To amma daga ni har yallabai ba abunda ya damemu ko da ace da ke da jawad kadai Allah Ya barmu kun ishe mu rayuwar dunia da lahira. Cikin firgici mahasi tace'kina nufin ba ke kika haifi nadir, umar, sauda, usman, zubaidah da nabilah ba? tace cikin murmushi ''Nadir dan abdulraheem da kanwata sadia ne,wadda daga baya hannu na ta dawo ta girma tay kara2 har ta shiga jami'a. Sauda diyar assha da alphat ce data sawa sunan inna na,amarya sabida kaunar dake tsakaninta da inna ta,usman kanin taheer karami ne watau dan bello ne fatyma ta kyautar mun tun daga lokacin yaye. Gabadaya 'ya'yan data haifa daga baya ni nake yaya mata su. Zubaidah diyar tom(taufiq) da matarshi maryam ya sanyawa suna na ni kuma na karbo na rike masu,shiko umar dan anti mubina ne wato kanin jawad ne.. Tace a dokance 'yauwa yanzu ina anti mubina? Kince mun ta dawo kun zauna tare alhalin ni tunda na taso ke kadai na taras nake kuma gani tare da daddy... Hawaye ya ciko idonta tasa hankici tana sharewa tace'ta rasu wurin haihuwar umar agaban mijinta
125....
Ashe ta dade tana fama da ciwon koda wanda 'hydroquinone' ya sanya mata bata fadawa kowa ba (hydroquinone yana cikin kayan shafe shafe wannan zamanin wanda mata da yawa suka raja'a akai da sunan canja launin fata ta hanyar toning, 'yammatasai a kula). Amma wlh har ta koma ga mahaliccinta musayen yawu wanna bamu taba yi ba. Ta danka min amanar jawad da umar tace ta tabbata a dunia bbu wanda zai rike mata su da amana kamar ni tace in rike taheer da kyau domin samun mutun irinshi a wannan zamanin wani abu ne da bazai yiwu ba,ko kuma a ce zai yi wuya. Yay kokari ya cika alkawarin da ya dauka na yin adalci a tsakanin mu da kokarin boye matsananciyar kaunar da yakemun akan idonta. Bamu taba yin wani abu da gangan wanda ya bata mata rai ba har ta koma ga sarki Allah. Wayar ta dake gefe ta shiga kidi mai dadi nuna alamun shigowar sako'text'. Ta mika hannu ta daukota cikin nutsuwa sako ne daga gudan ran ta MOHD JAWAD tun kamin ta karanta take murmushi data karanta sai ta zarce da daria. A takaice dai ga abunda jawad dake da ainin second lieutenant a barikin horas da sojoji dake jaji ya rubutowa uwarsa abin sonsa mama zubaidah. ''I grew up witout a care of a mother, but in all dis i realized u THE BEST MUM in d world..... Jawad.... Tace a cikin murmushi wanda baya rabo da kyakkyawar fuskarta 'Allah sarki jawad dina' Ta kira lambar shi a take ya dauka cikin zakuwa yace'hala momy kin manta da ni ne sbd 'ya'ya sun maki yawa yanzun? Ina my blvd sis? Tace'ka jira ni ina nan zuwa anjima kaima ka sani jawad in 'ya'ya sunyi dubu kai kadai ne nawa, dukkansu na RAINO ne.. Yay murmushin nan nasa cikin jin kansa ya fasu da kalamin mamarsa. Mahasi ta zaku a bata dan uwanta sai kokarin amsar wayar take a hannun momi,momin na sake zakulo sabuwar hira tsakanin ta da dan ta, shima yasan da gangan takeyi don yana iya jiyo magiyar da mahasin ke yi na a bata wayar yasan da gayya takeyi don ta kular da ita don idan akwai abunda mahasi ta tsana to wannan banbancin da momi ke nunawa akan jawad ne. Yace 'don Allah momi ki bani sister na. Tace 'tunda haka ne na fasa zuwa mahasin tazo ita kadai. Yace'ki rufamin asiri momi na tuba nabi Allah na biki har abada bani da wadda ta fiki,she is but a bloody sister... Ta mika ma mahasin tana murmushinta na UWA. Yau duk wani burinta na zama UWA ya cika. Ta RAINE su gashi a yau sun girma sun nagartu cikin kaunar junansu da kakkarfan zumunci mai dorewa har illa masha Allahu. Zubaidah(zuby) 'yar kimanin shekaru 3 ta taho da gudun gaske mamman ya biyota da duka tay azamar dauke ta tayi mata mafaka a bayanta. nadir ya taho yana kuka hannu a ido shi kuma cikin kawo karar saudat data gantsara masa cizo sai ta bar rabon fada ta koma alkalanci. Can kuma sai ga usman yace'momy kunu zan sha' Ta mike taje kicin ta dauko mishi zubaidar data sauke daga bayanta ta fashe da kuka cikin nuna rashin yarda da ajiyetan da akayi don a biya bukatar usman sai tay murmushi ta dawo ta goyeta sukayi kicin din tare.....
126...
Mahasi data karbi wayar daga hannun momi sai tayi dakinta ta tsaya bakin taga daga bisani kuma ta dawo ta rufe kofar har da key wato za'ayi sirri kenan da ita da yayanta,wanda ba'a son momi taji. Tace 'yaya jawad kasan kuwa ina cikin problem? Yace wace irin matsala ko dai dadi ne yay miki yawa mahasi,tace cikin rishin kuka 'daddy ne yace bazan auri ahmed ba sai mukhlas kafi kowa sanin irin son da mukewa juna sbd Allah anyi mun adalci? Yace'haba my sis tun yaushe nake gaya maki ki rabu dashi wannan soyyr taku bbu inda zataje. A tunanina ko ba'a kwabe ki ba bazaki zabi ahmed ki bar mukhlas ba, kina da wanda ya fishi ne a dunia bayan ni da iyayenmu? Cikin hawaye tace a'a to amma ai shi din bai taba nuna yana so na ba ahmed fa? Kana ganin irin yadda yake basar dani yana..... Yace'ba dole ya basar dake ba tunda kin nuna ba kya sonshi kinfi son bare dashi? Idan kin kwantar da hankalinki mahasi,mukhlas is a nyc person nd he luvs u dearly. Gashi dan uwanki daya san ciwon kanki yasan darajar iyayenki me kike nema a aure bayan wannan? Me kike nema a ahmed wanda baya dashi? Uwa-uba zaki farantawa iyayenmu ki cika masu dadadden burinsu a kanki ta yadda zasu zamo masu farinciki dake akullum. In fact nima zan bata dake batawa ta har abada idan baki bi umarnin iyayenki ba. Tunda nake kin taba jin nay musu da momyna? 'yar shagwabar sai tasa kuka tace 'Allah Yaya jawad na daina na yarda zan auri mukhlas amma shima kay masa magana ya daina yi mun wulakancin da yake yi mun,, yana daria sosai yace'ba wulakanci yake yi miki ba ajinsa yake ja kada ki rainashi bayan kuma baki aure shi ba amma mukhlas bashi da abunda yake so a dunia tamkar ki. Maza share hawayenki je ki gayama mummy abunda kika gayamun yanzun. Ta share hawayen da 'yan yatsun ta uku da sassarfa ta fito ta cimma momyn har yanzu tana nan a inda ta barta.
27... Tana zaune da zubaidah akan cinyarta lokaci guda kuma tana sharewa mamman hanci da tissue tana bashi kunu a baki. Mahasi tay kasake! Tana kallon ta tace (cikin tadin zuci)''Ita dai momi haka Allah yay ta? Ba abunda take so a rayuwarta irin kananan yara,bata da burin da ya wuce na RAINON KANANAN YARA. Tana matukar kaunar ta ganta goye da jariri tana jijjigashi tana yi masa rawa tana cilla shi tana cafewa yana bangala mata dariyar kauna irin ta UWA. To ko wannan ne sanadin da ya sayo mata soyayyah ta kwarai a zuciyar mazan kwarai irin TAHEER da BELLO? Ga yallabai kusan haka ne amma ga Bello kare martabar TALAUCIN ta ne da sanin ciwon talakan babanta. Aduk abunda ta zama aduk kwabon data samu a duk inda ta tsinci kanta bata da abun ambato sai BABANTA da INNARTA. Komi ta samu sune,komi taci sai ta kai masu duk kuma wannan ta same shine daga daurin gindin mijin kwarai yallabai TAHEER. Suna masu sanya mata albarka har suka kwanta dama. Wanda albarkar ce har yau ke bibiyarta. Abun tambayar anan shine shin ko ita din zata samu irin wannan jin kan daga 'YA'YAN data RAINA? Ance juma'ar da zaty kyau tun daga laraba ake gane ta. Akwai alamu daga 'ya'yan baki dayan su na cewa basu da abun kauna tamkarta hada da iyayen da suka haife su kuwa.(kuna ina iyaye mata wadanda 'ya'yan da muka haifa acikinmu kadai muka sani?). Mahasi ta taho sannu a hankali ta ture zuby cinyar momi daya ta yiwa kyakkyawar fuskarta matsagunni a cinya daya kai kace itama zubyn ce 'yar kimanin shekaru 3. Ta lumshe ido cikin kara kaunar mamanta.tana murmushi tana share hawayen tausayin momin don a ganin ta wannan son wahala ce kadai Allah Ya dora mata(ita kam bazata iya ba,don bata ga dalili ba) tace'na yarda momi zan auri mukhlas idan har hakan shine farin cikin ku. Kiyi mun adduar Allah Yasa nima yaso ni irin yadda UNCLE da DADDY ke sonki.
MASHA ALLAHU LA QUWATA ILLA BILLA.
Karshen littafin Tuna Baya shine roko daga group of Hype hausa novels book whatsapp suka kawo muku
Sai kunjimu asabon book din mu nagaba Mai suna********sai kunjimu
[11/3, 8:41 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*