← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 54

Sashe 53

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

121...
Lokaci daya wani tunani yazo mata duk wani shiri da tay na kuntatawa rayuwar zubaidah ta karfi da yaji,sai ya warware taji zubaidah ta burgeta ta kuma bata sha'awa. Idan tace zata kawo fi'ili ko kishi akan wannan gagara gasar mace, lallai ita zata kwashi kashinta a hannu. Ashe dai da talaka da mai kudi duka daya ne a wurin Allah sai ma ya daukaka talakan ya dankafar da mai kudin a sanda Yaso,Shi Allah bbu ruwan Shi kuma arziki nashi ne bbu inda baya yinsa. Kamin kowa ya tadda zubaidah ta runtumo da gudu ta rungumeta tace my little sister kunzo lafiya? Yallabai aka saki baki cikin mamakin abunda tayi wanda ko a kokon ran shi bai kawo hakan ba, to bashi kadai ba ni kaina nay mamaki. Mu duka biyun muka doshi al'ummar mu masu aikin camera nayi masu video nayi, shashashun'yan jarida kuwa tambayoyi suke tayi mana 'yaya zaka kwatanta farincikin ka mai girma Minister a wannan rana? Ganin cewa mubina dango tay nadamar abunda ta aikata tay murna da dawowar zubaidah? Hajiya mubina yanzu kin yarda da kaddara kenan zaki zauna da 'YAR RAINON Ki,koko na yau ne kawai? Shin zaki kwato dan ki ne koko kin hakura kin bar mata kin amince RAINO MA WANI ABUNE MAI MUHIMMANCI GA UWA TA TSAYA TA RAINI ABINTA? Ko kallon su batayi ba,ya dawo gareni''Hajia zubaidah me zakice kan tonon sililin da dango tay miki a dunia cikin jaridun mu da kafafen yada labarai? Anya zaku iya yafewa juna? Muka dubi juna nida anti mubina muka yi murmushi. Wannan kadai ya ishe su amsar su na cewa nida ita duka bbu mai kuma TUNA BAYA. Illa rayuwar da zamu gina a gaba. Dani da ita muka fada motar gidan kwamishina ibraheem hardo, shi kuwa yallabai yabi tawagar ofishin sa ne shi da Bello haka yayyuna da sauran mazan har su mukhlas duk sunbi babanninsu. A motar daga ni har anti ba wanda yace da kowa komi, hakannan ba wanda ya kalli kwayar idon dan uwansa. Haka kawai naji na samu kaina da kunyar anti mubina amma ita sai na lura jikinta a sanyaye yake tayi ladaf tay lakwas ta sakko ta saduda,ta kuma yi dammarar zana na fisabilillahi. Gidanmu ya sha gyara sai ma'aikata ke kai kawo suna entertaining bakinmu,tun safe har dare muna ta harkar jama'a bamu zauna ba. Sai karfe goma sha dayan dare kowa ya watse. Sai masu gadin. Anti mubina ke ta kai kawo tana shirya local dishes bisa dinning abunda ya bamu mamaki daga ni har yallabai,a raina nace lallai dunia mai juyi. Ban taba ganin anty ta shiga kicin da zummar dafa koda ruwan zafi ba tsayin shekaru 8 da nay tare da ita,dunia mkrnt ta ishi dan adam riga da wando,babbar riga har da hula (mata mu mike don Allah mu gyara rayuwar aurenmu lokaci bai kure ba. Son jiki da girman kai bbu inda zai kai mu a zuciyar mazajen mu saidai ya dankafar da mu inji takori). Ta kammala jera komi ta jefe mu da cokalin dake hannunta tace kowa yaci girki na yau zai bani lambar dana cancanta. Yallabai ya dago daga wayarshi da yake latsawa ya galla mata harara yace 'makarantar girkin kika shiga ko yaya da za'a baki makin? Na lura bata ji dadin gwasalen da yay mata ba ni kaina banji dadin ba nace'rabu dashi antynmu dole ne ma ya bada makin irin wannan gara haka? Ta sadda kai tana murza 'yan yatsunta kawai shi da kansa ya lura bai kyauta ba. Ya kira sunanta ta dago ya sakar mata murmushi yace'to me aka shirya mana? Maman jawad ta hakika? Anan ne tay murmushi tabbacin ya faranta mata tace 'ni da ke fried rice nay mana sai stuff marrow da stuff cabbage,shi kuwa dama local dishes dinsa ne gaya nan' nace'kin kyauta antin mu ya harareni a lokacin da ya kai lomar farko yace antinki dai nikam bandani don haka ki daina jimilla. Tay serving kowannenmu da abunda yake so ba tare data kula da zancen sa ba don ta lura neman baki yake da ita,ta tura min plate dina itako taja gongonin heinz beans ta tsoma cokali tana sha banyi mamaki ba don Tom ya taba gaya mun wai ita bata cin abunda ya hau wuta ba. Bayan mun kammala cin abincin yallabai ya kira mu main falonshi,dukkaninmu yay mana nasihohi masu ratsa zuciya,ya nemi hadin kanmu kan zaman lapia na har abada a gidan sa don dukkannin mu kowacce da muhimmanci ta gareshi. Ya kare da cewa'banajin zubaidah sai ke mubina don Allah ki canza halin ki, ni kuma In Sha Allah zan yi kokari in kasance mai adalci a tsakanin ku.

122...
To bayan watanni biyu ne na haife ki MAHASI, bayan matsananciyar nakuda, sunanki na usli MAIMUNATU kasancewar sunan fulani ne muke kiran ki mahasi. Rayuwa ta cigaba da gara mana yadda bamu zata ba da budi da cgb ta kowanne fanni. Anti mubina ta shayar da mu mamaki don daga ranar har inda yau ke motsi, bata taba kawo wani mugun hali ba. Mun dinke mun zama daya kamar Ya da kanwa don baka sani ba ko shigo gidanmu sai ka za ci ba kishiyoyi bane,Ya da kanwar ta ne. Duk wani akidun ta na banza da shirmenta na da ta rabu da shi tana koyi da komi daga gareni,hakana aikin ma ta aje shi ta daina sai kasuwanci. Saidai har gobe ita kanta tana da masaniyar cewa ita da ZUBAIDAH ba daya bane a zuciyar TAHEER. Ranar sunanki ne fatima ta gane cewa nice ATINEN BELLO. Data bude baki a ranar tafi minti ashirin bata rufe ba sabd mamaki da ta'ajjibi. Yadda akayi ta sani ma kuwa shine tana rike da ke a hannun ta tana fadin kamanninki da yallabai masu ban mamaki sai yay murmushi yace' Yar atinen-bello kenan ta koma 'yar fatin- bello... Bello yay murmushi a kunyace yana kawas da kai daga gareshi yace 'yallabai ai ba abun mamaki bane,tunda kuwa wani baya haihuwar dan wani kamar yadda wani baya taba auren matar wani. Wannan rubutaccen ne don haka ka daina TUNA BAYA..(past),just d present! Nidai fatana ko bayan raina inaiwa mukhlas rikon MAHASI. Hawaye suka zubo min na tausayin bello nay saurin daukewa kamin yallabai ya gani. Na tabbata Bello Waziri ba karamin kauna yake mun ba irin kaunar nan wadda har a nade dunia baza'a aina ba saidai alhmdlh yay dace da macen kwarai mai kaunar shi fiye da komi a rayuwarta. Kuma ko da ta ji nice atinen,ba abunda ya canza na amincin dake tsakanin mu.

123....
Hakika kauna ta gaskia wata aba ce da Allah Subhana ke dasa mana a zuci wadda kuma take a tsakanin abubuwa guda 2,samu ko rashi. Na sani na so Bello nd i still luv him(astagfirullah inji atine) shima yaso ni ba kadan ba to amma soyayyah ba itace aure ba. Allah bai kaddari akwai aure a tsakaninmu ba. Ya rigaya ya kaddaro cewa kowanne abokin rayuwarsa dabam ne dana dan uwansa wannan ne kawai abunda na yarda da shi. A tun ranar da aka haifeki a asibiti da mukhlas ya daukeki budar bakinsa sai cewa yay 'momyn jawad inasonta kyakkyawa ce zaki aura min ita? Nay murmushi nace'insha Allah ko bata son ka ka aureta ka gama muddin ina raye. Yallabai yace'balle ma me zai sa tace bata son shi? Alhalin ya fita kyau? Jawad yace 'a'ah daddy ban taba ganin kyakkyawar babe irin wannan ba, kamar ta daya da matata(fulani)'' Kowa yay daria. Dalili kenan da aka sa maki sunan fulani. Alkawari ne muka daukarwa bello da ni da mahaifinki na cewa a dunia baki da miji sai mukhlas wanda ko bayan ran mu muke fatanki taimakemu wurin cika shi. Na baki wannan labarinnawa ne don ki san falalar dake cikin biyayya ga iyaye da garabasar da ke cikin ta. Hakika wanda ya yiwa iyayensa biyayya,ya faranta musu shi ke da babban rabo a dunia da lahira,kuma wlh bazai taba tabewa ba sai dai yay ta cgb,da cgb da ganin farin ciki muddin rayuwar shi. Ki bar tunanin mahaifinki ya takura ki daya dage sai kin auri mukhlas ba wanda kike so ba. Yana son in da za'a so ki ne kamar yadda ake son mahaifiyarki. Uncle dinki da antynki fatyma masu kaunar mu ne da ko ba zancen aure tsakaninki da mukhlas,su masu rike ki ne da amana. Bello ya nunawa taheer halarci don daga wannan lokacin har yau shekaru ashirin da daya bai kara tada zancen ba,haka kuskuren da yay a baya ya nemi gafarar taheer yace sharrin zucia ne da son kai irin na dan adam wanda by nature kowa haka ne (kowa yana son kansa). Inda a take yallabai ya kalubance shi da cewa a'ah sharrin SO ne don haka baiga laifin sa ba.
Chapter 53 · 0% Book details