Sashe 41
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
74.
dukan su kwana makaranta suke balle ayi wanni zance wahalar kudin mota sai dai abin daza suci, bayan shekara guda kuma bawan Allah nan yazo har nan dakin ya gaidani ya gayami cewa hidimar da kike a gidansa ta karu wai kina girka masa abinci kina kuma kula da yaronsa don haka albashin dayake baki ya ninka shi zai rinka biyan mu N40,000 duk wata ba yadda banyi dashi ba amma ya kafe bazai canza ba,sai na fawwalawa Allah kan cewa aikin naki wata kofa ce ta rahamar Allah a gareni,ya koma biya biyan mu N40,000 duk wata? Kwata kwata cikin kudin nan baifi N10,000nake dauka ba in kashe inyi gararin gabana dashi ragowar kuma naba awal ya kai banki.cikin shekaru hudu kacal kudin da awal ya gayamun sun taru a banki ta tsora tani don ban taba tsammani wai ni mai kalwa zan taba mallakarsu ba,tun daga lokacin nabar saida kalwa akwai wani alh hashim a can ma'aikatar su awal a lagos dan kasuwa ne sosai kuma aboki na jiki ga awal shine ya kawo shawarar mu zuba hannu jari da kudin ciki kasuwanci sai mu ding raba ribar tare,haka akayi bayan shekaru biyu shi kansa ya kara karfi,yace zai ware wa awal jarinsa shi kadai domin lokacin jari mai tsoka sosai muka bude manya shaguna guda biyu a kanti kwari inda sani da awal ke zuwa kwatano suna shigo da shaddoji manya a na sayarwa kuma Allah yasa albarka acikin abin don in ana lissafin manya a dilolin shadda a kasuwar kwari inba ambaci awal na biyu ba za a ambace shi na uku abi yayi karfi da salisu ya gama sakandire sai ya rungimi shagon farko shi kuma rabiu ya rungumi na biyu sani kuma ke fita kwatano shi daya,awal ya rungumi aikinsa shi kadai don haka ayau atine ina mai farin cikin sanar dake cewa muma bamu a layin talakawa muna da kwakkwarar sanaa don cikin mu ba wadda ya kara saida kalwa bayan tafiyar ki,da karfi ki muka sami jari muka gina kanmu don haka awal yace duk ribar damuke da ita a banki taki ce duk abinda ke cikin gidan magaji gari nanan bayan gari inda yace zaki zauna kafin ya kare sabon gininshi na nan abuja
75 nakine mallakin kin kine ko cokali babu nashi aciki duk anyi waje dasu yasan inda yakai abinsa. don haka ki mike kafar ki kiyi iko da komi ayau ba wanda ya isa yayi miki gorin talauci don duk a wannan garin a yanzu ba alfahariba ba wanda zai ce kwadayi yasa na aurarwa da alh taheer ke kina jina?do haka koma mai uwar yaronan zatace dake tace kada ki damu,raino da wanke wanke ai neman halal ne ina neman halal ya taba zama abin kunya? kowa da kika gani aduniya da hanyar cin abincinsa da hanyar arzikinsa toh mu namu shine wanke wanke a yau awal yace in isar da godiyar shi mara iyaka a gareki don bashi da abinda zai saka miki illah duk wata bukata da kike da it a duniyar nan ki tambayeshi ko ta mecece kada ki dogara da abin hannu baban jawad muma muna dashi akwai motoci guda biyu suna nan awaje sani ya saya miki don amfanin kan ki a cikin su zaki tafi gidan ki awal da sani suna gini acan kano gidaje guda uku daya naki ne jere da nasu sai kiyi abinda kika gadama dashi auren mutane irin su mijinki atine sai mace mai juriyar gaske ,kici gaba da juriyar nan dana sanki da ita kisa Allah a gabanki, bayanki, hagunki da damanki a duk abinda zaki gabatar don nema rinjaye akan makiya da mahassada. kada kiji tsoron makiya domin idan baki dasu toh ki binciki imaninki da aiyukanki.kada ki nufi kowa da sharri kiyi komi da zuciya daya rayuwar lami da diyarta ta isheki ishara kingani daga ni har uwarki bamu san hanyar gidan bokaba makaminmu da kowa adduake jikar limami karayece, har kullum ki tuna wannan addua sai dai ki baiwa wasu,duk kuma mai nufi ki da sharri akansa zai ga abunsa kakanki bai rasuba saida yabar miki ayar Allah ki rike ba mutum ba ko aljan atine in har kin rike ayar Allah bai isa da ya cuce kiba.idan tsoron wani abu kike ji ko fargaba, kamin kice komi ayayin da kika hadu da abinnan kice SUBAHANAL MALIKIL KUDDUSI, RABBIL MALAI'TI WAR RUHI, JULLILATIL SAMAWATI WAL ARDHI BIL IZZATI WAL JABARUTI
77.
idan wani al'amari ne ya wuyata a gareki maimakon kije gurin boka ya bincika miki ko yayi miki maganin matsalar ki har a kwana arbain ba akarbi sallarkiba,atine zauna a dakinki kiyi ta lazimi QADDARALLAHU WA MA SHA'A FA'ALA zakiga warware war al'amuranki cikin ruwan sanyi da ubangiji mabuwayi ban horeki da komi ba sai wannan atine idan kika ga makiyinki ya doso ki ki rinka maimata IYYAKA NA'ABUDU WA IYYAKA NASTA'IN to koma me ya nufeki dashi kansa zai koma ga wata muhimmiyar madafa da liman yace duk ranar da za a kai ki gidan miji inbaki idan har kika lazimci ce ta atine akan dukkan bukatun ki ba mutum ba ba aljanba,duk wani abin halitta bazai yi nasara akanki ba ban horeki da fallasa rayuwar aurenki ba ga kowa ba uwata ,cikin kowanne hali kika tsinci kanki dauro alwala kiyi sallah rakaa biyu kowacce rakaa ki karanta fatiha daya da wannan ayar kafa bakwai bismillah ASSALAHU AN YAJ AL BAINAKUM WA BAINALLAZINA ADAITUM MIN HUM MAWADDATAN, WALLAHU QADEER WALLAHU GAFURUN RAHEEM X7 bayan sallama kiyi niyya.ki fadi bukatar ki ga lillahi sannan ki kalli gabas ki karanta ayar kafa 7o SAYUHZAMUL JAM'U WA YUWALLUNAD DUBUR da kuma FA'IN TAWALLAU FAQUL HASBIYYALLAHU LAILAH HA ILLAH HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBUL ARSHIL AZEEM kafa 30 bayan kowace sallar farillah ki lazimci karanta wannan aya ta sama kafa talatin addua ce ta neman biyan bukata kowace iri kuma kariya daga duk wani mai nufinki da sharri.wannan shine kadai gatan da nake jin zan iya miki a duniya atine kefa amarya me zakice?ta mike tana gyara daurin zaninta tace ai duk abinda zance mallam ka riga ka gayamata illa in tunasar dake kiyi biyyaya ga mijinki don samu rahamar Allah cikin rayuwar duniya da lahira kin ganni dai ko musu bai taba hadani da mallam ba don haka ace wai gani ga wane ya isa wanne tsoran allah ta shiga dakinta duk da ban kalleta ba nasan kuka take
78.
na rabuwa da ATINE ta akaro na biyu rabuwa ta har abada sai dai ko gani da yawo,hankalina bai kara tashiba sai da naji gudar talatu da sauran bayin gidan maimartaba a tsakar gidan mu tabbacin yan daukar amarya sunzo,sai nabi bayan innana na kankameta ina kuka mai tsuma rai da tada hankalin wanda ake mawa,tace ke bana son sakarci, cikani baba ya tashi ya fice sadiya ma ta kankameni muna tayiwa amarya kuka ina rokanta don Allah kar tabari su sake daukeni .ina tunawa ne da tafiya na wanke wanke inda na fada wata sabuwar rayuwa da ban taba mafarkin tsintar kaina ba,gashi kuma ayau zan tafi rayuwar AURE da ban san menene acikintaba ban ma san hakikanin makomata a zuciyar mijin dana auraba. ni kuka inna kuka yar kanwata sadiya kuka a haka aunty faty da hajiya rabi kanwar fulani (maman bello) da sauran dattijai dangisu da maman ashhsah, hajiya hafsi inna lami suka banbareni daga jikin amarya. talatu ta karkato dai dai kunnuwana tace ayiyirirrrrr! tasake karkace kai ta kuma cewa ayiyirirrrrr!! rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya.uwargijiyata zubaidah tamkar jiya ne nazo na daukeki na kai ki aikatau gidan yallabai ana wulakanta mu, ana kyamar mu, ana kyarar mu, ana toshe hanci amma gashi a yau zan maida ke matsayin matar gidan ina ruwan ubangiji! ta sake rangada gudar ina kuka komi na duniyar nan yayi mun duf a haka muka shiga motocina da awal ya sayamin su faty suka shiga wadanda suka zazzo a cikinsu muka tafi gidan maimartaba aka fara kaini.a falon fulani ayi abinda ake kira amana inda suka ce sun karba da hannu bibbiyu ubangiji Allah ya taya su riko.taba da turare da turmin atamfa super ingila guda biyar da turaruka da kudi naira dubu ishirin shine na sannu da zuwana cikin zuri'arsu daganan sai fadar maimartaba sarki yayi addua yasa mana albarka kana cikin raha yace zubaidah,muna fatan ba zaki mana rowar taheer ba,tamkar bakatafar matarshi? A uwar dakina dake gidan yallabai na bayan gari hajiya hafsi da maman ashshah keta nasihun su na manya
79.
cikin hikima tace zubaidah ki jure ki zama matar kwarai don Allah?kar kibari mijinki ya taba bada wata shaidar banza akanki ki zama mace daya tamkar da hudu,ki aje tsoron mubina da komi kiso mijinki,muna muku kyakkyawan fatan alkhary don Allah cikin daran nan ki saki jiki ki dauko min baby,shekara war haka inzo inganki rungume da jaririnki kina bashi nono in koma gyaran haihuwa,ta hakane zan yarda in amimce cewa gyarana yayi aiki sosai,gaba daya aka kwashe da dariya,ban dani dana ke kanainaye cikin mayafin lafaya duk suka tafi suka barni ni da faty da ashshah sai ragowar yan mata na suna ta hirarraki da dararrakinsu,yawanci duk shakiyanci ne suke man faty na tare mun tace in kuyi zuciya wata mai zuwa inga katin auren kowacceku ashshah tace me kike ci na baka na zuba? Allah ba inda zani yau sai nayi cinikin bakin yar Qaraye