Sashe 13
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
53
Tom ya kawo min abinici yana tamin bahaguwar hausar shi ina dariya, wai kwana daya kawai yaga nayi kyau, ga gashi mai kyalli yaga ya leko. A hankali sai ya mantar dani kewar Talatu. Ya kunna mun talbijin nace ''ni dama ka kashe ba jin abinda suke fadi nake ba, sai dai cikani da sur-sur-sur'' yayi dariya sosai ''idan kayi alkawarin koya min Hausa, ni kuma xan koya ma turanci, har da rubutu da karatu''. ''Xan koya maka mana. Hausa ba wuya, ko yanxu ka iya hausa, matsalarka daya kana ba mace sunan namiji, shikima namiji ka bashi sunan mace'' ''haka english abu ne mai sauki, Tine, in har kasa kanka xaka iya''. Ya koma, jim kadan ya dawo da farar takarda da alkalami ''wannan shine pencil da dan boko ke amfani dashi yayin koyon rubutu'' ya rubuta wasu haruffa daban-daban, kira su a nitse A, B, C, D. Yana fadi ina fadi har ya tabbatar na rike su a bakina. Yace in dubesu sosai in gane yadda ake rubuta kowannen su, na kuwa daddage na rubuta mai nan da nan. Cikin dan lokaci, kirista Tom, ya fahimci Atine yarinyace mai saurin fahimta, da xata ke makaranta, da anka kwaruwar yarinya. A daren kadai ta haddace A-Z sai dai rubuta su ke wahalar da ita. Washegari kamin ya fita sai da ya jaddada min in haddace rubutun su kafin ya dawo, in har ina son sabon darasi.
**********
Nayi wanka kamar yadda Talatu da koyar da ni, wato sai xuba abubuwan roba a ruwan wankan (turaren wanka, dettol da sauran abubuwan kashe kwayoyin cuta), sai naji fatata har wani tsantsi take, wani danko-danko da wani maiko-maiko da naxo dashi na kauye, duk ba ko kadan, haskena ya fara fitowa, na taje dogon siririn gashina na kallabe shi kalba daya, ta sauko har dokin wuyana na nufi sassan Uwargijiyata, sanye da farar karamar riga da ruwan bular siket mai fadi, yau ma waya take, amma kwance a cikin kujera... ''wallahi na sa Tom ya dinga bata abinci sau uku a rana... Me? In yi hira da ita? In ji ko tana da matsala? Tab, kaima kasan impossible (ba xai yiwu ba... ban bata aikin ba tukunna, sai na..... gama tsaftace ta... Kayi hakuri nace ko? (Ta sassauta murya) ai yau xan bata dama, ni kaina dattin ya ishe ni, dakina har yana ta soma taruwa...'' tayi tsaki ta yi cilli da abin maganar ''stupid kawai''.
54 Nayi mata sallama ta juyo, na xube a kasa na gaisheta, ta amsa kamar tayi bal da ni cikin kufula da daga murya tace ''sai yanxu kika ga damar tashi? To nan ba hutu kikaxo ba, kinji mai kafar shanshani? Ba a banxa xaki ci kudin aiki ba da lafiyar mu, lokacin mu da ilmin mu, mu hana idanuwan mu barci mu tafi mu tafi nema. Ki bar ganin komi baja-baja kamar na banxa, a kididdige yake cikin gidan nan. Na fiki sanin muhimmancin 'naira daya' sabida ni aiki nake tun safe har dare, yanxu haka da kika ganni a gida, hutun haihiwa na ke. Don haka in xaki yi aiki, ki mike kiyi axama. In banda Fulani ta kawo ki, ke dinnan baki isa kiyi mun aiki ba, ke duk 'yan garin ku ma wallahi baki isa ba. To ba yadda xanyi, tunda na auri Dan da Uwarsa ke juya al'amuran shi. Daga yau karfe bakwai xaki dinga tashi masamman in na koma aiki, kixo ki gyara mun daki da sassana gabadaya, ki wanke min toilet ki canxa min xanin gado kullum. Peter xai xo ya nuna miki yadda ake komi. Iya kacin aikin ki sassana ne kawai ba ruwanki da sauran bangarorin ko apartment na maigida na, duka aikin Peter ne. A sanda muka ci abinci sannan ake wanke kayan ba sai an barsu sun bushe ba, kina jina?'' Na gyada kai da sauri. ''Yaya sunan ki?'' ''Atine shine sunana'' ''meye kuma Atine? Atini ciwon kashin yara da naji ana fadi?'' ''A'ah sunan rana ne'' ''to meye na daren?'' ''Nima ban sani ba sai iyaye na, tunda na taso, Atine suke ce mini'' ''to na ji, ni a wuri na baxan iya fada ba, domin yana tuna mini da kashin yara. Daga yau sunan ki a gidan nan 'BLACK'. Sai ka'idodin xaman gida na. Da farko dai bama rasa abinci, duk abinda kike so Tom xai dafa ya baki. Iyakacin yawon ki daga nan sassan da xaki dinga gyarawa sai can dakin girki wajen Tom inda xaki dinga yin wanke-eanke. Babu 'yar aiki mace cikin gidan nan balle ki sami kawa, su Tom kiristoci ne da Inyamurai, don haka ki maida hankali kan aikin ki kadai, ko tsinke bana son gani cikin sassana.
55
Xakiyi wanka sau uku a rana, safe, rana da dare don karki canxa min atmosphere na daki kamar farkon xuwan ki. ''Ba yawo, ba kawa ba kaxanta''. Sune ka'ododi na. Idan miji na yana gari, kada ki sake in ganki a hanyar sassannan, domin in ya ganki, amai xai yi. Ko xaki xo kwasar kwanukan abinci, sai kin tabbatr ya tashi. Duk ranar da tsautsayi yasa ya tambayeki, ko ina kyautata miki? Kikace ba haka ba, wannan dogon jelar gashin da ke reto a wuyan ki xan cinnawa gas da ashana, kinji abubuwan da na gaya maki?'' Na gyada kai ''to Hajiya''. ''Uwarki ta kauye yaushe ta je Makkah da har kika sa mata Hajiya? Suna na, MUBINA, amma 'yan aiki na suna ce min ''Madam'', amma ke tunda 'yar wanke-wanke ce xaki ce mun Aunty''. Na gyada kai don tabbatar mata na ji abinda tace, na kuma dauka. Ta xaro ido tace ''ya sunana?'' ''Aunty Mubina'' ''ke kuma fa?'' ''Atine 'yar gidan Maikalwa'', ta mike ''nace miki 'BLACK' kin ce ATINE', sunan da na tsana a rayuwata. Har da bayanin gidan ku ko daddawa ce gidan ku na tambaye ki? Bari in baki maganin mantuwa, shige mu je''. Na bita a sanyaye, duk jikina ya mace. Tafiya muke lngu-lungu har muka xo kayataccen dakin da xuciyata ta gaya mib kichin ne, ba don nasan amfanin kayayyakin dake wurin ba, illa don ganin tukunyar girki da na yi. Ta bude wani farin abu kato mai fadi, iri biyu ne da dogo da gajere, ko ince dana tsaye dana kwance mai fadi, to mai fadin ta bude wai in shiga, bayan ta fidda lemukan dake ciki. Tsoro ya kamani, jikina ya soma kyarma, ta daka mun tawar data firgita ni, nayi kundumbala na fada, ta rufe kif, duhu ya mamayi ganina, wani irin sandarewa naji tsokar jikina nayi, in shaki numfashi, inji kamar ana tura min kankara a hanci. Nayi kara ba murya, sai can ta bude ni na fito, duk na sandare ji nake tsokata kamar ba tawa ba, da kyar gudun jini ma bai daskare a jikina ba ''gobe in kara cewa sunan ki ''Black'' ki ce ''Atine'', in kara gaya maki abu ki manta, shige ki tafi''.
[10/5, 7:50 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/5, 7:52 AM] A A Dboy: Tuna Baya 56-60
56.
Jikina sai bari yake da karkarwa, na kunna tafasashshen ruwan nan na surka kadan na shiga ciki na kwanta na soma kuka, jikina yayi min dadi naji ana kwankwasa kofa, na maida kayana na fito. Tom ne ya shigo yace ''maxa-maxa'' inje in yi wanke-wanke, ta gama karin kumallo, idan kuda ya hau mata kwano, komi tsadar shi a shara take sakawa''. Tun bai rufe baki ba, ai ni tuni har nayi nisa da gudu na, dariya ce sosai ta kamashi, ya tabbatar ba karamin tsorata nayi da Aunty Mubina ba. Na kwaso kwanukan na fara wankewa. Cikin wata guda kacal na fahimci Aunty Mubina kakaf. Irin mutayen 'yan gayun nan ne da har gayun ya so ya shafi ingancin addinin su. Tana son duniya, kuma ta same ta a yadda take so, tana cin karenta ba babbaka, cikin katafaren gidan ta kuma babu wulakantacce kuma kaskantacce a gareta kamar dan aikinta. A wurin ta dan aikin ta dabba ne kurum, da idan taga dama, xata ce ya kwanta ta taka shi ta wuce. Gogaggiyar mace ce 'yar duniya kuma 'yar boko, 'yar gata kuma wadda ta dauki auren ta da suna kawai. Abin nufi, komi da ke gabanta yafi auren muhummanci, haka rayuwar auren su da mijin ta, irin rayuwar auren nan ce ta kayi gabas inyi yamma, kowa yaje ya nemo nasa, ba mai jiran dan uwansa yaxo ya bashi. Duk da bansan hakikanin aikin ta ba na fahimci ba karamar ma'aikaciya bace, sabida irin jama'ar da take mu'amala da su, da irin motocin da take hawa na kece raini. Babban abinda yake bani mamaki da Uwargijiyata shine duk gayunta, ballagaxa ce, bata da kintsi ko kadan. Hatta panties din ta da bra in ta tube nan tsakar dakin take cillarwa, ni xan dauka in wanke in adana mata. In kuwa xata shirya, sai ta hautsina bakidaya dakin ta rikirkito da dukkan sitturun da take cikin sif. Komi ta dauka, haka xata cillar dashi komi tsadar shi, sai ni in bi in gyara, haka ko kayanta masu datti, bata san ta fitar ba a'ah, ni xanyi tunanin ai tasa wadannan jiya, in xauna kullum in ware mata masu dattin.