← Book details Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 54

Sashe 25

Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

104.
Idan nayi haka, ai nayi abin kunya, 'YAR WANKE- WANKE TA AURE MAI GIDA? Na tuna da maganar marigayiya Goggo na Indo. ''Ki guji duk wani abu da xai sa kiji kunyar mutane. Gara ki mutu da ki aikata ABIN KUNYA!'' Xan yi kokari in bar gidan nan haka, tun kamin abin kunya ya tabbata. In ba xolaya ba, xuciyata taki amincewa. Cewa take ''Zubaidah, baxa ki iya barin Jawad da Abban Jawad ba!'' Mutumin da ya mutunta ki, a yayin da aka wulakanta ki, mutumin da bai kyamace ki ba, a yayin da ake ce dake mai yalayen hakora, mutumin da ya suturta ki, a yayin da aka so kiyi yawo cikin tsiraici, mutumin da ya fidda ki daga matakin JAHILA xuwa DALIBA mai 'yanci. Mutum da ya dauki Dan shi sukutum, yace ya mallaka maki... Ya maida KYANDIR mutum. Ya maida MUBURGI muciya. Ya maida BLACK LIGHT, ya maida ATINE MAMMAN MAI KALWA ZUBAIDAH MUHAMMAD KARAYE... (these and many more), ai ya cancanci a so shi koda baya da abinda xa'a so shin, balle yana dashi, yana da komi tunda yana da halaye na kwarai, wanda mace baxa ta taba dana sanin auren shi ba. Mutum wanda ya san mutuncin dan adam, ya ke kiyaye martabar kauyen shi, kasar shi da al'adun shi na AREWA. Ban taba ganin mutum mai daukaka kasar shi da kare martabar al'adun shi a duniya irin Baban Jawad ba (Ethnocentrism). Mutum wanda yake karrama 'yan mahaifar shi TALAKAWA, wanda bai taba xagin MAI-KALWA ba mai xai hana ki aure shi Atine koda BA KYA SON SHI! Ki jiyar dashi dadin aure wanda bai samu ba a rayuwar shi, ki mutunta shi, mutuncin da bai samu daga Uwar Dan shi ba. Ki nuna mishi TALAKA BAI MANTA ALKHAIRI, ki mallaka mishi jikin da ya raina daga 'YAR SHILLA XUWA KAXA bai taba nuna yana kwadayi ba. Auren shi shine hanyar da gudan xuciyar ki JAWAD, rayuwa ta har abada! Shine sakamakon da ya dace da shi. In kika bijirewa soyayyar shi kin yi butulci balle ma kina so, kina son miji irin ''TAHEER'' wanda bai dauki rayuwa a bakin komi ba.

105.
Arxikin shi bai sanya shi ya maida duniya gidan kashe-ahi-ba. Kuma tabbas, xai darajja MAIKALWA xai mutunta AMARYA! Shin me kike nema a rayuwa da ya wuce wannan? Wasu irin hawayen dadi suka xubo mani, na mirgina na rungume Jawad, cike da tunanin wani magani xan bincikowa ciwon idon Abban Jawad?????? A bangaren 'yar boko, bata shigo gidan ba sai karfe 6:00pm. Sun shigo tare da wasu kabila 'yan office dinsu maxa guda biyu, inda ta sauke su har main falon ta. Abokan aikin ta ne, ita a dole ta nuna musu eh, ya ne! Mijin ta Minister ne. Don haka ne taki saukar su a falon baki, don bai kai haduwar nata ba ko kadan. Wasu takardu ne suka xo amsa da ya shafi aikinsu, ta xarce daki don ta binciko. Daga can sassan Yallabai, 'yar karamar na'ura mai kama da karamar talbijin, mai nuna masa wanda duk ya shigo ko ya fita cikin gidansa, haka in baya nan, xata dauka in ya dawo yayi rewinding ya gani. Ya hasko mishi Peter na jerawa bakin Aunty lemuka da kayan tande-tande, bai taa xaton xagewar Mubina har ta kai ta shigo mishi da abokan cinikin ta gidan auren sunnarsa ba. Inda duk ranshi yake, in yayi dubu ya baci, dama wai mai hakuri, bai iya fushi ba. Mubina ta fito daki da takardu a hannu, sai ganin falo tayi wayam. Ta leka ta taga, sojoji ta gani na ball dasu, har suka fidda su kofar godan ta. Ta san ba yin kansu bane, suna a bisa umarnin Ubangidan su ne. Ta ji haushi, amma ai fushin fari ba nata bane. Ta tuno rayuwar su da Taheer yawon amarci birnin Toronto. Da yaga wani abokinta sun gaisa ya sambace ta. Ita da abokin ya hada ya dinga tamaula dasu a harabar hotel din, kadan ya rage auren sati biyun ya tungule, sai da Alhajinta yayi masa kuka. To wannan taci sa'a kenan da ba'a hada da ita ba. Ita wannan ba shine damuwar ta ba, abinda ya dameta kawai, yadda xa'a dinga nunata a Bankin su ana mijin ta da take takama 'kidahumi ne'.
[10/8, 5:35 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[10/15, 9:14 AM] A A Dboy: Tuna Baya 106-110

106.
Hakannan wannan tamkar baraxana ne ga shirin su da Mansina, sai dai tasan Taheer sarai mutum ne mai tsananin tausayin mace, musamman in yaga tana kaskantar da kanta. Da wannan ta samu kwarin gwiwar xama ta fece kwalliya, ta cika cikinta da tsatsibe-tsatsiben kayan da'arsu 'yan duniya. Kwalliya ce da take ganin ko xaben Miss Nigeris ta shigo da ita ba abinda xai hanata lashe xaben. Wata riga ce da ko a turai ba'a ko'ina ake samunta ba, sai a wani boutique dake cikin birnin Beijing din China, da ta ba Yayanta Yahai dake karatu can sautu. Wuyanta ya rufe har saman wuyan mutum ruf. Hannun kuma an wani irin ketashi tun daga sama har xuwa 'armpits' din mace. Tsayinta iya cibi ne kawai, laushi gareta tamkar kirar (Romania) tasa wando ya taho a matse daga sama ya bude kadan daga gwiwar har xuwa kasa. Ya sha ce mata bai son kwalliyar ixgar dokin da take mishi don najasa ne, don haka ta hade shi cikin wani tafkeken ribbon mai ciki, kunnenta da wuyanta ta kawata shi da fashion na garari, wato majoricca-pearl, ta kawo turarukan ta duka sexies ta bulbula. Ana taku tamkar ana tausayin kasa, aka nufi sassan Daddyn Jawad. Shi har yayi shirin kwanciya, ya yi nafilolin shi ya kare, yana daure igiyar pyjamas dinshi, ta danna kararrawa, ba tare da jiran ya amsa ba, ta dannan kai, abinda ya tsana kenan ''wai ke bakya sallama ne? Annabi (SAW) ya ce; mafi rowarku shine wanda baya yiwa jama'ar musulmi sallama. Kullum ki danno min kai ba sallama, ance maki ni kafiri ne xaki ishe ni da kararrawa.

107.
Ta langwabar da kai ta rausayar da 'yan idanunta ''kayi hakuri Taheer, baxan sake ba''. Tun daga nan ya gane take-taken ta, tunda har ta bashi hakuri, tana wannan lallankwashewar shegiyar tata ta kawota. Ko dai shi ake so, ko kuma wani dalili nata na daban. Xa ko tasha mamaki, don shima yanxu kan mage ya waye, ya daina tolerating iskancin banxa. Ya bar ta nan tsaye, yayi light-up yabi lafiyar ni'imtaccen gadonshi, ya dauki remote ya karo karfin room heater. Kasancewar sanyi yayi nisa kwarai da gaske, farkon watan April. Barci mai dadi ke dibarsa, xuciyarshi cike da tunanin hanyar da xai bullowa 'yar yarinya Zubaidah, mai tsananin kunya da kawaici. Ruhinshi ke hasko mishi ranar da xai mallaki Zubaidah Uwar Jawad, a wannan katafaren gadon da ya narkarda dalolonshi amma bai taba samun nutsuwa a kanshi ba. Cikin shekarun shi masu tsayi, da aure sai shirme, sai fitsara, sai rashin kamun kai. Shi dai yana da yaqinin Zubaidah xata xam mai nutsuwa agare shi. Ya tuna a yau, taki yadda ta dauki Jawad a jikin shi gudun haduwar fatar jikinsu. Shi ko tashi matar tun kamin a yi auren take nuna mai kulaficinta a fili. Ba don ya kasance mutum wanda yafi karfin xuciyarshi ba, da Jawad yanxu Dan titi ne. Yayi Allah wadai da tarbiyar da Mr. Dango, yawa su Mubina dasu Mimi. In ba don kaddara ba! Me ya kai shi hada xuri'a da Balarabe Dango? Ji yayi ta rungume shi ta baya, ta soma magana cikin muryarta mai kama da an shaqeta. ''Taheer, ina ganin lokaci yayi da ya kamata mu MAI DA BLACK KARAYE.

108.
Iyayenta suyi mata aure, tunda Jawad ya girma xan iya kula dashi yanxu, tunda kaga ba xancen kashi da fitsari, ba xancen goyo da bada madara. Ajiye baligar yarinya kamar wannan a garemu bai dace ba. Ka duba fa ka gani ko su Tom na iya lalatata! Mu xo muna jin kunya, ai gara ayi abi lokacin da ya dace. Sai muyi mata kyauta ta musamman, ko 'yar mota ce da 'yan kudi, a bawa kauyawan iyayenta, kuma ita ma kanta na lura, ta matsu ta ga iyayenta, ko ya ka gani?''
Ta fada tana kara shige-mishi. ''Kai wannan yarinya, ba dai rainin hankali ba''. Ya fadi maganar a xuci ne, bai san har ta subuce, ta fito ta shiga kunnen ta ba. ''Dama nasan abinda ya kawo ki kenan?'' Ta kara narke mishi ''bayan wannan, wata da watanni, ina xaman jiran mijina ya dawo, ai dole in nemi hakkina na aure ko?''. Yayi murmushi, ya mike gabadaya ya sauka bakin gadon, ko kadan tarkonta bai kamashi ba. Lallai ne da aka ce bacin rai ke danne komi. Ya girgixa kai cikin matsanancin takaici ''Taso-taso nan Mubina''. Jikinta a bala'in sanyaye, ta xaro kafafunta ta xauna gefen gadon, kusa da shi. ''Hakkin aure kika ce ko? To a gaskiya, in gaya maki aurennan, aurennan namu da gyara a cikinsa, a addinance da al'adance. Shin ina kika taba ganin masu rayuwar aure irin namu?
Chapter 25 · 0% Book details