Sashe 1
Tuna Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
[9/23, 9:40 AM] A A Dboy: TUNA BAYA
Na
Sumaiya Abdulqadeer
KAUYEN KARAYE (1980)
1
A garin mu karaye, mahaifina, Malam Mamman, wanda aka fi sani da MAI KALWA, wadda ya gada tun iyaye da kakanni. Kowa ya taso a kauyen karaye, da sana'ar da ya san shi kenan. Kamilin dattijo, talaka tikis wanda bai aje ba,bai kuma ba wani ajiya ba. Mai wadatar xuci, bashi da kwadayin abin duniya ko kadan. Koda aka san shi a matsayin talaka, kowa yana girmama shi sabida mutuncin sa. Ga wanda duk ya san Maikalwa, xai shaideshi akan gudun duniya, kyamar abin hannun mutane, in ba wanda gumin sa ya amso mishi ba. Matar maikalwa, tun ta ladar noma, Indo, ita ce uwar manyan 'yan'yan sa maxa uku, akwai Auwalu, Sani da Salisu. Tun bayan haihuwar Salisu Indo bata sake haihuwa ba, sannan ya auro Lami, ta haifi Rabi'u da Atika, itama din kamar hadin baki daga kan Atika haihuwar ta tsaya mata cik. Lami 'yar babban gida ce, a garin karaye kowa ya san ubanta. Tun xuwan ta ta kame gida, Indo ta xama 'yar kallo, sai abinda tace xa'ayi, wanda ta hana, shima ya hanu. Sai kanshi Mai kalwa, shayin Lami yake, sabida masifar ta, inda Indo ta kasance, jarumar uwargida, babu abinda ya dame ta kamar harkar cikin gida tana kuma 'yan kulle-kullen omo, sugar, gishiri, barkono, kanwa, citta mai kwaya, masoro, kanumfari da sauran kayan kulli ta daurawa Sani da Salisu. Don haka duk ranar girkin Indo, Mai kalwa bai san kudin cefane ba, sai dai yaci mai kyau shi da iyalinsa, duka a aljihun jarumar uwargida Indo. Wannan ya bata wata daraja ta musamman a idon shi, da jama'ar gidan duka, har 'ya'yan Lami, suna mutunta Goggo Indo. Allah kuma ya sanya mata albarka cikin al'amuranta, har ta kai ga, Indo sai dai awo, kwano ko rabi. Ta nan ta samu ta tura 'ya'yan ta makaranta, bata ware ba, ta hada har da Rabi'u dan wajen Lami, dan shekaru takwas.
2
Tsakanin Indo, da mijinta Mallam Mamman Maikalwa, mutunta juna da darraja juna ne xiryan. Wannan ya haifar da kyakkyawar fahimtar juna a tsakanin su da 'ya'yansu duka. Don haka koda ya kawo batun kara aure, ya samu cikakken goyon baya daga Indo, da kyakkyawar addu'a daga 'ya'yan sa. A bangaren Lami, ta hana kanta xaune balle tsaye, yau gidan wannan mai rauhanai, gobe gidan wancan malami, wai a lalata xancen auren Maikalwa, da diyar Liman, yarinya Saudatu, amma da yake an ce matar mutum kabarinsa, saudatu ta tare a gidan Maikalwa, shekara na xagayowa ta haife ni, kamar mu daya da ita a komi. Na ci sunan mahaifiyar Maikalwa, kasancewar an haife ni ranar litini suke kira na 'Atine'. Gidan mu ginin kasa ne gaba da baya. Gida mafi talauci da kaskanci a layin gabadaya. Daga farko xaure xaka tadda, wanda ko rufi Allah baiyi xai samu ba, a cikin soron dakin yayan mu Auwal ne, daga katifar audugar shi, sai akwatin karfen kayan shi, da tarin littafan karatun shi, kasancewar shi mutum ne mai kwaxo a fannin karatu, sabanin Sani shi da yafi maida hankali ga bin baban mu kasuwa. Gefen dakin Auwal buhunhunan kalwa ne fiye da talatin, in har da warin kalwa yana cutarwa, da nace cikin mu babu wanda ya kawo matsayin da muke a yanxu. Faffadar tsakar gida mai dauke da katuwar bishiyar dalbejiya, wadda muke amfana daga ni'imar sanyinta, muyi wasa, muci abinci, muyi hira da Baban mu karkashinta. Galiban, anan iyayen mu suke aikin surfen, masara da dawa, anan kuma ake aunar da kayan kullin Guggon mu Indo. Turakar Malam ce ta fari daga dama, sannan dakin Guggo ciki da falo, daga hagu dakin Inna Lami ne, sannan dakin Innata, da muke kira, (Amarya). Rumfar dafa abinci na daga kudu-maso gabas din gidan, sai makewayi daga can bayan dakin Inna Lami, wanda xaka suturta kanka ta hanyar jawo langa- langa ka kare kofar.
3
Goggo Indo ita ta dauke ni a bakin nono, tun daga yaye kuwa na koma dakin ta kasancewar ita Allah bai nufe ta da haihuwar 'ya mace ba, ta dauki so, da kaunan duniya ta axa mani. Duk wani dan abin yayi idan ya taso, kamin ka gani a jikin Atika, ka ganshi a jikina. A da, ta so daukar rikon Atika, take- taken rashin kawaicin Inna ne ya tsoratata, ta kyale mata diyar ta, ita kanta Atikar ba karamar fitinanniya bace tamkar Innar ta. Maihaifiya ta Saude, diya ce ga Limamin Karaye, 'ya daya jal, da ya mallaka; ma'abociyar sani a addini ce sosai. A bokon ma tasan wani abu, domin tayi firamare. Kullum daren Allah matan anguwarmu (Limanci) take karantarwa littafan addini, daga karfe takwas xuwa goman dare. Goggo na ma, tana xama ta dauki karatu, tayi mata tambaya tamkar sauran dalibai. Babu xancen kishi a tsakanin su, ko kuma ganin kyashin juna, sai mutunta juna. Wannan ne yake kara min kaunar Guggo na a kullum. Bani da kamar ta, bani da abokon shawara sai Goggo. Mahaifiya ta tamkar kawaye muke, xamu je dakin ta ni da Atika, muyi hira, muyi dariya, mu tafi dakin Guggo, mu bata labari. Babu kunya ko kadan a tsakanina da ita irin na mutanen kauye ga 'ya'yan su na fari sai 'kawaici'. Wato duk wani al'amari da ya shafeni, baxa tayi ruwa tayi tsaki ba, wannan na Goggo ne. Tsakani na da Atika, shekaru biyu ne kwarara ta bani. Duk wata huduba da Inna kewa Atika game da mu, Atika bata dauka, asali ma kwasowa take ta gaya mani, in yi mata fadan, don me xata ke dauko hirar su da mahaifiyar ta, tana gaya mani? Sauda yawa xata ce ''uhm! Atine, kin ji Innata tace wai bakwa kaunar mu. Wai Amarya ta asirce Malam ya maiheta bora, wai Ina karama, Goggo ta xuba min shinkafar bera a koko, na kusan mutuwa, sai da anka kaini birni naga bokan turai.
4
Don haka in bar hige miki, wata rana xaku kaheni. Irin wannan tsegumi na Atika, yana da yawa, sai in yi murmushi ince, ''Atika, ba xan ce Innar ki tayi karya ba, amma da kaheki Goggo keda niyyar yi ai da baki kawo yau ba. Kwanan ki nawa a dakin ta, bata kahekin ba? Ni kuwa 'yar uwar ki ce, Uban mu daya, ina kaunar ki, ban taba tananin cutar dake ba. Abinda ke tsakanin iyayen mu, kishi ne, irin na matan sango, kada ki sake ki tsoma baki, babu ruwan ki.'' to da haka nake kashe gulmar Atika, duk da nike kasa da ita ni kaina nasan Atika ''doluwa'' ce. Na fi ta wayo da hankali, na fita kamun kai, ta fini son kwalliya, gwalli da iyayi. Don haka koda muka dan tasa samari ta ko ina ke kawo mata cafka. Gata da ingarman jiki, girma take cikin dan lokaci, girman jikin ta yafi shekarun ta kai kace hurata ake yi. A kauyen mu, Atikar gidan Maikalwa, tayi suna sosai a wurin samari, gata dai baka wuluk, amma kyakkyawa, mai ado da rangwada, Atikar Inna Lami kenan. Al'adar mu a kullum, idan mun tashi da Asubahi, bamu komawa barci, xamuyi sallah tare da baba, mu cigaba da laxumi, har xuwa ketowar alfijir. Mai girki cikin su. Ta tashi ta dama koko, ta dumama sauran tuwon dare. Idan aljihun Baba da albarka, ya aiki Ya Auwal, ya siyo mana kosai a hada da shi, ranar da babu kuwa, a sha koko,a ci dumame. Ni kuma in share tsakar gida, xaure, dakin Auwal dana Goggo na. Watarana Atika, in 'yan kirkin na kusa, ta share na Inna Lami, dana Amarya. Ta koma tabarma, ta ja filo ta mike, in ko basa kusa, da Baba ya fice kasuwa, xata koma sharar barci abinta. Son barci irin na Atika, ko kasa sai haka. In hada kwanuka, in dau guga in jawo ruwa, in dauraye su, in kada dan jangabo, in dauraye kewayen mu tas, Goggo tayi ta sa mani albarka ita da Amarya. Auwal, Sani, da Rabi'u su tafi makarantar boko, mukuma mu tafi allo. Ina goye da 'yar Innata Amarya da aka haifa mana daga baya. Haihuwar gidan mu tamkar tsari, sai dai tsari ne daga Allah, kamar bata mata kauye