← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 40

Chapter.....10

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍️


INA YIWA.....


Ɗaukacin Al'ummar Musulmi BARKA DA SALLAH!!! ALLAH Yakarɓi Ibadarmu Yasa Kuma Mun Rabauta Yakuma Nufi Musake Ganin Wani Azumin Cikin Rai da Lafiya 🙏.


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.

Bissmillahi Rahmanin Raheem


Nidae Bance Komai ba Cikin Sanyin Murya Nagaida Dady Ya'amsa min Cikin Kulawa Kafin Yajefomun Tambayar "Meya Haɗaki da Momyn Ku?" Sai da Nakalli Momy Dake Tamin Kallon Kamar Intaso In Shaƙeki Kafin Nasake Riƙe Wayar Nace, "Ba'akomi Dady." daga can yasauke Ajiyar Zuciya Sa'anan Yace, "Kina jina ai? "

"Eh Dady."

"Ki nisanci Abinda zai batawa Mamanki Rai Bana son Fitina kinji ko?"

"Dady Nifa banma ta Komai ba Alhaji ne yake Zuwa Ina....."

"Bana son Wani dogon Bayani kiyi Kawae yanda nace Kinji ko?"

Nace, "Shikenan Dady Insha'allah Zankula. " Daga Can ɓangaren Nasa Yace, "Yawwa ALLAH Yamiki Albarka. Ba Momy Taku Wayar."

Na'amsa Da Amin Kafin Namika ma Momy dake Ta Aikin Hararata Wayar.


Bansan Dame-Dame Suka ce Ba Don Miƙewa Nayi Nafito Nasoma Aikin Gidan da Nasan Ni ke Yinsa. Kawai dai Naga Momy taɗan Sake min Saɓanin Da can Farko Kamar Yadda ta Ɗau zafi Dani. Nima kuma naƙara bata Hakuri Tace Tayin Yauma Tare Muka Fita Wurinda Take Saide-Saidenta.


Da Misalin Karfe Tara da kwata Lokacin muna Falon Momy muna kallon Arewa24 Yaron Makwabtanmu Yashigo Tareda Yin Sallama Kafin ya gaida mu Sa'anan Yaɗora da Cewa, "Wai Ana Sallama da Khaleesat."

"Jeka ce waye ne?" Momy ce mai Wannan Maganar.

Nidae Ƙala bance Ba Maimakon ma Hakan Sai naƙara Gyara Kwanciyata Saman Dogowar Kujerar Danake Kwance Akai Ina cigaba da maida Hankali Na Ga Kallon danakeyi. Ba'a wani Daɗe ba Yaron Yadawo Yana mai Sanar mata Cewa, "Wai Alhaji Saminu ne. "

"Je kace Tana Zuwa." Amsar da tabawa Yaron kenan. Kafin tadubeni Tace "Ai sai kitashi Kije ko?"

Ban musa mata ba nasakala mayafina nafice Zuwa Gurin Alhaji Saminu Muka Sha Hirarmu Kafin Yacika ni da kuɗaɗe kamar Yadda Yasaba Yamin Sallama Yawuce.

Cikin Lokaci Ƙanƙani Natara Kuɗaɗe Masu Tsoka Daga Gurin Alhaji Saminu da Sauran Waɗɗansu Samarin Nawa. Wayanda Nakan Fito gurinsu A sace Batareda Sanin Momy ba nakan ce musu in sunzo Suce Sunan su Alhaji Saminu da wanan dubarar nake fitowa ta.


Kwata-kwata Yanzu Bana Sauraren Wanda Nasan Bazan Samu Kuɗi Gurinsa ba. Inkaga Muna Ɗasawa Tau Kasakarmin Bakin Aljihunka Ne. Saidai Koda Kuskure Ban Taɓa Bari Wani Daga cikinsu Ya yaudareni ba. Ganin Kuɗin Dana ke Ajiyewa Gida Sun ɗanyi Kauri Na yanke Shawarar Zuwa Banki In Buɗa Accaunt Insasu Ciki Dan Gudun Ɓacewar Rana.


Dan Haka da Sanyin Safiyar Litinin Na Shirya Na Nufi Banki Bayan Nayiwa Momy Ƙaryar Zanje Gurin Aminiyata Dubata batada Lafiya. Ban Samu Wani Jinkiri ba Akamin Bvn Number Bayan Nacika she Form Suka ce Inje Jibi Indawo In Anshi Atm. Tun Acikin Banki Na haɗu da Wani Alhajin Yamaƙalemin Yana ganin Nafito Shima yayi Zumut Yafito Waishi A Dole Zai ragemin Hanya.

Ban musa ba Nashiga Dan dama irinsu Nake Nema😋. Kafin Mukai Gida Hira ta ɓarke A Tsakanin Mu Mukayi Musayar Number Asanda Yakawo ni Bakin Gida Ya'aje Da Alkawalin Zai dawo da Dare Nabashi Lokacin da Zaizo mukayi Sallama yaja motarsa Nikuma Nashiga Gida.


*******

Tun Bayan Faruwar Wancan lamari Yayiwa Kansa Alkawalin Mantawa da Khaleesat da duk wani Abu da Yadanganceta Yanzun Aikinsa kawae yasa A Gaba Wanda in yadawo kuma yakanje Majalisar Wani Malami Ɗaukar Karatu.


Wani Sauayawar Tasa ba ƙaramin daɗi tayiwa Innarmu ba harma da Abubakar Yanzu Walwalar Gidan Tadawo Sunci Gaba da harkokisu Kamar ma Komai bai faru ba. Sai dai A koda Yaushe Abdul-wahab Sai Yayi da gaske kafin ya yakice Tunanin Khaleesat A Ransa Saboda Shi Yasan Cewa Sonta ba Kaɗan Yamasa Ta'annati ba kawai yana maida komai ba komai bane Saboda Yasamu Yaci ribar Rayuwarsa Ko dan Kuma Ganin Farincikin Innarmu Mussaman ma in ya tuna Irin Wulakanci da Khaleesat ɗin tayi Masa.

A koda Yaushe kwana yake Yatashi Da Tunanin Yaza'ayi Yasake Samun Damar Komawa Makaranta Yacigaba da Karatunsa Tunda Yatabbatar A Yanzun Ba wani Gata dazai yima kansa Wanda Yawuce Ya Tsaya Yayi Karatun.

Ga Abubakar Nan paper Karshe Suke Zanawa Yanzun Abdul-wahab Yana Ji Ina Ma'ace Shine? Da Wannan Nazarin Dayake Yasamu Shiga Makarantar Lawyer dake Cikin ƙaramar Hukumar wamakko.


Tunda Yasamu Yashiga Kuma sai yazama bashi da Wani Aiki sai Karatun ko da yaushe kaganshi inba wurin Aiki ba tau yana Karatun ne. Hakan kuma bakaramin daɗaɗawa Innarmu Yayi ba kullum Cikin yimasa Adu'a Take.


Khaleesat Fa?


Nazama Cikakkiyar Budurwar Manya Daka ganni Yanzu kasan Komai Yazauna Wayar da Nake Riƙe da ita ma kasan Takai balle Aje ga Maganar Suturar da nake Sawa Ƙawayena Kuwa Suma Sunsan Class yakaru Sai Huramin Kai Ake. Bana Harka da Ƙananan Mutane Sai Alhazai Masu Hannu da shuni.

Alhaji Saminu kuwa Tuni Mukai Baram-Baram Saboda tafito Fili Bawai da Gasken Aurena Yake Nema ba Kawae JIKINA YAKESO Nikuma Yatarar Ba irin sa bace dan haka Mukai Fata-fata Lamarin da yakaimu Gabansu daddy Kenan Ƙiri-Ƙiri Kuma Yanuna masu Cewa shi yafasa Aurena. Abun ba kaɗan yayiwa Su Daddy Ciwo ba Sunyi Nadama iya Nadama na Amince Masa Baremma Momy.


Lamarin Sha'anina da Alhazai kuwa Tuni Nabuɗe kasuwa da su Sosai Su Momy Sunyi Iya Nasu Ƙokari Harsun gaji Sun barni Wannan ma yasa sun Kara Nadama Akan Lamarin.


Karfe Biyar ne Lokacin da nake Gyara Parking ɗin Motata Wacce Alhaji Tanko (Sabon Alhajin da muke Harka dashi ) Yasiyamin Nafito Cikin Wata irin Ƙasaita Wacce Nakeji Ba Yanayi Duk Cikin Ƴan mata. Narufe Motar Kafin Nashiga Gida Ina Ƙoƙarin Danna key ɗin Motar Tawa Tayi Wata Irin Ƙara Kai Tsaye Nashiga Gida ba Kowa A gidan Dan Momy Izuwa Wannan Lokacin tana Wurin Saide-saidenta.

Kangado Nafaɗa Gajiye ina Hamma Wayata Najawo Wanene Yake Kirana Adaidai Wannan Lokacin? ALHAJI SHESHE! Sunan dake ta Yawo Kenan kan Fuskar Wayar Tawa Naɗan Tsurawa Wayar Ido Cikin Nazarin In ɗauka ko infita Batun sa? Karshe dai Harta Yanke bangama Shawara ba. Can sai ga Kiran Yasake Shigowa ɗan taɓe Baki Nayi Cikin Nazari Itama haka Ta Tsinke ban ɗaga ba.

Ƙarshe dae Watsi Nayi da Wayar kan gado, nadafe Kaina da Duka Hannaye Biyu Cikin Tunanin Wannan Rayuwar Yakamata Ace Angama Wasar Hakanan Inje Ga masoyina Na Hakika Wanda Zuciya ke kwana da Yini Cikeda Ƙaunarsa Ina da Yaƙini Cewa A halin Yanzu Natara Kuɗin da Zasu Ishemu Rayuwa In Mukayi Businezz dasu Kuwa, Tau Har jikokin mu Basu Ba Talauci Tau Saidai Anya Abdul-Wahab Zai Yarda Dani Yanzun Zai Iya ma Saurarata Har Yafahimta da Wannan GAME ɗin dana Buga Wadda Ba Komai Yasa Sai Don Ceto SOYAYYAR MU ba? babu Shakka Akwai Aiki ja Agabana.

Ganin Yanayin Garin Nakara rinewa tabbacin Kowa ne Lokacin Ana Iya Gocewa da Ruwan Sama Yasa Nayi Hanzarin miƙewa Na Sauya kaya Kafin Nararumi Jikkata Nasake Ficewa Kafin In Isa Gurin Motar Tawa har'an Fara Kaɗa Wani Iska Mai karfi.

Kai Tsaye Dambu Store Na nufa Ina Isa gurin Nagyara Parking Nafito daga Cikin ta nashige Ciki Nasoma Jidar Abubuwan da nake Buƙata Turarukka Masu Asalin kyau Naɗauka Nakwashi Mayuka da Biskit da Chacolate Masu Ɗan Karen Kyau harsu complaks Sai da naɗiba Saida Nayi Siyayyata Yanda Raina keso Kafin Nakai Gurin Masu Lissafi Akamin lissafi Namiƙa masu Atm Ɗina Suka Cire Kuɗinsu Injiyo Haka mukayi Karo da Mutum Kayan da ke Hannuna da Nasa dake Hannunsa Suka tarwatse Suka faɗi Kasa Sukayi ɗai-ɗai A tafkeken Gurin Naɗago Kai cikin Masifar Wannan wane irin Mutum ne marar lissafi cikin Lamurransa Da har zaice Baya ganin Abinda ke Gabansa Saidai Wanda Idanuna Sukayi Tozali Dashi Ba Zato Yasa Na nemi Masifar Na Rasa Nayi Saƙare Ina ƙare masa Kallo!


Abdul-wahab ne Sanye da wani tattausan Yadi Fari Kal! Kana Ma Iya hangen singlet ɗinsa saboda farin yadin Ga wani Mayen Kamshi da yake tashi A jikinsa Yarufe Kyakykyawar Fuskarsa da Wani Farin glass kana hangen kwayar idonsa Haka Kansa yana sanye da Fulla fara kal Irin ta Ustazai ɗinnan Wacce Sakkwatawa ke Cewa 'Taɓanni kasha Hadisi'

"Abdul-wahab!!! "

Naji Bakina yafurta Sunan nasa Batareda Nashirya hakan ba ko Nasan Na Furta ba.


Shikuwa Abdul tun Kallon Farko Bai yarda munsake Haɗa ido ba illah Yadurkusa Yasoma haɗa kan kayan sa da suke zube Kan Farin Tayes ɗin dake Malali A tafkeken Wurin.

Yana Kammallah kwashesu Yaje Aka masa Lissafi Yabiya Sa'annan yasake Juyowa yanufi Hanyar Fita. Duk Abinnan da'ake Ina nan Tsaye Kamar Wacce Aka dasa Gurin Inba Kallonsa Ba'abinda Nake.


Ganin Zai Fice yasa Nayi Saurin Haɗa kan kayana da Taimakon Ma'aikatan Wurin, Nakwaso Sauri Nabi Bayan Sa Ina Kwala Masa Kira, dae-dae Lokacin da Ƙaninsa Abubakar ke gyaran parking ɗin Mashin Yana Cewa "Hau Muje Yaya." Nikuma Naƙarasa Ina Cewa, "Abdul Katsaya ka Saurareni."

Abdul-wahab Yatsaya yana Kallo na Tacikin Farin glashinsa Wata Zuciyarsa Na Shawartarsa da Cewar Karka Tsaya yayinda wani Ɓangaren Nayi Masa gargaɗin "A Kul! Gara Ka tsaya Masoyiyarka ce Fa Wadda kake kwana da Tashi da Tunanin ta. Dan Haka sai Yatsaya Yana ji da Kallona.


Ganin Haka Abubakar Yayi ƙoƙarin saukowa daga kan Mashin ɗinda Yake yanufo Gurin da Muke Dai-Dai Lokacin da Nake Cemasa, "Kayi Hakuri Abdul duk Abinda nayi maka Shirine Kuma duk Abibda kaga ya..... " Abubakar yafisgi Hannunsa yana Cewa, "Yaya Karya take Karka saurareta Itaɗin Mayaudariyace. " Abdul-wahab Yaso Ya'amince da Abinda Ƙaninsa Abubakar ke Gayamasa Amma kuma Soyayyar Khaleesat Nata yunkurin Hana Ya yardar dan haka sai Yafisge Hannunsa Acikin na Abubakar Tareda Cewa, "Kadakata mana! " Cikin Mugun Mamaki Abubakar Yake Kallonsa Kafin Wasu Hawaye Masu Zafin Gaske Suka Wuto Akan Fuskar Abubakar ɗin Cikin Rawar Murya Yace, "Yaya Wallahi karka Saurare ta Yakamata Kagane itaɗin ba Alkairi bace Gareka. Karfa ka manta Irin Tashi Faɗin Da Innarmu keyi Akanmu Tayi Wanke-Wanke Tayi Share-share kai tayi Kowane irin Aiki Dan ganin ta Kyautata Rayuwar mu Lokaci ɗaya Wannan muguwar tazo ta tarwatsaka wanda yazama Silar Rasa Farincikimu sannan ya rusa ma Karatu Amma duk Wannan Yanzun kana Ƙokarin Mantawa Yaya? Shikenan Ai Amma Kasani Wannan Karon Bana Tareda Kai! " Waɗɗanan Kalaman Sai Suka zama Farkawa ga Abdul-wahab Akan Halin da Yatafi dan haka da hanzarinsa Yajuyo Yarike Hannun Kaninsa Batareda ya iya Furta Komai yajasa Nufin dae Suwuce Kenan.


Ganin haka Yasa Nabisu Cikin Wasu Irin Hawaye dakemin Saraftu A Fuskata Watau Mutanen nan irin Fassarar da Suka min Kenan? Nadubi Abubakar Cikin Hawayen da suke ta Faman Gow Slow A Fuskata ina Faɗin "Abubakar Kumin Mummunan Fahimta ne Amma Wallahi bahaka Bane Da zaka ku Tsaya kuji...... "


"Meza muji? Wanda bamuji ba Acan ba? Eh? " Abdul-wahab ke Wannan Maganar Cikin Rawar Murya Kafin yadubi Abubakar Yace, "Kayi Saurin ɗaukeni Daganan Abubakar inba haka ba Komai zai iya Faruwa." Cikin Zafin Nama Abubakar yayiwa Mashin ɗin Siterta Suka Bar Gurin Yayinda Abdul-wahab yakife Kansa A Kafaɗar Abubakar yana mai ci Gaba da Sauke Wasu irin tagwayen Numfashi jere da Juna Kamar mai Asma.


Ganin Sun Tafi ga kuma Yan tsirarun Mutane da Suka tsayu A gurin Suna kallon dramar da muke Yasa Nanufi Motata da Hanzari kafin Narufe ta Ruf Naja ta da Karfi Nabar Harabar Gurin.


Ikon ALLAH ne Yakaini Gida Kasa fitowa nayi daga Motar Sanda Na'iso Gidan Sai Kawai Na rumgume Sitarin Nafashe da Wani Irin Kuka Mai ɗaci. Yanzu Irin SAKAYYAR da Abdul-wahab Zaiyimin Kenan? Nazamo mai Sadaukarwa Akan SOYAYYAR mu Amma Shine Zai kasa saurarata Yaji Uzuri Na? Ba'akomi duk Abinda Yafaru LAIFI NANE! Eh Mana Laifina Mana Nida Na Sadaukar Masa da Komai Nawa.

No! Ba Laifin ki Bane SONE SILAR KOMAI! Wani Ɓangaren zuciyata ke cemin Hakan sai na samu kaina da girgiza Kaina cikin Murya Kuka ina Faɗin "ba Shakka Hakane.!!! " dai-dai Wannan Lokacin ne kuma Aka Gwafce da Wasu Irin Ruwa Masu Ƙarfi Harma da Iska Kasan Cewar Su Na Farko -Farkon Damina.


A Wannan Lokacin Nasha Kuka harna gode ALLAH Yanzu Banda Ajiyar Zuciya ba Abinda Nakeyi ina kuma Cike da Tunanin MAKOMATA. Gashi dae Nayiwa kaina Tambarin Zama ƳAR ISKA! Saboda Abinda Mafi Yawan yan Unguwa ke kallo na dashi kenan Hakama Iyaye Na. duk-da Cewar Kuwa ni A Raina bahaka bane kuma duk Abinda Nayin Nayine domin ceto Soyayyar mu, Sai dai Gashi Wanda nayi DominSa Shikuma A MAYAUDARIYA yake Kallona

Kenan dai BANI GA TSUNTSU BANI GA TARKO! Wannan Tunanin da Nayi sai Yakara mayarda Damuwata Sabuwa Fil! Nasake Fashewa da Wani Irin Gurshekeken Kuka kamar Raina zai Fita.


Su Abdul-wahab Fa?

............


Readers Shin Meke Shirin Faruwa Ne? Kuma Meyasa Wai SONE keta Zama SILAR KOMAI? Ba Shakka!! Akwai wani Ƙullallen Ƙulli da Warwara sa keda Matuƙar Fa'idar da kuma dacewar ji ga mabiyin👇👇👇

Labarin. SONE SILAR KOMAI
❤️❤️❤️

Dan haka Muje Tareda Alkalamin

FA'IK!!. ✍🏻✍🏻✍🏻
[9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 8 · 0% Book details