← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 26 OF 40

Chapter.....28

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


NOT EDITIN....... 🙏


Bissmillahi Rahmanin Raheem


Dai-dai Lokacin Kuma Masaalatan Unguwar Suka Soma Kwallah Kiraye-kirayen Sallar Magrib.

Dan Haka Dr Jabir Yamiƙe Yana Cewa, "Kun Shiririta ni Har An Soma Kiran Sallah da Kuma Naso naɗan Watsa Ruwa Inɗan Rage Gumi Nan (Zufa)Kafin Inje Massallaci."

Maman Asharaf Ta Kwashe Fayel ɗinda Yashigo dasu da Kuma Labcaot ɗinsa Tabisa dasu Tareda Cewa, "Bawani Gumi da Kayi! in Ma Kayin Ai Gumin Naka daɗi ne Dashi Dan Yafi Almiski Kamshi."

A hanzarce Yajuyo Yana Kallonta Cikin Son Tabbatar wa Kansa Itace Kuwa Tayi Wannan Maganar? Itama ta Fahimce shi dan Haka ta Maze Abinta Ta Raɓashi Zata Wuce yayi Hanzarin Jawo ta Jikinsa Tareda tsare ta da Manyan Idanunsa da Ke rikita duk Wani Mutum da ya Kalle sa Yace, " Sereously Maman Asharaf Ki Maimaita Abinda Kika Faɗa Nayi Missin ɗin Jin irin Wayyanan daddaɗan Kalaman daga gareki tun Sanda Aka Soma Shirin Aurena da Marigay...." Tai Hanzarin taresa ta hanyar Cewa, "Kaga Dr Anfa Soma Haramar tayarda Sallah Ko So Kake Shima Sai Ka Rasa Jam'i Kace Laifin Mu ne?"


Hannunsa Yakai Kan Lips ɗinta da Yasha witlips Sai Maiƙo Sukeyi, Tayi Hanzarin Kwalawa Asharaf kira Dr Jabir Yayi Hanzarin Saketa Suna Dariya.

Dai-dai Lokacin Asharaf ɗin Yazo Yana Cewa, "Momy Jani(gani)" Taja Hannunsa Haryanzun Bata Bar Dariyar ba Tana Faɗin Zomuje Kayi Arwallah Kabi Dadyn ka Zuwa Masjid.


Ɗan Harar ta Dr Jabir Yayi Tareda Nuna Kirjinsa Yace, "Ni Ko? Zamu gauraya ne. Sanda Wata Zata Shigo Hanunna Asharaf Na Ina?"

Gwalo tayi Masa Tareda Cewa, "Yanzun dai Natsira ɗin." Duk Suka ɗunguma Zuwa Cikin Sukayi Arwallah Shida Asharaf ɗin Suka Nufi Massallaci Bayan Yacanza Suit ɗinda Ke jikinsa Zuwa Jallabiya Kalar Ruwan Zuma Sai Tashin Ƙamshi Takeyi.

Ita Kuwa Nan Ta Kabbarta Tata Sallah Acikin ɗakin.


**********


Duk Yanda Mamar Walida taso dauriya daga Halinda ta Sami Ƙanin nata Ciki Sai Takasa Tafashe da Wani Irin Kuka Mai tsuma Zuciya.

Kai da ganin Yanda Abdul-wahab ɗin Yake Baccin Kasa Bana Lafiya bane Kuma Ba Acikin Hayyacinsa Yakeyin sa Ba. Abubakar ne Yake Tausarta Yana "Aunty Idan ke Kinyi Haka Mu Muyi Yaya Kenan? Kiyi Hakuri Dan ALLAH ya Abdull Adu'ar mu Yafi Buƙata A Yanzun Ba Kuka ba."

"Tayaya Bazanyi Kuka ba Auta? Wannan Wace Irin Jarabar SONEE? Dubi Kaga Halinda Abdull Yake Ciki, duk Wanda Yasan Abdull Ada Yazo Yanzun da Wuya Ya shaidashi Duk Dalilin SO! Sukuwa Iyayen Khaleesat waɗanne Irin Mutane ne Mararsa Imani ne da......"


"Aunty!!!! Dan ALLAH Kibar Wayannan Maganganun Tunda dai Yanzun duk Mai Faruwa ta Faru Abu Mafi Muhimmaci Shine Yaza'ayi Mu Samawa ɗan Uwan mu Lafiya Yadawo Hayyacinsa Shine Magana." Abubakar ne Mai Wannan Maganar Yana mai Ƙokarin maida Kwallar da Ke Son Zubo Masa Shima.

Babu Shakkah! Abdul-wahab Yana Cikin Wani Hali da Kowaye kai Inka Ganshi A Yanayin Zaka Tausaya Masa.


Cikin Barcin Nasa Sai Surutu Yakeyi, "Khaleesat Bamuyi Wannan dake Ba Baki Gayamin Zaki Mutu Ba Fa? Munyi dake Zamu Rumgumi Ƙaddarar mu Muyi Hakuri Akan Hukunci su Dady Akamu. Amma Meyasa Zaki Karya Alkawalin Nan Khaleesat? Mezai Sa Ki Mutu Ki Barni Acikin Wannan duniyar? Me Zanyi A Wannan Duniyar da Babuki?" Duk Sun Rufu A Kansa Suna Sauraren Sambatun Nasa.

Cikin Kasalar Jiki Abubakar Yakai Tafin Hannunsa Kan Bakin Abdull Tareda Furta,"Innalillahi Waa Inna Ilaaihi Raju'un! ALLAH Yakawo Maka Ɗauki Ya Abdull."

Dai-dai Lokacin ne Kuma Innarmu Tashigo Hannunta Riƙe da Carbi dan Sanda Maman Walida Ta'iso Tana Sallar Isha'i Kafin Kuma taɗora da Shafa'i da Wutiri. Shiyyasa ma Basu Gaisa Ba da Maman Walida Ba.

Ta kalle su daga Yanda Sukayi Cirko-Cirko Tana Tambayar Su Lafiya Kuwa? Maman Walida ce Tashare Hawayenta Tace, "Yanzun Mama Haka Abdull Yakoma? Wannan wane Irin Masifa Ce?"

Innarmu tagirgiza Kai Cikin Alhinin Abun Kafin taɗora da Cewa, "Kindai Gani Ɗazun Ma Da Yafarka Nema Yayi Yafice daga Asibitin nan Sai da Likitocin Suka danna Masa Allurar Bacci, Ai kedai Lamarin Abdul-wahab Sai du'i Kawai."

Maman Walida Tajawo Kujera Tazauna dan dai A Halin Yanzun Jitake inta ci Gaba da Tsayuwa Itama Zata Faɗi dan dai Babu Shakkah Ƙafafunta A Yanzun Baza su Iya ɗaukarta ba. Dan haka Ta rafka tagumi Cikin Salalar Hawaye.

Innarmu Tace, "Bafa Haka Yakamaceki Ba Auntynsu Adu'a ce Kawai Abunyi."

Maman Walida ta Girgiza Kai kawai Tareda Sanya Hannuta ta Share Hawayen da keta goslow Afuskartata. Innarmu Tace, "Ina Yaranne Kardai Kice Bakizo da Ko ɗaya ba?"

Cikin Nauyinda Bakinta Yayi Mata Tace, "Su Walida Suna gida tareda Babansu Kinsan Makaranta Shikuwa Hanif Yana nan gida Nabaro Inda Maman Nuwaila(Makwabciyar Su Innarmu )."

" Tau Kinyi Sallah?" Innarmu taɗora da Wannan Tambayar.

Girgiza kai Kawai Maman Walida Tayi.

"Tau tashi Kije kiyi Ruwa Na Nan Cikin Buta ta Gurin Shimfiɗa."

Maman Walida ta tashi Tanufi Yin Arwallah Tana Tafiya tana Waigen ɗan Uwan Nata.


Haka Suka Kasance Cikin Juyayi da tarin damuwa Akan halinda Ɗan Uwan Nasu Ke Ciki, Ko ƙadan Basu Runtsa ba domin dai Abdul-wahab Hauka Yakeyi tuburan! Wanda Kuka kam! Sun Shashi Harsun godewa ALLAH.


Dole Bashiri da Safe Bayan Dogon Bincike da cike-ciken Fayel da Akayi Aka Turasu Asibitin Mahaukata dake Cikin Ƙaramar Hukumar Kware.

Zo kaga Tashin Hankali Wurin Wayyanan Bayin ALLAH! Surutu Kala-kala Yakeyi Yayi Kuka? Yayi Dariya Yayita Harare-Harare. Wallahi Abun Gwanin ban Tausayi Musamman ma dai Ada Kasan Abdul-wahab ɗin Mutum mai Matuƙar Natsuwa!. Bayan Isarsu Asibitin ma dai dogon turanci ne Aka tsaya yi Siye wannan Kati Cike Wannan Rasiti Yi Wannan Tes! ɗin Kafin Fa Kuma Aka dangana su da inda Za'a Kwantar dashi.


Nanma dai duk wanda kagani Gwanin ban Tausayi Saboda ga Mutum dai Har Mutum Amma Yana Hauka.

Wasu Sha-shaye ne Sila Wasu Kuwa Asirine Wasu kuwa Rashin Lafiya ce Ya allah Haɗari ko dai Ciwon Kawai.

Su Innarmu Fa Sunga Rayuwa Irin wacce tunani da Hasashen Su bai taɓa kawo Masu Cewa zasu Riski Kansu Acikinsa ba.


Su Innarmu da Maman Walida Sun Kasa daina Hawaye Yayinda Abubakar ke Kukan Zucci Wanda Akace Yafi Na Zahiri CIWO.

Haka Suka Zauna Asibiti Na Tsawon Lokaci Suna Jinya Wanda Suka tsayu ba dare ba Rana Wajen Kai Kukansu ga ALLAH Wanda Babu Shakka sai suce Adu'ar ma tafi tasiri Sosai Sama da Maganin da Akeyi Masa. Kuɗi Kam Ancajesu Sosai wanda duk wani ɗan Tanadi da Sukayi Jinyar Ta laƙume Shi.

Damar su Basu Nema Gurin Kowa ba.

ALLAH yarufa Musu Asiri Hakanan Yan Uwa da Abokan Arziki Suna Kan Hanya Gurin Ziyartarsu Gwargwado Kuma Kowa yazo Yakanyi Musu Hasafi. Zuwan Mijin Maman Walida Ukku Gurinsu. Yan Garejin su Abdul-wahab ma Mota guda Sukayo harda Ogan su Aka zo duba Abdul-wahab! Hakanan Abokan Karatun sa Bus ɗin Makaranta ta kawo su Suma. Shikuwa Yusuf Kullum tafe yake Tsakanin Kware da Cikin Birnin Sakkwato Hargida Yaje Yasami Su Momy Yasanar dasu Irin Halinda Abdul-wahab Yake Ciki Ai kuwa Suma Sunzo dubinsa Momy Kam da Kuwa Wiwiwi Tabar Asibitin NADAMA Iya NADAMA Tayita.

Dady ma da Ya Nuradeen da Suka Shigo Gari Sunzo Dubiyar Sa.


Wannan Na ɗaya daga Abinda Yaragewa Su Innarmu Raɗaɗi daga halinda Suke Ciki dan Al'umma Sunyi Musu kara Suka ƙara yarda Cewar da'akayi, AL'UMMA RAHMANE.


Tau Cikin Ikon ALLAH dai Abdul-wahab Yadaina Sumbatun da Yakeyi da Surutai da Yawan Firgice-Firgece da Yakeyi.


Shidai Gashinan Sukuku ne ba Magana Sai Ido da yake bin mutane Dasu, Tau Amma me? Suna Zaune Yau da Sanyin Safiya.

Yayinda Shikuwa Yake Kwance Kan Gado Yana Lumshe da Idanunsa A hankali Yabuɗe Su yana Kallon bakin Ƙofa, Ai bashiri Yamiƙe Zaune Zumbur! Tareda Cewa, "Khaleesat?" da Wani Irin Mugum Mamaki Su Mama Suka Juya Suma Suna Kallon Inda Yake Kallon Khaleesat ɗince Kuwa Suma Suka Gani Tana tafe Yayinda Hawaye Ke Ci Gaba da Shatata A Fuskarta.

Abdul-wahab Wata irin Zabura Yayi Yamiƙe Tsaye Tareda Nufar Inda Take Yana Mai Cewa, "Dama Ni Nasani Baki MUTU ba Khaleesat! Dama Ni Nasani Wallahi Bazaki Mutu Ki Barni Ba Dama ni Nasani Ƙarya Akeyi."


Tare Suka Iso ga Juna Suka Rumgume Juna Cikin Wata Irin Matsainaiciyar Soyayya Mai haɗe da Wani Irin Zazzafan Shauƙin da Komai Ƙoƙarin Zuciya bazata iya danne sa Ba, Kawai Yazama Wajibi gareta ta Sallama. Kuka Wanda Ake Kira Kuka Suka Sanya Shida Khaleesat, Yayinda Bakin Abdul-wahab Yakasayin Shiru, "Khaleesat Ni Nasani Bazaki Tafi Ki Barni ba Ni Nasani Ƙarya Akeyi." Sai kuma Yajawo Hannunta Zuwa Wurinsu Innarmu da Maman Walida da Sukayi Mutuwar Zaune Wanda Ko kwakwaran Motsi Sunkasa Yi Duk Inda Jikinsu Yake Ɓari Yakeyi Tambaya Iri Ɗaya Sukeyi wa Kansun Shin Suma Sun Haukace ne Komeye?

Suna Nan Cikin Wannan Halin Har'izuwa Sanda Abdul-wahab Ya'iso Garesu Fuskarsa Cike da Hawaye, Yasoma Jawo Hannun Innarmu Tareda Cewa, "Innarmu Taɓa Kiji Wallahi Khaleesat ce Dama Nace Muku Ƙarya ne Bata Mutu ba Khaleesat ɗita bazata MUTU ta Barni Ba Kuka ƙi Yarda Kuka ɗaukeni MAHAUKACI."


Innarmu Muƙut! Tahaɗiye Wani Mugun Yawo da Yamaƙale Mata A Maƙwashi A sanadiyar tsayawar Wucin Gadin da Komai Nata Yayi. Tabbas Ga Hannunta Cikin Na Khaleesat Fa Kuma Ga Khaleesat ɗin Ita ma Gabanta Cikin Wani Irin Firgici Maman Walida Tamiƙe Tana Furta A'uzzubillah! Laaa'ilaha ilallahu Muhammadu Rasullullah! S A W. innahu Min Sulemanu Waa....."Kai Kasa Ƙarasa Tayi Tafice da Gudu daga ɗaƙin Tana Ihun Tashiga Ukku Itama ta Haukace.

Yo Inba Hauka Ba Yaza'ayi Wanda Yamutu Yadawo harma Kaganshi? Dai-dai Ƙofa Taci Karo da Abubakar Yadawo daga Siyen Maganin da Likita Yarubuta Masu Hannunsa Riƙe da ledar da ke ɗauke da Tambarin Chamis ɗin da Yaje Siyen Magani.

Aikuwa Maman Walida tacakumeshi Tana Kuka Sosai "Auta Nima Na Haukace Nakamu da Irin Ciwon Abdul-wahab Dan ALLAH Auta Kumin Gata Karku Barnin Inshiga Duniya Har In koma tsirara Kamar yadda naga Wasu Mahaukatan Nayi Ku Taimakeni Ku Kamani Ku ɗaure A Wuri ɗaya Har'izuwa Sanda ALLAH Zaiyi Ikonsa Akaina Kaji."


Misalata Irin Tashin Hankalin da Abubakar Ke Ciki Bazai taɓa Yuwa ba Abun Kawai Sai Wanda Yagani.


Tirkashi!!! Meke Shirin Faruwa ne Masu Karatu?

Muje Zuwa Tareda Alkalamin

FA'IK.
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 26 · 0% Book details