← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 40

Chapter.....16

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


Sai Bayan Sallar Isha'i Ruwan Saman Da'akeyi Yatsagaita Lokacin Su Dady Suna Cikin ɗakina Tareda Wani Mai Phamacy da kenan Cikin Unguwar Mu Dady Yakira shi Yazo yadubani Sa'annan Yabani Magunguna Yakuma Ɗora min Ƙarin Ruwa. Daganan Yayiwa Su Dady Sai da Safe! Bayan Dady Yasallamesa Suka Bishi da Kalamin Godiya Lokacin Ni kuma Wani Bacci Mai Ƙarfi Yayi Awon Gaba dani.

Da Safe Natashi Jikina Garas! Yayimin Sauki Sosai In Ba Yunwa Ba Abinda Nakeji, Dan Haka Nahaɗa Shayi Mai Kauri Na Jawo Bready Nahaɗa Nasoma Ci Ina Karewa Kuma Momy Takawo Soyayyar Indomi Itama Natashi da Ita tas! Momy tace, "Masha'allah Sauki Yasamu Kenan dai." Nidai Murmushi Kawai Nayi.

Kafin Namike Nayo Arwallah Nayi Sallah Lokacin Karfe shidda Na Safe Bayan Nagama Saiga Dady Shima A ɗakin da carbi A hanunsa Yazauna gefen Momy yana Mai Amsa gaisuwar Danakeyi Masa Yace, "Ikram Yajikin Naki?" "Jiki Yayi Sauki Dady." Momy ta Sanya Baki Acikin Maganar Tamu da Cewa, "Aikam Yayi Sauki, dan Tunda Asubar Fari Tahau Ciye-ciye." Duk mukayi Dariya Cikin Shagwaba Nace, "Kai Momy Wane Ciye - Ciye Tea ne Kawai Sai indomi fa?"

"Oh Su ba Abinci bane? " Momy tafaɗa gamida Rike Haɓa.

Dady yagra Zama Kafin yace, "Tau Alhamdullah, ALLAH Ƙara Baki Lafiya Amm Abinda Nake So dake Ikram, idan dae dagaske Wannan Yaron yake tau Kice Masa yaturo Magabatan sa Ayi A Kare Komai. Maganar Gaskiya Nagaji da Ire-iren Abubuwan dake Faruwa. Sauka Na Jiya Garinnan Duk fitar da Zanyi Sai Nasamu Mai Magana Akanki Kowa kuma da irin Abunda Yake tarbana Dashi Wani Ya'iya faɗar Magana Wani Kuma Zaki Samu Akasin Hakan Tau Amma dai duk Nashanye Na nuna Masu Ina Godiya da Hakken Makwabtaka da Suka Sauke Ƙari ga Haka Ina can Momy Tana kira na Akan Wayyanan Matsalolin duk-dai Nakawar da Kai ne Nakyale ki.

Tau Yanzun dai Ina So Ayi ta Taƙare Bayaga Haka Motar nan da Kika Amso Bana Bukatar Sake Ganinta A gidan Nan Kodai Ki Mayarwa mai ita Ko Ku san Yanda Zakuyi da Ita. Sa'annan ina ƙara Jaddada maki Dr Jabir Yaturo Magabatan sa Indai da gaske Yake In kuwa bahaka ba Ni Zan Samarmaki Wanda Nake Ganin Yadace dake Ina Fatar Ikram Ta jini?"

Kaina A Durkushe ƙasa Ina wasa da yatsun Hannuna Nagirgiza kai Kawai Batareda Na'iya Tofa Wani Abu ba. Tau Ma ko Inada Abin Cewar, Ba Dama Dan dai Dady nagama maganarsa Yafice daga ɗakin Momy ma Ta mara masa Baya Suka Barni Nikaɗai Cikeda Tarin Tunanin Irin Wannan Rayuwar tawa.


Haryanzun Nakasa Tantance Halin danake Ciki Ko Nake ji Gameda Dr Jabir Saidai Inaji Zan Iya Zama dashi Fiye da duk Wani da Dady ke Shirin ƙakaba Mani. Saidai Natabbata Manta Abdul-wahab A Raina Shine Abu Mafi Girma da Zai Kawo wa Rayuwa ta Barazana. Naji ina ma'ace Banyi Sharholiyar da nayi ba dan tarawa Abdul-wahab Kuɗin Danake ganin Sune Gatan da zai sa Ya Aure ni? Wata kila da Dady Bai Matsa Akan Auren Nawa ba. Haka dae Na lume Cikin Tarin Tunani da Damuwa Wacce Bansan Ranar ƙarewarta gareni ba daga Wannan sai Wannan.

Karo Na Farko A Rayuwa ta Namike Nayo Arwallah Nayi Nafila kafin Naɗauki Alkur'ani na danake Zuwa Islamiyya Nasoma Karantawa Lamarinda Yasoma Saukar min da Ita wata Irin Nutsuwar Zuci.


Abdul-wahab Kuwa......


Gari Na Waye wa Yamike Yasoma Shirin Shiga Skull Innarmu tafito daga madafi Tana Kallon kai kawon sa Kafin ta Sanya baki Da Cewa "Badai Makaranta Zaka je ba?" Yana Kakkaɓe Jakkarsa Yace, "Itace Zanje Innarmu." "Aikuwa dae da Kabari Harka samu Kwarin Jikinka Komai Ai Saida Lafiya." yace, "Innarmu Jarrabawa Muke Kuma Wannan ma Itace ta ƙarshe Aikinga ko Ba Maganar Fashi Kuma ma ni Wallahi Naji Sauki."


"Tau ALLAH Ƙara bida Lafiya, sai Kazo Ga Kummalon Ka Karya Ina Shi Auta Ko Haryanzun Bai tashi daga baccin Bane?" Innarmu tafaɗa gamida Juyawa Izuwa Kitchin ɗin.


Abdul-wahab Yace, "Bai Tashi ba yana can Yana baccin ƙa'ida ni inaga bazan tsaya karin nan ba in Akwai Kunun Zanɗauka Innaje Zan Sami Bons In haɗa."


"Wannan Kuma Shine Baka Isaba dole Katsaya kacika Cikinka." Innarmu Tafaɗa Sanda Take dakata wa daga Niyyar shiga madafin da Tayi.

Ya zaiyi dole Yatsaya yacika Cikinsa Sa'annan yafice zuwa Skull ɗin Yana mata sallamar Sai Yadawo. Yana tafe Yana Zancen Zuci Kumafa Gara da Ya Tsaya ɗin Yacika Cikinsa. Koda yaje Skull ɗin da Sauran Lokacin kafin shiga hall ɗin da zasu zana Exam ɗin, dan haka sai Yasamu guri Yana ci gaba da Nazartar Handout ɗinsa.


Karfe 2 Dai-dai Suka Fito Jarrabawa Fuskokinsu Akwai Alamun Gajiya sai dai kuma Suna cike da Annuri Alamun dai Jarrabawar Tayi daɗi dan haka Da Murna Ake ta Taɓewa da Abokai Anata shewa Irin Na ɗallibai Wayar sa ce Tayi ƙara Yaɗauka Yana Mai Cewa, "Shegen Sama Kamar Kasan Kaine A Raina!" daga can Yusuf yana Murmushi Yace "Ba Wani Nan ɗan iska Nidai da na Damu Da kai Nakira ka!"


"Kai Abokina Haka Zaka ce Ma Kenan Wallahi Muna Exam ne Shiyyasa kaga naɗan daina kiranka Amma ai kasan Nafi Ka Kira ko?" Abdul-wahab Yafaɗi yana Kokarin Samun Gurin Zama dan Yaji daɗin yin Wayar.

Yayinda daga Can Shikuma Yusuf yace, "Kaga Ni ɗan Iska Katyna Bai da Yawa dama Na Kira Ingayama Insha'allah Gobe Zan Taso.... "


"Kai da gaske Nawan?"Abdul-wahab Yakatse sa da faɗin Hakan Cikeda ɗaukin Zaiga Abokinsa da Yadaɗe Basu Haɗu ba, Saboda Fatauci da yaje yi A kudancin Ƙasar Nan. Yanzun Kusan Wattani Yana Can.


Daga Can Shima Yusuf Yana Mai Gyra Zamansa Yace, "Baka Bina Bashin Rantsuwa, kadai Kawai Jibi I war Haka Kasa A ranka Muna Tare! Kasan Kuma Ina Zamu Fara Zuwa?" Abdul-wahab Yagirgiza kai Kafin Yace, "Sai Ka Fa...." Kit!! Yaji Wayar Ta Yanke Watakil Katin Yusuf ɗinne Yaƙare. Dan haka Abdul-wahab da Kuzarinsa Yamiƙe yanufi Cikin Kafteriya ɗinsu, dan Yasamu Lemu Yasha daga nan yasa Kati Cikin Wayarsa Suƙarasa Magana da Abokin Nasa da Yake jinsa Tamkar Wani Rabi Na Jikinsa Saboda shaƙuwar dake Tsakani su.

Tau Yana cikin Wannan taɗin Zuccinne saiga Kiran Na Yusuf Yasake Shigowa Yaɗaga Yana mai Murmushi Kana Sukaci Gaba da Tattaunawa Irin Tasu Ta Aminai.


********

Har yaje Sallar Isha'i Yadawo Babuta Babu Labarinta Falon Wayam! Haka Yasake Binta Har bedroom ɗinta Yana Yimata Magana Amma Shiru ba'amsa dole Haka yadawo Falon Shikaɗai Yazuba Abinci Acikin Flet yasoma Ci Amma duk sai yaji Abinci Baya yi Masa daɗi dan haka yadire plet ɗin yaɗauko Lemu Yatsiyaya Acikin Cup Yasoma Sha Shima ɗin Baiji Wani daɗinsa ba Dan Haka Kawai Sai Yamiƙe Yabaro Danin Table ɗin Cikin Rashin Kuzari da kuma Tunanin Meye Mafita?


Nan Acikin Falon Yasamu doguwar Kujera Yakwanta Kafin Yajawo remot Yakamo Tashar CNN domin Kallon Labarai Wanda A Zahiri Baya cikin Nutsuwar Fahimta Me'ake Cewa A Labaran, Kawai dai Gashinan ne Yayi wa Tv ƙuru da Ido. yaɗan Sake Musƙutawa karo Na barkatai Yana mai Jan Tsaki! Taƙamaimai yarasa Meke damunsa? Shidai Yasan Yana Son Matarsa duk-da Kuwa ba Auren Nagani Ina So Sukayi Ba, Aure ne Na Zumunci (Watau Haɗin Iyaye) Amma Ƙauna da Kyakykyawar Mu'amala dake Tsakanin sa da Maman Ashraf ko Wayanda Suka yi Auren So! Basu Kaisu ba. Kuma Wannan Son da Yakeyi Yiwa Ƴar Momy bawai Yanayi ne dan Ya Wulakanta Matarsa ba, Yanayi ne da Yana son Itama Ƴar Momy Kuma Yana ji Idan har Bata Kasance Iyalinsa ba Tau Baya da Wani Sauran Sukuni. dan haka Tsakani da ALLAH bazai Fasa Abinda Yake Niyya ba Tunda ALLAH Ma Yahallata Masa. Ire-iren Wayyanan Tunanunka Suka ci Gaba da ƙara Masa ƙaimi Wajen Son Ƴar Momy gefe ɗaya Suka Nuna Masa Ai Matsalar Maman Ashraf Mai Sauƙi ce, Zai Ci gaba da Lallashinta Har'izuwa sanda Zata Sauko daga Kishin Nata.


Dan Haka Cikeda Karsashi Yajanyo ɗayan Wayarsa Yashiga Kiran Wayarsa ɗaya Wacce Yabarwa Khaleesat, taɗaga Wayar tasa Gamida kwararo Sallama Cikin Sanyaryar Muryar ta data ƙara dulmiyar da Dr Jabir ɗin Cikin Kogin Ƙaunarta Yakuma ƙara Hakiƙancewa Inba Khaleesat ba Sai Rijiya! Sai da Yaja Fasali Kafin Ya'amsa Sallamar Tata Yace, "Tawan Ina Fatar Kin Zama Normal Yanzun?" daga can nace, "Alhamdullah Sai dai Zazzaɓi Yakoma min Sai da Ma Aka min ƙarin Ruwa!" Yace, "Ƙarin Ruwa Kuma?"

"Eh!" nafaɗi cikin girgiza kai Kamar Yana Ganina.

Yace, "Amma Wannan Rashin Lafiya tayi Tsaurin Ido dazata Kama Har Matar Likita Sukutum?"


"Tau ba Dolenta ba tacika Umurni? Wanda Ya'aiko ta Ai shi yayi matar har Likitan Kuma Yake da iko akan Masarrafin Ƙaddarar Su ka ko ga ya wuce da haka ma ko?" nayi Masa Wannan Zancen Cikin Ƙara Natsuwa da Cewa Ko bana Son Wannan Likitan Zan Iya Zama Dashi.


"Hakane Kuma Matar Likita Kinyi Gaskiya?" Yafaɗi Hakan Tareda Miƙewa Yanufi Danin Table


"Natashi Daga Ƴar Momy Na Koma Matar Likita?"

"Ke Bakiga Alamun Haka ba?"

"Taya ya?" Nafaɗi Hakan Cikin Shauƙi


"Ta Yadda Yanzun Bani da Wani Buri Sai Mallakar Ƴar Momy tazamo Matata Kuma Inace Tuni Na Nemi Wannan Alfamar Gurin ƴar Momy Tace ta'amince hakane?" Wannan Karon Nakasa Amsa masa Sai Kawai Na girgiza Kaina a Wautata Zai gane. Sai da Naji daga can Yace, "Yadai Kika yi Shiru?" Nasauke Ajiyar Zuciya Kafin Nace Masa "Hakane!" Yace "Tau Yanzun Alfamar ɗaya Nake Nema A gurin ki Kimin Izini Turo Magabata na Dan A tabbatar Min Cewa Yar Momy Tazama Matar Likita!"

Naɗan gyara Kishingiɗata Ina ƙara maƙala Wayar a Kunne na dan Ba Shakka kai kana gani na kasan Wayar Nayimin daɗi Nace, "da Wuri Haka?"

Yajanyo Ƙaton Flask ɗinda ke Girke A Saman Danin Table ɗin Cikeda Ruwan Lipton. Yatsiyaya Acikin Cup Sannan Yajawo kwalin Shuga Yaɗibi Masu ɗan Yawa Yajefa Acikin Ruwan Lipton ɗin Kafin Yasanya ɗan Ƙaramin Cokali yana Juyawa.

Cikin Tunanin Ko Wayar ta tsinke ne? Najanye wayar daga Kunne na Naduba naga still yana kan Layi tau Meye ya...


"Ke bakiji Ance da Safe-Safe Ake Zuwa kamun Fara ba?" Yakatse Tunanin nawa cikin Fadar Hakan.

"Haka Naji Ana Faɗi."

"Tau dan haka Kawai Kimin Wannan Izinin." yafaɗi hakan yana mai Juyowa da Nufin dawowa Falo, Gefe ɗaya yana mai Kurɓar Ruwan Lipton ɗinsa

"Zamma Magana Insha'allah!" Nafadi Hakan Cikin Sanyin Murya.

"Zuwa Yaushe kenan?"

"Zuwa Sanda Nayiwa Su Momy Maganar."


"Tau Shikenan Ƴar Momy."

Naɗan Zaro Ido "ba Matar Likita ba?"

Yakama Baki, "Au? Kumafa Hakane."

Wayar dae da Muke tayi Itace Takwashe Kaso Mafi Yawa daga Cikin Damuwar da muke Ciki Yayinda Zukata mu Suka Samu Nutsuwar Cewar Lalle Muna Bukatar Rayuwa tare da Juna.

Dan Haka ta ɓangaren Dr Jabir Yakeji Zai Iya Jure Fuskantar Kowa ne Irin Kalubale ne dan Ganin Ya mallaki Khaleesat.


Yayinda Tawa Zuciyar Ki Ci gaba da Sanar dani Lalle Nan Duniya Bani da Wani Wanda Zai Cikemin Gurbin Abdul-wahab Sama da Dr Jabir Dan Haka Naji Na Amince Zan Rayu da Shi Muddin Rai!
Da Wayyanan tunanunka Mukwa Kashwe Lokaci mai Tsawo Muna Waya kafin Mukayi Sallama.

Kowanenmu kuma yakwanta Cikeda Saƙar Zuci da Tunanin Makomar Rayuwar Sa! Inda Ni Nake Ganin Cewa Babu Shakka! Dr Jabir Ya'isa Kuma Zan Mallaka Mashi Zuciyata Kuma Ai Dama A Rayuwa bai Zama Dole duk Abinda Kake So Kasamu ba! dan Haka Nabarwa Raina Cewa Abdul Kawai Ba Rabo Na Bane.

Yayinda Shima Dr Jabir ta ɓangaren sa Yakeji Cewa Yazama Wajibi ne Gareshi Auren Khaleesat bcause Itace Farincikinsa dan haka Yafi Maida Hankali ga Tunanin Tayaya Zai Haɗa Kan Matan Nasa Su Zauna Lafiya? Yana kuma Ayyana cewa Yazama Dole gareshi Wannan Satin Yaje Gida Dan Yagana da Su Ummarsa Kan Wannan Maganar. Saidai Wani ɓangaren Zuciyarsa Na Sanar dashi Anya Iyayensa Zasu Karɓi Auren sa da Khaleesat Kuwa? Musamman Mahaifiyarsa da yake Ganin duniya Ba wacce take so Sama da Maman Ashraf? Baya Tunanin Mahaifinsu Saboda Yasan Shiɗin Baya da Wata Matsalar Tunda Yasan Sunnar Ma'aiki S A W zai Raya.


Tau dai Haka Suka Kwana Cike da Tunani Mafitar Da kowane Yake Ganin Zata fisshe Shi.


Rashin Kwanciyar shi Da Wuri Yasa Yayi Jinkirin Tashi dan Ko da Yafarka Massalaci Unguwar tasu Suna Sallame Sallah, dan Haka A gagauce Yayi Arwallah Ba tareda yayi Wanka Kamar Yadda yasaba Ba Yanufi Massalaci Bayan Sallah Kuma Yashiga Yin Lazimi Yadan Jima Yana Lazimin Kafin Yadawo Cikin Gida, Kaitsaye Kitchin Yanufa Inda Yake Kyautata Zaton Zai Sametan. Illai Ko Yahangeta Tsaye A Tsakiyar Kitchin ɗin, Sai Aikin ɗorawa da Sauke wa Takeyi. Fuskar Nan Tata Fara fes! Sai Annuri Take kamar Ba Wani Abinda Ke damunta Sai dai Idanunta da Suka Kumbura Sukayi
Luhu-Luhu Tabbacin Tasha Kuka Harta Ƙoshi, Tajuya Masa Baya Dankalin turawa ne A hannunta Tana Ferewa.

Sannu A Hankali Yalallaɓo Da Nufin Yariƙota ta Baya, Kamar Yadda Yasaba Yi Mata, Amma Sai tai Maza ta Koma Gefe Tana Kallonsa da Idanunta dake Wadace da ɓacin Ransa. Baƙar Magana taso Yaɓasa Masa Amma Suna Ido Biyu Sai kwarjinin Sa Yasa Takasa! Tabar Abinda Zata Faɗa Yabi Iska Taci Gaba da Motsa Laɓɓanta Kawai.

Yafahimci Hakan dan haka Sai Yayi Murmushi yaƙarasa Inda Take da Murmushin A Fuskarsa Yana Cewa "Yana ga Idanunki Jawur Haka NURUL KHALBI?"


"Fetur Aka Watsa musu Ko Zaka Kyasta Ashana ne su Kama da Wuta?" Tafaɗi Hakan Cikin Ƙufula

Yamiƙa Hannu Zai Riƙota Taƙara Janye Jikin ta Tare da Cewa "Wai Meye Haka ne?"

"Ah! Mutum da Matar shi?" Yatambaya Cikin Mamaki

Kawai Sai Tafita Harkarsa Taci gaba da Abinda Takeyi tana jin Cewa duk Yasa ke Wani Yunƙurin Taɓata Kawai Yuƙar Zata Caka Masa! Kowa ma Yahuta. Dan A Yanda Zuciyarta Yanzun Ke Makance Da Kishi Tana ji Komai Zai Iya Faruwa!..........

Muje Zuwa Readers Tareda Alkalamin

FA'IK.... ✍🏻
[9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 14 · 0% Book details