← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 40

Chapter.....5

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

SADAUKARWA.

Wannan Pages Din Na Kyautar Ga Wayyanan Bayin ALLAH Wayanda Sune Kwarin Gwaiwa ta Ina Godiya Irin Trillions Dinnan 😅😅
ABUBAKAR AK SARAKI da Kuma
UMMU SADIQ Tareda Mr BABONI.
Sai Kuma HAJARU.(Yar Uwa)


A.......
Maimaikon Pages 123, Zankoma Da Yin Amfani Da Chapter.👌


Mallakar 👇

Fa'IK ✍️


Typing.....💻


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. 07039676994

Bissmillahi Rahmanin Raheem

Bandade ba, Nadawo Dauke Da Faranti Wanda Aka Jera Gorar Ruwa Da Kuma Bigi Fanta Sai Flet Da Aka Rufe Da Dan Uwansa Flet Soyayyen Dankali Ne Da aka Nannade Da Masar Kwai (wainar kwai) Na'aje Ina Cewa, "Gashi Ku karba Da Hakuri Yau Kasan Ana Fama Da Hidimar Sallah Bamuyi Abin Budin Baki ba Yau Ko Shago Momy Bata Fita ba." Nadago Ina Kallon Abdul-wahab Ashe Nidae Ke Magana Ta, Abdul-wahab Ya Manta A Ina Yake Ya Shagala Da Kallona Nai Azamar Rufe Fuskata Da tafukan Hannayena Zara-Zara Da Suke Zagaye Da Bakin Lalle Ina Murmushi Kafin Nace, "Kallonfa Ya'isa Haka." Yasauke Ajiyar Zuciya Yadora Da Cewa, "Tuba Nake Tawan Kece Duk Kika Tafi Dani Har Nakasa Control din Kaina. Anya Tawan Bazamu Gaggauta Gabatar da Kammu Gurin Dady Abani ke Ba?"


Nashiga Bude Masa Lemon Fantar Dana Kawo Kafin Namika Masa Ina Cewa, "Kaga Fara Sha Takwan Mayi Magana Inka Gama." Yakarba Ya kurba Sannan Ya kalleni Yana Cewa, "Yakamata Naji Amsarki Akan Wannan Maganar Fa?"
"Ina Zuwa."
Mikewa Nayi Daga Kan Dakalin Da Muke Zaune Ina Mai Daukar Gorar Cok Nanufi Inda Yusuf Ke Zaune, Namika Masa Nace, "Gashi Inafatar Baxaka Ki Karba ba?" Yayi Dariya Yana Amsawa Yace, "Wa? Ni Na'isa? Ai da Habibinki Yarufe ni." Mukayi Dariya Najuya Ina Cewa "Kaidai Oga Yusuf Baka Rabo Da Abin Dariya."

Yace, "Tau Ki Tambayeshi Kiji Mana."

Wajajen Karfe 2 Nadare Harma Da Wasu Yan Mintoti Suka Dawo Gida Sungaji Tibis! Dole Dai Yusuf Ya Kwana Gidansu Abdul-wahab Din Dan Dare Yaja, Dan Haka Sai Suka Bada Ajiyar Napep Din Yusuf Gurin Gidan Makwabta Dake Da yalwataccen Guri. Kafin Suka Shigo Cikin Gida Suna Ta Layi Itakam Innarmu Haryanzun Idonta Biyu Tana Bakin Kofar Dakinta Tajawo Soket Nan Bakin Kofar Dakinta Ta jona Fankarta Tana Daura Lallen Da Bata Samu Daurawa Da Rana Ba. Takallesu Sanda Suke Zama Kan Baranda Kofar Dakin Tana Cewa, "Sai Yanzun Kuka Dawo? Har Ina mitar Kun Tafi Kun Barni Nikadai A Gida Ga Wayata Ba Katy Balle Nakira ka." Abdul-wahab Yamike Yabude Frij Yana Jawo Kunun Ayar Da Innarmu Ke Saidawa Yamikawa Yusuf Gora Daya Kafin Shima Yabude Daya Yasoma Sha Sa'anan Yadubi Innarmu Yana Cewa, "Ina Autanki?" (Watau Abubakar Dan Shima Wani Lkcin in Yana Nishadi Yakan kirasa Da Haka). "Autana Yace Yau Can Zai Kwana Yace, So Yake Ya'ida Duk Dunkunan Mutane Dake Hannunsa."


"Yana Da Kyau." Abdul-wahab Yafadi Hakan Yana Mai Yar Mika da Hamma Alamun Gajiya.

Innarmu Ta dubeshi "Kai Kam Kacika Ragwantaka Wallahi, Yar Wannan Fitar Ce Duk Kake wa Raki Haka?" "Kema dai Ki Fadi Innarmu Bayan Kafin Mufita Kamar Zaiyi Tsuntsuwa." Yusuf Ne me Wannan Maganar. Innarmu Tace, "Taya Ni Gani Makaho Yaso Gulma." Abdul-wahab Yahararesa Kafin Yanufi Hanyar Dakinsu Yana Cewa, "Kai Mal Ni Ban iya Abinda Ka iyya ba. Innarmu Ni Zan kwanta Saboda Karna Makara Zuwa Sallar Idi." "Amma Yakamata Ku zuba Abinci Kuci Ko?"
" Nakoshi Nikam, Saidai In Yusuf Ne Zaici."

"A'a Wallah Nima Ba Guri, Wannan Ciye- Ciye-Da Mukayi Yau Ai ALLAH dae Yatsare Mu da Gurbacewar Ciki."
Innarmu Tayi Dariya Tana Cewa, "Tau ALLAH ya Takai ta."

Nan Dae Yabar Yusuf Da Innarmu Suna Firah Kan Yashiga Dakinsu Ya Tube Kayan Jikin Sa Ya Zura Jallabiya Mai Ruwan Zuma Yafito Waje Yadibi Ruwa Yafada Toilet Ya Watso. Kan Katifar sa Yazube Bayan Yafito Daga Wankan Kenan, Cike Da Gajiya Wacce Bawai Ta Tafiya Bace Ko Aiki A'a Wannan Kawai Ta Shaukin So ce Dake Nukurkusar Duk Wata Gaba Da Take Mallakinsa Ne. Ahankali Yalumshe Idanuwansa Kafin Yasake Budesu Yana Tsurawa Fankar Dakinsu Dake Ta Kai kawo Ido Domin Bawa Dakin Nasu Iska A Ransa Yakeji Cewa, Anya Bai Wuce Makadi Da Rawa ba Akan Son Khaleesat Ba? Wacce Baya da Tabbacin Ma Iyayen ta Zasu Bashi Aurenta In Sun Bashi Ma da Wane KWANJIN Zai Aureta? Suda Basu Da kowa Bayan ALLAH da Innarmu Da Yan Sana'o'i Hannun Da Sukeyi Wayyanda Suke Rufa Masu Asiri, A Ture Wannan ma Karatunsa Fa Wanda Yake Bukatar Kudi Da Lokacinsa Karatunda Yakula Matuka! Innarmu Tabashi Muhimmanci Da ko Shi Da yake yinsa Bai Bashi ba, Idan Akazo Abincinsu Yakare Ga Kuma Lalurar Karatunsa Innarmu Takance, "A Hakura Da Siyen Abincin Yaje Yayi Sabgar Karatun sa, Abincin Kuwa ALLAH Zai Rufa Asiri." Babu Shakka Yakwaso Jan Aiki Ma Kansa Wanda Bai Ma San Ta Inda Zai Fara Bullo Masa ba. Gashi Inka Cire Aminin Nasa Yusuf Ba Wanda Yagayawa Maganar, Tau Dae ire-iren Wayyanan Tunanen, Sune Suka Dami Zuciyar Abdul-wahab Suka Kara Saukar Masa Da Wata Irin Gajiya Harma Da kasala Bacci kuwa da Yace Zaiyi Ko kadan Bai Ziyarceshi Ba. Har Sanda Yaji Yusuf Da Innarmu Suna Sai Da safe. Dan Haka Dole Yatirsasawa Kansa Baccin Karya Hardasu Minshari. Dan Baya Son Surutu Kawai Yafi Son Yayi ta Tunaninka. Yusuf Dae Da Baisan Wainar Da Ake To Yawa ba Sai Yabawa Ransa Cewa Da gasken Abdul Din Bacci Yake Dan Haka Shima Yabi Lafiyar Katifa Ya kwanta.


***************

Basuyi Wani Bacci Ba ma Aka Soma Kiraye-kirayen Assalatu Dan Haka Dole Suka Tashi Sauke Farali Suna Dawowa Daga Massalaci Yusuf Yawuce Dan Baizo Da Dinkin Sallah Ba Dole Yasamu Ya'isa Gida Dawuri Ya Shirya.

Tunda Suka Dawo da Sallar Idi Suka Ci Abinci Shida Abubakar Suka kule Daki Sai Bacci, (Dama Shi Kunsan Ba'acin Bashinsa)
Suka bar Innarmu Da Diyan Makwabta Masu Shigowa Yawon Sallah Sai Budiri Sukeyi. Dan Sun Samu Sakewa Gurin Innarmu Adalilin Itadin Mai Saukin Kai ce Kuma Ga Son Yara Dan Haka Sai Suke ta Shishshigowa Gurin Innarmu Gida Kuwa Yakacame.
Abubakar da Abdul-wahab Basu Farka ba Sai La'asar Shima Bawai Dan Ya'ishesu ba Sai Dan Innarmu Da ta matsa Musu Su Tashin Saboda Suyi Sallah Ga Kuma La'asar Da Tayi.


A BANGAREN KHALEESAT FA?🙄

Shin Wacece Khaleesat ma Dae?

Nana KHADIJAT Shine Asalin Sunanta Iyayenta Auren So Sukayi, Dan Babanta Bafulatanin Adamawa ne Yayinda Mamarta Take Yaren 'Ibra' Yar Asalin Garin Kogi, Sunan Mahaifin ta Mustapha Mahaifiyar ta kuwa Sunanta 'Yawo.
Haduwar Yawo da Mustapha Ya Samo Asali Ne Sanda Aka Turashi Aiki Can Kasancewar Shidin 'Mopol' ne, Sun Hadu Da Yawo Gurin Da Take Sai Da Abincinta Wanda Suka Kamu Da Zazzafar Kauna Akan Juna Ansha Gwargwarmaya Kafin Auren Su Kasancewarsu Ba 'KABILA' Daya ba, Sai Dai Jajirce wasu Ta shanye Komai Dole Aka Barsu Sukai Aure Bayan Da Shi Mustapha Sai Da Akayi Masa Auren Zumunci Da Yar Uwarsa Take Kuma Zaune Can Adamawa Garinsu Kenan.

Zaman Su A Sakkwato Ya Samo Asali Ne Sanda Aka Dawo Dashi Aiki Nan, Sai Garin Yay Musu Dadi Mussamman Yawo Data Fara Sana'ar ta Ta Saida Kunu da kosai Dasu Dankali Harma Dasu Doya da Plantain Wani Lokacin har Kunun Zaki Takanyi Tasa A kula Kuma ALLAH yasama Abin Albarka Dan Duk Kazo Gurin Zaka Iske Cincirindon Yan Kabu-kabu(Yan Acaba) da Kuma Yan Kk Napep Da Sauran Tsirarun Mutane. Nuradden Shine Dansu Na Farko Yana Aiki A Legos Shi ma Aikin Kaki Yake Sai Kuma Nana KHADIJAT Wacce Kowanensu Ke Kiran ta Da Sunan Da Yayi Masa Dadi.

Dadynta Nace Mata Ikram Momy Kuwa Takance Mata Khaleesat Tau Khaleesat Dae Shine yafi Samun Karbuwa Tunda Kunsan Dama Uwa Tafi Kusanci Da Diyanta. Khaleesat Tana Zuwa Skull Both Boko An Isalamiyyah Kuma dae Rayuwar Gidansu Akwai Yanci Dan Ba'a Cika Tsarara Musu ba. Rayuwar Dadynta Baya Zama Guri Dae Yau Yana Wannan gari Gobe Wancan Jibi Yana Daya Daga Garin Matan Sa In Yazo wa Wannan A Wannan A Wanin Karon Yazo Wa Wannan (Yanayin Hakanne In Yasamu Sarari Agurin Aiki Nasu) Haka Rayuwarsa Take Tafiya.


Wannan Kenan 🤗

Kamar Yadda Kuka Sani Yaudin Ce Sallah Harma Yammaci Yayi, Kowa Ka Gani Ya kule A daka Ba Sauki😜
Gidanmu Ba kajin Kunne Saboda Hayaniya Da Yacika Gidan Namu, Mundade Ba'ayi Irin Wannan Haduwar ba Agidamu Watau Ga Babamu Ga Kuma Yaya Nuradden Duk Sundawo Gida, A Wannan Karon Ya Nuradden, Harda Iyalinsa Yazo Dasu wacce Tazamo yaren momy ce dan Haka tasu dazo daya da momy. Ga Kuma Kawayena Na Skull Da Suka Zomin Tayani Tarbar Daddy Da Kuma Ya Nuradden Munkule Dasu A dakina Da Yake Mallakina bakajin Komai Sai Sowa da Tafi. Abinci Kuwa Munyi Girki Yakai Kala Ukku Ga katan din Drinks da Ya Nuradden Suka Siyo Shida Daddy.

Daddy Yakirani Dan Haka Nafito da Hanzarina Ina Amsawa Nashiga Falon Shida Momy Suna Zaune Abinci Yagama Ci Yace, "kwashe Kayan Nan ki Kawo min Ruwa in Wanke Hannuna." Bayan Nakwashe Na kawo Masa Ruwan Cikin Roba Yana Wanke Hannu Yace, "Ikram Cikin Daki Ki Duba Jikkar Da Nazo Da Ita ki Duba Wayarki Na Nan Nasiyo Ma....." Ai Kafin Yagama Magana Nakai Kuryar Daki Da Zumudi Na Ina Ihun Murna Shida Momy Me Zasuyi In Ba Dariya Ba Nadawo Dauke Da Waya Sabuwa Dal! Cikin kwalinta Kirar Samsung Da Murna ta Nake Cewa, " Wow! Dadymu I love you, Thank you! Nagode Nagode Daddy...." Cikin Haka Ya Nuradden Yashigo Falon Yana Murmushi Yace, "Diyar Dadynta Me Akayi?" Cikin Zumudi Na Nuna Masa Wayar Hannuna Ina koro Masa Jawabin Dady Yasiyomin. Yanemi Guri Ya Zauna Yana Cewa, "A 'a Lalle Yar Daddy An gwangwajeki." Na Fallah Da Gudu Ina Cewa "Bari Naje Na Nunawa Su Halimo Nima Nafaso Gari...."


"Kinga." Ya Nuradden Yakirani Natsaya Jikina Na Tsuma Yashiga Laluben Aljuhunsa Yana Cewa, 'Bari Nayi Dobling Din Wannan Murnar ko." Yamiko min Yan Dari Biyu Sabbi Har Guda Biyar Yana Cewa, "Kya Sayi Katy, Yanzu Ba Kudi, Cash! Wahla Yake." Narungumesa Cikin Farinciki Sosai Gamida Cewa, "Wannan Ma Is Okay Yaya ALLAH yabarmin Ku Kaida Dady, ALLAH Ya....." Momy Ta Rarumo Fillo Kujerar Datake Zaune Tajefe Ni Dashi, "Mukuma Karya Barmu Ba Tunda Ba....." Nayi Saurin Isa Gareta Nace, "No no! Momy Harda ke Mana." Kafin Na Juya Da Hanzarina Dan Nuna Wa Kawayena Abin Arzikin Da Yasameni.

Acan Ma Dakin Nawa Murnar ce Dae, Kowacensu Da Irin Abinda Take Cewa. Na kunna Wayar Na sa Abata Caji Cike Da Zumudin In Tayi Caji Zankira Habibina (Abdul-wahab) Kawayena Muna Tare Sai Da Yamma Lis Rana Ta Tafi Zata Fadi Sannan Kowace Su Ta Soma Rarumar Jakarta Da Mayafi Kan Zasu Gida Na Rakesu Dakin Momy Sukayi Musu Sallama Inda Dady Yabani Dubu Dai Da Dari Biyar(1500) Kan Cewa Suyi Hakuri Dasu Ba Cash! Har Ina Karasa Masa Kalmar, Dan Ba Cash Yazama Jiki Yanzun Mukaje Dakin Da Ya Nuradden Ya sauka Shida Matarsa Nan Ma Sun Samu Dari Biyar (500) Sai Godiya Suke Tayi.

Har Bakin Titi Mukaje Sai Da Suka Shiga Kk Napep Sannan Na juyo Zuwa Gida Lokacin Wasu Masaalatan An Fara Kiran Sallar Magariba.

Dan Haka Ina Shiga Buta Kawai Nazara Nafada Toilet Nakama Ruwa Nafito Nayi Arwallah Nashiga Dakin Domin Yin Sallah Bayan Na ida Ina Sunce Hijabi Wayata Kawai Na Nufa Naje Falon Momy Nadauko Wayarta Na kwafe Number Abdul-wahab Sai Dai Wayar tawa Ashe Ba Katy Dole Dai Da Ta Mommy Nakirasa

Dai-Dai Lokacin Sunfito Masallaci Daga Sallar Magrib Yadaga Fuskarsa Cike Da wal-wala, "Babyna Barka Da Sallah!" Duk Mukayi Dariya Nace, "Dan Karna Rigaka Cewa Kabani Goron Sallah ko? Tau Sha Kuruminka Ni Yau Hajiya ce."


"Eyyeeee Hajiya Khaleesat Nikam ko Zanzo A Sammani ne Dan Yau Haka na Wuni Yammata Duk Sunkarbe min Kudi Da Sunan Abasu Goron Sallah.."

Nai Saurin Bata Fuska Kamar Yana Ganina Kafin Nace, "Yan Mata Kuma?" Yayi Hanzarin Cewa, "Au Sorry Yan Matan Fa Duk kwaila ne, Ko A Kwai Manya Ai ba Wadda Ta Isa ta Kama kafarki baby Na." Na Zunburi Baki Cikin Muryar Shagwaba Kamar Ina A Gaban sa, "Naji din Sai dai Duka Bana so, Dan ALLAH Habibi Na Kabar Kula kowace In Har Baka Son Nadinga Ma Kuka." Cikin Danne Dariyar Da Tazo Masa Yace, "Nabari Dama Ni Can Fa Zolayarki Nake Babyna."


Nayi Shiru Kawai Ina Maida Numfashi Daga Can Da Yaji Ba Amsa Yace, "Hello! Are we Together My Baby?" Nace, "No!" Cikin Wani Irin Salo Mai Tafiyar Da Hankali Yace, "Ohhhhhh My Baby Nace Fa Zolayarki Nake Sorry Kinji?"

Nace, "Tau Yayi Nahuce, Amma Karka Kara Kuma bana Son Kana kula Wasu Yan Mata manya ko kanana Kaji ko?" Yacemin, "Naji Zan Kula Baby."

"Yawwa! Kai Nawa ne Nikadai Nima Kuma Takace Kai Kadai Zamu Rayu Tareda Juna Har Aljannah."

Yayi Saurin Cewa, "Ina Fatar Hakan my baby." Kafin Dukamu Mukayi Shiru Sai Numfashi Mu Da Ke Tai Kai kawo Kowa Kuwa Da Irin Shaukin So Da Yakeji. Daga can Yasake Cewa, "Hello." Na'am Sa, "Uhummm"

"Ilove you" Yafadi Hakan Cikin Wata Irin Cool Voice Dinsa Mai kamar Yanzun Yatashi Daga Bacci Sai Da Naji Duk Tsikar Jikina Ta Tashi.

Nace "Me Too 😘" Kafin Nai Hanzarin Kashe Wayar Cikin Kunya Ina Rufe Fuskata Da Filo Jinake Kamar Ina Gabansa Wallahi Sai Wani Haki Nake.

Daga Can Shima Jin Takashe Wayar Sai Kawai Yayi Murmushi Kafin Yarubuta Sako Ya'aika Mata. Sannan Yakama Hanyar Gida Gaba Dae Ya Manta Da Abubakar Da Suka Fito Massalaci Sai Da Yaji Abubakar Din Yadauko Sauri Yana Cewa, "Ya Abdul Jirani Mana." Yayi Saurin Tirjewa Yana Susar Kai Gaba Dai Kunya Takamashi Na Yadda Yamanta Da Abubakar.

Abubakar Yamatso Gurinsa Yana Cewa, "Yaya You are In love Ba?" Abdul-wahab Yahararesa Yana Fuskewa Waishi Nan Gashinan Yaya, "Yaronan Kafa Raina Ni Da Yawa Wannan Wane Irin Batune?" Abubakar Yakama Hanyar Gida Yana Cewa, "ALLAH baka Hakuri Yaya." Kome Abdul-wahab Din Yatuna Yayi Saurin Jawo Kanin Nasa Yana Cewa, "Seriously Ina Cikin Wata Irin Zazzafar Soyyayar da bansan Yaushe Tashige ni ba A Yanzun Bani Da Wani Buri Kanina Face Nakasance Da Wannan Masoyiya Tawa A Inuwa Daya Matsayin Ma'aurata."
Abubakar Yakallesa Sosai Yana Kara Tabbarda Cewa Lalle Ya Abdul Yayi Nisa Kamar Yadda Yafada Kafin Yace, "Maganar Gaskiya Yaya Da kasharwarceni Da Baka Yi Wasa Da Rayuwar ka Irin Haka ba? Inaga kamar ka Manta Waye Mu Da Kuma Irin Karatun Da kake Wanda Yake Bukatar Nutsuwar ka, Da Kuma Irin Burin Da Innarmu Taciwa Karatun ka A Ture Wannan Ma Yanzu Idan Ka tattago Maganar Aure Ina Zaka Sa Matar ka? Yaya Ni Ina ga Ba Wannan Yafara Kamarta mu ba, Mufara Gina Rayuwarmu Mu Samu Madogara Mai Kyau Da Muhalli Kafin Mu Nemi Matar Da...." Cikin Facin Rai Abdul-wahab Yadaga Masa Hannu "Meyesa Zaka Ta Kashimin Kwarin Gwaiwa, Duk Kalamanka Auta Basa da Dadin Saurare Why?"


"Saboda Sudin Gaskiya Ce Gaskiya Kuwa Kasan Daci Gareta Saboda Sudin Sun Sabawa Bukatar ka Dan Haka Banga Yanda Zasu ma Dadi ba. Sai Dai Ni Ina Tunatar Da Kai Waye mune Da Abin da Yafi Kamantar mu Sa'anan Kasan Duk Duniya Nafi Kowa Sonka Da Duk Wani Abu Da Yadangaci Ci Gabanka Harma da Farinciki Ka." Abubakar Nagama Fadar Haka Yawuce Yabarshi Nan Tsaye Cike da Tunanunka Lalle Inzai Kauda Sonkai Yabar Gaskiya Tayi Aikin ta Tau Abinda Abubakar Yafada Masa Shine Yakama ceshi Tau Amma Zai Iya Barin Khaleesat? Zai iya Rayuwar da Ba Khaleesat Acikinta?

"Kai! Never." Yafurta Haka Da karfi A Kuma fili Wanda Hakan ya Tilas tawa Wasu Kallato Sa Cikin Mamakin Sa. Ganin Haka yasa yasoke Kansa Yanufi Gida.


KHALEESAT Fa?


Ina Cikin Wannan Haline Naji Wayar Momy Tayi Kara Alamar Anturo Sako Dan Haka A Kasalance Na janyo Wayar Izuwa Fuskata Da Tunanin Yan Gidan Layine Suka Yo Sakon Sai Naga Sunan Habibina Ranga Dau! Dan Haka Da Zumudi Nabude Sakon Nasoma Karantawa Kamar Haka!


Hummm Babyna Kunya ko? Ni Duk Kin Hanamun In Tambayeki Daddy Ya Suka Iso Da Ya Nuradden? In Dae Na Samu Sarari Zamu Bullo Gayarda Da Dadymu. Miss U my babyyyyyy. Naki Wahab."


Wani Irin Sanyin So Ne ke Shigata Wanda Yatilasta Min Rumgume Wayar Kamar Itace Masoyin Nawa.
Ina Cikin Laulayin So Ne Naji Momy Nakira Na. Dan Haka Dole Na wartsake Nafito Tsakar Gida Ina Cewa "Gani."

Ta nuna Min Kulolin Mutane Da Suka Kawo Abincin Sallah Yakamata Ki Duba Kulolin Nan Asan Da Tawaye Da Tawaye Ce Sa'anan Afitar Da Abincin Da ke Ciki Aba Mabukata Dan Kar Yalalace Sai A Wanke Su A Mayar. Har Tawuce Sa'anan Ta Dawo "Yawwa Kiyiwa Auntynku Magana Ta Kama Miki."

" To" Kawae Nafada .


Kafin Na Nufi Dakin Da Matar Ya Nuradden Suka Sauka, Na'isko Ta Tana Kokarin Sakawa Danta Muyyidim Famfas Tadago Kai Tana Kallo na A Sanda Nashigo, Ashe Tanajimu Da Momy Tace, "Zo Ki Karasa Shirya Danki Bari Inje Iniyi Aikin Ai Kekam Kingaji." Murmushi Kawai Nayi Ina Cewa, "A'a Aunty Baza'a yi Hakaba, Ai kunfi Gajiya Kuda Kuka Debo Hanya Daga Legos." Murmushi Kawai Tayi Tafita.

Nufin Dae Bata Bukatar Muyi Ta Jayayya Dan Haka Dole Dae Yanda Tace Din Akayi. Bayan Nagama Shirya Muyyidim Din Nasa Hijabi Nafita Shago Siyen Katy Saboda Kiran Habibi Na. Ina Fitowa Kuma Sai Ga kosassar Mota Na Dalle Ni Da Haske Daga Baya Kuma Sai Wanda Ke Cikinta Ya Soma Jera Horn.........


Anan Zan Nunfasa Sai Muje Chapter Ta Gaba Muje Wace Irin Chapter Za'ayi.
[9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typin...... 💻


💞 SONEEE....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 3 · 0% Book details