← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 30 OF 40

Chapter.....32

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem!!!


Abun Sai Wanda Yagani Ji Yakeyi Kamar yalula Sama Yayi ta Yawo Cikin Gajimare Saboda Tsananin Farinciki da Yake Cikinsa.

Yau ga Khaleesat ɗinsa Cikin Gidansu Tana Ta Kai Kawo ji yake Ina Ma'ace Da Igiyoyinsa Ukku Akanta? Duk Inda Tayi Yana biye da ita da Murmushin da Yakasa Ɓoyuwa A Fuskar sa. Ita kanta Khaleesat tana cikin Wannan Yanayin Saidai Ita kam Kunyar da Aka San Kowace ɗiya mace Ƴar Mutumci Takan Yima ta Burki Akan Komai.

Yayinda Su Innarmu Suka Ƙara Tabbatarwa Cewa Khaleesat da Abdul-wahab Haɗin ALLAH ne Shiga Tsakaninsu Kuwa Nufi ne Na Ba'a Son ɗaya daga Cikin su Yarayu. Hakanan Aɗan Zaman da Sukayi da Ita ALLAH yasaka Masu Wani Irin Sonta Acikin Zuciyoyinsu Sbda Kunyarta, Ladabinta, Son Addinta, ga Kuma Yawan Fara'a da Faran-faran da Mutane.

Itakanta Innarmu Jitake A wannan Karon Sai Inda Ƙarfinsu Yakare Wajen Nemawa Abdul-wahab Auren ta. Ruwa da Iska Ba'abinda Zai Rabasu da Khaleesat ɗin Tunda Sun Fahimci Muddin Suna Son Kwanciyar Hankali Abdull ɗin tau Abarsa da Abar Ƙauanarsa.


Bayan Kamallah Ayyukan Nasu ne Kuma Khaleesat ɗin Tacika Ruwa da Boket Taje Ta Wanke Bayin Nasu Tas! Kafin Kuma taɗebi Wasun Taje Tayi Wanka. Bayan tafito kuma Tayi Yan Shafe-Shafen ta da Yake Ita Ba Mai Son Kwalliyyah Bace Itadai Barta da Shafe-shafen Mayuka Masu Ƙamshi da Kuma Turarrukan Humra. Hakanan da Ka Kalli Khaleesat Kasan Tana Cikin Sahun Matanan da Suka Kasance Masu Natural Kyau Koda Kwalliya ko Babu. Fararen idanunta da ɗan Siririn Hancinta Kaɗai Ma Abin Kallo ne Balle Kuma Aka Zo Kan Fuskarta Fara Tas! Wacce Babu Kwarzane Ko Kaɗan A Kanta, Hakanan Kamar ka Latsa Jini Yafito Sbd Taushin Fatar Fuskarta da Kyaunta.

Bayan gama Shafe-shafen doguwar Riga Tasaka Wayanda Tun Bayan Barinta gida Bata da Kayan Sawa Sai Su.

Dan Sune Likita Mai ƁOYAYYEN Suna Yashiga butiuqe yakwaso Mata da Hijabai Harƙasa. Kowace Kuma Riga da Hijabinta Kalarsu Kuma ɗaya ga Kuma Tsanani Laushi da Yadin Keda Shi.

Bayan Ta Kimtsa Jikinta ne Tana Maida Kayan Cikin Yar Madai-daiciyar Akwatinta da duk Cikin Sayayyar Likita Mai ƁOYAYYEN Suna ne. Abdul-wahab Yafaɗo ɗakin Shima Cikin Shigar Jallabiya Kalar Ruwan Zuma Yaɗora Fullar Taɓanni Kasha Hadisi Inji Sakkwatawa😂(Ƴar Pakistan) sai Kamshi Yake baɗawa (Kamar Bashine Wanda Yayi Jinyar HAUKA BA.😜) Yamiƙo mata Rigar Sanyi Yana Cewa, "Kiɗora da Wannan Kinga Yau Akwai Sanyi Garin." Kallonsa Tayi da ɗan Murmushi nan da Ko Yaushe Baya Rabo da Fuskarta Koda Kuwa Tana Cikin Ɓacin Rai Ne. Ta'amshi Rigar Tana Ƙokarin Sakawa Tace, "Nagode!" Abdul-wahab Yajuya Yana Cewa, "Kedai Bakya Gajiya da Godiya Komai Ƙanƙantar Abu? Naje Massallaci Naji Suna Ƙokarin Tayarwa."

"Adawo Lafiya." Abunda tafaɗa kenan Agajarece. Kafin Itama ta Shimfiɗa Sallaya Tasoma Tata Sallar. Bayan Ta Idar Kuma Tasamu Su Innarmu Tsakar gida Suma Sun Idar da Tasu Sallar Jifa-Jifa Makwabtansu ne Ke Shigowa Haryanzu dan Musu Barka da Dawowa.

Innarmu Tadubi Khaleesat Sanda Take Ƙokarin Zama tana Cewa, "A'a Ai Bazama Zakiyi ba Kitashi Ga Abinci Nan Kiduba Wanda Yayi Maki Kici, Ina Lure dake Tun Sanda Muka Dawo Komai Baki Saka A Baki ba. Gamu Kila Cin da Mukayi Yakai Goma." Duk Wurin Sukayi Dariya Jin Yanda Innarmu ta Karashe Maganar.

Cikin Kunyar Khaleesat Tamiƙe Zuwa gurinda Aka Ajiye Cololin taɗauko Wace Taga Shinkafa da Wake Aciki Tadawo Gurin su Innarmu Tazauna. Innarmu tace, "Kema dai Irin Cimakar Wancan ne Kikafi Sha'awa ko? (Tana Nufin Abdul-wahab) tau Bari A Aika Maki Kwai da Kwai(Awara) dan Naga Dashi Yake Haɗawa.

Itadai Khaleesat Ba Baki Saboda Tana Kunyar Innarmu Sosai. Yayinda Ita Kuwa Innarmu Ke Ƙokarin Jawo ta Ajiki Saboda Tasake Sosai.

Tau Tunda Suka Dawo Sai Suke Wani Irin Zama Mai daɗi A Tsakanin Su Hakanan Jefi-jefi Baka Rasa Wayanda Suka Zo Yimusu Barka Har Mutanen Sanyyinah Sukan zo Suma. Wasun Su Kwana Wasun Kuwa Yini Kawai Sukeyi Su Koma.

A Irin Haka Sukayi Sati ɗaya Cif! Da Dawowa Wanda Zama Mai daɗin da Sukeyi Har Yasa Sun Sha'afa Da Zancen Likita Mai ƁOYAYYEN Suna. Zamantakewa Suke Maidaɗin Gaske Hakanan Su Abdul-wahab da Abubakar Sun Koma Kan Ayyukan Su Yayinda Innarmu Ta'azazzali Mmn Walida data Koma Itama Nata gidan Auren, Acewarta Ko Yanzun Ai Mijin Nata Yayi Musu Kara. Yayinda Ita Kuwa Mmn Walida Takan Noke Kafaɗa Cewar Gaskiya Ita Sai ta ƙara Hutawa A Irin Hakan Harta Haɗa Sati ɗaya.

Yaudai Dole Innarmu Kuma ta tuɓure mata Tayi Mata Jan Ido kan Dole Gobe ta Koma Gama ta Lura da Yawan Wayar da Babansu Walidar keta yowa Akai-Akai Yana Son Maiɗakin Nasa Takoma Ne. Dan Haka Mmn Walida Tashiga Shirin Komawar Gobe Tuni Tayi Banyar Kai Wata Makbaciyarsu Tashigo Ta Yarfa Mata Kitso.

Suna Gamawa Kuma Khaleesat Tahau Yimata Siffah (Lalle mai Zanen Fulawa.) Sai La'asar Suka Kammallah Mmn Walida taɗauki Buta Ta Tafi Wankewa. Yayinda Ita Kuwa Khaleesat Tayi Sallah Sa'anan Taci Abinci Daganan Kuma Tasoma Yiwa Innarmu Cirar Akaifa (Yankar Farce) Jefi-jefi Suna ɗan Taɓa Hira.

Innarmu Tace, "Yaudai Su Auta Shiru Ba Wanda Ya dawo."

"Humm! Kila Kuma Sunyi Nisan Kiwo ne Yau ɗin." Khaleesat ce Mai Yin Wannan Maganar Tana Karkare Farcen Na Innarmu.

Innarmu Ta'amsa da Cewa, "Ga dukkan Alama Kam." Shiru yaɗan Ratsa Gurin Nasu Kafin Innarmu taɗan Nisa Tace, "Nikam Ƴar Nan Intambayeki Wa...." Sallamar da Aketa Kwaɗawa Bakin Kofar Gidan ne Yakatse Innarmu daga Maganar da Ta Soma. Tadubi Khaleesat tana Cewa, "Kamar Fa Sallama Nakeji Anayi A Bagin Gida Ko?" Khaleesat Tace, "Lalle Nima Na...." Sallamar dai Aka Sakeyi.

Innarmu Tashiga Ƙokarin Miƙewa tana faɗin, "Bari Induba Inga Waye." Itama Khaleesat ta miƙe Tana Jawo Hijabinta dake Kan Yaggiyar Shanya dake Tsakar Gidan Tasaka Tareda Cewa, "Bari Inje Ni Innarmu."

Innarmu Tace, "A'a Nice Yafi Kamata da Inje Bari Inje Ingani." daga Haka Innarmu tafice Bakin Kofar Gidan.


Wata Ƙatuwar Jeep Ce Take Parke A Bakin Kofar Gidan, Jingine da Ita Dr ne Mai ƁOYAYYEN Suna Yana ɗan Karkaɗa Makkullan Motarsa A Hankali Yayinda ɗayan Hannunsa Ke Riƙe da Wayoyin sa.

Innarmu Takwaso Fara'a Tana, "Lale da Zuwan Dr. Maraba-maraba." Shikuwa Dr Sai Murmushi Yakeyi Cikin jin daɗin Irin Tarbar da Yasa mu.


Innarmu Tasake dubansa Karo Na Biyu Tace "Bismillah Mana Kushigo daga Ciki Mana! (Kasancewar ba Shi Kaɗai ne ba) Tare Suke Da Wani Dattijo Mai Matuƙar Kamanni da Dadyn Khaleesat. Ɗan Yunƙurowa Dr Yayi Tareda Duban Baba Tanimu Yace, "Baba Bismillah Muje ko?" Yaƙareshe Maganar Cikin Ladabi da Tsantsar Girmamawa ga Dattijon da Yakira da Baba Tanimu.

Bayan Sun Shigo gidan Innarmu Ta Malale Musu Tabarma Suka Zauna Nan Aka Ci Gabada Gaisawa Cikin Mutuntawa. Kafin Innarmu Taɗora da Faɗin, "Likita Ni Naga Kayi Kyaun Kai Da Ka Iya Gane Misalin Gidan Namu da Mukayi ma Fa?" Dariya yayi Sa'annan Yace, "Kai! Innarmu Ai Shiyyar Arkillah Gurin Zuwa Nane Kullum dan Kamar Gida Take Gareni Dan Momy na(Ƙanwar Mahaifiyata)Nan Take Zama Inaga Ma Kinsanta."

"Yana Yuwa Kila, Amma Meye Sunan ta?"Innarmu Tafaɗa Tana Ƙokarin Zama Kan Yar Tsuggunon da Ta'ajiye Gefen Su.

"Haj. Luba Mai Turare" Yafada Shima Cikin Murmushi.


"Ohhhh Ah Nasan Haj Luba Mai Turare Sosai Mutuniyar Kirki Ko Wallahi." Innarmu Tafaɗa Fuskarta Cike da Fara'a.

Shikuwa Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Yayi Murmushi Yana Mai Ƙokarin ɗaga Wayarsa da ke ta Ɓurari. Bayan Amsa Sallamar Yace, "Abdul-wahab Gamu Fa Mun Iso Gidan Ku Kaɗai Muke Jira?" Yaɗan Yi Shiru Yana Sauraro. kafin Yace, "Ok Tau Sai Kun Iso pls Sai Ku ɗan Hanzarto." Yasauke Wayar Yana duban Baba Tanimu Cikin Ladabi Yace, "Baba A ɗan Ƙara Haƙuri Suna Zuwa Yanzun Suka Ce Insha'allah." dai-dai Lokacin ne Kuma Khaleesat Take Ajiye Jug ɗin Ruwa Agabansu Tareda Tsugunnawa Tana Gaishesu Batareda ta ɗago Kanta ba, Tacigaba da Rusunar da Kanta tana Wasa da Yan Zara-zaran Faratanta.

Dai-dai Lokacin da Baba Tanimu ke Kallonta ba ko kyaftawa. Wai Khaleesat ce dasuka Turbuɗe da Hannunsu Sukayi AMMANA Ta MUTU Itace nan Gabansa. Babu Shakkah badan Kafin Yagantaba Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Yariga Yafaɗa Masa Komai ba, da Bazai Taɓa Yarda Cewa Itace Ba. Sannu A Hankali Yashafi Furfurarsa Mai Albarka Yace, "Khaleesat Hoe!" Cikin Wani Irin Bazata Taji Muryar Baba Tanimu Wanda Komai daɗewa da Zatayi A Doron duniya Basu Haɗu ba, Bazata Taɓa Mance Muryar ba. taɗago Kanta Tana Kallon Baba Tanimu da Wani Irin Yanayi da Nakasa Tantance Wane Iri ne. Kafin Cikin Rawar Jiki da Kukan da Yazo Mata Kai Tsaye Tanufi Gefen Nashi ta Zube tana Rera Wani Irin Kuka Mai Ban Tausayi Kafin Cikin Kukan Take Cewa, "Baba Kuyafemin Dan ALLAH....." Shima Lallashenta Yakeyi, "Ya'isa Daina Kukan Iyayen Ki Duk SUNE SILAR KOMAI Ko Kinada LAIFI kaɗanne."

Cikin Matuƙar Tashin Hankali Mmn Walida Ta Samu Idar da Sallar da Takeyi Batareda Yin Azkar Ta Runtomo Zuwa Waje dan Jin Meye Musababbin Wannan Kukan Na Khaleesat.

*******

Momy ce A Tsakar Gidan Tana Ta Kai Kawo Domin Yin Hidima da Baƙin BAZATA da Sukayi daga Adamawa Yayinda Aunty Shahuda(Matar Ya Nuradeen)Ke Tayata.

Bayan Aunty Shahuda Takai Masu Abin Jiƙa Maƙoshi Tadawo Kitchin ɗin dan ɗaukar Abincin da Momy Tashirya Musu A Ƙaton Faranti. Bayan taɗauka Momy ta Biyota da Sauran Kayan Suka Shiga Falon Yayinda Muyiddim Ke ta tsallen-tsallen sa A Falon Na Rashin Jin Magana. Dole Aunty Shahuda Tajanye sa Bayan Ta'ajiye Kuma Ta Gaishesu Suka Fice Tare Tana Cewa, "Muje In Maka Wanka, Dubi Kayan jikinka Kamar Ba Ɗazun-Ɗazun Nan Momy Tayi Maka Wanka Ba."

Dai-dai Lokacin Shima Ya Nuradeen Yake Shigowa Falon domin Gayar da Ƙanne da Yannen Dadynsa Da Suke Cike Maƙil A Falon. Kasancewar Dady Ɗan dangi kuma Masu Yawan Family.

Duk Sukayo Caaa!! Akansa "Ja'iri Marar Son Zumunchi....."

"Ai Ba Laifin Sa Bane. "Baba Tanko Ya katse Baba Bukar da Yafaɗi Hakan.

Baba Ado Ya'ajiye Cupin da Yasha Lemu Yana Cewa, "Tau Waye ne Mai Laifin?"


Muje Gaba Masu Karatu Dan Jin WAYE MAI LAIFIN? Hakanan Kuma Muji Meke Shirin Faruwa Da Irin Wannan Zuwan Bazata da Su Baba Sukayi Ma Dady. Inda Nanne Zakuji Warware war ƘULLALLEN ƘULLIN da Aketa Magana.

Tareda Alkalamin

FA'IK..
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 30 · 0% Book details