← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 13 OF 40

Chapter.....15

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


A Raina Nace Ashe Yana da Surutu Haka? Kamar Yasan Meke Raina Yace, "Bakiyi Zaton Ina Zuba Surutu haka ba ko? Tau Yazanyi Ƴar Momy Taɗaga min Hankali Kuma Gashi Ta Fini Miskilanci?" Yaƙarasa Maganar tasa Cikin Rausayar da Kansa Irin Kalar Tausayi ɗinan. Nan Ma Dariyar Nayi dan Wallahi Yabani dariya Cos Banyi Tsammani Irin Yadda yake da Tsare Gira Ɗinan Yana da Bakwanci Haka. Nasake dubansa Sanda Yake Cewa, "Izuwa Natabbata Yar Momy Ta san Meke Tafe da Likita Gurin dan dai Hausawa Sukace In kaga Kare Na Sunsunar Takalmi tau ɗauka Zaiyi Hakane.? Yaƙarasa Maganar yana dagemin Girarsa mai Matukar Kyau Nayi Murmushi Ina Sadda Idanuwa na A Ƙasa Saboda bana iya jurar Kallon Nasa Idanun dasuke ɗauke da Wani Irin Magana ɗisu Kafin Na motasa bakina Ina Cewa, "Hakane, Amma kuma Hausawane Sukace 'Waƙa Abakin Mai Ita Tafi daɗin Saurare ko?"


Yasanya Duka Hannayensa Cikin Aljihun Wandonsa Yana Jifana da Wani Mayen Kallo Sa'annan Yayi Murmushi Tareda Cewa, "Kice Kawai So Kike In Miki Gwari-Gwari Ini Matar Bagware ko?" Wannan Karon Dariya Har Sunkuya Nake Tareda Tambayar Kaina Wai dama Haka Miskilan Mutanen Nan Suke? Dai-dai Lokacin Naji Yana Cewa, "Shikenan Tunda Hakan kike so Ni A Yanzun bani da Ja Bana da Kuma Kataɓus Saboda Sonki Yariga da yagama Zama Jinin Jikina Dan Haka Komai kikace Dole In bada Kai Bori Ya Hau." Kai Wannan Mutumen Ƙarshe ne Ashe Wallahi ku...."


"Yar Momy...!" Yakatsamin Zancen Zucin da Nakeyi.


"Na'am!" Batareda iya dago Kaina in kallesa ba.


"Dubeni Mana!" Yafaɗa Yana Ƙokarin Rage Nisan dake Tsakani na Da shi. Nikuma Naɗan ja Baya Gamida Cewa, "Ni Bazan Iya Kallon ka ba?"


"Saboda ni Mummunane Ko?"


Nayi Saurin Girgiza Kaina "Bahaka Nake Nufi ba."

"Tau me kike nufi My Ƴar Momy?"

Naɗan Zumburi Baki Abinda Yazamemin Ɗabi'a Kafin Nace "Komai."

"Komai!" Shima Yamai maita Kamar Yadda na Faɗa Muka danyi Dariya Yace "Yar Momy INA SONKI INA MURADIN KASANCEWARKI MATATA Kema kinada Wannan Ra'ayin Akaina?" Nayi Shiru gamida Sunkuyar da Kaina Ƙasa ina Wasa da ɗan ƙaramin Zoben Azurfar dake Hannuna.


Yayi Murmushi Kafin Cikin dan Jidali haka-hakanan Yace "Ai Kuma Baki Isa ba! Kice in Miki Gwari-Gwari Sa'annan ke Kuma kizo kina Wani Sunne Kai kamar Wata Ma..... "

"Saboda ALLAH tau Mekake So Ince Maka?" Nakatse da Faɗar Hakan Cikin Shagwabar da Bansan meye Dalilin yi Masa Ita.


"Saboda ALLAH So Nake kema Kifurta Abinda Nafurta Bi Ma'ana kiban Amsar Tambayata In Har Kema Kina jin Abinda Nakeji Gameda ke."

Na Nuna Masa "kaga Hadari Nahaɗo wa Kar Ruwan Sama Yama duka." Yayi Dariya Kafin Yace, "Na Lura Yar Momy Banda Miskilanci Harda Zama Yar Daru Ko? Tau ko Za'a Gwabce dasu Yanzun Su ɗauke Wani Hadarin Yasake Haɗowa Yasamemu Nan Bazamu ɗaga ba Harsai Kin Amsar Tambaya ta."


Nakara Rumgume Hannaye na A Ƙirji Tareda Ƙara gyara Tsayuwa ta danake Jin Tana Neman Gagarata Saboda kwarjinin Wannan Talakin da Wani Irin So Nasa mai Shiga Da Zafi-Zafi Batareda Yanemi Izni Ba


"Uhummm Ke Nake Saurare." Yakatse Min Tunanin da Nakeyi.

Nace "Tau Kuma Shikenan Ba'a Barin Mutum Yayi Shawara."

"Babu Wannan Damar Gudun Wani Yacanza Maki Tunani dan Nasan Yadda Kike da zubin Hallitar Nan Mai Kyau da Jan Hankali Bazaki Rasa Wasu Manema ba Tau Nikuwa Mezaisa Ni Abari Yahuce......" "Tau Shikenan Na'amce." Faɗar Hakan danayi Sai da Naji Tsawa Acikin Kwakwalwar Kaina Wanda Yayi Dai-dai Tasowar Wani Iska Mai Ƙarfi Alamun dae Kowane lokaci Ruwan Saman Zasu iya gwacewa.

^^^^^^^^^^^^^^^


Wannan Yayi Dai-dai da Abdul-wahab Na Tsaye gaban Wata Motar Acikin Garejinsu Yana Kwal-kwale-kwale Acikin Ingimin Motar Zuciyarsa Tai Wata Irin Bugawa Wanda Sai da Yayi Taga-taga Kamar Zaifi Faɗi Cikin Ikon ALLAH Yasamu Yadafe Wani Ƙarfe dake Kusa dashi Kafin yakai Zaune Cikin Sauri Gamida dafe Saitin Zuciyarsa Yana mai Karanto Innalillahi! Duk Mutanen Wurin Sukayo Ruuuu Akansa Tareda Subhanallah!

Oga A Wurin Aikinsu Yariga Kowa ƙarasowa gareshi Kafin Yarike Sa Yana Cewa, "Abdul-wahab Meke Faruwa?" Abdul-wahab Cikin Runtse Ido Wanda Tuni Hawaye Sun Soma Zubo Masa Yace, "Oga Bansa ni Ba Nima." Ogan Yace, "Baka Sani Ba? Tau dama Baka da Lafiya ne ko da Kafito?"


Abdul-wahab Yagirgiza Kansa yana Cewa, "Lafiya lau Nabaro Gida Kuma Nanma Lafiya lau Nake Aiki Na. Kawai dai Yanzun ne Naji Abun Yataso Mun."

Kafin Kuma Yasoma Karkarwa Cikin Kiɗima Oga Yace, "Sunday Zo Ka Ƙarasa Gyaran Motar Nan Bari Naje dashi Asibiti." Abdul-wahab Yace, "Akaini Gida Kawai Zaifi."

Ogan Nasu Cikin Rashin Hausasar da Bai Kware ba Yace, "Bazaiyu ba Abdul Wannan Ko kana Gida Ne Yasameka Ai Asibiti Aka Nufa dakai Balle Kuma Muna nan gurin Aiki Tashi Muje Kagani." Yakama Abdul-wahab Suka Fito daga Garejin Yayinda Mutanen Gurin Musamman Abokan Aikin sa Suke Biye dasu Cikin Sanyi Jiki Da Matukar Mamaki "Sannu!" Kuwa Sunyi Ta Karanto Masa Harba Adadi Kasancewar Abdul-wahab Mutumen Mutane A Gurin Baya da Abokin Faɗa Kowa Yana Zaune dashi Cikin Mutum ci Da AMANA.

Wannan Ma Yasa Yazama YARO! Mafi Soyuwa A gurin Ogan Nasu Tun Abokan Aikin Nasu Na Hassada Har Wasun Suka Haƙura da Cewar Shiɗin Yaron Kirki ne Kuma Suma Yana Kyautata Musu Yayinda Wasun Kuwa Sukace Sai Sunga Abinda Yaturewa Buzu Naɗi. (Dama Haka ALLAH Yayi Mutanensa da Rayuwar!) Tuni wani daga Cikinsu yariga su Isa Bakin Titi yadawo masu da Kk Napep dan Haka Shida Ogansa da Wani Yaron Garejin Suka Hau Tareda Nufar Asibitin Suka bar Mutanen Gurin Cikeda Alhinin Lamarin.


==========


"Ya dai?" Dr Jabir ke Tambaya ta Sanda Nayi Maza Nadafe Kaina Tareda Sunkuya wa Ƙasa Ina Karanto Hassbunallahu! Duk Ƙokarinda Nayi In Amsa masa Nakasa.

Yaɗaga Kai Yakalli Yanda Gari Yayi Baƙi ƙirin Har ma An soma Yayyafi Kaɗan-kaɗan Yadurkusa Kusa Dani Cikin Zuciyar sa Yana Tunanin kodai Wannan Iskan ne da'ake yi Yatayar min Da Aljanu tunda Dama Su Mata baka Rabasu da Aljannu😂

Yayi gyaran Murya Gamida Cewa "Yar Momy Tashi Kishiga Gida Zamuyi Magana daga baya, Karɓi Ga ɗayan Wayata Zankira Ki Anjima Kinji?"

Babu Musu Nakarɓi Wayar jikina duk Gumi(Zufa) yake Kamar Ba Ana Iska ba. Najuya na nufi Cikin gidan Batareda ko Wai waye sa ba. Yadaɗe Jingine da Motar sa yana Kallona Har Sanda yaga Nashige Gida Kafin Yasauke Ajiyar Zuciya Cikin Mamakin Sauyawa ta Cikin Lokaci Ƙanƙani. Ganin Ruwan Da'ake Yasoma Karfi Haryajiƙa Masa Jiki Yayi Hanzarin Shiga Cikin Motarsa Yatayar Da ita Yawuce.

Sanda Nashigo cikin gida ba kowa A Tsakar gidan Sai Momy dana Hango can! A Cikin Kitchin Tana Rike da Lema Nasan Alalar dana ɗora Take Sauke wa. Ban Wani Saurara ba Na nufi ɗakin dayake Nawa ne, ina Zuwa kuma na faɗa kan ƙatuwar Katifa ta Na dunƙule Cikin Hijabi na Ina Makarkatar Sanyi. Can da jimawa Saiga Momy Tashigo ɗakin Nasan tayi Mamakin ganin kawai nawuto Ban bi Ta kanta ba.

Tahayo kan katifar tawa Tana yaye lulluɓin da naye gamida Cewa, "ke Lafiya? Dama Ni tunda Naga Yanayin Shigowar ki Nasan da Walakin....." Naka ra Ruƙumƙume Jikina Ina cewa, "Momy ki Rufe ni Sanyi Nakeji." Momy tace Subhanallah Kodai Ruwanan da'ake Yajiƙa ki Yasaukar Maki da Masassara(Zazzaɓi) Kuma kema dai Kinga Alamun Hadarin Ba Sai kuyi Sallama Ki Shigo gida ba tunda Kin Sanu Ba wani Cikakkar Lafiya ce dake ba?" Nidai Bantaka ba Ko Inada Ma Niyyar Tankawar Nakasa Saboda Wani Irin Zazzaɓi da Yarufeni Anan Take.

Momy Tajawo Bargo Tana Lulluɓeni Tana Cewa, "ALLAH Yasauwaka Bari Naje nagayawa Dadyn ku, Ana ma Ruwan Nan Wane Mai Chamist Ne Zaka Sama?... Bari A Samo Maki paracetamol Kisha Zuwa Sanda Ruwan Zai Tsagaita Sai A nemo maki Magani." Kafin Tajuya da Nufin fita Sai Kuma Tadawo "Ni Wannan, Ciwon Naki daki Yaƙi Ci Yaƙi Canyewa Tunda Kika Haɗu da Jarababben Yaro Nan (Abdul-wahab) Kikayi Ban kwana da duk Wani Farincikin ki Haba! Me Ake da Wannan ALAKAR? "

Momy Tayi ta Yan Faɗace-faɗacen ta Tagaji Sannan Tafito Tabarni Acikin Yanayin da Nakasa Tantance Ina ne Nake Tsakanin Duniyar Mutane da kuma ta Masu CIWON SO!


**********


Dai-dai Lokacin da Su Abdul-wahab Suke dawowa daga Asibiti Suna Bakin Gidan Su Abdul-wahab ɗin A Gwabce da Ruwan Masu Ƙarfi. Cikin Ruwan Kuma Suka Rika Abdul-wahab Sai Cikin Gida Suna Shiga Yazuɓe Kan Shimfiɗar Innarmu Sai Maida Numfashi Yake. Innarmu Tayi Hanzarin Sallame Nafilar datake Ta Iso Gareshi kafin Tajiyo Muryar Mutane A Ƙofar ɗakinta dake Cikin Baranda Sama-Sama. Dan Haka Sai Ta Fito Wajen.


"Mama Ina Wuni?" Abinda Ogan Nasu Abdul-wahab Yatareda Shi Kenan Tace, "Lafiya Lau. Ah Zayyanu (Watau dayan Abokin Aiki Nasu Dayake Shi Sun Saba zuwa da Abdul-wahab Gidan Innarmu Tasanshi) Na Shima Ya Gaisheta Shima Kafin Kuma Yakoro Mata Jawabin duk Abinda Yafaru Innarmu Sai Girgiza kai take Tana salallami Daganan Suka Sake Gaisawa da Ogan Nasu Abdul-wahab Harma tayi Masa Godiya da irin Karamcinsa ga Abdul-wahab da kuma Wani Lokacin Aiken da Yake Yo Mata Ta Hannun Abdul-wahab ɗin.


Ruwa kuwa Sai Ƙara Ƙarfi Yake duk Feshinsa dake Shigowa Cikin Barandar Yajiƙasu Hakan Yasa Sukayi Mata Sallama Tareda Miƙo Mata Ledar Maganin Na Abdul-wahab. Rokon duniya Innarmu tayi Masu kan Su Shigo ɗakinta ko ɗakinsu Abdul-wahab ɗin Harzuwa Sanda Ruwan zai Tsagaita Amma Sukaƙi.

Dole Cikin Ruwan Tayi Masu Rakiya Tareda Binsu da Kalaman Godiya harba Adadi. Duk kuwa da irin Rokon da Sukeyi Mata Suma na Cewa Takoma Kar Ruwan Saman Yajiƙata. Dole Sanda Aka kawo Bakin Ƙofar Gidan Sukayi Sallama Yayinda Suka Rumtuma da gudu Suka Faɗa Cikin Kk Napep ɗinda Suke tare da ita. Itama Innarmu Tajuya Cikin Gidan Cikin Tarin Mamakin Irin Wayyanan Rashin Lafiyoyin Abdul-wahab Da Suka Ƙi Ƙarewa. Tama Lura Kai Tun Sanda Abdul ɗin Yahaɗu da Jarabbar Yarinyar Nan (Khaleesat) Sai kuma duk Yafita Hayyacinsa da Walwalarsa Tau Me Ake da Wannan Soyayyar Marar Kan Gado?

"Tashi Kasha Maganin Sannnan ka Kwanta Zaifi." Abinda Innarmu ke Cewa Abdul-wahab Kenan Sanda Tashigo ɗakin Yayinda Shikuwa Yaƙara dunƙulewa Tareda Cewa, "Innarmu Nasha tun Acan Asibiti harma Allura Sukamin, Dan ALLAH ki lulluɓeni Innarmu Sanyi Nakeji." "Tau Bazakaci Abinci ba? Ai kasha Koda Kunun Zaƙi ne Ko?"


"Innarmu Bana Bukata, Dan ALLAH ki Lullubeni." Abdul-wahab Yasake Faɗar hakan Yana Mai Ƙara dunƙulewa Guri ɗaya. Innarmu Tajawo Bargonta Ta lulluɓa Masa tareda Tofa masa Adu'a Sa'anan Tamike Takoma Kan Sallayarta Tana Cewa, "ALLAH ya yaye Maka Wannan Lalurar Abdul Dan Alfamar Ma'aiki (S A W). Kafin Tasoma jan Carbinta Tana Mai Sauraro daga Ruwan da Ake ta Ci gaba da Tsugawa Kamar da Bakin ƙwarya.


***********


Shima dae Cikin Ruwan Saman Yayi parking ɗin Motar sa Yafito, Kafin Maman Ashraf Tafito da Lema ta taryeshi Yaɗora Hannunsa Kan Kafaɗar ta Suna Cikin Lemar Suka Nufi Cikin Gida. Sai Sannu Take yima sa. Shikuwa yana mata Murmushi Tareda Cewa, "Karki damu, Dama Shi Watan August Yagaji Hakan."

Tace, "Wallahi Kam! Ni Nama ɗauka Bazaka Taso Yanzun ba Tunda Kaga Ruwan."


"Bari Kawai! Saman Hanya Suka Riskeni Wallahi." Dr Jabir Yafaɗi Hakan Yana Mai Cire Jiƙaƙƙun Kayan dake Jikinsa Kasancewar Sun Shigo ɗakinsa Yayinda Maman Ashraf Tashiga Tayashi Cirewar Bakinta Kuma Bai Huta da Amba ta masa Sannu! Ba. Shikuwa yana Amsawa gamida Karramata da Wata irin Sahihiyar Ƙauna Wacce take Tasowa Tundaga Cikin Zuciyar sa Har Izuwa ga Maƙwagoro.

Kaitsaye Toilet Yashiga Yagasa Jikinsa da Ruwan Zafi Sa'anan Yayi Wanka Da Ruwa Masu Ɗumi Kafin Yafito Ɗaure da Tawul A Ƙugunsa Yana kuma Rike da ɗaya yana Tsane Ruwan Jikinsa da shi. Maman Ashraf tamiƙo Masa Ruwan Lipton mai ɗan Zafi Da Yaji Haɗin Citta, ta'amshi Tawul ɗin tashiga Aikin Tsane masa Jikin nasa Yayinda Shikuma yake Kurɓa Ruwan A Hankali ɗaɗinsu Na Gauraye masa Maƙoshi Kafin Yace Mata "ina Mutume Nane(Ashraf)?"

Tace, "Yana Bacci Tunda Aka Soma Ruwan Sai muka Shige ɗaki Muka Kwanta Kasan Mutumen da Tsoron Tsawa! Ingayama duk Yabi Yaruƙumeni daganan Sai Bacci."

Dr Jabir Yayi Murmushi Tareda Cewa "Ɗan Baba Kenan!" Jallabiya Yazura Suka Fito Falo Lokacin Ruwan Sun ɗan Tsagaita Sai Yan Lam-lam Da'akeyi. Kan 3Searter Suka Zauna Atare Kafin Maman Ashraf tace dashi "Akawo Abinci?" Yadubi Agogo Kamin Yamai do Kallon Sa gareta Magarib Tagaba to, A Bari Har in dawo Sallah." Yajanyo Remote ɗinda ke Kan Hannun Kujerar Yana mai Ƙokarin Kunna Tv Kafin Yace, "Wai Nikam In Tambayeki 'ƴar Momy?" Yayi Saurin dafe Bakinsa Yayinda Maman Ashraf Kuwa Tahaɗe Girar Sama da ta Ƙasa Izuwa Yanzun Tasoma Gundura da jin Wannan Sunan Haka Jiya Suna Barci Yakwana Kiran Mata Yar Momy! Yar Momy!! Kamar Wanda Ke Mafarki Ta Tayar dashi Ya dinga Zamewa A'a Wai Ai itace yake Mafarkin Yana tsokana Haka da Safe Zai Fita "Sai Nadawo Yar Momy." Still Gashi Yanzun Yar Momy.

Kuma ga dukkan Alamun Yanda Yasha Jinin Jikinsa A Yanzun da Yasake Suɓutar Baki Yaƙara Tabbatar Mata Cewa Kowacece dai Yar Momy ɗinan Ba Alkairi bace Itakam Gareta. Dan Haka Cikin Sanyin Jiki Tazare Hannunta Dake Cikin Nasa dai-dai Lokacin da Wasu Hawaye Masu Zafi Suka Sulalo Mata Tamike Tanufi Part ɗinta Shikuwa Sai Kiran ta Yake, Tayi Masa Banza dan Haka da Hanzari Yamike yabiyotan Ita kuwa tahaɗa Harda gudunta ta'isa ɗakinta Kafin Tarufo Ƙofar ta da ƙarfi Sanan tajingine da ƙofar Tana mai da Numfashi "Namiji Ƙanin Ajali Namiji ba ɗan goyo ba Namiji Ƙudan Zuma!!!" Wayyanan Kalamin Sukaita Mata Yawo A Kwakwalwar ta Bata san Sanda ta Sulale Ƙasa ba Jingine da Ƙofar Tareda Fashewa da Wani Irin Kuka Mai Ratsa Duk Wata Zuciyar Mai Sauraron ta. Bugun Duniya Da Kiran Sunan ta Dr Jabir Yayi Amma Taki Buɗewa Haka Yajuya Yakoma Falon Yana Mai dafe Kansa Tareda Tambayar Kansa "What is Wrong Wit me? Meyake Damuna ne?"


Tau fa Readers Dr Jabir Na Tambaya Mu Gayamashi Ko Mubarshi? Hummm SO! Kenan! SO! BABBAR CUTA Meke Shirin Faruwa Ne? Wane Irin SONE Wannan da Yayi Musu Kamun Kazar Kuku? Shin Wai Haryanzun SO ƊINAN BAI GAMA ZAMA SILAR KOMAI BA? Haryanzun Muje Zuwa..........


Tareda Alkalamin


FA'IK ✍🏻✍🏻✍🏻
[9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 13 · 0% Book details