← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 40 OF 40

Chapter.....42

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

➡➡➡ ENDING(ƘARSHE)


Mallakar 👇

Fa'IK ✍


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


GARGADI.
Duk wata dama a littafin nan a kare ta ke,komai za'a aiwatar sai da izinin mai littafin dan Haka a kiyaye.

FADAKARWA.

Yi wa rubutu na kyakyawar fahimta B banyishi dan kowa ba. Na yi ne dan ilimantarwa da nishad'antar wa. A kuma shirye na ke wajen kar'bar kowanne irin gyara cikin fahimta ba da cin zarafi ba🙏.


Godiya ta musamman
ga ALLAH sarkin sarauta da ya bani aron rai da lafiya na kammala wannan litaffin. 🙏🙏🙏

BUGU DA ƘARI!!!

Littafin nan nawa bazai kammala ba har sai na jadadda godiya ta ga
'yar uwa Hajaru M Bello Abubakar Ak Saraki, tare da Basira AB Musa UMMU SHUKURAH (shugaba) tare da dukkan wani member na k'ungiyar mu mai albarka kuma gagara gasar masu gasa end of discotions wato.
JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION.
Haka nan ina miƙa godiya ga mutanen arzik'i da suke taya ni yad'a wannan rubutun irin su, Haulat Abubakar, Nana (ƴar Saudiyah) da kuma Nafeesat (itama tana taya ni duk da kuwa babu sanayya a tsakanin mu)
da sauran dukkan wad'anda ajizanci na d'an adam yasa ban samu na lissafo su ba ina godiya ALLAH ya yi muku sakayya da gidan ALJANNAH MAƊAUKAKIYA 🙏🙏🙏


Bismillahir rahamanin raheem!!!


Domin dai tsakani da ALLAH yadnlda Innarmu ta ce haka ne zullumin bai bar ni na ci komai ba. Kazar ma abaki ya rik'a ba ni mukaci sosai muka kora da tsaftatacciyar madara mai sanyi sannan kuma ya shiga taya ni kwashe kayan zuwa kitchen. Bayan na ɗauraye kayan shi kuwa a lokacin ya fito daga shi sai Jallabiya ya cika ruwa a boket zaiyi wanka. Ni kuma na ɗauki brosh ina matsa maclean sannan na soma wanke baki na.

"Karki taɓa bari mijinki ya shaƙi wani abu a gare ki wanda ba k'amshi ba." Huduɓar Momy ta faɗomin a rai kamar yanzu ta ke faɗamin ita. Na samu kaina da yin murmushi a fili na ce, ALLAH ya saka ku Aljannah Momy da ke da Dady da kuma Yaya Nuradeen har......"

" Da Sauran Al'ummar musulmi." Abdul-wahab ya ƙarasa wannan maganar lokacin yana miƙo min kwandon da ke ɗauke da soso da sabulun wanƙa mai k'amshin strawbeery. Dariya Mukayi dukkan mu sannan ya ce, "Ga ruwan wanka can na kai miki Toilet jeki ki yi wanka amarya."
'Dariya na yi,amma ai ni nafi can_canta da inyi maka haka ko?".Ya yi murmushi shi ma yana matso maclean a brosh ɗinsa sannan ya ce, "Ita kyautatawa tana can_canta akan kowa Ma."


"Abdul-wahab ya dafe kai na ya na karanto addu'o'i kala-kala bayan mun gama nafila kenan. Ya kuma yi min tambayoyi akan addini na inda na sani na bashi amsa inda ban sani ba kuma ya yimin k'arin bayani a nan ne wani daɗi ya ƙara lulluɓe ni jin cewa angon nawa Malami ne sosai.

Kallo na ya yi ya ce min. "Kin iya wankan haila ko?". Na kaɗa kai na alamun eh." Ya ce, "To haka akeyin na janaba ma ban_bancin su kawai niyah ce."
Daga nan muka canza kaya zuwa na bacci.

Na ɗan tsaya gaban madubi ina shafe-shafen da suka zamo min al'ada ta shi kuwa ya na gefen gado zaune riƙe da wayar sa.Saƙon ban gajiya da kuma godiya ya ke turawa abokan sa, kafin kuma ya ajiye yayar ya laƙato wani lotion wai zai taya ni shafawa.
Tun daga nan komai ya rikice mana saboda numfashin mu da ke dukan juna ga kuma k'amshin juna da muke shaƙa wanda yana kankaro duk wata k'auna da soyayya da muke yiwa juna tana saukar nana da kasala. Ban yi aune ba sai jin nakinsa na yi cikin nawa ya na min wani irin tsotsa kamar wanda ya samu alawar lolipop daga nan kuma abin da ya biyo baya bazan iya tan_tance sa ba saboda wani hali ne na shiga wanda na rasa gane Duniyar da na ke ciki. Tun ya na kiran suna na ina amsawa har amsawar ta gagare ni. Duk wata tsantsar k'auna da take maƙale a cikin zuciyar Abdul-wahab a ranar sai da ya fitar da ita a wannan daren ne kuma sukaji ashe can da ba son juna sukeyi ba, sai yau ne suke k'aunar juna domin dai kowanne daga cikin su ji yake kamar ya haɗiye d'an uwan sa aaboda k'auna. Kuka kam nasha shi y'an gidan mu kuwa ba wanda ban kira ba dan neman ceto. Idanun Abdul-wahab biyu lokacin da Ladanin Masallacin unguwar ya kwaɗa kiran sallar asuba na farko ya miƙe cikin wani irin karsashi ya ɗauro alwala bayan ya yi wanka ya fito da Gas ɗin su waje ya kunna sannan ya ɗora ruwan zafi Bayan sunyi zafi ne ya juye ruwan cikin boket ya ƙara ɗora wasu ya tafi ya sirka ruwan dai-dai yanda za'a iya amfani da su.

Sannan kuma yaje ya tallafo ni ya shigar da ni bayin navsoma yin wankan na gasa jiki na. Sai da na fito sannan na kimtsa kai na,ina kan sallaya ne ya tabbatar da ya taimaka min sannan shi ma ya nufi Masallaci.

*******

BAYAN WASU ƳAN SHEKARU............


Abubuwa da dama sun faru wasu sasu daɗi wasu kuma marasa daɗi haka kuma rayuwa tana shurawa sosai ta kuma sauya sosai an kuma samu cigaba akan rayuwar su Khaleesat.

Abdul-wahab dai ya kammala karatun sa bayan k'alubale da gwagwarmayar da aka sha yanzu ya zama cikakken Lawyer mai zaman kansa.

In da Shi ma dai Abubakar ya gama na sa karatun ya zama babban Enginier da ke zana manya-manyan gidaje har wajen Nigeria akan nemesa da aiki. Arzik'i dai ya ɓalle musu sosai yanzun. Tuni kuma Shi ma Abubakar d'in ya ke tare da amaryar sa Safiya 'yar gidan su Dr Jabir k'anwar Maman Asharaf da a yanzu Dr Jabir da Dr Faisal da kuma su Abdul-wahab tare da su Yaya Nuradeen da kuma abokin Abdul-wahab ɗin wato Yusuf suka k'ulle suka zama ZURI'A ƊAYA. Suke kuma fantamawa a Duniya ba inda sunan su bai kai ba baboda kujba_kujbar nema da sukeyi da kuma gidauniyoyi da suke dasu na taimakon al'umma. Hakanan yanzu sun gina wani katafaren gida a cikin unguwar Sama road wanda masana sukayi ittifaƙin cewa babu irin sa a faɗin jahar Sokoto a yanzu in dai gurin kyau da tsaruwa ne. To abu na ka..... Enginer sukutum ya yi wa wasu balle kansa Kuma? Yanzu haka Maman Walida sun dawo Sokoto da zama saboda mijinta da su Abdul-wahab suka bawa jagorancin Companyn su mai sarrafa shinkafa. Companyn da mutane da yawa ke ci k'arkashin sa ciki kuwa harda y'an uwansu na sanayyah.


A cikin shekarun nan dai Abdul-wahab suna da y'a'ya biyar maza uku mata biyu yayin da Abubakar ke da ukku mata Biyu namiji ɗaya.

Innarmu kuwa girma ya kamata ta koma KAKALLIYAH.

Yanzu haka 'yan mata da mazan na su Abdul-wahab ɗin, suna shashenta suna ta tsula tsiya dai-dai lokacin na ke k'ok'arin shigowa sanye da wani tsadadden less sai k'yalli na keyi. Na zama babbar mace ina tare da mijina abin k'aunata Alhaji Abdul-wahab na rakoshi ne gurin Hajiya Innarmu da ke zaune a sashenta kan lallausan kujerun da suka yiwa falonta k'awanya. Shari'a ta keyi tsakanin yaran yayin da Asharaf ɗin Dr Jabir ke gefe sanye da Suit sai shan k'amshi ya ke yi. Yaron akwai misƙilanci ba inda ya baro Dadyn sa.

Na durƙusa gefe ina faɗin Innarmu barka da hutawa.
Ta ce, "Ina naga hutu yaran nan sun tasa ni a gaba da iya shege? Wai Afrah('yar wajen Abdul-wahab) ta ce zata min kitso shine fa Rumana(ƴar wajen Abubakar) ta hana ai aikin ta ne ita ta saba yimin shi ne na ce duka su bari bana so zan kira Malika ('yar wajen Abdul-wahab mai bin Afrah kenan) na ke so tayi min kinga ita kuwa sai wani shan k'amshi take yimin ala dole gata 'yar izzah ko ina ta gaji wannan shan k'amshin oho, dan dai Auta da Abdul-wahab basu da wannan miskilancin.

Nuwaila 'yar gidan Yusuf ta yi maza ta ce,"Wallahi mijinta Yaya Asharaf ne ya koyamata." Gaba ɗaya yaran da ke parlon sukayi dariya da shewa.

Shi kuwa Asharaf harara ya watsamata kamar zaiyi magana sai kuma kawai yavhaɗe abinsa ba tare da ya yi maganar ba ya cigaba da dannar wayarsa.

Dai-dai lokacin kuma Malika ta shigo d'auke da faranti ta ajiye gaban Asharaf ɗin har ta miƙe ya ce, "Ina spoon?" Ta kama baki "Lahh!! Bara na ɗauko."

Me yaran zasuyi idan ba ihu ba. Yayin da ni da Abbansu mukayi murmushi ita kuwa Innarmu ta toshe kunnenta ta na faɗin, "Ni dai na shiga uku yaran nan zasu toshe min kunne." Dai-dai lokacin Abubakar ya shigo parlorn ya na saɓe babbar rigarsa wai zashi ɗaurin auren 'yar wani abokin su. Safiyah ta na biye da shi ta na riƙe da hularsa dama k'a'ida ne duk zasu fita zasu biyo gurin Innarmu.


Ya ce, "A'a me ye haka yara kuna neman maida mana gida kamar gidan kallon k'wallo?" Nan take kuma suka shiga taitayin su dan sun san Baba k'arami baya wasa. Daga can Asharaf na cin abincin sa ya ce, "Maganin ku kenan." In banda Malika da ke kusa da shi ba wanda ya iya jinsa. Nan fa duka samu parlorn ya ɗan natsa suka samu hankalin KAKALLIYAH(Innarmu) ya dawo kansu ta dube su cikin farinciki da har abada idan tana ganinsu a wannan matakin da bata taɓa tunanin ganinsu akai ba baya gushewa. Ta yi murmushi tare da cewa, "Sai ina sojojin Inna?" Suma dai murmushi sukayi Abdul-wahab ne ya fara magana ya ce, "Zan je Abuja ne Innarmu domin akwai wata shari'a da zanyi handling kuma ina ganin shari'ar zata ɗauke ni tsawon sati ɗaya."

Abubakar kuwa ya ce, "Ni kam ba nisan kiwo zanyi ba,d'aurin auren 'yar abokin mu zamuje nan Tamaje." Innarmu ta sakeyin murmushi ta ɗan muskuta cikin jin daɗi da BURIN ina ma marigayi zai dawo yaga marayun da ya bari cikin kulawar Ubangiji da ta ke kai kukanta gurin sa ba dare B ba R rana matakin da yak aisu ta ce, "Masha Allah,amma kai mai zuwa Abuja jar sati ɗaya baka ganin yafi kamata ka tafi da iyalin ka?" Ya ɗan musƙuta ya ce, "Ni ma na so hakan amma sun ce suna da shirin fita siyo kayan d'akin auren y'ay'an su."

"Ƴay'ansu kuma?" Innarmu Ta maimaita maganar cikin son tuno su waye.

Abubakar ya yi murmushi ya ce, "Innarmu girma ya fara shiga ko? Batun Walida(Walidar Maman Walida) da Haroon (dan Dr Faisal) da za'ayi, to kuma jiya ma mun aama yanke hukuncin haɗa na Asharaf (d'an wajen Dr Jabir) da Malika (y'ar wajen Abdul-wahab) da kuma Rumana(y'ar wajen Abubakar) da Abdulrazak (d'an wajen Dr Jabir mai bin Asharaf kenan) sai kuma Afrah (ƴar wajen Abdul-wahab) da Musty (ɗan Wajen Yusuf) Nuwaila(y'ar wajen Yusuf)da Affan(d'an wajen Abubakar)."

Innarmu ta yi murmushi a karo na barkatai ta ce, "Masha Allah abu ya yi kyau kuma ya yi sha'awa to amma kun binciki Yayan?" Abdul-wahab ya ce, "A'a bamu bincika ba sai dai muna kyautata zaton haɗin na mu mun yi sara kan gaɓa kuma dama mun ce ke zamu bari da wannan aikin ki bincike su kiji tun da ai k'awayen ki ne sai abokan ki ko?" Ya k'arasa maganar cikin raha.

Duk sukayi murmushi kafin ta ce, "Ni ma ina kyautata zaton haɗin da ku kayi kunyi dai-dai sai dai zan ƙara bincikar su muji,amma duk da haka bazai yu ba,ita ce ta ce bazata bika ba kuma wannan ba hujja bace kuje kawai alabarshi idan sun tashi siyayyar ta su su biya ta can wurin ta(Abuja)sai su wuce. Dan haka tashi kije ki haɗo kayan ki kibi mijin ki." Innarmu ta k'arasa maganar tana kallo na yayin da ni kuma na shawagaɓe kamar ba ni ce mai surukai ba. ta ce, "Ƴar nan aure ibada ne Aljannah kuwa sai ka dage,maza tashi."
"Miƙewa na yi zuwa part ɗin mu ina wani bana so. Shi kuwa Alhaji Abdul-wahab ya faki idanun mutanen ya yimin gwalo.Ni kuma nai masa kallon zaka santa ne. Nan kuwa cikin raina zallar farinciki ne dama ina son bin mijina kawai dai kar su Maman Walida suga a zarɓaɓi na ne. Shi ma kuma in ɗan ja aasa ajin nan namu na mata. Wannan kuma na ɗaya daga cikin dalilin da ke k'ara kimar Innarmu a cikin ran mu dan ta ɗauke mu duka kamar y'aƴanta. Duk yanda zata yi wa Maman Walida muma haka zata yi mana. Shiyasa ko da yaushe gidan mu muke zaune lafiya kuma cikin albarka.

Minti biyar na haɗa kaya na na fito janye da troly na. Daga nan Innarmu ta ce kowa ya matso ayiwa su ABBA addu'ar sa'a zasu Fita.

Nan kowa ya matso ta soma kwararo addu'a muna cewa ameen.

Wanna jazamun ne dama! Duk zamuyi tafiya tau takan yi mana hakan. Idan yaran sunanan basuje School ba ayi dasu idan kuma sunje daga mu sai mazajen mu ne za'ayi.


ALHAMDULILLAH!!!

Masu karatu anan na kawo k'arshen wannan labarin nawa mai suna SONEE SILAR KOMAI.

Ina fatar kuma ya k'ayatar da ku kuma za'a faɗakartu dashi A wa'azantu a kuma nishaɗantu.
Ina fatar samun goyon bayan ku dan shi ne zai k'arfafe ni domin cigaba da zak'ulo muku labarai masu k'ayatarwa.


Sai n afito muku a..............

Muje zuwa tare da alk'alamin


FA'IK. 🙏🙏🙏
Chapter 40 · 0% Book details