← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 40

Chapter.....12

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍️


INA YIWA.....


Ɗaukacin Al'ummar Musulmi BARKA DA SALLAH!!! ALLAH Yakarɓi Ibadarmu Yasa Kuma Mun Rabauta Yakuma Nufi Musake Ganin Wani Azumin Cikin Rai da Lafiya 🙏.


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


Not Edating.... Cos Am 2 buzyyyyy. 🙏🙏🙏.


Suna Cikin Wannan Halin Abubakar yafaɗo Gidan Cikin Tashin Hankali Yanufi inda Suke Yana "Innarmu meyafaru? Meyasa meshi? "


Cikin Kukan da Yasuɓucewa Innarmu Tace, "Bansani ba Auta Kawai naga Yashigo min Cikin Wannan Halin." Yayinda Shikuwa Abdul-wahab Bakinsa Bai daina Ambatar "Kasheni Zatayi Innarmu!! Hauka ta ni Zatayi Innarmu!!"


"Kama minshi Mukaishi Asibiti Ni Nashiga Ukku na Lalace..... " harta Nufi ɗaki Sai kuma Tadawo tana Cewa, "Abdul-wahab Ko Gamo Kayi? " Innarmu dae keta Sambatu Wayanda ke Nuni Ta ruɗe Yayinda Shikuwa Abubakar Yaɗauki Abdul-wahab Ɗin Zuwa ɗakin Innarmu.


Innarmu tabiyo Bayan shi Tana Cewa, "Wane Ɗaki Zaka Kai shi Kai da nake Cewa Kaje ka samo mana Abib Hawa Mukai shi Asibiti." Abubakar yajuyo ga Innarmu Sanda Yashimfiɗe Abdul-wahab Saman Shimfiɗar dake Tsakiyar ɗakin na Innarmu Yace, "Innarmu ki Natsu Wannan lalurar bata Asibiti Bace Bani Ruwa cikin Cupi ki Gani. "

Cikin Azama Innarmu tajuya taɗebo Ruwan Bakinta kuma bai Futa da Kiran ALLAH ba. Tasami Abubakar Rike da Abdul-wahab Ɗin yana ta karanto Adu'o'i yana Tofa Masa Yakarɓi Kofin Yasoma Karanto duk Wata Adu'a da yasani ta maganin Ƙunci Yana tofawa Acikin Kofin Yakaranto ayatul kursiyu Falaki da Nasi da Ikhlas Tareda Adu'a Annabi Yusuf (AS) sanda Yashiga Kurku da Kuma Adu'a Annabi Yunus (AS) Sanda Yashiga Cikin Kifi da duk Wata Adu'a da Yasani Sannan Yashiga Shafa ma Abdul-wahab Ajiki Musamman Saman Zuciyarsa Take Abdul-wahab Yayi tsit Yana maida Numfashi Ya runtse Idanuwansa Tamau Yan Tsirarun Hawaye Nata Sulmiyowa Tacikin Idonsa.


Abubakar Yamike Yaɗauko Hisnul muslim Yabudo Masa Dai-dai Shafinda Yake Magana Akan Adu'ar Tafiyar da kuncin Zuciya da Damuwa Yamiƙa Masa Babu Musu Abdul-wahab Ɗin yasa Hannu yakarɓa yasoma Karantawa.

Yayinda Innarmu Takoma gefen Gadon ta tazauna Tana maicigaba da Tasbihi ga ALLAH tana Mai Ƙara Godiya ga ALLAH da Yaba ta Ikon Tsayuwa Akan 'ƴaƴanta Har Sai da Sukayi Karatun Isilama.

Abubakar Yamike yana mai Cewa "Bari ni Inje Inɗan Watsa Ruwa Innarmu dama Nashigo ne Inshirya Zamuje dubin Baban Aliyu Asibiti Nida Abokanamu. "


"Ayyah! ALLAH Bashi Lafiya, Amma Kafin katafi Yakamata Kaci Abinci dan tun ɗazun na Kamallah."

Abubakar Yadawo Yaɗauki Flet Yana Cewa, "Kuma Hakama dae-dae ne Innarmu. Dan dama Yunwa Nakeji Kawai naɗauka baki gama Bane. "

"A'a tun ɗazu na 'ida. Daddawar da Zan Aikawa Auntynku Nake Shanyawa Yayanka Yashigo min A firgice."

"ALLAH Ya kyau ta." Abubakar Yafaɗi Hakan Yana mai Zama Kusada Innarmu Bayan Yazubo Abincin.


"Tau Ameen, Amma Yayanka Yahaɗu da lalura ALLAH dae Ya yaye Masa."


"Allahumma Ameen Innarmu. " Haka dae Sukaci gaba da Tattaunawar Akan Matsalar ta Abdul-wahab Ɗin. Yayinda Shikuwa Abdul-wahab yayi Shiru kamar baya gurin Adu'o,in dake Cikin Littafin Hisnul muslim yake ta Duba wa yana Karantawa har Wani Irin ƙaƙƙafar Bacci Yazo yayi Awon Gaba Dashi. Ita kuma Innarmu Lokaci -Lokaci takan Yima sa firfita da mafefeci Saboda Zufar da yake tayi Kamar Ana kwarara masa Ruwa.


Khaleesat Kuwa.......


Tunda Suka Isa Asibiti Kai Tsaye likitoci Suka Amshe ta Saboda Dama Daddy yabuɗa Masu Fayel A gurin Dan haka duk Matsalar rashin Lafiya ta Taso Su Nan Suke Zuwa.

Momy Kam Sai Safa da Marwah take Ta Kasa Tsayawa Takasa Zama Siyo Wannan Maganin Karɓo Wancan Resit. Bata Taɓa Jin Haushin Rashin Zaman Dady Harma da Ya Nuradden Agarin ba Sai Wannan Karon da Suna nan Ai da Suntaya ta Wannan Zirga -Zirga da kuma Sunyi Raba dae-dae na Wannan Tashin Hankalin.


Bayan gwaje -gwaje da Aune-Aune Sakamako Yafito Likita Yakira Momy Zuwa Office ɗinsa Dan yi Mata Bayanin Abinda ke damun Khaleesat. Momy kamar Zata Kifa Tashiga Ofishi. Wani Irin Zullumi da Bugu Zuciyar ta keyi dahaka Tazauna Kan Kujerar dake Kallon Likitan.

Dr Jabir Naduƙe Yana Yan Rubuce-rubuce Cikin Fayel ɗin dake Gabansa Kafin Yaɗan Kawar dasu Gefe Yaɗago Fararen Idanuwansa da suke Sakaye Cikin Farin glass Yana Kallon Momy


"Kece Mahaifiyar Khaleesat Mustapha?" ya Tambayi Momy.


"Eh....E.. H Eh.. Eh Nice Dr." Momy Tafaɗi Hakan Cikin Tsoron Me Kunnuwanta Zasuji.


Kamar Shima Likitan Yakula da Hakan Kuma Yanga Dama Ɗabi'ar sa ce Kamar Wata Macce. Saida Ya bushi Iska Kafin Yace, "Ki Kwantar da Hankalinki Ba Wata Matsala Bace Mai Girma Tana da Miji?"

"Shikenan Na Bani Na Lalace Yau ni YAWO nagama Yawon Duniya Heeee chinekeee Ere meleko Adaburo." Momy Ke Wannan Sumbatun Cikin Yanke Kauna Cewar Shikenan Khaleesat tagama jawo mata Abin kunya da Abin Faɗe Acikin Ahalinta.

Dr Jabir Yayi Saurin Tushe Kunnuwansa Saboda Wannan Ƙyaƙyar Ta Momy Kafin Cikin Sauri Yace, "Bafa Komai Bane Yasa Natambaya Tana Da Miji Ba Saboda Kinga Shine Suke Tare Dan Haka Shi Yafi Kamata A gayama Dan Yakula. Kuma Olcer ce Kawai takama ƴarki Kuma Tayi Mata Kamun Kwarai Because batacin Abinci Shiyyasa Yanzun Ma Kummalo Yakamata Kingane?"


Momy Cikin Farinciki Tadakata daga Kukan ta Tace, "Olcer?" Dr Jabir Yace, "Eh." Momy Tace "Tau Ai Alhamdullah!" Dr Jabir Cikin Hanzari Yaɗago Yana kallon Momy Yana Mamakin Furucinta. Momy dataga Kallon Da Yake Mata Tace, "Eh Ai da Acemin Ciki Gara Ace Olcer ne Sai Muyi Jinyar Abu Ɗaya." Abin Gwanin ban dariya ma Wallah yanda Momy Tawartsake Kamar ba Ita Ba Sai Bayani Take Korowa Dr Jabir.

Shikam Rubuce- Rubuce- yayi Sannan Yamiko Mata Resit ɗin Tareda Cewa, "Wayyanan Magunguna ne Daza'a Saye Mata Tarika Sha. Wanna ɗayar Allura ce Asiyo Yanzun Sai Inyi Mata. "

Cikin Hanzari Momy Takarɓi Takardun Tanufi Saye.

A hankali Nabuɗe idanuwana Tareda Yin Miƙa Saboda duk Jikina tsami Yakeyi min Ina Mai Kara Tantance Ina Ne Nake? Jin Hannuna Na Tamke Yasa Nabi Wurin da Kallo Har'izuwa Sanda Nayi Tozali da Ƙarin Ruwa Da'akeyi Mani Yayinda Momy Ke gefen Nawa Rike da Hannun tana Cewa, "Yi A Hankali Khaleesat Karki tsinke Igiyar kijiwa kanki Ciwo. "

Bance Komai ba Nakoma Kawai na Kwanta Fuskata Na Kallon Rufin ɗakin Ina Tunano Abinda Yafaru Tsakani na da Abdul-wahab Komai Yana zuwar min Kamar Yanzu ne Wasu Hawaye Suka Shiga Gangaro min Kan Damdamalin Kuma tuna Bandamu da Inshare Su Ba sai Ma Cewa da Nake "Abdul-wahab Kamin Mummunan Fahimta ne Amma Wallahi Bana Nufin Cutarka da ka tsaya ka Saurare ni Kaji Uzuri Na. " kafin Nafashe da Wani Irin Kuka.

Momy Ta taso Tana Cewa "Khaleesat Natsu Mene Yake Faruwa ne? Ko Bakiga Ina ne Muke?"

"Meye Ruwana da ina Muke Momy Ai duk Abinda Yafaru KUNE SILAR KOMAI Wallahi Inba Abdul-wahab ba Bazan Iya Rayuwa da Kowane ɗa namiji ba Nagwammace In Mutu Banyi Aure ba.... "
Shigowar Dr Jabir Yasa Momy tarufe min Baki Tana Khaleesat "Subhanallah Khaleesat Ko Kin Taɓu ne?"

Kasa Cewa Komai Nayi Saboda Ganin Ba mu kaɗai bane Sai Kawai Nayi Juyi Ina Funskatar Bangon ɗakin ina Ci Gaba da kuka Marar Sauti.

Dr Jabir Yafashe wata Yar Ƙaramar kwalba Yasa Sirinji Yazuƙo Ruwan da ke Cikin kwalbar Kafin Ya saita Dai-Dai Yanda yake Ganin Zasuyi Mishi Kafin Yadubi Momy Yana Cewa "ina Fatar Ɗiyar Momy Bata Tsoron Allura?"


Momy Tace, "Wannan Sarkin Rakin? Ai Inaga Sai Annemo Masu Danneta."

Yanufo ni da Allurar Yana Cewa, "Haba ita Tasoma Duk Kwalisar Nan tata."

Nidae Ƙala Bance Musu ba Harsanda Naji Yana Lalubar inda Zaimin Allura Nayi Saurin Miƙa masa Hannuna Nace, "Kamin Anan." Yayi min Wani Shu'umin Kallo Mai Cike da Tarin Ma'anoni Kafin Yace, "Nikam Koda Naji Nasan Yar Momy Jaruma Ce." Yariƙa Hannuna Yamin Allurar Sa'annan Yajuya ga Momy Yana cire Handglos(Safar Hannu) ɗinda ke Hannunsa Yana mai Cewa, "Zuwa Anjima Ruwan Suka Kare Zaku Iya Tafiya Gida Insha'allah. Sai dai Dan ALLAH Yar Momy.... "


Yajuyo Gareni, "Ki Kula da Cin Abinci Saboda Karki Jamana Asara Muda Su Momy."

Nai Masa Kallon Kai A Suwa Tau? Kafin Najuya Naci gaba da Lugwaiguwata Wurin da Yamin Allurar dan Nasan Bakaramin Jarumta nayi Ba Dan dai Kawai Ina cikin Damuwar da Tafi Ta Allurar ne Kawai Da Sai Mun kwashi Yan Kallo Nasani saidai A Wannan Halin da nake Ciki Ba Allurar ba Komeye Za'ayimin Banajin Girman sa Yakai Girman Halin da Nake Ciki.


Shikam Dr Jabir Juyawa yayi yana duban Momy "Ko ba Haka bane Momy? "

"Ah Tau Ai Tasani kam." Momy ke Mayar Masa Da Amsa.

Yahaɗa Kayan Aikinsa Yana Cewa, "Tau Gara dae Ta kiyaye Inba Hakaba Aka Saki Kawo ta Asibiti Rike ta Zamuyi Sai Nan da Shekaru Aru-Aru Mun Tabbatarda Tayi Sabo da Cin Abinci Sannan. Mubata Sallama."

"Dadai Yafi." Momy Tabashi Amsa.

Yajuya Yafice Yana Cewa, "ALLAH ya sauwaka Momy. Na lura Yar Momy Bancin Olcer Harda Ciwon Baki Tana Fhama dashi. "

"Momy Wallahi Bazan Jira Ruwan Nan Yakare Gida Zamuwuce Haka Kawai."


"Ke! Kya Soma Ma. Dole ma kijira Ruwa Nan Ya..... " Wayar ta ce Tai Kara Dan haka takatse Zancen da Take. Ganin Dady ne Tayi Saurin Ɗaukar Waya Tasoma Kwararo Masa Bayani Ina Yashiga Tai takiran Wayarsa Bai ɗaga ba?

Duk-da Bana A Yanayi Mai Daɗi Sai da Nayi Dariyar Momy.

Araina Nace, "Momy Na Hoe!😁"

Ina jin Su Suna Magana Dady Har Sanda Yace Mata Tabani Wayar Tabani Muka Gaisa Yamin Yajiki Sa'anan Yaɗora da Cewa "ALLAH Ya sauwaka Ina Nan Tafe Cikin Satinan Insha'allah."

"Ameen Dady ALLAH kuma Yakawo ka Lafiya." Nafaɗi Hakan Ina Mai Miƙawa Momy Wayar Ina Jin Sanda Yake Cewa Ameen. Suka ɗan Taɓa Magana Yayi Ma Momy Sallamar Tareda Sanarda Ita Ma Kamar Yadda Ya sanarmin Watau "ALLAH Ya sauwaka Ina Nan Tafe Cikin Satinan Insha'allah."

Basu Jima Da Gama Waya Ba Kiran Ya Nuradden Shima Yashigo Wayar Momy. Taɗaga Shima Suka Gaisa Kafin Tagayamasa Cewa Nice Bana jin Daɗi Muna Ma Asibiti. Yace, "Subhanallah Meyasa meta?"

"A'a Ai Da Sauki Gata Ma Kwayi Magana." Momy tafaɗi Hakan Tareda mikamin Wayar.


Ina Karɓar Wayar Nafashe Masa Da Kuka Nantake Yakara Ruɗewa "A'a Lafiya Me Yafaru Khalee
(Sunan da Yake kirana Dashi Kenan).


"Ya? Maganar Bazatayu A waya ba Dan ALLAH Kasamu Kashigo Ina Cikin Matsa..... " Momy Tafisge Wayar Tana Hararata Kafin Tasoma Magana dashi Shikuwa Sai Tambaya Yake "Please Momy Meyake Faruwa Ne? Dan ALLAH Ku..... " "Kaga Fa Karka Wani Tashi Hankalinka Taɓara ce Kawai Ta Khaleesat. Amai Takeyu Muka Zo Asibiti Shine fah Likita Yake Gayamana Olcer Ce Tamana Mummunan Kamu Kuma Yama ce Da Ruwan Da Aka ɗora mata Sun Kare Zamu Iya Wucewa Gida. " daga Can Ya Nuradden Yasauke Ajiyar Zuciya Kafin Yace, "Tau ALLAH Bata Lafiya Maganar Kuɗi Fa? Ko Zanturo Maku Ne?"

"A'a Likita Yayi Magana da Dadyn ku Kuma Inaga Harsun Gayamasa Abinda Suka Caje Mu Ya kuma Turo Masu."


"Tau ALLAH yasauwaka Sai Nakira Ina Gurin Aiki Ne."

"Tau Shikenan Badamuwa." Momy Tasauke Ta Soma Min Faɗa Kamar Ba Wacce Ake Jinya ba. Wai Bana da Hankali Ina Legos Ina Sakkawato Da Zan Tayar Masa Da Hankali Haka?

Inda Tashiga Banan Take Fita ba Nidai Bantan ka ba. Nayi Shiru Kawai Ina Sauraren ta. Gefe daya Na zuciyata Naci Gaba Sanarmin Shikenan Fa Narasa Masoyina Abdul-wahab.

Da Sauri Na zabura Ina Faɗin, "Ina Bazai Taɓa Yuwa ba Abdul-wahab Nawane Nikaɗai Nima Tasa ce Shi Kaɗai An hallicemu Dan Junan Mu Kawai." Lamari Na Sai Yakoma Ba Momy Tsoro Yabar Bata Haushi Tashiga Karanta Duk Wata Adu'a da Tasani Tana Tofamun.

Da Wannan Naɗan Natsu Nayi Lamo Kamar Mai Bacci Saidai Idanuwa Biyu Kawai dai Naɗan Samu releaf ne Nafaɗa Duniyar Tunani. Harsanda Ruwan da Akemin Ƙari Suka Kare Momy Takira Wata Nos Da Nufin Tazo Taciremin Amma Saiga Dr Jabir Kamar Wanda Aka Jefo Yace Taje Abunta Zai Ceremin Bayan Yacire Mun Saida Yatabbatar Yasa Mana Abun Hawa daga nan Cikin Harabar Asibitin Tasu Yabiya Kuɗin Sa'annan Yajuya.

Wannan Karon Ba'a Wata Magana da Yayi Sai Ayyukan Sa dake Nunawa Girmamawarsa Garemu. Momy Kam Sai Godiya Takeyi Masa Iya Godiya. Sanda Zai Wuce ne Yajuyo Yamin Wani Irin Kallo Natsakar Ido Wanda Saida Naji Tsikar Jikina Ta Tashi duk yanda Naso Watsi Da Sakon Nasa Sai Nagagara Sai Kawai Nasame Kaina da lumshe Idanuwana Da Sukayi Luhu-luhu Saboda Kukan Nake Tilas tasu Dashi.

Ganin Saƙon Nasa Yasamu Karɓuwa Yajuyawarsa Cikin Tafiyarsa Ta Ingarman Namiji Yana Wani Shu'umin Murmushi Wanda Shi kaɗai Yasan Ma'anarsa.


Yayinda Mai Kk Napep ɗimu Yaja Muka Soma Tafiya Nalura Dr Jabir Miskili ne Na Bugawa A Jarida Kuma Daga Ganin Sa Dan Babban Gida Ne Kuma Kai Kasan Ilimi Yazauna Masa Sosai Ga Wasu Kyakykyawan Id... Subhanallah Meyake Shirin Faruwa Danine Ina Kuma Ruwana Da Dr. Jabir? Babu Shakka Wannan Kawai Sharrin Shaiɗain Ne. Dan Haka Nai Maza na Kawar da Tunanin Sa Ina Yin Istigfari Kamar Wacce Tayi Saɓo Ina Cewa Ni Ta Abdul-wahab Ce!! Wata Zuciyar Tace min "Tau Dama Yace Yana Sonki Ne? " Kawai Sai Nasami Kaina da Fashewa da Wani Irin Kuka Mai ɗaci Nasanya Hannaye na Afuskata Nadurkar Da Kaina Akan Cinyoyina Ina Mai Cigaba da rero Kukan da Nake Ganin Bani da Wani Abu Mafi Soyuwa Sama Dashi Mai Kk Napep Yaruɗe Yana "Subhanallah Mama Lafiya? "


"Bata da Lafiya ne. " Momyn Da Yatambaya Tabashi Amsa Cikin ɗacin Rai Akan Tonon Sililin Danake Mata.

Yajuya Yaci Gaba da Tuki Tareda Cewa, "ALLAH Sarki, ALLAH bata Lafiya."

Momy Tace, "Ameen."


Tirkashi! Ana Wata Ga Wata Ana dara Ga dare Yayi Inji Yan Caca Tau Waye Dr Jabir? Meye Kuma Manufarsa Akan Khaleesat? Duk-da Ma Khaleesat Tayi Hanzarin Cewa Itakam Nan Duniyar Sai Abdul-wahab Domin Junansu Kaɗai Aka Hallicesu Tau Amma Kuma Ai Baice Yana Sonta ba(Inji Khaleesat ɗin) Saidai Nikuma FA'IK Nace Inkaga Kare Na Shinshinar Takalme Tau Ɗauka Zaiyi. Kawae Readers Muci Gaba da Bibiyar Labarin SONE SILAR KOMAI dan Babu Shakka Akwai Tashin Sanse! Tsantsar Soyayya Tsagwaronta Da Kuma TAUSAYI ga Rayuwar Khaleesat harma da Shi Shalelen Nata
Abdul-wahab Kudai Muje Zuwa Har'izuwa Matsayar Domin dae Komai nada Iyaka In Banda Ikon Jallah Sarkin Sarauta Dan Haka Ni FA'IK Nayi Gaba Da Alkamina Izuwa ga Fage Nagaba

👇👇👇👇

..........
[9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 10 · 0% Book details