← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 15 OF 40

Chapter.....17

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem

Shi Kanshi Yalura da Yadda take Cika Tana Batsewa dan haka sai Kawai Ya yanke Shawarar Bari Yatafiyar sa Kawai Yabarta Harta Huce, Sai dai Yana Juyawa Yaji Tafashe da Wani Irin Kuka Mai Razana duk Wani mai Sauraren sa Yadawo Da Hanzari Tareda Cewa, "Subhanallah Maman Ashraf Meyayi Zaf...."

"Kada Kataɓa ni!" Tafaɗi hakan Cikin Muryar Kuka.

"Haba Maman Ashraf! Wai Meke damunki Ne daga jiya duk Nakasa Gane Kanki Ne? Kinbi Kin ɗaga Mana Hankali?"

"Oh Nine Ma Naɗaga Mana Hankalin? Tau Shikenan ai." Tana Faɗin haka kuma Tajuya cikin Hanzari Tabar Kitchin ɗin.

Har Yabita Kuma Yasake dawowa Sai da Yakashe duk Wata Na'ura data Kunna Kafin Yafito dan Zuwa ɗakin Nata Yaji Meye Matsalar ta ne? Amma me Sai Ganin ta Yayi Ɗaɗɗake Da Akwatin Kayanta Ta Nufi ƙofar Falon tana Kuka. da Hanzarinsa Ya'isa Gareta Yakama Hannunta Yarike. Duk Ƙokarin da Tayi na kubcewa Riƙon Nasa tagagara Dan ƙarfin ba ɗaya ba dan Haka Sai Kawai Tazube Gurin Tana Kuka Sosai! Dr Jabir yarasa ta'inda Zai Soma dan Haka sai Kawai Yatafi Ya murza Wa Ƙofar Falon Nasu Key, Yajefa Key ɗin Cikin Aljihunsa Wanda Hakan da Yayi Yaƙara Fusata Maman Ashraf Tasake Zabura da Duk Karfin ta tana Faɗin "Ni Wallahi Gida Zani."

"Tau Gida Zakije Dalili ne Na Sai kin tadawa Mutane Hankali? Ko Sanda Kika Saba Zuwa Gidan Sai Anyi Yaƙi Ne?" Dr Jabir Yafaɗi Hakan yana kallonta A wannan Karon Shima yaɗan Soma Hasala da Ita.

"Ni ban tambaye ka Wannan dogon Jawabin ba Kawai Nace ma Gida Zanje dan...... "

"Tau Bazaki je gidan Ba Inke kike da Iko da Kanki Sai Inji."

"Ni kuma Wallahi Sai Naje." Tafaɗi Hakan Kana Takwa so Sauri Ta Nufi Kofa Sai ta tuna Ai Yarufe, dan Haka sai ta zube Bakin Ƙofar Tacigaba da Kuka Mai tsuma Zuciya Wanda Yayi Sanadiyar Tashin Ashraf daga Bacci Shima Yazo Yarumgume ta Yana Kukan Duk Sai Suka Sukurkucewa Dr Jabir Zuciya, Yayi Tsaye kawai Yana Kallon Su Kana Yana Tambayar Kansa Dama Su Mata Duk Hankalin Su In Aka Zo Maganar KISHI Sai Ka Nemi shi Ka Rasa? Wai Wannan Ma Mai Saukin Ce Saboda Maman Ashraf ce Kuma dama can Ita bamai Surutu Bace Kuma bata da Tsiwa, tau Yanzun da Mai Tsiwa ce Fin Haka ma Kenan? Cikin Rashin Kuzari Yatako Zuwa inda Suke durƙushe Ita da Ashraf Suna Aikin Kuka Yace, "Wannan Aikin Bai Kama ceki Ba, A Nawa tunanin Ba'abin da Yafi Karfin Fahimta Kuma A Sani na Muna da Wannan Agender Kafin Komai Yakamata Ki Gayamin Menayi Maki Maman Ashraf?" yadan yi Shiru Yana jan Fasali Kuma ga dukkan Alamun Maganar tasa tayi Tasiri Acikin Zuciyar Gimbiyar tasa dan haka Sai Yaƙara Kwantar da Murya tareda mai da kansa Kalar Tausayi yasoma Rattabo Mata Jawabi Wanda Afakaice Lallashinta Yakeyi, Hardai Yasa tattausan Hannun sa yana Share Mata Hawaye kafin Yariko Hannunta Yajawo Akawatin ta gefe daya Ashraf Nabiye dasu Shima tunda Mahaifiyar sa Tayi Shiru Shima Sai Yayi Shiru.


Kan Kujera Suka Zauna Yana Ci gaba da gayamata Muhimmanci ta Acikin Rayuwarsa, da irin yanda Yakamata Su riƙa Fahimtar Juna Idan Irin Wannan Matsalar ta taso, yakare da Cewa, "Kin Fahimce ni Maman Ashraf?" Takasa Yin Magana sai dai Girgiza Kai kawai Alamun dae "Eh! "

Yace, "Yawwa Tawan, izuwa Yanzun yakamata Kigane Cewa Bazan iya Rayuwar da babu ki Acikin ta ba. dan haka ki daina ɗaukar Rabuwar mu Abu ne Mai Sauki Ko Yiyuwa, kawai Inna miki Laifi Zaunar dani Ki Sanar dani Nikuma bazan ƙi Gyarawa ba Kin Gane?" Nan ma Girgiza kai Tayi yace, "Ba Girgiza kai Zakiyi ba, Baki Zaki Buɗe Muyi Magana."

Taɗan Share Hawaye Kafin tace, "Amma kai Kana ga kayimin adalci Yin tarraya da Wata Bayan duk wata kula da ta kamata ina Ƙokarin ganin Nabaka ita hakanan duk wani Abu Dakake So Inayi. ka gayamin da me narage ka harda wata zata janye hankalin ka harka kazo Kana ta min mafarkin ta da Sumbatun Kiran Sunan ta?" takarashe Maganar tana tsura masa ido wanda ada can bata iya yin hakan.

Dr Jabir yasami Kansa da jin Kunyar ta har hakan yasa ya rusunar da kansa ƙasa Cikin Nazarin Wace Amsa zai bata zai ce matane Wacce zai Aura ce? In har yace Wacce zai Aura ce Wace Hujja gareshi Na Iyayenta Sun bashi Aurenta? Ko zai ce Wadda yake So ne? Anya in yace Haka Cin Fuskar bai yi Yawa ba? Kuma ɗan Shirin da Suka Soma Yanzu bazai lalace ba? Haka dae yajima cikin Nazarin hardai Yazaɓi Kawai yabata Hakurin Kawai, dan Haka yaɗago kan Nasa Haryanzun Shi take kallo da Kumbararrun Idanunta Cikin Sanyin Murya Yace, "Ban kyauta ba, kuma kiyi Hakuri Insha'allah bazan ƙara ba." yakarasa Maganar yana mai haɗe Hannayensa guri ɗaya Alamun Ban Hakuri. Maman Ashraf Ta kawar da kanta Cikin Nazarin Duk Sanda Dr Jabir yace zai haɗa ta da Wata matar Mutuwa kawai zatayi, dan tana ji A ranta Cewa bazata iya raba dae-dai Akan Mijinta da kowace Macce ba.


"Yakikayi Shiru ko Haryanzun baki Huce ba?" yafada Cikin ƙara Sanyaya Muryar sa.

Tace, "Nahuce Yawuce Kuma."

Yamike yadawo kusa da ita Yana mai kara Share mata Hawayen da takasa tsai da wa yace, "Tau Ya'isa Hakanan Kinji?" ta sake Girgiza kai Yaɗan Sake Kallon ta Yace, "I Love You my NURUL KHALBI!" shiru Kawai Tayi Masa Yasake Cewa, "Ko Baki Huce Bane? Yakamta Kiyi Murmushi Dan in tabbatar."

Haka dai yayi ta Amfani da dubaru yana Lallashinta har sanda ya tabbatar komai Yawuce, sannan Yamike yaje ya shirya A gagauce. Koda Yafito harta Shirya Ashraf Cikin Uniform din skull dinsa. Braek kaɗai ne Bata Kamallah ba, tana ta Ƙokarin taga komai ya kamallah. Yadan gyara Wuyan rigarsa gamida Cewa, "Inaga yau Mun Makara Maman Ashraf Babu Lokacin da Zamuyi Break." tace "Haba dae Na kusa Kamalla wa Fa, Dan ALLAH Kujira, Shi Ashraf ban sa Masa Komai A Coolern sa ba fa?" Yasake Duban Agogon dake ɗaure A tsintsiyar Hannunsa Yace, "30 minute Kawai Muke da Kina ga zai Samu Kafin Lokacin?" Tayi Hanzarin Nufar Kitchin ɗin Tareda Cewa "Bazai ma kai Lokacin ba insha'allah Just One minute."

Cikin yan mintocin ƙalilan Ta Wadata su Da Break ɗin, tayi Savin ɗin su Cikin Matukar Kula. Wanda Yaƙara Tabbatarwa da Dr. Jabir cewa Ba Shakka Kwanciyar Hankalin Iyalin sa Shine Nashi Kuma Farincikinsu Shine Nashi.


*********

Yauma bayan Yataso Aiki Sai da Yabiyo Ta Gidanmu Kuma dai Na'isar Masa da Saƙon Dady Kuma Yayi Farinciki da jin Hakan Yayi Mani Alkwalin Cewa Cikin Satinan Zasu Iso Insha'allah.

Munsha Hira Sosai Wacce taƙara tabbatar min Cewa Lalle shiɗin Na Musamman ne Ko Acikin Maza, kuma Zan iya ƙare Rayuwa ta Tareda shi. Ban taɓa Yardar wa kaina Cewa Ma Wai yana da Aure ba. Ni kwai Abinda Nabarwa Raina Harga ALLAH, Dr Jabir Saurayi ne. Shima Kuma bai min Magana makamanciyar Wannan ba. Tau haka dai Kuka Rabu Cikin Wata ƙauna da muhimmancin sa da yasamar Acikin raina.


Ina shiga gida Na kimtsa Nayi ma Momy Sallama Kafin Na nufi Gurin Saloon dan Raben da In wani gyra kaina Harna Manta. Dady yaɗauko kuɗi Yabani harda na Kk Napep Tareda gargaɗin Kar na daɗe.


******


Bayan Sunfito Sallar Isha'i Shida Abubakar ne da kuma Abokin sa Yusuf da Yadira A garin Yau. Sune ke zaune kan Barandar gidan ta su Abdul-wahab ɗin Suna ta Firar Bayan Rabo, Yusuf yana ta basu Labarin Kudu da kuma Yanayin Al'adunsu. Wasun suyi ta mamaki wasun Suyi dariya, har zuwa sanda Jibril Abokin Abubakar yazo yajanye shi Suka Shige Suma Yin Sabgogin su, Suka Bar Yusuf da Abdul-wahab Nan nata taɗi Irin Na Aminan Juna. Acikin Firar tasu ne har Suka sauko Kan Abinda Yadanganci Tsakanin sa da Khaleesat Inda nanne Yusuf ke Cewa, "ya labarin Mutumniyar Taka Khaleesat?" da Yusuf Yakula yanda Abdul-wahab ɗin yahaɗe Girar Sama da Takasa da Yabar Zance tau amma da yake Bai Kula ba sai yaci Gaba da Cewa, "Abokina Wallahi Kai kam Kayi dace da Mai Sonka tsakani da ALLAH. ALLAH Yasa Nima Maryam ɗita Zata Soni Kamar Haka!


Kai kaga yanda Khaleesat ke faɗin Tashin Akan Soyayyar ku takai Labari Akan fa An....."

"excuse me! Excuse me!!" Abdul-wahab Yafaɗi Yana ɗaga Masa Hannu Kafin Cikin Fusata Yaɗora da Cewa, "Kaga Mal Karka Cika ni da Surutun wata Khaleesat kai ka Santa. Ni ban san ta ba."


Yusuf Baki Yasaki Galala yana kallon Abdul-wahab Cikin Mamaki Kafin yace, "Abokina Lafiya? Kardai kacemin Haryanzun komai bai Wuce ba a taksanin ku?"


"Bai Wuce ba, ba kuma zai taɓa Wuce wa ba indae Akan Wannan mayaudariyar ce."Abdul-wahab Yafaɗa Cikin ɗacin Rai!

Yusuf Yace, "Amma ko Abdul kacuci Khaleesat kuma kai butulu ne Wallahi, kuma kasani ALLAH zai Saka Mata ha...."

"Ya'isa! Yusuf ya Isa! Menayi Mata?" Abdul-wahab Ya tambaye sa Kamar zai tashi yashaƙe sa.


Yusuf yace, "karka manta irin son da Khaleesat takeyi maka Abdul. A kanka ta saɓa da Iyayenta Akan Ance ba'a yin Auren ku da ita, Saboda baka da madogara Khaleesat tashiga tafita tadinga tatsar masu kuɗi dan kawae ta tara ma kuɗɗin da zaka ka tsayu A Ƙafafun ka. Abdul Akan Soyayyar ka Khaleesat ta kwana Kuka tayi Jinya Sa'annan ƙarshe tazo tana Bibiyar ka Amma kaƙi Saurarata ka koreta da Wulakanci.


Kana ganin Haka kamata Adalci Kenan? Kana ganin A irin Wannan Lokacin da Zamanin Namu Za'a samu masoyiya Irin ta? Meya Haɗani da Na'ima tawa Lokacin Eh?" Yusuf yaɗan Tsagaita Cikin runtse ido yanajin wani bakinciki Na Taso masa kamar Lokacin ne abunda tayi masa Yafaru, kafin yamatso kusa da Abdul-wahab da yayi Shiru, yadafe Kansa dake Sara Masa kamar Zai rabe gida biyu, yana ji wai Akan sa Khaleesat Tayi Abinda tayin dan ta Samar masa kuɗi tunda Anyi Masa gorin baya da Kuɗɗi. Tau Amma meyasa Taƙi kulashi A Wancan Lokacin Meyasa Kuma Bata gaya ma....


Yusuf yakatse masa Tunanin sa ta hanyar Cigaba da Cewa, "Na Sani tayi Wauta Akan Abinda Tayin, Wanda ita Ana ta Kuskuren tana ga shine zai sa ku mallaki Juna A Matsayin ma'aurata, Amma Abokina mezai hana kadubi Girman So da takeyi maka? Abdul!...."
Yusuf yaɗan Tsagaita kafin yaɗora da Cewa, "Wallahi Wallahi kaji na Rantse ma? Khaleesat na sonka kuma idan ka rasata bazaka sake samun Wacce take maka makamancin Son da takeyi Maka ba, duk Abinda Tayi tana gayamin kuma ina da labarin Komai, kawai Bangayama Ne ba, Saboda ta gargaɗeni Akan cewa Tagayamin Amana ce, Sannan ko A Sanda tazo gida da safe Ni Na kawo ta Sbd irin magiyar da tayi ta yimin da Irin tabbatar war da nayi cewa itaɗin mai sonka ce tsakani Da ALLAH.


Dan haka Katsaya ka ƙara Nazari, A Rayuwar nan babu wani DACEWA irin ka Auri Wacce ke Son ka, Domin itace wacce zatayi hakurin Zama da kai Acikin Kowane Yanayi, itace Wacce Zata Riƙe ma Amana, kai itace zatayi duk wani abu da zai faranta ma Albarkacin Wannan Son da Takeyi ma, dan haka Abokina Ka gode ma ALLAH da yahaɗa ka da masoyiya ta haƙiƙa,kuma ka gaggauta Zuwa gareta dan ku SULHUNTA."


Readers ɗina Anan zan Numfasa muje daku A gaba dan jin yanda Tirƙa-tirƙar zata Kaya dan dae Akwai KWAMACALA Harma da BADAƘALA!!!! Dan haka Muje Zuwa Nidae nayi gaba Acikin Littafin na SONE SILAR KOMAI.........
[9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 15 · 0% Book details