← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 25 OF 40

Chapter.....27

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


Yusuf da Jikinsa Shima yayi sanyi Yace, "Kadaina Tunanin Hakan Auta Insha'allah Zaiji Sauki. Damuwa Ce Kawai Tasashi Haka Bi'iznillah Zai Warware, Kaidai Kawai Muyi ta Adu'a ba Abunda yagagari Ubangiji."


Abubakar Yacire gilashin da ke Fuskarsa Kafin Yasa kyalle Yashare Hawayen da ke Zubo Masa Gamida Cewa, "Insha'allah Muna Fatar Hakan Yaya."


"Yawwa Auta Sannan dan ALLAH kadinga Ɓoye Damuwar ka Saboda Kaine ƙwarin gwaiwar Innarmu Kaine kuma Mai Lallashinta Kaga In Kaima Aka Gagara Samun Hakan daga Gareka Damuwar Sai tayi wa Innarmu Yawa." Abubakar Yagirgiza Kansa Yanajin Tabbas Abinda Yusuf Ke Gayamasa Gaskiya ne.


"Ina Maman Walida Kun Sanar Mata ne?" Yusuf ya Tambaya


"Eh Tana Ma Kan hanya! Nama kirasun ɗazun tace Suna Dai-dai Lambar Tureta."


Yusuf Yace, "Ah Sun Kawo ma Yanzun ma Zaka ganta Sun Iso. ALLAH Yakawo su Lafiya, Bari Inje Suna jira na Anjima Zandawo Insha'allah."


"A'a Ya Yusuf Kai Zaman ka dan ALLAH Zirganiyar Ai Tayi Yawa!"


Yusuf Yahararesa tareda Cewa, "Amma ma Kaɓatamin Rai Auta. dan Ma Ga Ayanayin da Abun Yazo da Akwai Wanda Zai Zauna da Abdul-wahab ɗinne Sama dani? Pls karka Sakemin Irin Wannan Zancen Bana so!"

Abubakar Yace, "Dan ALLAH kayi Haƙuri Ya Yusuf ban Faɗa da Nufin ɓatama ka Rai ba Nima Yanayin ne na duba."

Yusuf Yace, "Duk-da Haka Nidai. Amshi Ga Abinda Ke Hannuna Koda Za'a Buƙaci Wani Abun." Har Abubakar Yatashi Cewa Yabari Amma da Ya tuno Yanda suka kwashen Yanzun. gudun Sake Wani Laifin Sai Yasa Hannu Yaƙarɓi Kuɗin Gamida Cewa, "ALLAH Yaƙara buɗi Ya Yusuf Yakuma bawa Abdul-wahab ɗinmu Lafiya Yakuma Fitar Masa da Wannan Masifaffen Son A Ransa Ya Bashi Wata Yarinyar Wadda Tafi Wannan da Yake So."


Cikin jin daɗin Adu'ar Tasa Yusuf Yarumgumo Kafaɗar Abubakar ɗin Suka Nufo Inda Abokan Nasu Shida Abdul-wahab Ke Jiransa Yana Cewa, "Ameen Autan Innarmu Autanmu Muma, Amma Kadaina Zargin Masifafen So Ne ALLAH Kaɗai Yasan dalilin sa Nayin Haka Kuma Ƙiyayya ma Tana da tata Ranar Balle Kuma Soyayya dan Haka Mu kyautata masu Zato Mu Kuma bisu da Adu'ar Fatar Alkairi daga Shi har MARIGAYIYAR Kaji Auta?"


Abubakar Yagirgiza Kansa Cikin Gamsuwa da Maganar ta Yusuf ɗin.

Yusuf yaɗan Bubbugi Kafaɗarsa Gamida Cewa, "Yawwa Sai Anjima!"

Nandai Sukai Hannu da Yusuf Tareda Sauran Abokan Yana Mai Yi Musu Godiya daganan Yajuya Yabarsu Suna Ƙokarin tayarda Ababen Hawan Nasu dan Su Wuce.

Tafe Yake Yana Tambayar Kansa Kan Maganar da Yusuf Yai Masa Wai Ƙiyayya ma Tana da Tata Ranar tau Ta Ina? Can Cikin Kunne sa Yaji FA'IK Na Raɗa Masa Cewa, "Maganar Yusuf Gaskiya Ce dan In Ana Nuna Ma Ƙiyayya Kafi Sanin Ciwon Kanka dan Bazaka Yarda kai Abinda Zaisa Maƙiyan Nan naka Suyi maka Dariya ba."

Afili Abubakar Yace, "Hakane kuma Fa!" Kafin Yajawo Wayarsa dake Cikin Aljihu tana ta Ringin Number Maman Walida Ce yagani nata Yawo Kan Fuskar Wayar Tashi dan haka Yaɗaga Tareda Yin Sallama Bayan Ta'amsa Masa Sallamar Take Sanar da shi Gata Cikin Asibitin Suna ta Wane Waje ne? Jin Hakan Sai yajuyo zuwa bakin Gete Yana mai Yi Mata misalin Inda Zasu Haɗu.

Tau Abdul-wahab Nima dai Nace ALLAH Yabaka Lafiya Saidai Anya Zaka Samu Wacce Kafi So Fin Khaleesat? Tau Bazan ja ba Tunda ALLAH Aka Ce.


***********

Gidan Makokin Fa?


Ga Alama Yau Ake Adu'ar Ukku dan Taron Yau Yafi Na Kowane Lokaci Ga Kuma Malamai Nan Sai Ƙus! Ƙus! Sukeyi Atsakanin Su Alamun dai Yaza'a Tsara Abun?

Can gefe Na Hango Dady Zaune Riƙe da Carbi Yana ta tasbihi Cikin Kwana Ukku duk Yazube Kamar Wanda Yayi Shekara yana Jinya. gefen sa Ya Nuradeen ne Ke Zaune Shima Sai Aikin Kallon Mutane Yake.

A iya Cewa Yama fi Dady Ramewa dan shi Harda Ɓaki Yayi Kuma Har Yanzun Idanunsa Basu daina Zubar da Hawayen KEWA Da SABO ba yana dai Ƙokarin ɓoyewa Mutane ne Halinda Yake Ciki! Ƙara Tambayar Kansa yake Shikenan fa dai Dagasken Khaleesat ɗinsu Ƙanwarsa Abar Ƙaunar sa da Baya da Wata Ƴar Uwa sai Ita ta tafi Tafiya kuma ta Har'abada Tabarshi Shikaɗai Ba Ƴa ba Ƙanwa.


Nan take Yashiga Karanto "Innalillahi waa inna Ilaahin Raaju'un." Karanto tan da Yakeyi Sai Yasamu Nutsuwa.


Cikin Gidan Na Nufa Inda Matan Suke Birjik! Momy ce Zaune Tsakiyar Yan Uwanta da Abokai Harma da makwabta tana Cikin Hijab Hannunta Kuwa riƙe Yake da Carbi Duk wanda ya San Momy Yakuma ganta A Yanzun Tabbas Zai shaida Cewa Ba kaɗan Mutuwar Ta Taɓata Ba dan ta Rame Sosai Haryanzu Kuwa idanun ta Basu daina Zubar da Hawaye ba.


Daga Wajen dai ɗan Aike Yashigo Yana Sanar Musu da Cewa Za'a Fara Adu'a. dan haka Kowa Yanutsu daganan Cikin Matan Wata Malama Tasoma Karanto Adu'o'i Masu Ratsa Zuciyar duk Wani Mumuni.


A Can ma Wajen hakance Takasance Wani Malami Yasoma Kafin Yaba Ma Wani Shima Yayi Tasa.


Haka dai Aka Kammallah Adu'ar Cike da Alhini daganan Mutane Suka Soma Haramar Tafiya Musamman ma Na nesa Irin Yan Uwan Dady na Garin Adamawa da kuma Na Momy Yan Kogi.
Nanne fa Mutuwar Tadawowa Su Momy Sabuwa Fil Momy dai Tashiga Kuka Wiwiwi Dole Yan Uwanta Sukayi Shawarar Mami Iyabo Ta Zauna taɗan Kwana Biyu Hakanan Ya Nuradeen Shima Yabar Matar Tasa Nan In Yaso Sai yadinga Zuwa.


Tau Zaman Nasu Anan Yayi Ma Momy Rana dan dai Sune Masu Tausarta Musamman ma Mami Iyabo.


Hakanan Dady Yaɗan Jima Kafin Yakoma Bakin Aiki Saidai Kullum Yana kan Kira Dan Ƙara Kwantarwa da Momy Hankali!


Hakanan Shima Ya Nuradeen Bai Fasa Kira ba ko yaushe! Wannan yaɗan Samarwa Momy Salama Acikin Rai Ba wai dan ta Manta da Khaleesat ɗin ba.


*********

Ta ɓangaren su Dr. Jabir Kuwa Tun Bayan Kamallah Zaman Makoki Yasoma Shirye-shiryen Tafiyar da Zaiyi, Shi Kansa Idan Kagansa Zaka Shaida Cewa Mutuwar Ta Taɓa Shi Shima Saboda Komai Yanayin sa ne Sukuku! Komai dai Na Tafiyar tasa Ya Kammallah.


Da Yammacin Yau da Yakasance Jibi Zasuyi Tafiyar, Maman Asharaf ce keta kai Kawo A cikin gidanta Inda Take Ƙokarin haɗa kan gidan Abunda Zai lalace tuni Tafitar ta kyautar ga Maigadin gidan Hakanan duk Wani Abu da zata buƙata A tafiyar tata tahaɗa Gidan ma Ta kimtsa shi Sosai.

Yanzun Girki da Zasuci takeyi Musu Tana ta kai kawo daga Kitchin ɗin zuwa Falo Asharaf kuwa Yana kan Kujera Yana ta Aikin Buga Tv game Sai Surutu Yakeyi.


Yanzun Zaman Lafiya A gidan Yadawo
dai-dai Lokacin Yayi parkinq ɗin Motarsa Yafito rike da Wasu Fayel gefe ɗaya kuma Labcaot ɗinsa Ce Fara kal! Yariƙe.

Maigadin gidan Yakira Yakwashe ledojin Suka Nufi Cikin gidan. Da da gudu Ashraf Yarumgume Baba Nasa Yana masa Oyoyo, Shikuwa yacaɓeshi Yaɗora Kan Kafaɗa Yana Tambayar sa Yau Me Momynsa Tadafa Musu ne da Yacika Gida da Kamshi Ne Haka? Maigadin kuwa na Ajiye ledojin Yajuya Yakoma Wajen Aikinsa.

Yayinda Dr Jabir yabishi da Kalmar "Sannu da Ƙokari, Inna Fito Sallar Magrib Zamuyi Magana."

Maigadin Yarusuna yana Cewa, "Tau Shikenan Allaji Afito Lafiya."

Dai-dai Lokacin ne Maman Asharaf Tafito daga Kitchin Tallabe da Faranti da tajere Manyan Kololi A sama da Jug! Wani Kallo Aka bita dashi Mai Tafiyar da Hankali Kafin Yace, "Madam Sannu da Aiki?" sai da Ta Mayar masa da Martanin Kallon Itama Kafin Tace, "Oga barka da Zuwa."


"Barka kade Madam." yafaɗa Tareda Zaman kan dogowar Kujera dake Falon Asharaf kuwa Na cakume dashi Kamar Wanda Za'a ƙwace Masa Shi. Remot Yajawo Yasoma Laluben Tashar ALJAZEERA Dae-dai Lokacin Maman Asharaf ta Tsiyayo Ruwa Farare tasa daga Cikin gorar Faro da Taɗauka daga cikin ɗan Karamin Frij ɗinda ke Girke Acikin Falon Nasu.

Karɓar Cup ɗin Yayi Yana Kaiwa Bakinsa Sai da Yashanye tas Yamiƙa mata kopin Gamida Cewa, "Alhamdullah Matar Kirki ALLAH yayi maki Albarka." Murmushi tayi tareda Cewa, "Ameen Tareda kai Mijin Kirki."


"Ga dukkan Alamu Komai Is Ready dan Falon Ma Naga Yanuna Alamar Hakan." Dr Jabir yafadi Hakan Yana mai Ƙarewa Falon Kallo da Shaƙar daddaɗan Kasmhin turaren dake tashi A kowane Saƙon Na Falon.


"Insha'allah! Gobe Sai Kitso da Lalle Munyi Waya ma da Sajida Tace Inje Goben Unguwar tasu Za'a Min Kaga Gobe Inzaka Fita Saika Ajeyimu Ko?" Maman Asharaf Tadire Maganar Tareda Kallonsa.

Lumshe Idanunsa Yayi Cikin Alamun Yar gajiya dake Tareda shi Kafin yabuɗesu Tar Akanta Sa'anan Yace, "Ba Wannan Maganar Coz Gobe Ina da Abubuwan yi da Yawa Kuma kinga Goben Kaɗai Ce Damu A Ƙasarnan, So In Zaiyu Ita Mai Lallen da Kitso Tazo Nan gida ta mike Za'a Biyata Ko Nawane."


Ta Zumburi Baki Irin Shagwabar Nan Tareda Cewa, "Kai HUBBI! Bafa Guda Bace Mai yin Kitson daban Mai Lalle daban....."

"Tau duka Biyun Suzo Kowa Yayi Aikinsa Sai Abashi Haƙƙensa." Yakatse ta da Faɗar Hakan.

A Bazata Suka ji Shima Asharaf Ya Maimaita Abinda Baban Nasa Yafaɗa.

Bashiri duk Sukayi Dariya.


Anan Zan Nisa Muje daku Chapter ta Gaba.

Tareda Alkalamin

FA'IK.
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 25 · 0% Book details