← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 34 OF 40

Chapter.....37

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem!!!


Fahimtar Hakan da Nayi Nikuma Naci Gaba da Ribatarsa da Kalamai Masu taushi Wayyanda Nake Ganin Zasu Sashi Yafahimci Halinda Nake Ciki da Kuma Halinda Zanshiga Idan Ban Samu Wannan Taimakon daga Gareshi ba Da Kuma Makoma ta Akan Auren da Su Dady Ke Shiri Yimin da Irin Mutumci da Girmama Juna dake Tsakanin mu dashi Haryasa Na Zaɓeshi Amatsayin Wanda zai Taimaka Min.

Wayyanan Lamuran Su Sukayi Tasiri Ga Sani Harya Amince Zai Min Wannan Taimakon Zai Kuma Nemi Amintattun Abokan sa dan Su Tayashi Yin Wannan Aikin. Daganan Nikuma Na bashi Sabulai da Mayukan da Naɗauko Masa Wayyanda Ko Dama Can Nasaba Yimasa Irin Wannan Kyautar.

Mukayi Sallamar Cikin Girmamawa da Mutunci Kowane mu Yanufi Inda Zashi. Yayinda Nadawo Cikin Gida Da Tunanin Yanda Al'amurrah Zasu Gudana Tareda Adu'ar ALLAH Ya Bani Nasara Su Tafi Dai-dai Yanda Nake Buƙata.

Tau Haka dai Akayi Washe Gari Sai ga Sani Yazo da Amintattun Nasa Muka Kashe Muka Binne Akan Abubuwan da Za'ayi Batareda Kowa Yasani Ba. Nakawo Kuɗɗi Masu Tsoka Na basu Kyauta Sa'annan Nadawo Gida Cikin Farinciki Cewa Aikina Zai Tafi dai-dai. Daganan Na Kira Dr Jabir A Waya Nasanar Dashi Duk Halinda Ake Ciki Ya Jinjina min Sosai Akan Irin Tawa Hazaƙar Nima.

Tau Shine Kafin Afara 'Kamu' Naje Gurin Dr Jabir Yayi min Wannan Allurar Tareda Faɗamin Sanda Zata Fara Aiki da Kuma Sanda Zata Ƙare Aiki dan Haka In Kula Sosai Fa Kar Asamu Matsala Kuma Na Jadadda wa Su Sani Karsu Yi Ƙwaurin Zuwa Su Tononi Sbda In Suka Wuce Lokacin Za'a Iya Samun Matsala. Nace, "Insha'allah. Zan Kula." Haka Nayima Sa Godiya Iya Godiya Nabaro Wurin Sa Nadawo Gida Bayan Naga Sani Naƙara Jadadda Masa Shima Yace, "Zasu Kula." Sa'annan ne fa Hankali na Ya kwanta Nadawo Cikin Jama'a Aka Shiga Harkokin Buki."


Haka Kuwa Akayi, duk Yadda Muka Tsara Abubuwan Haka Suka Kasance Har'izuwa Sanda Su Sani Suka ɗauko ni daga Maƙabarta Zuwa Gidan Dr Mai ƁOYAYYEN Suna da Kuke Ganin Mu Yanzun Atare Wanda da Taimakon Sa Komai Ke Tafiya.

Nanne Nasamu Labarin Halinda Abdul-wahab Yake Ciki Nashiga Tashin Hankali Matuƙa Tun Suna Asibiti Naso Inje, Amma Sai suka Hana ni da Cewar, 'Ba yanzu ne Yakamata In Bayyana ba Harzuwa Sanda Aka ce Ya Haukace Tuɓuran DuK Ina Samun Labari ne ta Wajen su Dr Harzuwa Sanda Aka Kaishi Asibitin Mahaukata Ta Ƙaramar Hukumar Kware.

Ranar Nayi Kuka Harna Ba Ukku Lada, Haka dai Su Dr Sukayi ta Tausa ta Da Cewar Haƙuri dai Zaniyi In Ba Haka ba Zan Iya Wargaje Mana Shiri Dahaka dai Na Haƙura Har Lokacin da Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Ya Buƙaci Inzo Yaukam Lokaci Yayi Zamuje ne Asibiti Infara Ganawa da Su Abdul-wahab Gama Yana Ganin Yanzun Jikin Nasa Yayi Sauki.


Tau Shine Fa Muka Zo Suma Kuma Innarmu Sun Shiga Kwatankwacin Irin Wannan tashin Hankalin da RUƊANI A Sanda Suka Ganni Abdul-wahab ne Kawai Bai Wani Nuna ba Wanda Ni Kaina Nayi Mamakin sa, Tau Amma Sai Nabar wa Raina Cewar Maybe Saboda Tsananin Soyayyar da Mukeyi Wa Juna ne Yasa. A gurin su Na Zauna Har'izuwa Sanda Yauɗin Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Yaje Shida Baba Tanimu Mukazo Nan Gurin ku. yayinda Na Kawo Nan A Jawabina Sai Muryata Ta Soma Rawa Nacigaba da Cewa, "Tabbas Na Aikata Babban Kuskure Wanda In Baku Ya...." Baba Tanimu Yakatse ni Ta hanyar Cewa, "Ya'isa Haka Khaleesat Zamu Zo Wannan Gurin." Yajuya Gurin Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Yace, "Munji daga Khaleesat Yanzun Kaine Muke Buƙatar Ji Daga Gareka Kamar Yadda Ka Buƙaci Mu Taro Anan ɗin dan Kayi Mana Bayani." Gabaki ɗaya Falon Yayi Tsit! Kowanen mu da Irin Al'amurrah da Ke Kai Komo Acikin Zuciyarsa.


Wasu Kuwa Hawaye ne Shaɓe-Shaɓe (Irin su Momy Kenan da Ya Nuradeen) Yayinda Tsantsar Mamakin Ɗan Yau da Tarin NADAMA Suke Shinfiɗe A Fuskar Dattijan Gurin (Musamman Dady) Duk Mun San Wannan BayanineTa Hanyar Dr Mai ƁOYAYYEN Suna dake Bin Kowanen su da Ido Yana Kuma Karantar Yanayin da Suke Ciki. Daganan dai Yayi gyaran Murya Kafin Yasoma Cewa, "Da Fari dai Sunana Dr Faisal Kuma Ni Abokine na Ƙut-Ƙut ga Dr Jabir. Baya Ɓoyemin Komai Nasa Kamar Yadda Nima Bana Ɓoye Masa Maganar Gaskiya Akwai Fahimtar Juna Sosai Tsakaninmu. "

Yaɗan Nisa Acikin Zancen Nasa Yayinda Kowa Na Falon Ke Binsa da Kallo Lura Da Hakan da Dr Faisal Yayi Yasa Yaɗan yi Murmushi Sa'annan Yaci Gaba da Cewa, "Tau Kamar dai Yadda Khaleesat tafaɗa Maku Haka Abin Yake Kuma Abokina Watau Dr Jabir Yana Tsaka da Aikin Nanne Kuma Saiga Sunan sa Yafito daga Jerin Sunayen da Gwammanti Zata Tura Ƙsar Waje domin Ƙaro Ilimi Akan Abinda Yadangaci Wata Sabuwar Cuta da Ta Ɓulla. Dan Haka A Wani Dare Bayan Nadawo daga Aikina Inagida Tareda Iyalina Yaziryaceni Bayan Sungaisa da Matata Takuma Gabatar Mana da Abin Motsa Baki Sai Tabamu Waje. Domin dai Su Matan Namu Sun san Mafi Yawa Indai Muka Ziyarci Juna A Irin Wannan Lokacin, Tau da Kwai Magana Mai Muhimmaci da Zamuyi.

Dan Haka Bayan Mun Keɓe Dai Dr Jabir Yake Sanar dani Wannan Maganar da Kuma Buƙatar da Yake da Ita Na Barin Lamarin A Hannuna Dan In Kammallah Abinda Yafara. Da Fari Na Nuna Masa Rashin Amincewa ta Saboda Ina Ganin Rashin Dacewar Abin Domin Ai Baidace Ayiwa Iyayenta Irin Wannan Yawo da Hankali ba.

Tau Amma da Yamatsa min da Bayani da Kuma Nusar Dani Ire-iren Abubuwan da ke Nan Ya Ƙara Gayamin Shirin Na Yarin Na Guduwa Zuwa Wata Duniyar Da Rashin Sani Abinda Illar Hakan Zai Haifar Ga Iyayen da Ita Kanta Yarinyar da Sauran Matsaloli Ma Banbanta da Ya Lissafa Min A Wancan Ranar Kawai Sai Na'amince.

Muke Gudanar da Aikin Tare Harzuwa Sanda Lokacin Tafiyarsa Tayi Yabar Komai A Hannuna Nake Ci Gaba da Aiwatar Dashi Ko A Wancan Ranar da Kuka Kawo Khaleesat ɗin Asibiti Ina Cikin Jerin Likitocin da Sukai ta Kai-kawo Akan Halinda Tashiga Saidai Yana yin da Kuke Ciki Bazai Bari Ku Lura Ba. Haka Abubuwan Suka Ci Gaba da Tafiya Kamar Yadda Muka Tsara Harzuwa Sanda Muka ga Yakamata Khaleesat ta Bayyana dan Haka Naɗauke ta da Mota Zuwa Asibitin da Dama Can Nake Aiki Kuma Nike Lura da Abdul-wahab Bawai dan Wasun Basa Lura dashi Ba Saidon Ni Dai Nashiga Lamarin Sosai da Nunawa Yan Uwana Likitocin Cewa Ai Family nane Su. Bayan Nakai Khaleesat ɗin Su Innarmu Sun Shiga RUƊANI Irin Wanda Bazai Misaltu ba Sai Wanda Yagani Kawai. Dan Ita Yayar Tasu Sai da Ta Kwanta Gado Saboda Tsabar Rikicewa da RUƊANIN da Tashiga.


Zan dakata Anan Kuma Ina Fatar Muje daku A Chapter Na Gaba
Tareda Alkalamin

FA'IK. ✍🏼
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 34 · 0% Book details