Chapter.....25
So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Mallakar 👇
Fa'IK ✍
GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.
FADAKARWA.
Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.
Bissmillahi Rahmanin Raheem
Hakanne yazaburar da Mami Iyabo Itama Takama Kalmar tariƙe Daganan ta Nufi Yar uwarta (Momy) Takamo ta tana mai Lallashinta Tariƙe ta tamau Adai-dai Lokacin Dr. Jabir Yasake Shigowa ɗakin Idanunsa Jaziri Kamar gauta Kai da ganin Kasan Garama Yasamu Yayi Kuka Bisaga Wannan Kunar Zuci da Yake Tareda Ita!
Kai tsaye Ya Nuradeen Yajawo A Jikinsa yana Bashi Baki Tareda Nuna Masa Muhimmacin Tawakkali gamida Cemasa Idan Harshi Yayi Haka Waye Kuma zai Tsaya Ya Lallashi Wayyanan Tsoffin wayyanda Ruhi da gangar Jikinsu ke Cike da Rauni! "Khaleesat dai tarigamu gidan Gaskiya Babu Wani Gata da Zamuyi mata da Yawuce Mu Kama GAWAR ta mu Suturta ta mu Sada ta da Makwancinta Mu Bita da Adu'ar ALLAH Yayi Mata RAHMA!"
Wayyanan Kalaman Kalilanne Amma Abinda Suka haddasa Acikin Zuciyoyin Mutanen Nan Yafi A Ƙirga Hakanan kuma baya da ma Adadi dan dai Kawai Sunyi Ƙarfin Haline Kila da Sai sun zagi Dr. Jabir ɗin dake gaya musu Wannan Baƙar Maganar mai Ƙokarin Raba su da jinsu.
Tau Amma yazasuyi? Tunda Gaskiya ce Yake gayamusu dama dai Ita gaskiyar ɗaci ne da ita Kamar yadda masu iya Magana Kance.
Dole dai Abinda Nan da Yace Shine Akayi. Motar Ambulance Aka Kawo dan dai Dama shi Makwabcinsu da dady yanemo Yana kawo su Yakoma. Suna gani Aka Turo Gawar Kan gado Zuwa Cikin Motar Lamarin da Yaƙara Tunzura Zukatansu Kenan.
Wanda Yasa Momy tasake Ɓarkewa da Wani Irin Kuka da duk Wani Mahaluƙi dake Cikin Asibitin Saida Yaji! Kasancewar daman Asibitin Bawani Girma ne dashi Ba Falo ɗayane Mai ɗauke ɗakukka daban-daban. Hakanan Gashi tsakar Darene Daman Komai Yayi tsif! Ko ƙaramin Motsi Akayi Zakaji.
Haka Suka Shigo Motar zuwa Gida Cikin Wani Irin Tashin Hankali Marar Misaltuwa.
Nanne ma Dady Yasamu yaɗan dawo Hayyacinsa Yasoma Buge-Bugen Waya Yana Sanarda Yan Uwa da Abokan Arziki Rasuwar Khaleesat ɗin.
Dawowar Su Gidane Kuma Fa Komai Yaƙara Kacamewa Harda Masu Some-Some Ciki Kuwa harda Matar Yaya Nuradeen dan Itama Khaleesat Mutumniyar ta ce Suna ɗasawa Sosai. Bata tuna wani Abu da Khaleesat tayi mata tun Sanda ALLAH yasa ta Auri Yayan Khaleesat ɗin, Saima Girmamata da Kuma Son ɗansu da Takeyi take kuma Bashi Kulawa kamar itace ta tsugguna tahaifeshi.
Kafin Kace Kwabo Mutuwar Amarya Khaleesat Yayi Tambari Acikin Lungu da Saƙo Na Ilahirin Masu ALAƘA da Ita. dama dai Ance Inkaji Shiru Tau LAFIYA Ne.
Da Safe Kowa yazo Ɗaurin Aure Sai Ya turje Jin Cewa Abu Yakoma Jana'iza.
Kai dole Ka Tausaya Wannan Lamarin Mai Imani ma Sai Yazubar da Hawaye Saboda Tsabar Tausayin Al'amarin Dady da Ya Nuradeen Duk Sunyi Firgai-Firgai Daga Jiya Zuwa Yau da Safe Kamar Wayyanda Suka Shekara Acikin Jinya babu ci Babu Sha! Itakam Momy ma Ba'a Maganar ta! Dan Yan Uwanta Ne Taushe da Ita Ruwa ma Sai Sun ɗura Mata.
Shikuwa Abdul-wahab Ana gama ɗaurin Auren Amininsa Yusuf, Yasulale yanufo nan Gidan su Khaleesat ɗin domin Halartar Ɗaurin Auren ta duk kuwa da Irin Tullin Aikin dake gabansa Amatsayin sa Na Babban Aboki Ga Angon Amma Haka ya Watsar! Wayarsa ma dan Karsu Isheshi da Kira Sai Yasa ta A Flightmode(Jirgi) Daga Sanda ya doso Gurin Yakejinsa A Wani Iri.
Bugun Zuciyarsa Na Ƙara Tsanan ta Saidai Yana dangan ta Hakan da Cewa Kawai Bai Wuce Damuwar da Yake Ciki na Gimbiyarsa Kuma Masoyiyar sa Khaleesat Zata Auri Wani A Yau Wanda Ba shi ba.
Wanda hakan Na Nufin Yarabu da Ita Rabuwa ta Har'abada wanda Hakan Yasa Yakeji Shida Aure Kuwa koda Ba Har'abada tau Ba Yanzun ba. dan Baiga Wacce Zai so Makamancin Son da Zaiyiwa Khaleesat ba.
Haɗa Idanu Sukayi da Ya Nuradeen Ganin sa Yasa Ya Nuradeen ɗin Nufosa Cikin Hanzari Yana Mai Ƙokarin danne Kukan da ke Neman kufce Masa Sai Shima Abdul-wahab Yaji Jikinsa Yaɗauki Makarkata Yana Neman Faɗowa Ƙasa, Amma Sai Yayi Hanzari Yadafa Bangon dake kusa dashi Yana Mai Kiran Sunan ALLAH. dai-dai lokacin ne Kuma Ya Nuradeen ya iso Garesa Yana gayamasa Maganar da Yakejin tunda Innarmu Tahaifoshi Duniya baitaɓa Jin Magana Mafi ɗacin ɗanɗano Irin ta ba! Maganar da Yakejin ko A MUGUN MAFARKI Bai Kamata yaji Irinta ba dan Haka Sai Yabar Abun Akan Baiji Abinda Ya Nuradeen ke Sanarda shi Bane dan Haka Cikin Ruɗani Yake Tambayar Ya Nuradeen Cewa, "Nakasa Gane Mekake Nufi Ya Nuradeen Shin Abinda Naji kana Faɗa dai-dai ne Kodai Nine ke Neman Haukace wa?"
Ya Nuradeen Yace, "Abinda Kajin dai Shine dai-dai Abdull Khaleesat ta tafi tabarmu Har'abada Muda Ganin ta Sai A Hoto Dan ALLAH Kayafemata duk Abinda Tayi Maka." yaƙarashe Maganar yana mai haɗe Hannayen sa guri Biyu Alamun Neman Afuwa! Kafin Yaɗora da Cewa, "Auren ku da Baiyu ba kuwa, Kada ka zargeta ba Laifinta Bane Ni Na shaida Khaleesat tasoka da Zuciya ɗaya Kawai Laifin Su Dady ne da Suka ƙi Fahimtar ta, Gashinan yanzun Sunsa Zuciyarta ta Buga Tabarsu Musu duniyar gabaɗai yanzun kuma Sai Su nemi Wacce zasu Yiwa Auren dole...."
Shi kam Abdul-wahab Ganin Kawai Yakeyi Bakin Ya Nuradeen Na Motsawa Amma Bayajin Komeye Yake Cewa Illai Bayanin sa kawai Nafarko da yaji Cewa "Khaleesat TA RASU!" Bayan Shi babu Abinda Yasake ji.
Mezai Gani? GAWAR ce Kuwa Aka Fito da ita Mutane Na Ƙokarin gyara sahun su dan yin SALLAH Gareta Can Kuma Gungun Mutane ne ke ta Fahma da Momy dake ta Kururuwar Ba Inda Za'a kai Mata ɗiya Wallahi bata Mutu ba "WALLAHI BATA MUTU BA!" Kalamin da Momy keta nanatawa kenan Wanda Kai da Ganin Momy Kasan Ba Hayyacinta take ba!
Wata irin Kururuwar Abdul-wahab Yayi Yanufi Makarar Da Iya gudunsa Wanda Yasanya Fullar dake kansa tafaɗi tanemi Gurinta Yarike Makarar Yana Wani Irin Gunjin Kuka da Surutai
"Khaleesat Bamuyi Haka dake ba! Munyi Alkawalin Zamuyi Hakuri Mu Rumguni Ƙaddarar mu da Hannu Biyu Mu Yarda Cewa ALLAH Bai Nufa Zamu Auri Juna Ba Amma Bakice min Zaki Mutu ba.
Dan Girman ALLAH Khaleesat Kitashi Ni Ko Baki Aure ni Ba BURINA naji Ance Kawai Kina raye A ɗakin Mijinki Kinyi Ma Su Dady Biyayya Hakanan Kiyiwa Mijin ki Biyayya Wannan Shine Alkawalin da kikayimin Meyasa Zaki Karya? Meyasa Baki Gayamin Zaki MUTU ba! Nima inzo Mu Mutu Tare Mezanyi A duniyar da Babu ke? Khaleesat!!!" Yafaɗi Hakan da Wani Irin Sauti Mai Ratsa dukkan Wani Bil'adama dake Gurin Harcikin tsoka da ƙashi Balle Kuma ZUCIYA.
Duk Juriyar Dady Saida Yafashe da Kuka Wiwiwi Shikam Ya Nuradeen Nan Take A Gurin Ya Faɗi Some Abinda Yaƙara Karya Zuciyar Jama'ar dake Wajen Kenan.
Masu Raunin Zuciya Suka Shiga Tayasu Kuka Masu Karfin Kuwa Suka Soma Sharar Ƙwalla!
Tashin Hankali Wanda Ba'a Samaka Rana!!! Dole Wasu Suka Tallafi Ya Nuradeen Akayi Dashi Cikin Gida Ana Ƙokarin Yayyafa Masa Ruwa Shima dai Nan Abdul-wahab dakyar Aka ɓanɓare sa Daga GAWAR Mutane Suka Rufu Akanshi Ana ta Bashi Baki.
A haka dai Suka Samu Suka Taushe Shi Suka Sakashi A tsakiyar su Yashiga Sahun Sallah Bawai dan Yana da Nutsuwar Yinta ba.
Liman Na Sallame wa. Wasu daga Cikin Yan Uwa Aka ɗaga Makarar Gawar Zuwa Motar da Za'a Tafi Maƙabarta da Ita. A wannan Lokacin ne Wani irin duhu Ya Mamaye Ganin Abdul-wahab Daganan Kuma Bai Koma Sanin Meke Faruwa dashi Ba.
Kai Jama'a Sunga MUTUWAR da Suka daɗe Basuga Mai Alhinin Irinta ba. Haka aka Kai Amarya Khaleesat Maƙabarta Aka Yi Abinda Akanyiwa Kowane Mamaci Kafin Suka Juyo Cike da Kewa da Tarin Tausayi.
Aka Dawo Aka Shiga Zaman Makoki NADAMA Mai Suna Nadama dai Tashiga Dady Yayi Dana Sani Babu Adadi Tabbas da Yasani da Yadubi GIRMAN SO da Ke Tsakanin Wayyanan Yaran Yabarsu Sun Auri Juna Gashi Akan ɗan Karamin Dalilin su Shida Momy ya salwantar da Ran Ƴarsu Shima dai Abdul-wahab Tunda Su Yusuf Sukayi Ta Neman sa Basu Ganshi Ba Yusuf Ya Ayyana A ransa Cewa Tabbas yana nan Gurin da Ake ɗaurin Auren dan dama Yace Masa Shifa Sai Yazo! harya Zolaye sa da Cewa Baya Kishi Ne? Dan Haka dai da Suka Lalube sa basu Ganshi Ba sai Suka biyo Sahunsa Shine Fa Suma Suka Ci Karo Da Abinda Ke Faruwa Suka tattaleshi Rai kwakwai Mutu kwakwai!
Lamarin Uwargidan Dr Jabir Fa?
(Maman Asharaf)
Tunda Dr Jabir Yadawo Musu da Labarin Mutuwar Amarya Khaleesat Jikin su Yayi Sanyi Ƙalau!
Duk Wani Toye-toyen da Girke-girke da Sukeyi Aka Ajiye. Aka Shiga Zullumin Wannan Lamarin. Tsakani da ALLAH Maman Asharaf Har Ranta Taji Wannan Mutuwar Takuma Shiga Alhinin Abun.
Ga Mamakinta Sai gata tana Hawaye Shaɓe-Shaɓe A Fuskarta tana mai Nadamar Ayyukan Da Ta Aikata Ashe Ita Amaryar ma Ba mai Tsawon Rai Bace.
Yanzun kam Ba Ma Dr Jabir Ba Duniyar ma Gaba ɗai Tabarma ta Ta tsinci duk Abinda Zata tsinta Acikinta! Yanzun Inda Bata Samu Iyaye tsayayyu ba Tana Gida Tana Yaji Ita A dole Wacce Za'a Yiwa KISHIYA Lalle tasani da Kunyar da Zataji Sai ta Fi Wannan ma Kenan.
Kamar Yadda Dr Jabir Yayi ta Juyi Akan Gadon Haka itama tai ta Juyi Cikinsu Aka Rasa mai Baiwa ɗan Uwan Sa Magana. Dole Shi Yamiƙe Yasanyo Arwallah Yashiga Doka Nafil-fili Yana mai Nemawa Khaleesat Gafara Da Rahmar ALLAH Wanda A gurin Adu'ar duk Juriyar sa Saida Yafashe da Kuka! Kuka dai Wanda Ake Cema Kuka.
Da Hanzarin Maman Asharaf ta Runtomo daga kan gadon Tazo Ta Rumgume Shi Itama Tashiga Yin Kukan Dama ita ma A wuya Take.
Mai Neman Kuka ne Aka jefeshi da Kashin Awaki. Sai Nanatawa Takeyi, "Naji KUNYA Baban Asharaf Kayafemin Kai Mani gafara! ALLAH YAJIKAN KHALEESAT!!!!"
Abun Tausayi Abun Alhini ga Zuciyar Mai Imani. Sun ɗau Dogon Lokaci Acikin Wannan Halin Kafin Dr. Jabir Ya Umurci Maman Asharaf Cewa taje tayo Arwallah Tazo Suyi Sallar Zai Fiye Masu Fa'ida. Bata Musa ba tayi Yanda Yace Suka Shiga doka Nafilfili Har Kiran Assallatu Yariske su A Haka.
Raka'atanul Fajri Yayi Kafin Yamiƙe Yanufi Massallaci dake Jikin gidan Makwabcinsu! Ko A Massallaci Yajima Yana Nemawa Khaleesat gafara Kafin Yanufo Gida Lokacin Karfe 6 Nasafe Yatarar Maman Asharaf Tana Shirya Asharaf ɗin Tayo Masa Wanka Mai Take Shafa Mashi.
Bayan Sungaisa Yakarɓi Asharaf ɗin Yace Kawo Naƙarasa Shiryashi Je ki haɗa Masa Lonchbox ɗinsa. Hakan kuwa Akayi.
Yashirya Asharaf ɗin tsaf Acikin uniform ɗinsa Na Isilamiyyah Sai Surutu Yakeyi Ma Baban Nasa (Yaro Kenan Shikam baisan Halin da Ake Ciki ba)Lokacinne Maman Asharaf ɗin Tashigo Ta'ajiye Abincin Nasa na Zuwa Skull ɗin da tashirya masa Kafin Ta nufi Juyawa.
Cikin Sanyin Murya Dr Jabir Yakira ta Tajuyo Yace, "Kizo Kishirya da Wuri Mu'aje Shi Skull Ina so Mutafi Gidan su ..... Sai Yayi Shiru Yana Tunanin tau Mezai ce Ma Khaleesat ko Marigayiya?"
Masu Karatu Zan ɗan Nisa Anan......
Muje A Shafi Na Gaba
Tareda Alkalamin
FA'IK.
[9/5, 9:15 PM] FA'IK: Typing....... 💻
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
💪🏻J.A.W 💪🏻
❤❤SONEEE ....💕💕
(Silar Komai.)